Showing 54001 words to 57000 words out of 103469 words

Chapter 19 - GALADIMA FAMILY Complete Hausa novel

07 Sep 2024

6895

nasamu lada a gidan aure na"yakarisa magana tana shiga toilet din don hada masa ruwan wanka,sosai yake mamakin karfin hali da budewan Ido na yarinyar yarasa dalilin da yasa sam bata tsoron shi,wata zuciyar tace _Aibata yarda ta hada ido dakai balle takarance yanayinka._ Zama yayi zuwa can babu jimawa tafito jikinta har rawan farin ciki yakeyi ta nufosa tace"honey gashi can na hada ma,mikewa Sauban yayi batare da yayi magana ba yanufi toilet din,muryan ta yajiyo tana cewa"ko nazo na temaka maka ne honey?cikin sauri ya murza ma kofan key,kanshi nasake daurewa da bude idon yarinyar,kafin yafito tabude closet dinsa tafito masa da kayan da zaisa.
Yadan Jima a toilet din kana yafito,waist dinshi daure da towel bata dakin cikin jin dadi ya sauke wata ajiyar zuciya,kofan bedroom din yanufa ya sanya key yarufe,gaban mirror yadawo yafara shiryawa,yanajin sanda take knocking yayi mata banza sai da yagama shirya ko kallon kayan da tafito masa dashi baiyi ba yabude yaciro wasu kayan ya shirya yayi matukar kyau,sosai kwarjinin sa da zatin sa suka sake bayyana,cikin takun sa na isa yafito.Kallo daya Akeela ta masa tasake rikicewa don tabbas ya hadu iya haduwa sai dai ganin face dinsa da tayi yasa tadan shiga taitayin sa,dubanshi tayi tace"ga lunch can an aiko dashi"batare daya dubeta ba yace"zanje masallaci daga can zanshiga cikin gida nayi acan,wani kululin bakin ciki taji yazo mata makoshi ya tokare cikin yanayi nanuna rashin jindadi tace"nikam gaskiya banajin dadin abinda kakemin don Allah idan bazaka iya zama dani ba ka sawwake mun yanzu natafi niba makiyiyar ka bace face masoyiyar ka don haka bazan tilasta maka saika so niba"takarisa maganar cikin muryan kuka sosai takashe masa jiki sai dai duk kwakwan ka bazaka fahimci haka,sam baya fatan abinda zai bata ran iyayen nasa kwana biyu da aure ace amarya tayi yaji,danne zuciyan sa yayi batare da yayi magana ba kaitsaye taga ya nufi kofan barin parloun,maganar sa tajiyo"idan nafito zandawo nayi lunch din"yana gama fadar haka yafita,wani murmushi Akeela tasaki a fili tace"Sauban nida kai dan halas kafasa lallai kuwa nagano lagon ka Wallahi koda bala'i sai ka soni,cikin farin ciki tanufi dining din,wasu pills ta balle a satchet nasu tacire guda biyu tazuba a cikin lemon Fairless ta girgiza sosai sannan tasake tamke murfin,ranta fal nishadi,batare da maganar sallah ba tasamu waje tazauna.

Yadauki tsawon 35 mnt sannan yadawo,cike da kissa ta tarbesa kaitsaye dinning din yanufa,cikin bariki tafara serving dinsa,tuwon shinkafa ne miyan zogale sai farfesun kayan ciki,nan ta gabatar mai da komai itama ta zauna tafara cin abincin,cikin natsuwa yakecin abincin nashi yanayi yana sipping juice din,har ya kammala ya mike tare da daukan ragowar juice dinsa yakoma parloun sa yazauna,wani nishadi Akeela takeji donji take kaman ammata wani gagarumin kyauta,bayan kamar 5 minute Sauban yaji wani bakon al'amari duk da ada yana fama da matsalar sai dai yadan dade baitaso mishi ba,dannewa yaci gaba dayi,dai-dai lokacin Akeela takariso wajen tana zama agefenta jikinsu na gogan na juna hannunta tasa tasaqalo ta wuyansa,sosai Sauban yasake tsare gidan sa duk da wani mahaukacin feeling da takejin yana taso masa but haka yaketa dannewa,cikin tsananin shedanci Akeela tafara yimishi wasu shirmen hira tana shasshafa jikinsa.Sauban kuwa banda zufa babu abinda yakeyi sosai yake kokarin danne matsalar sa,mikewa yayi yana dan matsar da Akeela sai dai kokafin yayi magana yaji hannunta a federal government dinsa🙈wani rintse ido yayi yanajin wani takaicin ta agefe kuma ga azaba daya ishesa,juyowa yayi cike da niyyar yimata tijara,sai dai arban da yayi da maka-makan gugunanta yasa ya daskare a tsaye🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏽‍♀️sai dai duk yanda yaso yayi kokarin control din kansa kasawa yayi don yakai limit dinda shikansa bazai iya controlling kansa ba,su Akeela ansamu abinda akeso nanfa tafara aikama da ya Sauban wasu manyan sako,tun yana basarwa kai hardai yabada kai bori yahau,sosai suka fara al'amuran su batare dashi kansa Sauban din yana gane halin da yake ciki ba duk da a kasan ransa ba hakan yaso ba amma bayajin zai iya wasa da damanshi,a haka Allah yatemakesa yasamu natsuwa da Akeela batare da wani abu yashiga tsakaninsa da ita ba duk kuwa yanda taso wani abu yafaru yakiya,kuka tasanya masa tana cewa tunda shi yasamu ya faranta ma ransa ai dole ita ya maidata ko oho,cikin takaicinta ya dafe kai don gabadaya yagama fahimtar Anya yarinyar ba 'yar hannu bace?duba da wasu dabi'unta,ganin tagaza yin shiru cikin karfin hali yafara magana"Niba jahili bane inason na gudanar da Daren farkona wajen nuna godiya ga mahallicina,sannan mubi dokokin da aka sanar Mana a addinance,buyi sallah na nuna godiyan mu ga Allah ba sai mufara wani Abu?I can't! Yana gama fadar hakan yanufi bedroom dinsa kaitsaye toilet yafada, Akeela kuwa cij yatsa tayi a fili tace"Allah yakai damo ga harawa,yanda ka tayarmin da hankali nima dole nasamu me biyamin bukata bari nanemi Suby,takarisa maganar tana me mikewa tafita daga apertment din.
Wanka Sauban yayi cikin dan natsuwan da ya samu shiryawa yayi cikin kananun kaya marasa nauyi yanufi gidan su,tundaga shigowan shi ya hangosu zaune akan plastic chair sai hira sukeyi cikin nishadi,hada Ido tayi dashi gsbanta yayi wani mummunan fadi,batare da komai ba yawuce ko sake dubansu beyiba,wani boyayyen ajiyan zuciya zuhra tasaki tana godiya ga Allah.

*****

A KADUNA kuwa abubuwa sun fara cakude ma Adda zainab yanzu hk zaune take suna tattaunawa da aminiyar ta,cikin wani irin damuwa take magana"Wallahi bansan yanda zanyi ba aminiya,damuwa yamin yawa Alhaji tun dawowan shi da kwana biyu ya sauya nagaza gane kansa,Wai sai rannan na kamashi yana waya da mace harma da maganar wai yatura manyansa,hauka ne kawai banyi ba,ni Alhaji iliyasu zai tozarta? wallahi da naga Alhaji da wata mace gwara naga motuwar sa kowa ma yahuta"tayi maganar tana cire dankwalin ta ta ajiye a side, hajiya Aliya tace"hmmm namiji kenan su totally nasu abin kunya baya musu wahala bacin haka ina Alhaji iliyasu ina wani sure?Koda kinsan wani me budurwan zuciya ce,kuma kada kiyi mamaki yaje yadauko Miki budurwa.....batare da takai aya ba Adda zainab ta mulmulo wani ashar! "Tabbas da itama saina kasheta aminiyata kinema min mafita kada na hadiye zuciya na mutu wallahi bazan iya ganin Alhaji da wata mace ba,lokacin da nasha wahala na kafin yayi kudin wayasani?sai yanzu da yayi arziki ne yakeda muhimmanci?don Allah munje wajen boka hatsabibi"takarasa maganar tana tagumi da sakin wasu wahayen bakin ciki.
Hajiya Aliya kuwa a ranta murmushi takeyi kawai najin dadi domin tabbas tasan idan tashiga gidan Alhaji iliyasu kashin hajiya zainab ya bushe don alkawari tadauka sai ta wulakanta ta,sai ta tozarta ta,gyaran murya tayi tafara magana"Kinga sai dai nakirashi a waya duk yanda mukayi dashi zan sanar dake amma Kisha kurumin ki muddin kinatare dani kindena zubda hawaye,me akayi akai kishiya aminiya?meyasa kike zubda hawayen ki a banza? Adda zainab dai takasa magana sai hmmm da hmmm take cewa, abubuwa sun taru sun mata yawa ga rashin samin nasara akan kanwarta bilkisou yanzu kuma ga matsalar miji ta kunno kai,sai dai taji dadi da sassaucin kalaman aminiyar tata sosai.

****

Amare kuwa zama yayi dadi a gidajen biyu Mashahuda da muneefa amarcin su suke ci da tsinke ana zuba soyayya,Akeela kuwa Suby tadawo tatare a gidan tareda da wata yarinya sabuwan hannu suke biyawa Akeela bukatan ta,duk abinda ke faruwa shikam baisani ba,don shi yama fara shirye²n komawa nanda 5 day's,shedanci da kazantar da akeyi a gidan Sauban ya tsananta wanda ba kowane yasani ba,domin kuwa madigo babban bala'i ce a doron kasa don har su hjy daharatu Suma zuwa sukeyi, akwai wata rana da sukazo sun gama iskancin su duk suna zaune a parlour sukaji karar door bell,lekawa Suby tayi da sauri tadawo take sanar da Akeela Guggo Laure ce,kikkimtsawa suka sakeyi sannan akaje aka bude mata kofar,tunda taga bakin fuska a gidan tafara harhada rai fuskan ta babu wani cikakken annuri,gaisheta suka fara sai dai dakyar take amsa musu,ganin haka yasa suka tattara yanasu yanasu suka bar gidan,koda suka watse cike da masifa Guggo Laure tafara magana"Ashe Akeela har yanzu bakiyi hankali ba?har yanzu bakidena tara wadannnan tambadaddun yaran ba?wai nikam sai yaushe ne zakiyi hankali?wallahi kikiyaye wadannan yaran,daga ganin idanunsu a soye gogaggun 'yan iska nefa.A raina nace _hajiya Guggo Laure kenan ita Akeelan bakiga gogewan nata ba saina yaran wasu kike hangowa?_ bata fuska Akeela tayi batare da tayi magana ba don tasan yanzu tadinga naci kenan,can dai tace"Guggo zan kiyaye don Allah kibar maganar haka"katseta tayi cikin fada"bazan bar maganar ba aikece kikajawo tun yaushe nake rabaki da wadannan yaran amma bakijin magana?harda wadanda sunma haifeki amma kince a makarnat kuka hadu,wallahi zan gayawa mansir dinner tunda ke bakijin magana,ni don Allah tashi kisama min abin Kari me kyau da soyayyen kwai guda bakawai"tayi magana tana gyara zamanta a kujerar,mikewa Akeela tayi tana mejin haushin zuwan nata a dai-dai wannan lokacin,don harga Allah batason ba don bawai ta gamsu bane,da alama kuma Guggo Laure yini zatayi.Bata wani Jima ba tahado mata lafiyayyen breakfast.

A dai-dai lokacin da su hajiya daharatu suka fito a lokacin ne kuma sauban yafito daga sashen sa don raka wasu bakinsa,ganin shi yasa duk suka gigice don kwarjinin sa da kyansa na tafiya da 'yàn mata da dama,jikinsu na rawa suka shiga gaisheshi shida abokansa,abokan duk sun amsa amma shi ko tankawa beyi ba illa nazarin su day yashiga yi ganin sam ba mutanen arziki bane,sai dai yaso yagane Suby,cikin sauri suka bar gidan.
Shima raka abokan nasa yayi koda yadawo apartment din sa yawuce dai dai nan kuma wayansa tayi kara alamun message yashigo,bayan ya zauna ne yajawo 💻 dinsa har zai bude sai kuma yatuna abu yashigo dazu don haka yabude wayan,kaitsaye ta wahtsapp yaga notification din tunda always data a kunne ne,shiga yayi still da number da akaturo masa messag3 din kwanaki still dashi aka turo wannan kuma duk video's ne,shiga cikin profile din yayi,ko bude pics din dake DP din beyi ba,gani yayi an rubuta....batare da yabi takan komai ba yaja tsaki,jawo laptop dinsa yayi ya kunna don sunada meeting da ma'aikatan company nasu shi ta video call zaiyi don an bashi hutun amarci gashi saura 5 day's yakoma.

Xahratty CE🥰
Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️.
20/6/23.
[6/24, 17:31] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳

Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now

*_GALADIMA FAMILY_*

Page 55/56

______Zaune suke cike da so da kaunar juna suke hirarsu cikin kwanciyar hankali da jin dadi,zaune suke akan plastic chairs kamar dai yanda suka saba,bude gate din security sukayi anan motoci biyu suka kunno kai cikin gidan,motar gaba ta Daddy ce ta biyu kuma kirar Benz ta ya Sauban, ZUHRA jitayi kirjinta ya shiga dakan lugude don wannan shine rana ta farko dasu Daddy zasu kamata a irin wannan yanayin,sannan tabbas tasan dokan gidan,balle murfin motar sukayi suka fito Daddy da Baba Hasheem tun daga nesa idanuwan su Daddy ke kansu,shikuwa Sauban kallo daya ya musu ya kauda kai,ganin sun kawo kusa dasu tunda dai-dai apartment din Ammi dama suke zama cikin sauri zuhra ta nufesu, cikin girmamawa tafara magana"Daddy sannu da zuwa, Baba sannu da zuwa"amsawa sukayi duk cikan su suna duban Shuraim wanda yake karisowa,cikin girmamawa Shuraim ya duka ya shiga gaishe dasu Daddy,face dinsu Daddy kadaran kadahan suka amsa,zuwa can shiru yaratsa wajen,dubanshi Daddy yayi yace"gashi kuma bamu gane ba malam daga ina kake?dan sosa kai Shuraim yayi yafara inda² saboda ganin da yayi zuhra ta koma tsumu-tsumu.
Baba Hasheem da yaga gane duk abinda suke 6oyewa da yanayin zuhra yace"tambayar ka ake daga ina kayi shiru?yayi maganar cikin dan hassala,cikin sauri Shuraim yace"Dama wajen zuhra nazo hira"Baba Hashim yace"Hira kamar Yaya?Shuraim yace"dama nida zuhra son juna muke kuma nida niyyar aure nake son ta bada wasa ba.Shiru duk sukayi suna zubanya mishi na mujiya,ita kuwa zuhra banda rawa babu abinda jikinta keyi don tabbas tasan idan ba'ayi wasa ba to tata takare yau.
"Bakasan tana da iyaye bane da bakazo kanemi izinin su ba kafin kafara zuwa wajen ta? Baba Hasheem yayi ma Shuraim tambayar face dinsa babu alamun wasa ko kadan,shikan shi Shuraim yasha jinin jikinsa musamman da Baba Hasheem,cikin sauri yace"Nasani Baba,sai dai nayi kokarin zuwa sai.....yayi shiru batare da yakarisa ba,"Baba Hashim yace"sai kuma baka zoba?maida duban sa yayi ga zuhra yace"kin kyauta tunda kece keda iko da kanki? yanzu har kinyi girman da zaki kira saurayi yazo zance gidan ku batare da kingama makaranta ba?batare da annemi izinin iyayen ki ba?shiru zuhra tayi jikinta babu inda baya rawa.
Cikin daka tsawa dayasa Ammi dasu Laila fitowa yace"Ba magana nake miki ba kike girgiza min kai kamar kadangaruwa?
Cikin muryan kuka zuhra tace"don Allah Baba kuyahakuri"girgiza kai kawai Daddy yayi sannan yayi gaba, Baba Hasheem yace"kin kyauta domin duk abinda yafaru kece sila,kenan a school dinma samari kike kulawa ba karatu kikeyi ba kenan?da sauri zuhra tadago tana girgiza kanta hawaye na mata zarya.
Batare da yasake magana ba ya wuce, Sauban ma bin bayansa yayi,zuhra kuwa atake anan ta duke tana me salkin wani irin kuka me ban tausayi domin bata kawo zuwan ranar nan kusa,shikan shi Shuraim hankalinsa ba karamin tashi yayi ba,duban ta yayi cike da tausayawa, Ammi ce takaraso wajen tana me kama zuhra suka nufi cikin apartment dinta,jikinsa yayi bala'in sanyi,a gefe daya kuma ga tausayin kawunan su,dama a waje yake parking motar shi,direct gate ya nufa ya fice daga gidan gabadaya.

Haka dai takara sa yinin ranar tayi shi sukuku babu walwala ga tarin fargaba da ya hadu ya mata yawa don kuwa tabbas tanaji a jikinta shirun Daddy ba alheri bane.
Bayan sallan isha'i zsune take a dinning sam abincin takasa ci tsakura wa kawai takeyi,sam bakinta babu apatite hakanan tarasa abinda ke mata dadi,Laila ce tashigo cikin sanyin jiki ta dubeta"Sis kitashi kije Daddy nakira wai suna parlour Galadima"jitayi kirjinta ya tsananta bugawa fargaban ta yakaru,ko kaffara bazatayi ba tabbas akanta ne za'ayi wannan zaman,mikewa tayi cikin sanyin jiki tana duban Laila idon ta na cikowa da ruwan hawaye,dafa kafadanta kawai Laila tayi tana mejin tausayin 'yar uwan tata.
Cikin sanyin jiki ta yafa gyalin Egyptian gown din dake jikinta tanufi apartment din Bodejo,da sallama tashiga parlour,zaune suke Galadima, Bodejo, Daddy, Baba Hasheem, Ammi, Ummie, Mom sai kuma Sauban dake zaune gefen kafar Galadima ahankali takarisu parlour cikin sanyin jiki,wani irin kallo Ummie ke aika mata dashi don ita batasan meyafaru ba sai a bakin Mom takeji.
Zama tayi akan hadadden carpet din wanda ya qawata parlour sosai,gaishesu tashiga yi cikin jam'i,cike da tsokana Galadima yace"feel free mana amaryas,sai kame² kikeyi ba?ai asirin ki ya tonu wato nema kike kimin Kishiya saboda kinga natsufa ko?to komin abinki ba'a canzawa tuwo suna"yakarasa maganar yana gyara zaman shade din fuskan sa, Bodejo tace"Hmmm ai kayi kagama ni me kishi dani sai ya shirya"duk dariya aka Sanya banda Sauban daketa daddana wayar,shiru ne ya gifta zuwa can Daddy yayi gyaran murya yana duban zuhra"mamana! Muryan zuhra na rawa tace"na'am Daddy, Daddy yace"kinsan zaman nan akan wa mukayi shi ba sai anyi dogon jawabi ba ko?daga kai zuhra tayi alamun Ea.
Daddy yace"Masha Allah,tunda muke a gidannan tun kama daga kan Addojinki su Maryam babu wacce tataba kula wani saurayi kafin aure hatta su Mashahuda batare da anzo annemi izinin mu ba,kece ta farko da kika fara karya dokar gidan nan harki dinga kula wani saurayi ku kulla soyayya batare da duk munsani ba,bazan boye miki ba raina yayi mummunan 6aci domin kuwa hakan babban zunubi ne agareki.
Shiru parlour ya dauka zuwa can ya cigaba"nema kike ki maida mu mutanen banza?a'ina har kika samu karfin gwiwwan haka?waye shi a'ina kuka hadu?jikin zuhra yasake sanyi muryan ta na rawa ta shiga basu labarin haduwar ta dashi tundaga farko har karshe,cikin muryan kuka tace"wallahi Daddy ba karya nakeyi ba ka tambayi Aunty Mashahuda da Aunty Safeena,domin dan uwan Ouncle Asheer ne,sosai tabawa su Daddy tausayi amma sukaki nuna mata hakan,cigaba da magana tayi"sannan yaso ya sameku nice na hanasa nace sai na gama school amma don Allah kuyahakuri bazan kara ba.
"Hmmm abinda yasa muke hanaku kula da wasu mazan ba komai bane face gudun matsala,domin ke akanki hakan ne ke shirin faruwa dake domin akwai aure akanki"ai a gigice Ummie, Mom,zuhra ke duban Daddy, Ammi kuwa mamaki ne ya kashe ta,jikin ta babu inda baya rawa tamike tanaso tayi magana takasa saboda tashin hankalin da tashiga, Daddy ya cigaba da magana"Marigayi Sadeeq yabar mana wasiyyar idan yarasu yanaso ranar addu'an ukun shi a hada da auren ku,domin yace tun sanda aka haifeki da wannan kudurin a ransa,ranar da Sadeeq ya cika kwana uku da rasuwa a ranar aka daura auren ki da yayan ki Sauban!zuhra jitayi kanta na juya mata lokaci daya taji wata jiri na dibanta,wannan karan Mom ce ta zabura ta mike tsaye tana kokarin magana sukaji karar fadin mutum timmm!!! Gabadaya juyawa sukayi wajen inda sukaji karar faduwan,zuhra ce ta yanke jiki ta fadi a take anan, da wani azababben gudu Sauban yanufe ta yana me jawo ta ya rungume,duk cikan 'yan parlour zagayeta sukayi banda Galadima da Ummie da suke zaune, Ummie wani hawayen farin ciki ne ya shiga sirnano mata,tabbas abinda tadinga addu'an samu kenan tundaga sanda tadawo hayyacinta take fatan Sauban da zuhra su fahimci juna,sai dai rashin jituwar su ba karamin daga mata hankali yakeyi ba.
Da sauri Ammi tabude fridge din dake nan parlour,bottle water medan sanyi ta dauko,balle murfin tayi tashiga tsiyaya ma Sauban a hannu,shikuma yana shafa mata haka sukayi har kusan sau biyu ana ukun ne taja ajiyar zuciya tana me sakin wani irin kuka,duk ajiyan zuciya suka sauke sannan suma suka koma suka zazzauna"zaunar da ita Sauban"cewar Baba Hasheem,zaunar da ita yayi sannan yana dan matsawa gefe cikin kamewa,rarrafawa tayi tana dafe kafar Daddy cikin muryan kuka gwanin ban tausayi tace"please...please Daddy don Allah kuyahakuri kada kubarni dashi bazan iya rayuwar aure da.....maganar ce tatsaya cak a dalilin marin da Ummie ta sauke mata,tana huci takai hannu zata sake mata wani marin cikin sauri Ammi ta tare,6acin rai kwance a fuskar ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login