Showing 24001 words to 27000 words out of 103469 words

Chapter 9 - GALADIMA FAMILY Complete Hausa novel

07 Sep 2024

6878

ta galabaita itama sannan mutuwan Abbie ba karamin girgiza ta yayi ba,takasa mance maganganunsa wadanda sosai su sukafi tasiri a zuciyar ta( _Bilkisou inaso kisani bana fatan na mutu banga kin daidaita da Zuhra ba._ ) sosai wannan maganar yake dawo mata a kai saboda sosai tafara tsorata da lamarin nata ita kanta hakan yasa hawayen idaniyar ta suka gaza tsayawa.
Ammi ne da Mommy da Mom suka kariso tare da kama Ummie kaitsaye apartment din Abbie nanan suka nufa don su Amma da hajiya Zainab suna can zaune.

Zazzabi ne me zafi ya saukar ma Zuhra saboda kukan da tasha gashi har muryanta ya dishe,mijin Aunty Safeena da mahaifiyar shi sai yayyen shi mata su biyu sunzo don Shuraim ma yajawo su a motar,su kansu sun tausaya ma ahalin musamman ma Zuhra don da alama Abbie irin mutanen nan ne masu tsayawa a rai.
Koda Zuhra tafito don su gaisa da Shuraim kasawa tayi saboda kukan da yaci karfinta,ga abinci da sam ba cinsa take ba.

Tabbas Galadima jarumin tsoho ne don kaf 'yayan sa yafisu dauriya kukan zuci kawai yakeyi wanda kowa yasan yafi na fili azaftarwa da radadi.
A ranar Aunty Labeeba itama ta diro da mijinta sosai fa gida ya cika.

*MALAYSIA*

Sosai yashiga rudu da tashin hankali da rasuwar Abbie din,don har Saida zazzabi me zafi yanemi kwantar dashi,duk da a bayyane ba lallai ka fahimci hakan ba.
Sosai Abba ya kwantar masa da hankali duk da yaso yazo kasar a ranar amma baisamu izinin haka a wajen na sama dashi ba dole ya hakura,sanar dashi halin da Ummie tashiga shima sai yasake gigitashi.

A haka yadinga dai zuwa office din zazzabi nata cinsa a tsattsaye,duk da kullum cikin video call yake da Taufeeq ko Ammi akan jin halin da Ummie ke ciki.

******

Bayan kwana uku da rasuwar Abbie,anan ne wasu daga cikin dangi da 'yan uwa suka wawwatse sai dai na jikinsa suna nan.

Anan Daddy yakira meeting parlon Galadima,sosai kowa ya halarta a cikin ahalin gidan,Banda Guggo Laure dai,'yayan Galadima kawai ake bukata.
Nan Galadima ya bude taro da addu'ah yayi addu'o'i wa Abbie, Daddy kuma ya amshe.
Nasiha maishiga jiki yafara yiwa Ummie,tare da sanar da ita abinda dan uwansa yamutu da burin ganin yacika shine shiryawan ta da diyar ta Daddy ya cigaba"Sadeeq yace muddin kika ja marainiyar Allah a jiki kingama masa komai,ga Hashim nan abinda yadinga maimaita wa kenan kafin Allah yadau rayuwansa yakuma CE shi yayafewa kowa don bashi da kullin kowa a ransa.
"Bilkisou kiji tsoron Allah ki kula da diyarki ki cikama abubakar burinsa mudai a iya saninmu baki da matsala kuma Alhamdulillah a kullum abubakar cikin yabon kyawawan halayyarki yakeyi illa matsala guda shine wannan matsalar,Wai ko kin manta Zuhra nada ciwon zuciya ne?kinsan dalilin da yasa a koda yaushe abubakar ke debe mata kewa kenan?don Allah menene matsalar bilkisou?
Cikin muryan kuka Ummie tace"inason ta amma narasa meyasa nakejin tsanar ta? wallahi ina kewanta da begenta sai dai sam banaso ta rabe inda nake.

Gyararan murya Abba yayi yafara magana"Ina ganin Yaya kamar maganar Yaya Sadeeq gaskiya ne da koda yaushe yake cewa shi yana zargin sihiri a lamarin,nima kuma gaskiya na sake a minta,da sauri Aunty Maryam tace"wallahi kuwa Yaya nima haka nake gani.

"Hmmm nidai nace saboda taya uwa zata ki danda ta duka ta haifesa?sannan ko son da aka haifi Zuhra Bilkisou na tsananin son ta daga baya ne komai ya canza,Ammi tayi maganar.
Shidai Taufeeq kansa na duke don shikadai ne a yaran gida yake parlon.
Baba Hashim yace"toh me zehana anemi malamai masana addinin islama aji ta bakinsu?

"Wannan gaskiya ne Yaya, cewar Labeeba.

GALADIMA ne yayi gyaran murya,gabadaya wajen yayi tsit magana yafara kamar haka.


Xahratty CE🥰
Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️

14/03/23.
[3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳

Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now

*_GALADIMA FAMILY_*

Page 21-22

_Bismillahir-rahmanir-raheem._

___Sosai GALADIMA yayi nasihohi masu shiga jikin duk wani wanda yake zaune a wajen,inda a ka tsaida magana za'a ma wani aminin GALADIMA magana dake wani kauye anan maidugrin don masanin harkan sihiri ne kuma yana bada magani sosai,nan aka sake yiwa juna gaisuwa kafin kowa ya watse.

Bayan kwana daya,ana masu amsan gaisuwa suka cigaba da tururuwar zuwa,hajiya Biba ma tazo ganin yanda Galadima family yasake tsaruwa ne yasa tasake kudira a ranta cewa lallai yakamata Rammat ta shigo gidannan,sawa tayi aka kaita sashin ammi,anan fa tadinga fadanci a wajen Ammi tare da yabon halayyan Sauban.
Ammi tacika da mamakin hajiya Biba amma sai sam bata nuna ba,itakuwa Mom ta cika tayi Damm saboda yanda taga hajiya Biba na neman kwanta ma Ammi tayi wuff tace.
"Hajiya kizo muje kiyima iyalen Abbie gaisuwa mana.
Mikewa hajiya Biba tayi Rammat tana bayanta itama cike da kissa ta rissinawa Ammi tana mata sallama.

Kaitsaye apartment din Abbie nanan suka isa sosai hajiya Biba tanuna jimaminta,itakuwa zuhra tana rakube gefen Ummie jikin kafar Adda zainab.

A haka rayuwa ta cigaba da tafiya har yau gashi bakwan rasuwar Abbie a ranar ne kuma Sauban yadiro garin babu zato bare tsammani,idan kallesa baka isa ka tantance a yanayin da yake ba sai dai fuskar sa da take a dinke,ta gabanshi tazo ta wuce cikin sanyinta long hijjab ne a jikinta brown colour yayi mata kyau sosai,fuskar ta daka kalla kasan mutuwar tana dukanta.
Ta wutsiyar Ido yabita da kallo har tashiga wajen Ammi,kaitsaye shikuwa apartment din Ummie yashiga bakinsa dauke da siririyar sallama,da Ummie suka fara hada ido,ai tuni tasaki kuka mai tsuma zuciya,da sassarfa yakariso gareta da sauri ya kama mata hannu.
"A'ah Ummie don Allah kada kiyi kuka Abbie insha Allah ya dace,ko nima so kike kisanya ni kukan Ummie?please.

Girgiza masa kai Ummie tashiga yi tanajan gunjin kukan hawaye wani na riga wani muryanta na rawa tace"Sauban Abbien yara ya tafi ya tafi yabarni da nauyij zuhra ya zanyi please?
"Kiyahakuri don rashi mungriga da munyi Allah yajikan Abbie ubangiji yasada sa da rahamarsa.
Da Ameen 'yan dakin suka amsa don a yau zasu bi jirgi su koma har da Ummien ma don tace can kaduna zata koma,shima Abba da mommy zasu tafi.

******

"Zuhra kifa dunga cin abinci koko so kike ki dora ma kanki wani lalurar? Ammi tayi maganar tana jawo Zuhra.
Hawaye ne yashiga yimata sintiri, Laila takama hannunta"Zuhra please kici abincin kinji?ko so kike kitayar ma da mutane hankali?
"Rashin Abbie bake kadai kikayi ba amma tabbas ke zaifi miki zafi kiyahakuri, Nihal takarisa maganar.

"Yawwa ku kwantar mata da hankali, Laila maza kishiga dakina kidaukomin makullin dakin yayanku da aka gyara masa dazu.

Mikewa Laila tayi tanufi bedroom din Ammi don dauki keys din.

Cin abincin kawai takeyi badon tanajin test nashi a bakinta ba,sallamar mommy ne yasasu dagowa.
"Zuhra yanzu kika fara cin abincin ne?mommy tayi maganar.
"Eah mommy yanzu nafara.
"Ok to kiyi kigama zamu koma kd yanzu tare da Ummien ki kizo muje kiyi mata sallama.

"Nidai mommy kubarta tatafi don Allah nidai ina gaisheta".Tayi maganar cikin sanyin murya.

"A'ah haba zuhra taya mahaifiyar ki zata tafi kice agaisheta? a'ah tashi kije kiyimata sallama.
"Ammi inajin tsoro ne please Ummie tace nadena bari tana ganin bakar fuskata,tayi maganar hawaye suna zuba.
Kamota Ammi tayi taahare mata hawayen sannan takama hannunta tace"Hauwa muje nasan sun fito tun dazu ko?
Mommy tace"sunanan wajen mota.

Farfajiyar gidan suka fito inda su Mom, Bodejo, Amma Adda Zainab suke tsaye dasu Aunty Maryam,zuhra kanta a kasa tana tafiya idanuwanta ya cika taf da hawaye.

Har gaban Ummie Ammi takaita,da dan hanzari Ummie ta matsa,duk wadanda ke wajen basuji dadin hakan ba,cikin rawar murya zuhra tafara magana.
"Ummie ku gaida gida Allah yatsare, Allah yakara hakuri da juriya",tana gama fadar haka tajuya tatafi.

'yan labba Ummie kawai ta amsa,anafa kowa yafara musu sallama don ya Sauban ne zai kaisu airport,mota biyu sukayi dayar Aseef kejanta,haka suka jera sukayi na airport din.

Haka suka tafi suna dagawa juna hannu, Ummie kuwa haka tadake saboda kukan dake neman kwace mata,hajiya Amma tadan dube Ummie tare da tabe baki taciro medical glass dinta ta sanya tare da kankance idanuwa.
"Yanzu ke fisabilillah Bilkisou bazaki iya daukar diyarki takoma hannunki ba?kijata a jiki?
Nannauyan ajiyan zuciya Ummie ta sauke tace"To Amma taya zan daukota alhalin school tafara zuwa anan?kuma Abbie nata shida kanshi suka yanke hukunci dasu Galadima da Yaya kan tadawo nan.
"Yo ba dole ba?ai dole suyi haka,kada kinemi sabauta masu diya,kinga ko babu komai sun nuna miki sunfiki sonta da sanin darajar ta,ance tana fama da ciwon zuciya zasu barmiki itace ki karasa musu?takarisa maganar tana kawar da fuskanta kamar ba itace tayi maganar.
Duban Adda zainab Ummie tayi tace"Adda don Allah kiyima Amma bayani ta fahimceni bawai fa banson zuhra bane.....
"Kinga Bilkisou ni babu wani bayani dazanyi miki kiyi kokari kawai kija diyarki ajiki,tayi maganar tana sake tamke fuska.

Sosai Ummien nashi tabashi tausayi saboda ganin yanda duk suke mata kallon mai lefi.
"Ni Amma sai nake ganin kaman maganar su Yaya da gaskiya da sukace lamarina da yarinyar can kamar akwai sihiri a ciki.
Gyara zama Amma tayi tamaida hankalinta wajen Ummie tace"ko Bilkisou?
Daga kai Amma tayi tace"Ea nima kuma sai nafara zargin hakan,saboda me zuhra tayimin ne da nake mata haka?nice fa uwar dana tsuguna na haifeta...
"Kinji Kuma wani magana Amma?asiri kike nufi?to taya za'a muku asiri?kudai kudena daukar wa kanku jita-jita da zargi kuna sanyawa zukatanku,wallahi Bilkisou duk lefinki ne amma kinki yarda ai shikenan.
A daidai nan suka kariso filin jirgin.

Duk firfitowa sukayi daga motar,anan Amma kecewa bataga Taufeeq ba,shine Abba yace ai Galadima yace yabari sai jibi yakoma.
Murmushi kwance a saman fuskar Amma tace"Haroun kunadai nema ku kwace duka yaran su koma maidugri da zama,ba za'a bar mata ko guda daya bane anan?
Shima Abba cike da dattaku yace"a'ah hajiya Amma taya za'a kwacesu?ai Bilkisou tananan a gidanta shima Taufeeq din sako yatsaya ya amsar mata wajen Galadima.

******

Duk cikansu sunyi jugum suna sauraren babban Aminini Galadima, tsoho Mai ran karfe shima masani ne akan abinda ya shafi sihiri kuma yana karya sihiri da yardan Allah yazama kamar ba'ayi ba.
"Lallai lallai muhammadu farraqu akayima yarinyar nan da uwarta don bokan da yayi wannan aikin bakaramin ahedani bane,sannan a yanzu haka ba zaiyuwu in karya asirin ba har sai anje kasan gadon ita mahaifiyar yarinyar andauko wani tukunyar kasa wanda aka tsafacesa sosai akawo.
"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un!!!!sautin dake tahi Kenan a babban zauren Malam Baba.
A kofar shiga sashen nata gefen fulawoyi shima anhaka rami anbinne wani abu, wallahi muhammadu ban isa nakarya wannan abin ba har sai an binno wadannan abubuwan don tabbas wacce tayi wannan abin ta zalincesu kuma taci amanar su.
Bodejo tace"Malam Baba itakuwa wacece wannan?don Allah kafada don a hukunta ta.
Dan murmushi Malam Baba yayi yace"ai hajiya bodejo fadar baida wani amfani saboda lokaci na dauka wacce tayi abin da kanta zata kawo kanta gareku amma tabbas hatsabibiya ce.
Daddy yace"lallai koma wacece mu bazamu yafe mata ba Allah ma yagani.
Duban Taufeeq Malam Baba yayi yace"yanzu malam Taufeeq Kaine aikin nan ke gabanka,zaka iya?.
Cike da kwarin gwiwwa Taufeeq ya dagama Malam Baba kai yace"anya kuwa?saboda anason mai dakakken zuciya wanda sam bashida tsoro,yakarisa maganar yana kurawa Taufeeq Ido.
Shiko tsakani da Allah Taufeeq yariga yasan kansa akan tsoro don haka sai ya girgiza kai.
Murmushi Malam Baba yayi yace"toh kunemi wanda zaije Taleeb,idan kunyanke hukunci kubashi wannan man yashafa,man zaitun ne dana habba akayi mishi hadi da magunguna"yakarisa maganar yana dauko wata 'yar kwalba wacce sai kamshi take zubawa inda yacce da andauko ko kwana biyu kada abari yayi ba'a kawo masa ba.
Sosai sukayi mishi godiya inda anan ne kuma akasa almajiran Malam Baba suka dinga shigo da buhunhunan abinci,dama duk shekara Galadima na aiko masa da zakka amma wannan ihisani ne kawai.
Daddy anan yabashi dubu hamsin, Baba Hashim yakara mishi da ashirin.
Almajiran kuwa Galadima yaraba musu 'yan dari bibbiyu.

Anan akayi sallama suka baro kauyen su Bodejo sukayi cikin gari,da yake mota biyu sukayo a mota kowa da abinda yake sakawa,basu suka shigo gida ba sai bayan isha'i.

****** *KADUNA* *****

Anguwan rimi kaduna gidane hadadde na gani na fada sai dai ko kai gidansu Ummie beyiba.
Hankalinta atashe yake banda gumi babu abinda takeyi jikinta har rawa yakeyi tana magana.
"Hajiya Aliya don Allah kidena wannan maganar asirina nagab da tonuwa fa,nidai mushirya muje nijar din tunkafin su sa akarya musu asirin nan,kina gani a lokacin da akayi wani irin asara ne banyi ba na kashe kudade da kadarori.
"A'ah ba nufina kenan ba ai ba asara bane tunda bukata ta biya nasani amma wallahi banaso akarya nibanki har Bilkisou tabar gidan duniyar nanba batare da tashirya da diyar ta ba.
Tadan tsagaita saboda maganar da ake acan bangaren.
"Toh menene?wancen ma ba maradin mukaje ba?nidai bukata kawai nake nema,ke ko nawane zan iya kashewa idan har zan samu abinda nakeso.
Magana aka cigaba da mata tacan bangaren.
To Shikenan kikirashin don Allah bakiga yanda na tsure ba inama taoro ne kada asiri na ya tonu,wallahi nayi zawo babu adadi tsaban tsoro.
Nagode nagode hajiya Aliya babu abinda zance miki don kina temakona.
Aje wayan tayi tana sauke ajiyar zuciya,gumi kuwa haka yake tsattsafo mata.
( _Itakuwa wannan ni fatsima🤔 reader's ko ku kunfahimci wacece ita?_ )


Xahratty CE🥰
𝐋𝐚𝐥𝐥𝐚𝐢 𝐀𝐥𝐪𝐚𝐥𝐚𝐦𝐢🖊️𝐘𝐚𝐟𝐢 𝐭𝐚𝐤𝐨𝐛𝐢🗡️

19/3/23.
[3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳

Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now

*_GALADIMA FAMILY_*

Page 23/24

_Bismillahir-rahmanir-raheem.


_____Acan gida kuwa bayan Daddy sun dawo daga sallar magrib anan suka sake tattaunawa inda Sauban ya daddage akan shine zai ciro duk abubuwan nan da akace don Taufeeq sosai ya tsorata yakuma nuna tsoron nashi a bayyane.
Duk sunji dadi,anan aka yanke hukuncin jibi Sauban zasu koma dasu Aseef don daga Aseef har mahaifiyar shi babu wanda yasan halin da ake ciki.

*****

"Gaskiya Guggo kiyi dagaske inba haka ba Sauban na gab da subucemun, Akeela tayi maganar tana turo mouth gaba.
Dan harara Guggo Laure ta aika mata dashi tace"inyi dagaske?ko kema kiyi da gaske?bari kiji inaso ki shirya kikoma gidan da zama sannan ba sasan kowa zaki sauka ba saina Aisha,ke bakisan zamanin ba saida kissa da kisisina?
"Amma Guggo kinsan Daddy da wuya ya yarda sai dai idan ke zakiyi mishi magana.

"Badole ya yarda ba?yanzu kije kihada duk wani abin bukatanki yanzu zansa waya nakirashi,saboda da wuri nakeso kije gidan,koda nida kaina ma zankaiki.
Akeela tayi murmushi tace"yawwa Guggo dama ke yakamata kikaini.

"Aiko zankaiki kedai jeki hada kaya yanzu zankira manseer din a wayata,cike da farin ciki Akeela tafita tanufi gate kaitsaye dama ana jiranta a waje,Suby tabita da wani kallo tace.
"Wallahi kina ruwa akeey kinsan mommy daharatu tana fushi dake tunda taji ansa miki ranar aure?tace kin munafunce kungiya? wallahi babu ruwana.
A razane Akeela take duban Suby wani mulmulallen ashariya tasaki"kutumar ubancan uban waye yafada mata? wani munafuki ne zai sanar mata?
Wani banzan kallo Suby tayi mata tace"lallai ma akeey kinmanta abubuwan da kika dingayi a tiktok da IG dinki?magana tariga tanata trending a social media?har 'yan bakin ciki suna bayyana kawunansu.
"Mtsewwww to wallahi babu Wanda ya isa ya hanani aure kamar yanda babu wanda ya isa yahanani neman mata da binsu,ina son aure don kinsan nidama nimai son harkan nanne inason wancan abinma,haka kuma inason madigo,to aknme ban matsama wani ba wani yanemi matsamin.
Kinga rakani naje wajen mommyn inshawo kanta nasan harda takaicin rashin ganina da batayi bane kwana biyu.

Suby murmushi tayi tace"lallai akeey wai kinmanta mommy da sharrin ta kenan?juyar dakai Akeela tayi inda banda bugawa babu abinda kirjinta keyi.
"Hmmm Suby nifa inaso ma nadena wannan harkan kwatakwata tunda Allah yabani miji wanda babu abinda yarasa.

Suby tace"kina nufin zakibar kungiya?to kindebo ruwa kuma komai tayi miki kece kikaja.
"Naji don Allah mubar maganar nan.

Washegari wajen karfe 7:30 su ya Sauban suka nufi filin jirgi,a lokacin ne babu jimawa Guggo Laure da Akeela suka isa Galadima family,sosai Galadima da Bodejo bsukayi mamakin ganinsu,don shi Galadima ma yana bedroom dinsa Zuhra na matsamai kafafuwa.
Cike da natsuwa take tafiya koda tashigo parlon kallo daya tama su Guggo Laure ta kauda kai saboda wani irin kallo da Akeela ta aika mata dashi,cikin natsuwa tasamu kusa da Bodejo ta zauna tace"Bodejo barka da safiya Ina kwana?
"Lafiya Lou Zuhra harkin gama matsa masa kafafuwan?

"Ea nagama don har na hada masa ruwan wanka yashiga kema yanzu zanje na hadamiki.
"Yawwa Allah yamiki albarka yabaki miji nagari mejin kanki da kaunar ki.

"Ameen Bodejo na,tayi magana kaitsaye tare da mikewa tace"bari nashiga wanka saboda zanje school"duban Guggo Laure tayi tace.
"Guggo kune da sammako haka?sai kace wacce ake koranki daga gida?tayi maganar cike da zolaya.

Guggo Laure tace"nida gidan mu?ai babu maganar sammako anan Fatima kinsan da zafi-zafi ake bugun karfe.
Murmushi Zuhra tayi tace"gaskiya ne to sannu da zuwa,tana gama fadar haka tanufi dakinta.
Basu dade da zama ba Galadima yashigo inda Bodejo tashiga hada masa breakfast,duban Akeela tayi tace"tashi kihado muku abin kari.

Dan yatsina tayi tana mikewa tanufi kitchen din Bodejo tana wani karairaya uwa zata balle tanufi kitchen din.
"Laure kece da safennan haka? Allah yasa lafiya dai?

Dan murmushi Guggo Laure tayi tace"Yaya muhammadu kenan kunata fadin sammako kamar wacce tayi asibanci?nikam maganar yaran nan yakawoni......au Wai kaji,tayi subul da baka.
"Au Akeela nakawo nan ta zauna koda sati biyu ne zuwa uku tayi anan tafara sabawa da gidan duk da gidan su ne.
Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Bodejo da Galadima.

Sauke ajiyan zuciya Galadima yayi yace"toh ai Shikenan sai su zauna da Zuhra a dakin zuhran koh?
Da sauri Guggo Laure tace"A'ah ba haka za'ayi ba,ni nace taje can,tanufi wajen Aisha ta zauna tadinga tayata ayyuka abubuwan bukata ko kuwa?
Gwalo idanuwa Bodejo tayi cikin mamaki tace"a bangaren surukar tata zata zauna?tun kafin akawo ta gidan?
Dan tabe baki Guggo Laure tayi tace"Toh menene aciki? Aisha fa uwarta ce koda kuwa ba maganarta da Sauban.

Dan murmushi GALADIMA yayi yace"Laure kenan ninakan rasa a Ina kika samu wannan wayewar kamar jinin fulani baya yawo a jikinki,ita Aishan tanuna miki bukatan son akeela tazo ne?koko tace miki bata da maid's ne?

Guggo Laure tatsuke fuska tare da kankantar da idanuwa tace"yanzu munkoma gida kenan?to ai shikenan babu komai takarisa maganar tana latso hawaye tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login