Showing 66001 words to 69000 words out of 103469 words

Chapter 23 - GALADIMA FAMILY Complete Hausa novel

07 Sep 2024

6892

an shawo kan matsalar ko don yankewan zumuncin nasu"sai a sannan Ammi tayi magana"Wallahi kuwa Ummien yara yayanke hukunci cikin fushi,ni a tsarina Sauban bazai sake Akeela ba yabarta duniya ma ta isheta.
Carab Mom tace"Ca6! Kazanta wallahi ko jini bazamu yarda muhada da 'yar madigo ba,wai Aunty Aisha kin mance illarsa ne?kin mance girman zunubin sa? Ai wannan abinda yayi shine dai-dai kuma beyi lefi ba da yake dai ita Guggo Laure a yanda na fahimce ta sam batason lefin wannan yarinyar,ni tun sanda nafara ganinta bata kwanta min ba bata burgeni ba yarinya ido a bude sai kace sandar snooker?ai gara da Allah ya tona mata asiri,ga matansa nan kawai asa tarewan su kowa ma ya huta"takarisa maganar tana nuna Zuhra wacce tayi tsuru² dajin furucin Mommy na karshe.
Mom tace"yanda kikajin nan Aunty Hauwa,ai mu munyi mummunan gani munshiga tashin hankali.
"Nikaina a yanzu nafi bukatan asa kawai ranar tarewar su ko sati guda ma inda za'abi ta nawa kada ayi,shi kanshi ma ya samu natsuwa"Ummie tace.
"Gaskiya ne idan aka gama wannan abin komai ya lafa sai ayi maganar"Ammi tafada,mikewa Zuhra tayi jikinta nayin bala'in sanyi don harga Allah ita tasan batajin san ya Sauban acikin ranta,zuciyar ta a dagule tashiga bedroom din Mashahuda nada inda tattada ta tana kwance tare dasu Laila da Nihal,da yake tanata fama da laulayin ciki shiyasa,kwalla ne ya taru mata a ido tanajin damuwa lokaci guda ya dirar mata.
Muneefa ce ta shigo da 'yar dariyar ta tace"Amaryan mu gaskiya ya kamata ayi shagalin biki kafin ki tare, Mashahuda ta mike ta zauna itama dariyar take tace"anyi maganar tarewar ne? Muneefa tace"maganar dasu mommy suke kenan a palour"wani ihu Nihal da Laila suka sanya,cikin tsokana Nihal tace"ai wallahi kuwa gara kitare Yaya ya tafi dake can Canada kikarasa karatunki, Mashahuda tace"Ai banjin zai iya tafiya da ita yanzu kila nan zata fara zama"hawayen da take makalewa ne ya samu daman gangarowa,kamota Muneefa tayi ta zaunar da ita kan gadon tace"a'ah menene kuma abin kukan yanzu daga magana?dagowa Zuhra tayi cikin muryan kuka tace"Bazaku gane bane,ni ni bana son sa Allah yasani don Allah kusa baki yasakeni.....bata karisa taji Mashahuda ta buge mata baki,cikin 6acin rai tafara magana"kinada hankali kuwa Zuhra?kinsan abinda kike fada?to tun wuri kishiga taitayin ki domin wallahi idan su Abba sukaji kalmar nan daga bakin ki sai na lahira yafiki jin dadi,ke bama su ba ya Taufeeq naji sai kinsha mamaki,'yan mata nawa ne ke neman irin damar ki basu samu ba?kinsan yanda 'yan mata ke rushing kan Yaya?to wallahi kisan maganar da zaki na furtawa gudun kada ya koma kunnensu da Daddy, Muneefa tace"Hmmm Zuhra kenan duk wannan abin da kikeyi yarinta da wauta ne kawai yake damunki,Amma I know ko badade ko bajima keda kanki zakiyi alfahari da samun ya Sauban matsayin miji,don koni naso shi amma nasan ba lalai yasoni ba,gashi Allah yamin canji damafi alheri.
Duk shiru dakin ya dauka banda shesshekan kukan Zuhra babu abinda ke tashi, Laila tace"Allah ya ganar dake,kuma ko mutum naso ko baiso dole ya tare"tayi maganar tana sakin ma Zuhra gwalo tare da ficewa da gudu tana dariya,kokarin binta Zuhra keyi tana karama kukan ta volume.
Dayake asibitin su Dr Ahmad akwai kula don asibiti ne me masifar tsada nurse's ke kula da mutum,wannan dalilin yasa karfe 10 su Daddy duk suka baro asibitin.
Taufeeq da Sauban apartment din Ummie suka wuce, Zuhra ce zaune a parloun kasa tana cin abinci,don Ummie tashiga ciki watsa ruwa,sallamar su ce yasata dagowa tana amsawa idanunsa akanta duk da yacce face dinsa yake a tamke hakan behanashi kashe ta dana mujiya ba kamar wacce ta masa lefi,cikin tsananin farin cikin ganin Taufeeq tataso tare da hugging dinsa"Yaya ur welcome,shafa kanta Taufeeq yayi yace"thank you little,hope kina lafiya? Zuhra tace"fine Yaya I think ma nafika cikakkiyar lafiya",dariya suka sanya itadashi,shikuwa Sauban remote ya dauka ya kunna Ball,wanda yau akwai wasa 10:30 tsakanin Manchester United da kuma Arsenal.
"Ina Ummien take?tajiyo muryan sa yana tambayar ta,da kamar bazata amsa ba Taufeeq yace"little dakefa akeyi"cikin sanyin murya tace"tana sama.
Babu wanda yasake magana duk da kuwa yanda Akeela kejin ta a takure zamansa a wajen, Ummie ce tafara sakkowa daga stairs din.
Zama tayi inda nan suka shiga gaisheta da mata sannu da gida,amsawa tayi cikin dan damuwan dake kan face dinta tace"ya kuka baro jikin Galadiman?suma cikin alhini Sauban yace"Ummie jiki sai godiyan Allah,jibin dai za'a wuce dashi can,nima jibin zan koma office ana jirana,daga can nakesa ran naje na duba jikin nasa"Ummie ta girgiza kai tsce"Allah yabashi lafiya,kai kuma Allah yabaka ikon zuwan,dan duban gefen da Zuhra take tayi tace"kitashi ki zubo hado musu abinci mana.
Mikewa Zuhra tayi duk kunya ta isheta saboda bomshort dinda ta sanya tare da vest,cinyoyin nan katar katar sai juyawa sukeyi,a sace yake kallon ta,yanajin wani abu na taso masa,bata wani jimaba tadawo inda suke dauke da basket,juyawa ta kumayi taje tadawo da tray,inda plates,spoons da glass cup da bottle water suke da drinks ta ajiye,tana kokarin mikewa tajiyo muryan Ummie"kihada musu abincin mana.
Babu yanda ta iya nan tashiga serving dinsu,shikanshi sai da ya lumshe ido saboda kamshin abincin, Taufeeq kuwa kasa hakuri yayi yace"Little halan ke kikayi girkin nan?shiru Zuhra tayi tana murmushi,ganin hakan ya tabbatar masa da lallai itace tayi abincin"yi kizuba mana tun safe Muna asibiti bamu iya cin komai ba sai bottle water da muketa antaya ma cikin mu Ummie"Ummien tace"to ya za'ayi? hankali ne sam ba'a kwance ba.
White Basmati rice wanda aka dan watsa Kara's,grean beans nd parsley sai gasmeat Wanda sosai yaji kayan hadi,shi ta zuba ma kowa a plate dinsa,sannan ta samusu farfesun kan rago dai-dai,ruwa ta zuba musu a glass cup batare da ta zuba lemo ba,bismillah,ta furta wanda hakan ya zama sabon ta kuma al'adar ta.
Cikin natsuwa suka sakko kasa kan carpet suka fara jan girki.
"Ummie wanka zanshiga idan kinji shiru nayi bacci"Zuhra tafada hakan tana hayewa stairs,wannan karan ba Satan kallon ta yayi ba,bude ido sosai yayi yana kallon ta ko kunyar Ummien ma bayaji.
[7/9, 21:30] 𝐗𝐚𝐡𝐫𝐚 𝐗𝐚𝐡𝐫𝐚𝐭𝐭𝐲🥰: 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_* 👨🏽‍🦳

Page:- 67/68

_____Sosai suka ci abincin don ko wannen su sai da yakara sai dai Taufeeq yafi karawa da yawa don dama shidin yafi Sauban cin abinci sosai, Ummie ma tayi mamakin abincin da Sauban din yaci,cuz a iya sanin ta shi din ba ba ma'abocin cin abinci ne ba,bashshi da kayan snack's musamman pizza da Burger,haka suka gama cin abinci sai da yafada musu sannan Sauban ya dubi Ummie yace"Ummie bari naje na duba Ammi gud night"murmushi Ummie tayi tace"Au dama ba can kuka fara zuwa ba?tayi maganar tana musu hararar wasa, Taufeeq yace"ai tare muka dawo dasu Daddy so kinga shima yana bukatan kulawa,shiyasa muka tawo nan ke kuma ki bamu tamu kulawar"dariya Ummie tayi Sauban kuma na sakin murmushi,dan kwalla ta share a dalilin tuno da Abbie da tayi,Sauban har yafita sai kuma yadawo tare da tsayawa kofan palour yace"Ummie please idan babu damuwa coffee"yayi maganar yana dan marairaice face, Ummie tace"Sauban har yanzu baka dena shan coffee ba?
"Ummie ai sai dai arage" Ummie tace"ikon Allah to kaje zansa Zuhra ta hada maka"murmushin jindadi yayi"tnx my only Ummie"yayi maganar yan fita. "Zuhra! Zuhra!! Ummie ta shiga kwala mata kira,amsawa tayi tana sakkowa sanye da wani night gown har kasa maroon colour,ta ciki hannun vest ne,sai falmarar sama me gajeran hannu duk da ba kamata yayi ba sai dai da yake yadin silk ne irin me mannewa a jikin nan,a hankalin ta kariso"wayyo Ummie har fa nafara bacci"tayi maganar kamar me shirin kuka, Ummie tace"Kuma dole kitashi ba,dama yayanki ne keson coffee bani ba",da sauri Zuhra ta dubi Taufeeq tace"kai yaya yanzu fa wajen 11 ake nema"takarisa maganar tana mere baki da mutsitstsike ido,harar Taufeeq ya wurga mata,cikin sauri ta mike ta nufi hanyar kitchen din don duk a tunanin ta Taufeeq ne keson coffee din,bata wani jima ba tafito hannunta dauke da tray din coffee jug,gefe kananun glass cup din ne,a center table dinda ke gefensa ta ajiye.
Ummie tace"Sauban ke bukata ba Taufeeq ba kishiga kidauko mayafi kikai masa"a hargitse Zuhra ta dubi Ummie tace"innalillahi wa Inna ilaihirraji'un,ni Ummie ina zangan shi yanzu?wani harara Ummien ta galla mata me dauke da ma'anar ina wasa dake ne? Zuhra da kwallan ta tace"A'ah ta furta sannan ta mike tadau tray din tanaji kwalla yana taruwar mata,fita tayi daga palourn ta fito farfajiyar gidan kaitsaye apartment din Ammi ta nufa,koda tashiga parlour Laila ta gani tana waya cikin nishadi wanda kp ba'a fada ba kasan da wanda takeyi wato Shuraim,ganin Zuhra da tayi da niki-nikin tray yasa tace mishi bari tana zuwa,a dai-dai gabanta ta ajiye tray din tare da cewa"Laila ya Sauban yafita ne? Laila tadaga mata kai alamar eah tana kallon ta,dan narkar da face Zuhra tayi"please dan kira shi muji yana inane kice mishi ga coffee din"wani murmushi Laila tayi tana dan mere baki koda takira ba'a dauka ba,sai dai ko minti biyu batayi ba kira yashigo,dauka Laila tayi cikin mutunmtawa kamar yana gaban ta tace"barka Yaya",Bata jira amsar sa ba ta cigaba"dama coffee dinka ne Zuhra takawo nan ta zata kananan ne,magana akayi ta can bangaren,ita kuma ta amsa da "Okay bari na fada mata"takarisa maganar tana kallon Zuhra da tayi sagalo, Laila tace"Yaya yace yana tsohon apartment din shi kikai masa can"da sauri Zuhra ta mike tana dafa Laila"please sis don Allah ki kai masa"Laila ta dafe kirji like taga wani abin tsoro"Ni?ki rufamin asiri,in mutu maza su kaini salin alin,ai yasan dani be ce nahada masa,ke matar sa kece yaga dacewan ki hada masa,so kike a faffala min mari kenan?wallahi bazan kai ba"tayi maganar tana watsa yatsu, Zuhra tace"shikenan naji tom muje kirakani nakai" ja da baya Laila tayi"wallahi wallahi bazani ba karfe nawa yanzu ne da bazaki iya zuwa apartment din ba?yasan zaki iya zuwan ne shiyasa yace ace kikai masa can"tayi maganar tana hayewa stairs tare da dariyar shakiyan ci,mikewa Zuhra tayi tadau tray din tafita,kaitsaye sashen ta isa,sosai kirjinta ke wani irin luguden duka gabanta na tsananta faduwa,hannu takai ta fara knocking,sai da tayi sau biyu ana ukun ne aka bude,kan ta a kasa, kamshi St.ives body wash ne ya cika mata hanci,"idan kin gaji da tsayuwan kya shigo"yayi maganar tare da juyawa,shigowa parlour tayi duk da karami ne amma yayi bala'in haduwa sannan babu tarkace a ciki,sosai dakin yayi kyau,dagowa tayi da niyyar duban stool din da zata aniye tray din,gabanta ne yayi wani mahaukacin faduwa a dalilin Ido biyu da tayi da murdadden jikinsa,wanda banda glowing babu abinda yakeyi,ruwane a jikin yayi masifan kyau,towel ne daure a waist dinsa,cikin gaggawa ta runtse idanuwan ta,jikinta na wani irin rawa"idan kika zubar min da coffee sai na faffala miki mari,kikawo min ciki"shigewa bedroom din yayi ita kuwa zuhra tsaye tayi kirjinta na wani faduwa,tana tsaye har na tsawon minti bakwai,fitowa yayi sanye da wata designer jallabiya coffee colour tayi masa kyau gaya"i amذ your mate? Yayi maganar face dinsa babu alamun wasa ko miskala zarratan,takowa tafara,shi kuma ya koma ciki, shiga tayi ganin sa kan sallaya yasa ta sauke wani ajiyan zuciya,nufan inda bedside drower tayi ta ajiye tray din sannan ta juya da niyyar fita,gyaraln muryan da taji yayi ne yasata duban sa da sauri,raka'a biyu yayi batare da tasan zai sallame ba tayi azamar fita a dalilin shawarar da zuciyar ta tabata,fisgota taji anyi,a gigice ta kwalla kara,babu tsato babu tsammani taji mouth dinsa kan lips dinta,jikinta ne yafara rawa,ta kwalo idanuwan nan ta saka cikin nasa wanda shima itadin yake kallo,mutsu mutsu tafara hawaye na sakko mata,wani karfi ne yazo mata aiko ta turesa a dalilin sakin da jikinsa yafara"cikin kuka Zuhra tace"banyafe ba Kuma sai na fada ma Ammi kai ma dan iska ne,mugu azzalum.....bata karisa ba taji ya damki bakinta da nasa bakin,cikin salon mugunta yake tsotse lip's dinta,wani radadin azaba takeji a bakinta,sai dai kukan ma bazai yuwu ba banda hawaye,daka kalle fuskan sa da idanuwan sa kasan cikin bala'in bacin rai da hassaluwa yake,yadau tsawon minti biyar kafin yasaki mouth dinta,anan Zuhra ta zamiye tafadi kasa tana fashewa da wani irin kuka tare da dafe bakin,muryan sa ne ta sauya da tsantsan bacin rai"Duk randa kika sake cemin dan iska mugu azzalumi,wallahi ranar sai na miki abinda yafi wannan,ni sa'anki ne?akan hakkina kike neman zagina da min rashin kunya?stupid kawa dalla tashi ki hadamin coffee"jikin Zuhra na rawa ta mike,ga hawaye takasa denawa,zuba masa tayi takai masa bakin gadon,amsa yayi yana Kura mata ido,sosai takejin zafin kukan nata hakan yasashi lumshe ido yana kai cup din bakinsa tare da sipping,duk tana tsaye tana ahare hawaye,muryan shi tajiyo"kishiga toilet ki share hawayen ki ki wanke face dinki"yayi maganar cikin murya Shiba sanyi ba kuma ba fada ba,juyawa tayi ta shiga toilet tana ja masa Allah ya isa"Nike zagi?tajiyo muryansa,ai a kidime tajiyo tana me sakin wani irin kuka ganin ya taso"wallahi ni ban zage kaba"tayi maganar da muryan ta da yafara dishewa,rumfa ya mata yana hadata da jikin bango,cikin muryan kuka tace"please Yaya don Allah kayahakuri ban zageka b"gani tayi ya lumshe ido ya matso da bakinsa saitin nata sai dai me?jitayi yabata peck a forehead dinta yana matsawa,face din nan a daure,kamo hannunta yayi,wani laushi yaji me masifar dadi,sosai hankalin sa ya tashi,a makoshi yayi magana"muje na kaiki apartment din ku"binshi tayi kamar rakumi da akala,cikin izzan sa yake tafiya don shi mutum ne me zafin nama a haka ya kaita har apartment din Ummie,bude kofan parloun yayi babu kowa,wani ajiyan zuciya Zuhra ta sauki har sai da ya kalleta"what! Ya tambaye ta yana tsura mata sexy eyes din sa wanda lokaci guda sun sauya,girgiza kai Zuhra tayi da sauri"No... nothing"shima Sauban girgiza kai yayi"ban yarda ba,tell me the truth"Zuhra cikin shagwababbiyan murya tace"Nace fa babu komai,tayi maganar tana zumburo mouth gaba"sosai hakan yayi bala'in burgesa sai dai bazaka fahimci hakan ba"Okay oya let's go"yayi maganar yana nuna mata stairs,cikin sauri ta nufi stairs,sosai yake kallon yanda ass dinta ke kadawa,muryan sa tajiyo"Babu sallama?dan juyowa tayi tace"Gud night"da sauri takarisa hayewa,murmushi Sauban yayi yana lumshe ido,firgitacciyan fuskan ta yake hangowa sanda take cewa wallahi Yaya ban zageka ba,shafa sajensa yayi yana fita daga apartment din,ita kuwa Zuhra jingina tayi a jikin kofan tana dafe da kirjinta,sosai wani irin tsoron sa ya shigeta,kaitsaye toilet ta nufa ta dauro alwala, alqur'anin dake kan bedside drower dinta tadauka tafara karanta suratul Muhammad,bayan ta gama ta karanta Suratul mulk wanda hakan yazama al'adar ta, addu'o'i tayi sannan taja blancket,bata wani jima ba sai bacci.
Shikuwa Sauban koda ya koma shima Shirin bacci yayi bayan yayi addu'o'in sa sannan ya kwanta,kokarin bacci yake,Amma baccin yaki zuwa da ya runtse ido face din yarinyar yake gani"Oh my God, Sauban wat's wrong with you?yarinya karama ce fa, she's still young fa,idan ina lissafi dai-dai yarinyar nan zatayi 19?So why not am thinking about her?huh ya rabb,I know am not loving her"yayi maganar yana runtse ido da kyar bacci yayi awon gaba da shi.

********

Washegari kuwa duk sunje asibiti 'yan gidan Kama daga kan yara har manya,motoci biyar sukayi,ko wacce number mota sai kaga sunan G FAMILY muddin suka wuce ansan sune sai an daga musu hannu saboda temakon tsohon,wanda labarin laruran da yasamu har ya watsu a gari,mutane da dama na masa fatan samun sauki, Bodejo sosai take kuka a lokacin wajen 8:30 su Daddy da Abba ne zasu tafi kasar Malaysia da Galadima cikin muryan kuka Bodejo tace"haba Laure me Galadima yayi miki da ya cancan ci hakan daga gareki?mutum ne me kaunar ki tare da tsananin son ki amma akan jika kikayi sanadiyyar zamowan sa haka,meyasa?tayi maganar tana fadawa jikin Daddy, Daddy, Abba, Baba Hasheem duk rungume ta sukayi suma tana kokarin sasu kuka,sallama su Aunty labeeba sukayi,kaitsaye suna nufar gadon Galadima,suma kukan suka sanya suna fadawa jikinsa,wannan dalilin yayi sanadiyyar tashin sa.
Shima hawayen ne ke zuba kawai a idon sa,komai baya motsi sai kwayan idon sa yana murmushi,duk nufar sa sukayi, Aunty Maryam cikin muryan kuka tace"Bodejo me yasame shi hakan?mun tafi min barshi lafiya lou, meyafaru? Bodejo cikin muryan kuka tace"kaddara mairo komai ya faru mukaddari ne sai dai da sanadi.
Galadima kuwa kura ma Zuhra Ido yayi duk da murmushin nasa ba kowa ke ganewa ba amma angane,sannan yamai da duban sa ga Sauban yana murmushin,alama ya musu da kai dasu zo,don bakinsa babu halin magana,karasawa sukayi garesa,murmushi yayi yana girgiza kai alamun yana jin dadi.
Dr Ahmad ne ya shigo tare da wasu doctor's din, duban Daddy yayi"Alhaji Taleeb lokacin wucewan ku yayi yanzu 9:00,duk juyowa sukayi hankalun su nadawo wa kanshi,wani daga cikin Dr din yace"sunana Dr Amjad Aliyu tare dani zamu tafi"nan kuwa suka fara shirye-shiryen su,gabadaya shisshiga motan sukayi don rakasu airport,goma saura minti 7 suka isa airport din,nan Sauban da Taufeeq sai Abba suka shiga ciki don tayasu kimtse kimtse na visa da sauran su dama already anyi.
Karfe 10:40 aka fara sanarwan passengers,sosai Bodejo dasu Aunty Maryam ke kuka, Ammi da Ummie ma haka,sai Mommy da Mom ne suka koma rarrashi,sai da sukaga tashin jirginsu sannan suka nufi wajen motocin su,hannun ta taji an kamo a tsorace ta juya,kamar ba shine riqe da hannun nata ba don fuskewa yayi gabadaya,ita kuwa Zuhra a tsorace take tsananin kunya ya kamata,ga fargaban kada wani ya gansu sai dai abinda bata sani ba shine, Baba Hasheem, Ummie Bodejo, Mom duk sun gansu,sakinta yayi tashiga mota tare dasu Aunty Mashahuda don Taufeeq ne ke jansu, Mashahuda, Laila, Muneefa, Nihal,ita.
Sai motan Sauban Baba Hasheem, Bodejo,sai dayar motan Aseef keja Mom ce a ciki,dayan kuma Aunty Maryam keja Ummie, Ammi,sai dayan Aunty labeeba keja Mommy ce sai kuma yara da akasa a wasu motocin,haka suka tafi abinsu gunin sha'awa.

Koda suka koma a sashen Bodejo aka yada zango,nan aka shiga maida magana, Mom ce tashiga bada labarin abinda yafaru tun daga zuwan Zuhra da zuwan su Ammi dasu Daddy sashen Sauban din da abinda suma suka gani,sai zuwan Guggo Laure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login