Showing 63001 words to 66000 words out of 103469 words
kiki,amma ita da zarar tamiki kike binta ki tafi?to bari kiji a yanzu Hajiya Aliya tafimin ke nesa ma ba kusa ba.
Wani kuka Adda Zainab tasa tace"wallahi baka isa ba Alhaji,wallahi sai na illata hajiya Aliya sai na maidata abar kwatance"tana karisa fadar hakan tafita tana share hawaye tare da jin matsananaciyar Hajiya Aliya da Alhaji iliyasu a ranta,zuciyar ta sai ingizata takeyi akan wani kuduri nata.
Shikuwa Alhaji iliyasu sam baiji dar ba hasalima waya yadauka yakira hajiya Aliya akan tagama shirinta su wuce.
Sosai komai ya dagulewa Adda Zainab,gashi boka hatsabibi yadena sauraranta kwata-kwata hakan yasa tafara bin malamai akan dai sabauta Ummie don tadau alwashin sai ta sabauta ta tana ganin duk abinda yake faruwa a gidan ta ba komai bane kamar matsalar ta da Ummie ( _Kai jama'a hassada mugun ciwo,mu guji kanmu da hassada domin kuwa masifa ne,gadai Adda Zainab nan haka kawai babu abinda Ummie ta mata amma ta tsaneta sam bata son ko bude ido tayi taganta a doron kasa, Allah yasa mudace ya rabamu da ciwon hassada Ameen 🤲🏽 domin maganinsa nada matukar wahala_. )
Tarasa me zatayi burinta ya cika ganin da tayi dukiyoyin ta zai tafi a banza a wofi yasa tadawo bangaren kuma Hajiya Aliya,itadai islaha sosai yakema mahaifiyar tata nasiha sai dai da alamun kamar tayi nisa batajin kira domin a duk sa'ad da tamata fada ranar kwana take zaginta har ta waya take kiranta ta cimata mutumci,hakan be hana islaha yima mahaifiyar tata nasiha.
Satin su Alhaji iliyasu uku suka dawo gida daga honeymoon din tare da murnar samun cikin Hajiya Aliya,bakaramin razana da gigita Adda Zainab tashiga ba domin har Suma tayi ta tayi tare da sumbatu,wanda hakan ya haifar mata da kwanciyar asibiti,hankalin yaranta yayi kololuwan tashi yayi,su Amma duk sunzo fada sosai Amma tayi mata akan wannan halin da tadauka tadorawa kanta, Ummie ma da Mommy da Mashahuda sunje,jin yanda Adda Zainab keta sumbatun Hajiya Aliya ta ci amanarta yasa duk jikinsu sanyi,sai dai ita a bangaren ta ba haka bane domin kuwa gani Ummie ba karamin wani tsanar ta takuma ji ba.
******
Sosai ta wahala da abortion din da tayi,dubara ce tafado musu,cikin sauri suka hanzarta komawa gida,inda Akeela tayi kace-kace da toilet da jini,a hanzarce su Hajiya dahara suka bar gidan,a cewar su yanda plan dinsu zai tafi yanda suke so,haka Akeela tayi faca² da jini,takun Sauban tafaraji yanufo bedroom din nata,nanfa ta juyar da idanuwa tafara nishe nishen karya,a hanzarce ya nufota yana me tallafota izuwa jikinsa,kuka tafashe dashi tace"honey nayi miscarriage ka kallo jinin dake fita daga jikina....ai da hanzari Sauban ya dauke yafice da ita,dawowan sa kenan daga Kiran da Daddy yamusu shida Zuhra,inda aka samata tsauraran dokoki.
Kaitsaye hospital din su Dr Ahmad ya nufa da ita,temakon gaggawa suka shiga bata,anan Dr Ahmad ke tabbatar ma da Sauban cewa lallai Akeela tayi miscarriage din cike na 1months nd 6days, Sosai Sauban yaji zafin hakan sai dai yasama ransa haka Allah ya tsara.
*******
Babban tashin hankalin da ya taru a gidan Alhaji iliyasu shine anga gawarsa shida amaryarsa wadanda aka saka mudu Poison a cikin cofeeeeeee
Xahratty CE🥰
Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️.
👨🏽🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽🦳
Page:- 63/64
____Sosai tashin hankali ya bayyana a cikin wannan family din da rudu inda su islaha banda kuka babu abinda sukeyi jin yacce ake la'antar mahaifiyar su daga bakuna da dama,ita kanta Amma tasha zagi duk da batasan hawa ba batasan sauka ba, domin dai a sashen Adda Zainab aka ga kwalaben poison dinda aka kashe su hajiya Aliya gashi kuma an nemeta an rasa,anzuba jami'an tsaro kota ko'ina, Ummie kuka takeyi sosai hankalinta yayi kololuwar tashi wanda yayi sanadiyar da tafadi,hawan jini yayi mata mugun hawa,daga mutanen kadunan har maidugri babu kwanciyar hankali,su Daddy cikin tashin hankali tare da Sauban, Baba Hasheem, Ammi, Mom harda Zuhra suka nufo kaduna,sosai suka taradda tashin hankali domin kuwa har gidan Ummie 'yar uwan Alhaji iliyasu ke zuwa suna tada kayar baya,sai da su Daddy suka iso sannan akasa jami'an tsaro shine fa komai yazo da sauki, Ummie na kuka Amma ma tanayi, cikin muryan kuka Amma tace"mezesa ki aikata haka Zainab?wani irin zafin kishi ne dake haka?wallahi ba irin tarbiyyan da namiki bane domin ko mahaifiyar ki ba haka take ba munyi zaman lafiya da amana, innalillahi wa Inna ilaihirraji'un kin cucemu kin cuce yaranki kin cuce kanki,sai lallashin ta akeyi.
Acan kuwa cin zarafin da dangin Alhaji iliyasu kema su islaha kamar ba jinin su ba yasa itada da kanwar ta gudu daga suka nufo gidan ummie,duk da yaune akayi rasuwar amma a yacce suke musu kamar zasu kashesu Suma.
Kota ina bincike ake koda Allah zaisa aga Adda Zainab amma ina ba'a ganta ba har dare,wannan ahalin dai haka sukayi kwana bakin ciki sam basu rintsaba, washegari su Daddy suka wuce harda Zuhra cuz tana da Exam,sun bar sallahun duk abinda ake ciki ummie ta sanar dasu.
Washegari haka suka shirya suka nufi gidan Alhaji iliyasu,tare da manya²n kuloli na abincin sadaka,sun ma maza 'yan waje gaisuwa don sosai yayyen Alhaji iliyasu maza da kannen su suka amsa cikin kulawa sai da suka shiga gidan ne gida ya hargitse domin har masu iskokai sai da suka tashi kan idan su Amma basu bar gidan ba sai sun kashesu,sosai sukaga tashin hankali wata kanwar Alhaji iliyasu tana kuka tace"Dangin masifa dangin bala'i wallahi munyi dana sanin sanin ku,ashe Yaya iliyasu da ajalinsa yake zaune duk tsawon shekarun nan?wallahi bamu yafe ba kuma sai mun dauki fansa, Allah ya isa tsakanin mu daku"Amma kuka Ummie ma kuka haka su islaha ma, Ammar ne ya kariso yace"Haba Guggo mu bada son ranmu momy zatayi haka ba domin lefin wani baya shafar wani sannan muma mahaifin mu fa aka kashe,muma munajin zafin hakan fa matuka,sannan me su Amma sukayi da zaku hada dasu?yakarisa maganar cikin 6acin rai, cike da masifa tace"dalla can rufemin baki,wayasa dakai?ai bazaku ga lefinta ba tunda ba ita aka kashe ba, la'ananniya shedaniya"takarisa maganar cikin muryan kuka,yayyen Alhaji iliyasu maza biyu ne suka shigo cikin 6acin rai suka fara magana"Wai talatu lafiyan ki lou kuwa?ku meyasa idan baku tayar da fitina ba bakujin dadi?kubar mamata su samu salama ma ya isa,sannan kinada tabbacin hajiya Zainab ce takashe su?cikin muryan kuka tafara magana"Yaya waye zai kashesu idan ba ita ba?tunda yayi auren nan bata ta6a barin shi yayi sukuni ba,fitinar yau daban ta gobe daban sannan da bakinta take fadar mugayen abinda zata aikata musu,wani bincike ake so ayi?bayan ga hujjoji?cikin fada yace"talatu banson masifa wallahi yanzu zakibar gidan nan"maida duban sa yayi gasu Ummie yace"don Allah kuyahakuri kusamu waje ku zauna"cikin sauri Amma tace"A'ah Alhaji ai munyi gaisuwa yanzu zamu tafi Allah kajikan su Allah ya musu rahama,yanda 'yan uwankun nan suke a fusace sai su cinye mu danye ai anan"tayi maganar tana goge kwallar idon ta tasanya medical glass din.
Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya da dadi babu dadi gashi a yau Alhaji iliyasu sun cika sati guda da rasuwa,inda bincike be tsaya ba neman hajiya Zainab ake ruwa ya jallo,su islaha sunyi kuka sun gaji me ma lallashinta mijinta ne da mahaifan sa.
******
Zuhra sun kammala Exam dinsu lafiya inda take dan hutun sati guda,bikin Kareem da Rammat kuma ya gabato shirye-shirye kawai akeyi domin saura wata guda.
Sauban ma ya tattara ya koma Canada sai biki kuma kila yadawo,wannan dalilin yasa Akeela cin karenta babu babbaka da akwai ranar da Bodejo ta aike Zuhra gidan Sauban din,duk da bataso ba don har kuka sai da tayi amma Bodejo tace sai taje don duk wani guje²n ta gidan zata koma da zama,haka ta amsa sakon ta tafi badon ranta yaso ba,koda taje sallama tadinga babu response ganin hakan yasa tashiga parlon,abinda tagani sai da yasa ganinta daukewa na wucin gadi,domin kuwa Akeela tagani akan wata mata suna lesbianism inda Akeela ke goga al'auran ta ana matan ita kuma matan ta kama..... Akeela sai shansu takeyi,ihu gabadaya ya cika palourn,da wani mahaukacin gudu Zuhra tabar gidan don da alama ma basusan shigowar ta,sashen Ammi tanufa inda ta ciddata da Mom suna hirar bikin Kareem da Rammat,ganin yanda tashigo a gigice ne yasa Mom kamota"ke Zuhra lafiyanki kuwa?ganin banda zufa da rawa babu abinda jikinta keyi,hanyar waje tafara nunawa daqyar ta iya bude baki tace"s....sa....gidan ya sa....sau...ban.
Mom da Ammi suka hada baki wajen cewa"me yasame gidan Sauban din,cikin gigita Zuhra tace"Akeel....ai bata karasa ba atake anan ta zube sumammiya,wannan abin yayi matukar tayar musu da hankali a dai dai lokacin ne kuma su Daddy suka shigo nanfa suka shiga tambayar abinda ke faruwa, Ammi tashiga sanar dasu yanda zuhran tashigo a gigice,ai da sauri Daddy, Baba Hasheem, Ammi suka nufi apartment din Sauban, Mom kuma ta zauna da Zuhra tana yayyafa mata ruwa,cikin tsananin tashin hankali.
Ammi dasu Daddy dake bayanta haka suka nufi gidan Sauban,ganin kofan palourn a bude yasa Ammi fadawa,abinda tagani ne yasata sakin salatin me hade da kiran Daddy,a lokaci daya suka zabura Akeela da wannan hajiyar dake kanta cikin gigita,a kuma dai-dai lokacin ne kuma su Daddy suka fado parlour,inda Ammi tazube sumammiya.
Tashin hankali su Daddy suka shiga ganin su Akeela a wannan mummunan yanayin,inda yanufi Ammi yadagata, Baba Hashim kuwa cikin sauri yafita daga palourn yana rintse idanuwa,wannan wane irin masifa ne?
Ranga² Daddy yadauki Ammi yanufi gida da ita,nanfa Mom tashiga tambyar abinda ke faruwa,sai dai babu amsa, fifita aka shiga yiwa Ammi don Zuhra ta farfado banda kuka babu abinda takeyi,ta isa wajen Ammi tana mata fifita haka Mom ma"Wai Baban Aseef meke faruwa ne?na tambaye Zuhra tunda ta farfado batace min komai ba kuma bata bar kuka,kuku ma kunshigo da Ammi ranga²"batare da Baba Hasheem ya tanka mata ba yakara waya a kunne,babu jimawa akayi picking"Assalamu alaikum, Dr barka da warhaka,daga can 6angaren aka amsa,magana ya cigaba"don Allah Dr munason ganinka ne yanzu anan gida"amsa masa akayi tacan bangaren"To shikenan sai ka iso,yafada yana aje wayar ya cigaba da cewa"innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, hasbunallahu wa ni'imal wakeel.
*****
Babu jimawa Dr Ahmad ya iso,yanayin da yaga jikin Ammin ne yasa yace gaskiya sai fa anje asibiti,aiko haka suka dunguma asibitin, Zuhra akace taje ta sanar da Bodejo.
Taimakon gaggawa aka shiga bawa Ammi don ceto numfashin ta,kusan awa biyar kenan ana kanta,ana cikin hakan ne kuma Galadima da Bodejo da zuhra suka shigo.
"Ikon Allah Aisha kuma lokaci daya ace ciwo ya sauka?lallai Allah me iko"Mom tace"wallahi kuwa bodejo barka da zuwa,bodejo tace"yawwa Rabi,nan suka cigaba da tsayuwa, Dr Ahmad ne ya fito yadubi su Daddy yace"Alhaji muje office"da okay Daddy ya amsa sannan shida Baba Hasheem suka nufi office din harda Galadima,waje suka zauna nan Dr Ahmad yafara bayani"babu komai kawai firgice tayi da alama taga wani abu daya firgita,but Insha Allah everything will be okay,yanzu haka ma ta farfado zaku iya dubata"godiya sosai sukayi masa suna fiata daga office din,duk cikansu suka rankaya dakin, Ammi na zaune banda hawaye babu abinda yake mata,duk sannu suka shiga yimata, amsawa tayi tana me duban Daddy dakyar ta bude baki tace"Daddyn yara ALLAH yasa mafarki nake ba gaske ba,ina jin tsoron abinda na gani ya zama gaskiya,gyaran murya Daddy yace"Uhmm please Aisha calm down cuz likita yace baki bukatar hayaniya....carab bodejo ta ca6e"ku mana bayani mana Taleeb wai meke faruwa ne? Mom tace"gaskiya kam saboda kinga Zuhra tafara ganin abinda ke faruwa sannan a sashin Sauban, Galadima yace"ya isa haka kubarta ta samu natsuwa idan anje gida duk a tattauna.
A ranar Dr Ahmad yabama Ammi sallama.
******
Akeela kuwa ganin abinda yafaru ba karamin rudewa da tashin hankali ta shiga ba,kuka takeyi tana fadar ta shiga uku shikenan tasan ita auren ta yanzu ya gama yawo,itakuwa hajiyar ganin abinda yafaru yasa ta tattara yanata yanata tabar gidan gudun wani mummunan abu ya auko,aiko Akeela cikin tsananin rudu da damuwa tanufi gidansu tana kuka kaitsaye sasan Guggo Laure ta nufa,da tashin hankali Guggo Laure ta tareta tana kamata suka shiga daki,ananfa Akeela ta shirga ma Guggo Laure karya da gaskiya ita kuma tahau ta zauna, bala'i tafara zazzagawa,nan kuwa ta shirya ta nufi gidan Galadima,a dai-dai lokacin su kuma suka dawo daga hospital,da kuka Guggo Laure da taresu don su sam basu lura da ita bama,duk cikansu mamaki sukeyi,musamman Daddy da Baba Hasheem,kaitsaye Ammi ta tunkara tana nuna ta da yatsa tare da kumfar baki"Aisha baki isa ki yanke abinda Allah shi da kansa ya kulla ba,dama tunda akafara maganar auren Akeela da Sauban na lura da take²n ki bakiso,taya za'ace tunda tazo gida kullum sai kinshiga gidan ta kin tayar mata da hankali?wai me ta tsare miki,kwanaki ma da tayi 6ari tace kece kika zuba mata abu a lemu tasha cikinta ya zub........bata karasa ba Baba Hashim ya katseta cikin 6acin rai,domin dai da alama yau Guggon nasu ta kure shi"Don Allah ya isa haka Guggo ya isa,ita shedaniyar jikan takice tafada miki wannan kanzon kuregen?wallahi da na kama yarinyar nan a gidan nan yau dukan mutuwa zan mata domin itadin annoba ce a cikin ahalinmu,ko makiyin mu bazamuyi fatan ya hada zuri'ah da me irin halayen yarinyar nan ba"cikin daga murya Galadima yace"Hasheem kana hauka ne? Guggon naka kake fadawa haka?gabadaya idon Baba Hashim ya juye da bala'i yace"Galadima kadena sauraren maganar Guggo,domin duk halin da Aisha tashiga Akeela ce sila,domin dai Akeela 'yar madigo CE!nan yashiga basu labarin abinda ke faruwa tundaga zuwan Zuhra da suman da tayi har zuwan su dasu Daddy da sumar da Ammi tayi,gabadaya Galadima, Bodejo, Guggo laure salati suka sanya Daddy na tayasu,cikin kuka Guggo Laure tace"Karya kukeyi hasheemu wallahi sharri kukeyi Allah ya isa tsakanina daku da yardan Allah sai Allah yasakama Akeela, Allah ya isa"tana fada tana kuka haka yafita tabar gidan.
Taga² Galadima yayi zai fadi,cikin sauri suka taresa,fadi yake nine Laure yau takema 'yayana Allah ya isa? innalillahi wa Inna ilaihirraji'un,gabadaya gida ya hargitse kamasa sukayi suka kaishi bedrooms dinsa suna masa fifita, Galadima kuwa sai maimaita magana guda daya yakeyi abinka da tsufa yafara riska,shekaru 82 ba wasa ba ai"Nine Laure kema yarana Allah ya isa?a ranar dai sai da jinin Galadima yahau, Sauban ma ammishi waya kan gobe zai iso, Abba ma haka.
Gabadaya ahalin kwanan rashin dadi da natsuwa sukayi domin tsiya sosai Guggo Laure takeyi Alhaji mansir na tayata, Baba sani kuwa cewa yayi abari ayi bincike,nanfa Guggo Laure da Alhaji mansir suka dirar masa wai shima ya yarda da sharrin da akama Akeela.
Da daddare kuwa Akeela ba gida ta kwana ba,can tatafi suka sake cin Karen su babu babbaka,domin gani takeyi yanda tahada wannan maganar komai zaizo da sauki.
Washegari kuwa da wajen 1:30 babu abinda kakeji na tashi sai hayaniya gidan Galadima family wanda har yaja koke koke domin kuwa Guggo Laure ta dage kan wallahi muddin aka raba auren Akeela da Sauban itama ta rabu da Galadima bata bashi babu zuri'ar sa rabuwa kuma ta har abada,a'inda Bodejo itama ta rantse kan wallahi sai Sauban ya saki Akeela don bazasu zauna da annoba,Sauban idanuwan nan sunyi jajawur nan yashiga recalling din abubuwa da dama,sannan tabbas shima yasha zargin sa da haka,nan yashiga bayanin komai shima,sannan Ammi tasamu shedar tunda akayi bikin Sauban bata shiga sashin ba sai jiya,sosai rayuka suka 6aci hankula suka tashi,ita kuwa shedaniyar batasan meke wakana tana can suna madigon su,duk da a gefe guda na zuciyan ta tanajin bazata iya rabuwa da Sauban ba.Gida kuwa sai kuka da kuka domin Guggo Laure tace"anuna musu sheda na kama Akeela da akayi tana madigo"Bodejo tace"sheda ai Allah ne shaida kuma insha Allah sai Allah yatoni asirinta mudaije zuwa.
Wata kalma da ya girgiza su ne yasa mutane biyu zuciyoyin su rawa lokaci guda wato Galadima da Guggo Laure domin kuwa a take anan Sauban yace"ni Muhammad Taleeb Muhammad nasaki matata Akeela saki daya,biyu.....baikarisa na ukun ba yaji wani gigitaccen mari,da hanzari yadago lokaci daya, Daddy ne ya maresa"Sauban ka gwammace ka yanke zumuncin 'yan uwa biyu?Ashe baka da hankai? Sauban yace"Daddy ko na cigaba da zama da Akeela babu aure domin zargin ta zan fara,kuma aure da zargi babu aure.
Ihu Guggo Laure tasa kamar mahaukaciya tana fadar"Allah ya isa tsakanina da ahalinki Yaya Muhammadu bani bakai,insha Allah abinda kukamin sai Allah yayi muku"tana fadar hakan tabar gidan tana kuka, Alhaji mansir yabi bayanta.
Atake anan Galadima ya yanke jiki yafadi,wanda yayi sanadiyar karkacewan mouth dinsa tashi daya.
*_LALLAI WADANNAN AHALIN SUNA CIKIN CAKWALKWALIN TASHIN HANKALI,A GEFE GUDA GA ADDA ZAINAB WACCE BA'A MASAN INDA TAKEBA,KOMAIFA YA RINCA6E YA LALACE😱_*
[7/9, 13:44] 𝐗𝐚𝐡𝐫𝐚 𝐗𝐚𝐡𝐫𝐚𝐭𝐭𝐲🥰: 👨🏽🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽🦳
Page:- 65/66
____Hankulan su yayi kololuwan tashi a lokacin da sakamako yafito kan Galadima ya kamu da paralys daga 'yayan har jikokin hankulansu yayi kololuwan tashi,lokaci guda aka fara kokarin hadawa mishi Visa shida Daddy da Abba don zasu nufi Malaysia gidan Abbie nacan zasu sauka idan komai ya dai-dai ta,family kuwa sai kuka da kuka.
Sauban yayi nadama matuka akan hukuncin da ya yanke domin Daddy lefinsa yake gani inda dashi kanshi ma yake ganin shine silar komai, Bodejo kuwa kuka take sosai cikin muryan kuka tace"Duk abinda ya samesa Laure ce sila babu ruwan saudan domin shidin ya kasance meson 'yar uwansa ne ganin su biyu kawai iyayen su suka haifa,sam baya son damuwan ta shiyasa yake mata abinda zai faranta mata duk da kuwa yasan halinta na rashin kirki amma haka yake shanye komai, Allah yasani wannan yarinyar ta cucemu.
Basu tare da natsuwa, Taufeeq dasu ummie ma sun karaso,inda jibi zasu bi jirgin karfe 10:00.
Duk an mayar da matan gidan mazan ne kawai suka kasance a asibitin da jikokin nasa,acan gida kuwa sai maida zancen akeyi, Mom nabawa Ummie da Mommy labarin duk abinda ya faru harda cin mutumcin da Guggo Laure tayi daya haddasa haka.
"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un wannan abu sam beyi dadi ba,mezesa son ya yanke hukunci cikin fushi?da anbari duk