Showing 36001 words to 39000 words out of 103469 words
Kuma kinsani,to mezesa muyi kokarin yaudarar kanmu?nina ma hakura dashi don ina rokon Allah yaciremin son shi,duk idan nayi sallah sai nayi addu'ah zabin mafi alkhairi.
"Ke dalla tafi can kibani waje,wallahi bakinki yasari danyan Kashi Rammat,kinsan Allah kifita idona na rufe,meye Akeelan zata nuna miki?alhalin kinfita komai,yarinyar da ba abinda tasani sai gantali daga bin maza sai madigo,a haka kuma kikeso nabari suyi nasara? inason kudi Rammat!inason su,kina kallo 'yar uwanki duk a gidan mijinta ne baikai sauran karfi ba amma duk watan duniya shike ciyar damu cima mai kyau,shine kike kokarin yimin asaran samun mai kaini hajji da umara duk shekara?hajiya Biba takarisa maganar tana zaro ma Rammat idanuwa.
"No hajiya ba haka nake nufi ba idan munada rabo ai ba lalai sai shiba kawai kimin zabin nagari.
Tana kare fadan haka ta mike tare da wucewa kitchen.
Da harara hajiya Biba tabita"ku kujimin 'ya 'yar bakin ciki,to baki Isa ba wallahi.
XAHRATTY CE🥰
Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️
[5/9, 19:38] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽🦳
Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*
Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now
*_GALADIMA FAMILY_*
Page:- 35/36
_Bismillahir-rahmanir-raheem._
*THIS PAGE IS DEDICATED TO MY SWEET SISTER BILKISOU M BELLO,SHEKARU BIYU CIKIN NA UKU KENAN DA RASUWAR KI,ALLAH YAKAI RAHAMAR SA MAKWANCIN KI🤲🏽NAYI RASHIN AMINIYA,ABOKIYAR SHAWARA,WANDA SAMUN KAMARTA ZAIYI WUYA ALWAYS I MISS YOU AUNTY BILLY🥹*
_____Guggo Laure ne zaune a daya daga cikin kujerun farlon Galadima,tsaban yanda masifa ke cinta idanuwan nan an kankance su,sauraran bayanan Galadima takeyi har yakai aya sannan tadora.
"Yaya muhammadu nifa ba haka nake nufi ba,sam abinda Sauban yakeyi baya kyautawa,kamar yama mance da ranar auren shi da Akeela a kansa?tunda akasanya rana banaji yaron nan yataba nemanta a waya koda sau daya ne,sai kace wanda za'a aura masa makiyiyar sa?takarisa maganar tana sake tsuke fuska.
Shidai Daddy shiru yayi gabadaya yana mamaki tare da shocked din halin guggon nasa wanda kullum babu alheri sai tashin hankali,gyaran murya Baba Hashim yayi yace"yanzu Guggo ita yarinyar ce duk ke fada miki haka?
"Ai Hashimu koda Akeela bata fadamin ba abune da yake a bayyane domin kuwa ina gani da idanuwa na,ga damuwa karara tattare da ita,nasan baya sonta amma hakanan zai aureta kodan karfafa zumuncin mu,shi nakeso ta aura, Kuma ko baya sonta dole ya zauna da ita wallahi"takai aya tana zazzare idanuwa.
"To yanzu menene abinda kikeso ayi Laure?
"Tambayar da tuntuni ya kamata ace kamin kenan Yaya,sonake asashi yakira ta a waya kuma ko babu komai yadinga kulata ko yaya ne,amma yarinya tana neman ramewa da karewa a banza a wofi?
"Shikenan Allah yashige mana gaba,insha Allah za'a kirashi amasa magana,amma maganar gaskiya Laure niban fiye son yawan korafe-korafe ba,haka za'ayi auren ana korafi dakawo kara?alhalin irin auren nan babu inda baya zuwa?gaskiya banso yakamata kizaunar da ita kikara fahimtar da ita menene aure?don shirmenta yayi yawa"Galadima yayi maganar yana bayyana bacin ransa karara.
"Kayahakuri Yaya muhammadu za'a kiyaye.
"Aini ba wani abu nace ba kuskuren da ake tatkawa nake kokarin gyarawa don bazamu zuba idanuwa muna gani ayita kawo korafe-korafen matsaloli ba,don Allah kinatsar da ita.
Sosai jikin Guggo Laure yayi sanyi,gudun kada yayan nata ya botsare yasa tamike tare da yimusu sallama tafita,jingina Galadima yayi da jkin hadadden kujeran nasa yana me lumshe idanuwa,muryan Baba Hashim ya tsinkayo"ni wallahi lamarin auren Sauban da yarinyar nan fa yafara fitamin a rai,ace tun yanzu korafe-korafe sunfara shigowa ciki to inaga ma anyi?ita Guggo ko la'akari batayi da yaron nan fa auren dole za'a masa,auren biyayya zaiyi,yafada shi baya son yarinyar nd baya son abinda zai bata zumunci,to gaskiya za'a wa tufkar hanci tun wuri.
Ajiyan zuciya Daddy ya sauke tare da cewa Allah ya kyauta nan suka cigaba da tattaunawan su akan tsaida ranar bikin tunda iyayen ma'aruf mijin da zai aure muneefa suka basu dama.
Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya har takama yau saura wata guda biki,akuma ranar ne Ammi da Ummie suka shirya sai kasar Dubai don siyoma yara kayan kitchen don ko Mom bata sani ba,a gefen ta itama sai shiri takeyi batare da tasaka kowa a cikinsu ba don tayi alkawarin sai ta shayar da kowa mamaki da kayan kitchen din muneefa hakan ce yasa takira kawarta daga Lagos kan a turo mata da kayan kitchen na million 1.
Bangaren su Ummie kuwa kwanansu biyu suka gama shirye-shiryen su don juyowa saboda kayansu tun a ranar suka isa Lagos daganan aka wutu dasu kaduna JABI ROAD wajen mommy,don agidan abokin Abbie suka sauka wani balarabe me suna Omerr Aslam,sun kuma samu tarba me kyau inda suka masu Ummie alkawarin zuwa biki insha Allah shida babban dansa,da zasu tafi suka musu kyautan sha tara na arziki don mahaukatan yadika da shaddo di yayi akwati guda yace na Taufeeq da Sauban,ko wanne 10 10 yrd kusan set biyar² zasu tashi dashi,sosai su Ummie sukayi godiya matan shi kuma hajiya Amna ta hadama amare akwati guda na dogayen riguna, zuhra ma ta mata akwati guda haka su Ummie suka bari Dubai cike dajin dadi,kwanan Ummie da Ammi biyu a kaduna suka wuceZaria kai tsaye dukkan su anguwan su Ammi suka nufa saboda ita iyayenta sun rasu sai 'yan uwa don haka zata ta kwana daya gobe da safe tazo gidan su Ummie don zasubi jirgin 4:30 ne sai su wuce gida.
Sosai ko wacce 'yan uwa sunyi murna da ganinta, washegari kuwa suka nufi gida.
**********
"Aminiyata nifa a tsorace nake haryanzu ba'a kirani ance gashi wani abu yasameta ba,ke in takaice miki ma har Zaria sunje itada matan Alhaji Taleeb sun kwana"Adda Zainab ne ke maganar nan.
"Hmmm nifa lamarin matan nan hajiya Zainab yafara bani tsoro,kinsan Kuma aikin nan yanda aka umurce mu haka muka gudanar,to amma bari nakira boka hatsabibi"hajiya Aliya ta ida fada tana dauko wayarta dake aje kan center table,nan tashiga laluben number boka amma abin mamaki babu ita babu alamanta,sake dai bincika wa tayi amma still bata gani number,nandanan tamike tsaye cikin tashin hankali tare da dafe kirji tace"Nashiga uku ni Aliya,taya lefin wani zai shafe wani?da sauri Adda Zainab tamike tana dubanta.
"Lafiya aminiya meke faruwa ne?naga hankalinki atashe kuma ga abinda kikace?duban hajiya Zainab hajiya Aliya tayi tace.
"Narasa number boka hatsabibi kuma wallahi ko kaffara bazanyi ba munyi masa gagarumin aiki mun lalata masa aiki,nidai da nasan haka ne wallahi da nabarki ke kadai kinyi aikin ki da bansa hannu ba,nashiga uku gashi iya duba na naduba banga number ba,aikin banza kema ba number ne gareki ba.
"Munshiga uku yanzu Yaya zamuyi.
Yaya zamuyi kuwa tafiya ce ta ganmu don kuwa tunda kikaga babu number turo aljanu yayi suka goge don yasan dole mu nemesa kinsan abinda yace fa tun farko.
"Nasani sai dai gaskiya nikam wannan karan da wuya nakoma don gudun zargi banso a zarge ni.Wani banzan kallo hajiya Aliya ta aikama Adda Zainab"mekike nufi kenan hajiya Zainab?kina nufin nikadai zanje?cabdijam!wallahi baki isa ba aikin kifa akeyi.
Kasa da murya Adda Zainab tayi tare da marairaice fuska tace"A'ah ko daya ba haka nake nufi ba,banason abinda zaisa idon mutane sufara sauka kan mu kingane?ke widowed ce nikuma kinga matan aure CE so sai afi samin Ido ba'a samiki ba,sannan kinsan halin Alhaji na ciki da bai kinsan halinshi sarai,don Allah kiyahakuri kije mana duk abinda ke akwai inkin dawo sai muji kokuwa?
Dan sakin fuska hajiya Aliya tayi tace"Ahto 😏 kada a maidani wata bican fa, saboda ni for sale CE.
Dariya Adda Zainab tayi"A'ah ko daya wallahi matsayin ki ya wuce haka a wajena kedin ta daban ce so kisha kurumin ki nidake we're together"takarisa zancen suna tafawa da juna tare da kyalkyalewa da dariya.
"Nima idan naje akwai aikin da nakeso yamin don inaso nayi wufff da wani Alhaji dana gani lokaci daya yashiga zuciya ta yayi kane-kane.
"Au dagaske?Kai amma matan nan ke shedaniya ce shine bani da labari ko a sanarmin,?to a'ina aka samosa?
"Hmmmm kedai bari nifa hajiya Zainab da kafar dama nashiga GALADIMA house don anan naga MIJIN Aure.
😳Diddilo idanuwa hajiya Zainab tayi gabanta na masifan faduwa cikin mamaki tace"kekuwa wanene wannan?
Wani dariyan hajiya Aliya ta kyalkyale dashi tare da cewa kedai bari ayi sha'ani kawai,tana sake kyalkyala dariya.
Itakuwa Adda Zainab gabanta ne yashiga dakan lugude a zuciyar ta tace _Da yarda bi'izinillah babu ke babu shiga gidan GALADIMA hajiya Aliya,shedaniya kawai niban shiga gidan bane kece zaki shiga?_ a fili kuwa tasaki dariya tare da cewa"Ayyoririrrriiiiii amarya amarya amarya a gidan GALADIMA house,pls kifadamun wa idonki ya kyallo ne?
Fari hajiya Aliya tashiga yi da idanuwa kamar wata budurwa.
*GALADIMA FAMILY*
Kafin kace me sha'anin biki yagama kankama yinshi kawai akeyi babu kama hannun yaro, Rammat tayi kuka sosai saboda tasan cewa bazata taba samun Sauban ba sosai tamika lamuran ta ga Allah ta fawwala masa komai,inda hajiya Biba ko takasa natsuwa shige shigen malamai ko takasa sai canye mata kudade sukeyi ko wanne da karyan dayake lafta mata,hakan ba karamin sosa zuciyar Rammatc set yakeyi ba
A lokacin da biki yarage saura sati uku da kafini daya dangin ma'aruf gobe zasu kawo lefe,kafin kace me anfara tarbansu tun daren ranar,duk wani kalolin girki Ummie da Ammi ne sukayi tare da Mashahuda da zuhra harda ma muneefan.
Washegari kuwa takama asabar su Mashahuda,muneefa,duk basunan sunje gidan da ake musu gyaran jiki su kuma su zuhra,Laila da nihal suna gida.
Wajen karfe daya mommy da Abba suka diro mota biyu sukayo don babu wanda yasan da zuwan su,sai karar Horn dana motoci akafara ji,ko kafin kace me ma'aikatan gidan sun bude dayar motar Sharon sunfara fiddo da akwatuna suna nufar sashen Galadima,a lokacin mutanen gidan suka firfito ko wanne baki bude cike da mamaki akwatuna sha shidda cif.
Ummie tadubi mommy tace"Kai mommyn yara wannan wane irin zuwa ne haka?nuna Abba tayi tace"surprise ne daga Abba babu ruwana, dai-dai nan Zuhra tazo da gudu ta cafeta tsananin murna,Suma su nihal karisowa sukayi suna ihun murna,kafin kace me gida yafara hautsinewa da hayaniya don maimoon da Ateek ganin Zuhra suma yasasu murna nan su Ummie suka koma ciki don shiryawa su kuma suka mika apartment din Galadima don mika gaisuwa, da sallama suka shiga sashen inda suka cidda Bodejo rike da haba tana karewa lefen kallo.
"Hauwa wannan lefen na waye haka kuka taho dashi?ni fatsuma.
"Ai dai kyabari su sasara ko?daga shigowa ko hutawa ba'a yiba bare maganar gaisawa sai ki fara da lefe?
Murmushi Abba da mommy sukayi,nan suka fara gaggaisawa da juna, sun gaisa sosai sannan mommy tamike tace bari taje tayi sallah.
Anan Abba ke sanar dashi kayan lefen Taufeeq ne daya hado masa shine nasa gudummawar don har ya sanar dashi yace kada yahada,dama shida Sauban yaso hada musu amma sai yace shi tuntun-tuni ya gama hada lefen shi idan zaidawo zai taho dasu,naso duk da haka na masa amma sai yanuna min kada ayi almubazzaranci.
Galadima yace"gaskiya ne kaga da da hankali ko, shikenan Allah ya musu albarka yanzu yaushe yace ma zeshigo?gaskiya bamuyi maganar ba amma ai dole next week yashigo Galadima.
"Masha Allah Haroun Allah ya muku albarka ubangiji ya kara hada mun kawunan ku.
Ameen suka amsa shida Bodejo.
Nan yasake gyaran murya sai Kuma su matan na biya musu kujeran umra,shima Sauban da wannan nake tunanin na biyama yarinyar da zai auran.
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Allah ya maka albarka harouna ka kyauta kaima Allah ya saka da alkhairi.
Da ameen still ya amsa nan suka dasa hira Bodejo da Galadima zuciyoyin su wasai da jin dadi.
Xahratty CE🥰
Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️
10/3/23.
[5/24, 17:48] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽🦳
Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*
Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now
*_GALADIMA FAMILY_*
Page:- 37/38
_Bismillahir-rahmanir-raheem._
______Da la'asar family din ma'aruf suka iso,sosai suka samu tarba me girma da karamci a farlon Galadima don maza ne suka kawo lefen,su kansu sai da suka tabbatar da ba auren kwadayi dansu yayi ba tabbas ya aure 'yar gidan tarbiyya da mutumci saboda yanda Daddy, Abba Baba Hasheem suka tarbesu cike da mutumtawa,gefe daya ga tsoho me ran karfe yasha wata mahaukaciyar danyar shadda fara tasss sai maiko takeyi,shikanshi ya burgesu yanda sukaji Yana magana cike da dattaku da ilimin addini.
An gabatar musu da abinci,namomi,lemukan gora, fruits kaloli inda suka so kin ci amma Galadima ya nuna musu ba ahaka dole kowa yaci abincin Yana santi don dama gaskiya surikan Galadima gwanaye ne wajen girki musamman Ammi, Ummie kuwa ta kware wajen iya na kasashen waje saboda rayuwar da sukafi yinta acan,mommy da Mom ma ba baya don idan Ammi da Ummie basu waje to sudinfa on top ne.
Sai wajen karfe shida suka fita tare da tsaraban kalolin snaks sunfa kala biyar anyi raping nasu a kwalaye sai katan-katan lemuka da ruwa ammafa babu tukwici don anyi ba'ayi bane,wannan ma don gidan masu kudi ne shiyasa,sosai sukaji dadi su shidda ne haka suka tafi suna yabon wadannan ahalin.
BAYAN magrib su Daddy sukasa ma'aikatan gidan maida akwatunan babban farlon Bodejo, nanfa mommy dasu nihal suka takarkare suka dinga sakin guda,don kaya kuwa Masha Allah komai washabban washabban don akwatuna goma sha hudu ne gasunan aka kawo,nanfa aka shisshigo dana Mashahuda akwatuna sha shida,gida fa ya kacame don sai da Galadima yayi musu gyaran murya don duk Wanda kaga fuskanshi kasan yana cikin farin ciki.
Mom ma tayi murna don bata taba arzikin su ma'aruf dinma har takai haka ba,nanfa ta sulale tafara kiran 'yan uwanta da abokan arziki tana sanar musu, Ammi ma taji dadi sai dai damuwa karara ya bayyana kan fuskanta bayan mommy tamata bayanin abinda Sauban yace akan maganar lefensa.
"Gaskiya yaron nan be kyauta ba memakon yayi komai nashi cikin kamata gaskiya sai na batama Sauban rai, Ummie ne ta dakatar da ita.
"Haba Ammi kinaji fa anmiki Karin bayani yace yahada nasa bayason almubazzaranci ne shiyasa,don Allah ki kwantar da halinki ninasan yaro na wallahi ba daga baya ba", Mommy tace"Aifa kara tuna mata Ummie.
*BAYAN KWANA BIYU*
Akeela ce kwance akan gadon ta tana bacci, vibration din wayarta ne yatashe ta,dan tsaki taja kafin tayi picking cikin muryan bacci tace"Kai Suby barci fa nakeyi,kinsan da anshiga next week ba isasshen baccin za'ayi ba"daga can bangaren Suby tace"ke dalla can ba wannan ba ki shiga account din Rammat,kiga yanda tayi posting videos din lefen kannen mijinki,mahaukatan kayan lefe gashinan IG ta dauka.
Zabura Akeela tayi ta tashi zaune cikin sauri tace"suwa kenan?
"Hmm kannen mijinki da za'ayi bikin ku rada day.....ai Suby bata karisa magana ba Akeela ta datse wayar.
Kaitsaye Instagram tahau,Nan ta watsa fiki-fikin idanuwan ta kan wayar,da sauri tamike tare da kama mouth"Ewwee!ai da gudu tafita bedroom dinta"Mom! Mom!! Tashiga kwalama mamanta Kira,da sauri tafito daga kitchen,"Akeela wane irin Kira ne haka?
"Mom kallah,tayi maganar tana mika mata wayar,ansa tayi.
Wannan lefen na waye haka?tayi mgnr ta diddilo idanuwa.
"Hhhhhhhh! GALADIMA FAMILY Kenan ana fada miki, kayan lefen kannen bby Sauban ne.
"Kai Masha Allah kaya sunyi kyau,Wai wai ko wacce gidan manya zata shiga kenan?
"Ea daya zata aure Dan gidan maishanu family,dayan kuma dan Abbie daya rasu zata aura.
"Kai Masha Allah kaya sunyi kyau,Allah yasanya alkhairi ya kade fitina,ubangiji ya basu zaman lafiya.
"Mom saura nawa,amma ainima yaka mata ace ankawo nawa yanzu,tayi maganar tana bata fuska .
Harara ta wugamata tare da shogewa kitchen din,da sauri itama Akeela tanufi kofan fita,kaitsaye sashin Guggo Laure ta nufa,itama nuna mata videon tayi,ai bata gama gani ba tafara sallallami"duk ankawo nasu amma ke basu kawo naki ba?to me mutanen nan suke nufi danine?sannan akasa kirana a amsa kayan dani?wallahi sai yau nasake tabbatar da Yaya Bodejo bata sona,bata son jinina,lallai ko yanzu zanje gidan.
Caraf Akeela tayi"wallahi dani zaki Guggo don inason ganin lefen nan azahirance, shikenan maza ki shirya muje.
Aiko cikin farin ciki Akeela ta fita, Guggo Laure bata jima ba tashirya tafito tana mitan har yanzu Akeela bata fito ba?Nan mujaheed dandan Baba sani yashigo gidan da mashin dinshi kirar jincheng roba -roba.
"Guggo fita zakiyi ne haka?
"Ea wallahi mujaheed zanje gidan Yaya muhammadu ne nadawo nida Akeela, murmushi kwance saman fuskansa yace"Au da amarya zaku fita?ni mumma dade bamu hadu da Akeela ba Guggo.
Yatsine baki Guggo Laure tayi tace"to kunyar wa mujaheed?ai kunyarka,kuna gida daya bazaka shiga kaduba ta ba?
"Guggo kenan,ko nashiga wataran mom zatace bata tashi ba ko batanan,to Yaya zanyi?
Mere Guggo Laure tayi da baki tare da cewa"kaga bari nashiga naga dalilin da yasa ja'irar yarinyar nan shanya ni,takarisa maganar tana shiga sashen,nan tafara juyo fadar Mom.
"Waike Akeela sai yaushe zakiyi hankali? meyasa baki da kunya?wallahi kika fita gidan nan nidake ne,bubbuga kafafuwa Akeela tafara.
"To yayane meke faruwa ne?ni inacan waje inajiran ki ke kuma kinshanya ni.
"To ba Mom bane wai bazani ba,haka kawai tace bazani ba,kafin Guggo tayi magana Mom ta cabe"fisabilillah Guggo taya za'a barta taje gidan surukai saura sati biyu biki?wallahi rashin kunyar Akeela kullum gaba yakeyi.
"Maimuna kedai sai kayi bagidajiya ko mu tsofaffin da bazamu dinga wannan abinba bare ku yara,yanzu lefi ne don Akeela ta shirya munje gidan Yaya muhammadu da ita?ke don ma banyi niyya bane da wallahi ranar asabar mai zuwa zata koma can da zama,zo muje kinji",tana kare fadan hakan suka fita Akeela nabiye da ita tasha wani dan ziririn mayafi tana karkada shafaffen baya kamar andanne da iron.
Mom din Akeela kuwa sakin baki tayi tana duban su har suka bar farlon,a fili ta furta"Wallahi sam abinda Guggo take bata dacewa,wannan ina mutum zai yarda yabata danshi?mtsewww taja tsaki tare da juyawa ta koma kitchen din.
Su Guggo Laure kuwa koda suka isa gidan sun cidda ya sake kacamewa don Aunty Maryam ma ta iso,wasu daga cikin 'yan uwan Bodejo su uku suma sunzo,hannu bibbiyu aka tarbeta kamar yanda aka saba,nan aka shiga gaishe-gaishe Guggo Laure tace"Ashe kuma ankawo lefen yara banida labari don ba'a kirani a amsa kaya dani ba,shima a waya yanzu Akeela take nuna min shine nace bari nazo naga zahiri"tayi maganar tana dariya kasa-kasa.
"To menene a amsan lefe Laure kinmanta shi taufeeq mune zamu hada mukawo? Harouna su suka kawo lefen Mashahuda shida hauwa'u daga kaduna,a ranar kuma aka kawo na muneefa,to ai ba wani abu bane,sannan