Showing 33001 words to 36000 words out of 103469 words
da bacin rai har neman number suby takeyi bata samu ba har kwallan takaici tayi.
Sai wajen karfe takwas Ammi taga dai shiru shiru bata fito ba gashi za'a ci abinci amma babu ita duban Daddy tayi tace"Oh ni Aisha koyau Akeela lafiya bata fito ba,tashi Mashahuda kikirata kice tazo tayi dinner.
"Please Ammi kirabu da ita wallahi ba yunwar takeji ba da tanajin yunwa ai zata fito yin dinner din, Mashahuda tayi maganar tana yatsine face.
Dagowa Ammi tayi da niyyar sake mata magana wayar Daddy yafara ringing,ganin sunan Guggo Laure yayi cikin dattaku ya amsa kiran tare da fara gaisheta ko aya bekai a maganar ba tafara zazzaga fada.
"Taleeb wai me akeso a maidani a gidan nan ne naku?yanzu fisabilillah wani ahalina bashi da iko a gidan nan har bare ace yafishi?
"Subhanallah Guggo meyafaru ne haka?
"Yanzu ramatu ne ta yayyarfa ma Akeela mari waye ubanta?dangartakan me mukedasu da har tasamu wannan zarrar?sosai Daddy kanshi ya kulle yarasa wacece take magana akai,cike da kamewan sa yace"Guggo wacece kuma ramatu wallahi bangane maganar da kike akaiba.
"To bari nasanar maka da abinda ke faruwa,nan Guggu Laure tafada Daddy duk abinda Akeela tace mata ta ida zancen da cewa"kuma wai saboda raahin mutumcin irin na rabi a gabanta akayi komai amma ta kasa kwabawa.
Nannauyan ajiyan zuciya Daddy yasauke tare da bawa Guggo Laure hakuri sannan ya cemata itama Akeela bata kyauta ba don kawai haka tafaru ta tattaro kayanta tadawo gida sam beyi ba ko bata fada musu abinda yafaru ba ai ta musu sallama.
"Yo taya zata muku sallama tunda an sakota gaba da musifa tunda akace ansa ranar ta da Sauban makiya keta bayyana kawunan su gabadaya ansata a gaba.
Shiru Daddy yayi tare da mamakin halayen Guggon nasu nakin gaskiya sam ita batason gaskiya kuma bataso ka gyara mata kuskurenta komai kankantar sa.
"Shikenan Guggo kiyahakuri insha Allah za'a wa tufkan hanci,nan sukayi sallama.
Cikin bacin rai Mashahuda ta dubi Daddy tace.
"Wallahi Daddy sam Akeelan nan bata dace da Yaya ba,kuma wallahi bataji fa"wani mugun kallo Ammi ta watsa mata wanda yasata Jan bakinta ta dinke.
A bangaren Ummie kuwa sai nan nan sukeyi da Zuhra ita da Amma har ma dama-dama Amma tana sakin mata amma sam takasa sakin jiki da Ummie duk da kuwa yanda Ummien ke nuna kukawar ta agareta,mikewa tayi tare da cewa"Ummie bari naje na amso abincin ku wajen Bodejo wai tasa ayi muku faten alkama takarisa maganar batare da tajira abinda ko wannensu zaice ba,da kallo duk suka bita dashi.
Ummie ta sauke wani nannauyan ajiyar zuciya tare da goge 'yar kwallan da ta taru mata tace"kingani ko Amma? Zuhra bazata taba sakin Jikinta dani ba sam,duk wanda ya shiga tsakanina da diyata haka tsawon shekarun nan bazan taba yafemasa ba ko wanene.
"Kiyahakuri bilkisou aikomai a hankali ake binsa kuma a hankali zata saki jikin nata dake,inace ba yau bane aka warware komai?to komai zai dawo dai-dai yanda baki tunani ki kwantar da hankali,insha Allah ninarasa meyasa mu number addanku duk idan nakira baya shiga.
Tayi maganar tana me latsa layin Adda Zainab din,cikin sa'a kuwa taji tashiga.
"Kinga kuma tashiga bari muji lafiya kuwa.
Daga can bangaren akayi picking call din,nan suka shiga gaisuwa anan Amma ke sanar da ita abinda ke faruwa sannan tafada mata tana maidugrin.
Sosai tanuna jajantawar ta tare da alhini ta Kuma ce insha Allah Alhaji yau idan yadawo zata taho gobe da sassafe.
Anan sukayi sallama da junan su inda Adda Zainab tacika da tsananin farin ciki don ko babu komai burinta na gabda cika koma tace yacika,landanan ta latsa kiran aminiyarta hajiya Aliya anan ta sanar da ita yanda sukayi da Amma.
Itama taji dadi ta Kuma ce lallai tafiyar da ita za'ayi don aiwatar da aikin yanda ya kamata,sallama suakyi cike da kosawa ma garin ya waye.
*WASHEGARI*
Su Adda Zainab tun 7:00 suka fita amma basu suka isa ba sai wajen 6:30 sosai suka wahala don motar haya suka bi inda suka samu tarba na girma da kulawa.
Sai da aka bari sukayi wanka suka ci abinci sannan aka fara gaishe-gaishe har sashen Galadima sukaje don mika gaisuwan su agareshi,cike da dattaku ya amsa sannan suka koma sashen Ummie nan aka dasa hirar yaushe gamo inda Zuhra tadan saki jikinta sosai don hajiya Aliya macece mai barkwanci da ban dariya,itadai Ummie na kwance akan hadadden gadon ta, Zuhra ne tashiga toilet din Ummien.
Tadan bata lokaci kafin tafito tare da duban Ummie tace"Ummie ga ruwan wankan can nahada miki da komai da komai a ciki",cikin jin dadi ta dubeta tace"tnx my lovely daughter Allah yama rayuwar ki albarka.
Da ameen duk 'yan farlon suka amsa.
Ammi tace"kawa muje sashen Bodejo na dan taba hira nadawo",Zuhra tace"to muje.
Ummie ma mikewa tayi don shiga wankan,kallon juna Adda Zainab da hajiya Aliya sukayi tare da sakin murmushin jin dadi,bayan tashiga toilet din dama maganin na jikin zanin Adda Zainab da sauri ta kwantoshi tare da mikewa dai-dai inda suka ga Ummie nasa kai nan suka daga pillow din tare da dan yaye gefen bedshit suka cidda duvet still akasan bedshit din,suka sake daga duvet din sannan suka tarda matress din,cikin sauri suka barbade maganin tass tare da barbajeshi.
Nan sukq maida komai normal tare da duban juna duka saki dariyar jin dadi,cikin sauri suka fita dakin tare da nufar masaukin su.
**********
"Barki kiji hajiya Laure nibazan lamunci cin zarafin ki ba akan yara,ni ina ruwana da abinda yashiga tsakanin Rammat da Akeela?da Akeela da Rammat duk abu daya ne a wajena......
"Karya kike Biba ba haka kika daukesu ba,me kike nufi ko kiso ko kada kiso Akeela jinin Sauban ne kuma aure kamar anyi angama.
"Hhhhhhhhh casss! Auren da auren manufa zaki hada?ai Yaya Laure duk wanda yayi hulda dake yasan halinki ciki da bai,dadin abin ragowa zai sama don nasan duk rashin jin diyata bata aikata munanan lefukan da jikanki ke aikata wanda ko karya sai haka.
Bude baki Guggo Laure cike da mamakin irin kalaman hajiya Biba"Biba nizakiwa sharri kiyiwa jinina?wallahi sai nabaki mamaki sai na nuna miki dani kike zance.
"Ina sauraren ki nidake kafasa,kuma niba sharri nake mata ba gaskiya nafada amma kijira lokaci komai zai bayyana kansa"! Tana gama fadar haka tajuya tashige daki tare da rufe kofar.
Nanfa Guggo Laure tashiga zage-zage sai tsinewa Rammat albarka takeyi ta kuma ce tajira taga abinda zai faru sai ta bata mamaki.
Hartana kwallan ta tsaban takaici haka tajuya gida.
*******
Banda nishi babu abinda kakeji natashi a dakin hajiya daharatu,da ita da Akeela ne suke aikata masha'arsu cikin kwanciyar hankali.
Hajiya dahara sai sumbatu take"please baby kada kibar ni koda kinyi,don nima inason abinda kikeso don Allah ki kara rikeni gam"nan ta cigaba da shirmenta Akeela nataya ta gabadayansu haihuwar uwayeensu da ubayensu( _wa'iyazubillah! Allah yakawo mu zamanin da aikata sabo yazoma ba abin komai ba,don Allah 'yan uwa me muke nema da wannan rayuwar?meyasa muka mance cewa duniya bafa ma tabbata bace? meyasa muke mance banda wannan rayuwar akwai wata da zamuyi anan gaba?Wai mun mance wancan rayuwar ba'a ciwo ne?ba tsufa ne?haka zalika ba'a mutuwa ne?duka ba'ayi,in wuta wutane idan aljanna aljanna ne straight babu kwana......don Allah 'yan uwa muji tsoron Allah mufa dunga tuna duk rintsi akwai mutuwa kuma dole ko wane mai rai yadandani nacinta.Yau ina annabi Adam AS?Ina annabi Ibrahim AS ina annabi Yusuf AS ina shugaban annabi Muhammad SAW? Duk cikansu sun koma ga Allah,to shin kai waye da bazaka koma ga Allah ba?ya Allah kajikan magabatan mu,kajikan iyayen mu,kajikan muπ€²π½ya ubangiji kayima na karshe mekyau._ )
++++ *MALAYSIA* ++++
Zaune yake a office dinsa kunnensa makale da waya sai dariya yakeyi"ah haba Galadima sai kace wani ragon namiji?wai me kadaukeni ne tsohon nan?nafa fika jarumta wallahi kaima kasan haka,dariya yasakeyi kana ya cigaba "To ya jikin Ummien?Masha Allah,aidama ita sai a hankali zata sakewa da ita Allah dai yakara lafiya da tsarewa,yanzu zan shiga meeting ne Galadima I will call yhu back,katse Kiran yayi yana mikewa tare da gyara suit din dake jikinsa.
ππππππππ πππ₯°
πππ₯π₯ππ’ ππ₯πͺππ₯ππ¦π’ποΈ ππππ’ πππ€π¨ππ’π‘οΈ.
03/5/23.
[5/7, 14:18] Xahratty (OUM AJMAL): π¨π½β𦳠*_GALADIMA FAMILY_*π¨π½βπ¦³
Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*
Marubuciyar‡οΈ
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now
*_GALADIMA FAMILY_*
Page:- 33/34
_Bismillahir-rahmanir-raheem._
_____'Yan mata da dama sun mutu akan soyayyan Sauban a kasar sai dai wasu masu aji basu iya tunkararsa,wasu ko tsoro da shakkan sa ne yasa basu iya yimasa magana,wasu ko da kansu suke kai kansu office dinsa har sai da yahana sakatariyan shi bari ashigo saboda rashin hankalin 'yan matan yakoma bashi tsoro matuka,ya maida hankali sosai akan aikinshi daga can bangaren kuma yaron mai company din na shirye-shiryen dawowa zai amsa mukamin Sauban,dama can nashi ne rashin kammala master's din nasa ne ya hana abashi kujerun yana America karatu.
**** *NIGERIA* ****
Ummie kuwa a natse tafito daga bayin bayan ta kammala wankan,cikin nutsuwa tashirya tasanya wata Dubai gown fara tass tare da mayafinsa mai Kama da hijjab don har hannayenta ya rufe mata, gadon ta nufa tafara dube-dube sai dai da alama bataga abinda take nema ba, dai-dai lokacin Zuhra tayi sallama tashigo hannunta dauke da basket din kayan abinci,ajiyewa tayi tare da nufo inda take saboda ganin yanda taketa bincike.
"Ummie lafiya?ko wani abun kike nema ne? dagowa Ummie tayi fuskar ta dauke da alhini tare da mamaki tace"Wai casbaha na nake nema amma ko sama ko kasa babu shi kuma akan bed din na ajiye don ko sanda nayi sallan magrib anan na aje gefen pillow dinnan amma kinga babu,gashi na kaku dana tada sallar,tayi maganar tana cilla pillow din gefe guda.
"Ummie please kije kiyi sallan bari naduba kafin ki idar angani.
"Ok my baby! Ummie ta ambata tare da tayar da sallan,nanfa Zuhra tayi dai- dai da gadon harda su yaye bedsheet da duvet din sai can gefen saqon tsakanin matress din da gadon tagani aiko tajawo tare da kokarin maida duvet din,fasawa tayi tare da sake yaye kayan shimfidan ta kakkabe kan katifar sosai tayi mai tatas sannan tadau bedsheets din da duvet din taje can corridor dinda zai sadaka da toilet tabude laundry basket ta saka su,adai dai nan Ummie ta idar da sallan.
Ikon Allah Zuhra daga neman casbaha sai Kuma a bige da gyaran gado? murmushi kwance akan fuskar ta tace"Ummie wallahi sunyi datti ne naga sosai ga kuma datti harda kasa-kasa akan katifar shiyasa nacire"takarisa maganar tana bude closet,wanda bangare guda yake shake da bedsheets colours mabanbanta,duvets nd etc.
Jawo wani tayi colour daya da wancan sai dai zane ne ya bambanta shima sai kalura ne zaka gane,wannan karan bata dauko duvet ba dama akwai wanda take lulluba dashi still a gefen bed din,shinfidawa tayi takuwa liliye gadon tsaf tare da sake gyaggyara pillows din,bayan ta kammala tajawo stool gaban kujeran da Ummie ke zaune ta ajiye,tana kokarin dauko basket dinne takatseta"Kinga ai kan carpet zan sauka naji kafata nayimin tsami,kije kikira addan ku kice nace suzo ga abincin idan kuma a kawo musu ne to.Zuhra tace.
"Ok bari nasanar dasu,tayi maganar tare da fita,jingina ummie tayi da jikin gadon tare da rufe ido a haka taji sallamar zuhra.
"Ummie sunce gasunan zuwa,babu kuwa jumawa da shigowan ta sai gasu suma sun shigo,da sauri Adda zainab tanufo ummie fuskanta cike da murmushi tace"bilkisou har kin fito wankan ne?Ummie tace"aiko nafito Adda ai ko kafin nafito naga kuntafi.
"Ea muma munje muyi sallan ne,hajiya Aliya tace"sannu hajiya bilkisou ya jikin naki? Ummie tace"Alhamdulillah ai naji sauki wallahi.
"To Masha Allah Allah dai yakaro mana lafiya dai,ubangji yabarki da diyarki"tayi maganar tana me shafa kan zuhra tana dariya.
"Hajiya Aliya kenan Amin nagode.
Nan Zuhra ta shiga zuzzuba musu abincin kowa na zabar abinda zaici, kallonta Ummie tayi tace"baby ke kinsa abincin kinci?
"Ea Ummie naci tare dasu Bodejo da Amma aimu faten alkaman Bodejo mukasha,Kinga kuma itama Amma tanada diabetes in so sai yau akayi danan yawa,kuma fa nasa musu wadataccen kayan ciki.
Adda zainab tace"ah lallai diyar albarka kinaji da wadannan kakannin naki,nikuwa bilkisou yanzu kindena cin dan gauda ne?dariya Ummie tayi"mekika gani Adda?
"A'ah tambayace kawai naga kwana biyu banjin labarin dan gaudan.
"Uhummm Adda kenan shekarun da yawa inaji rabona da cin dan gauda tun sanda nakeda cikin Zuhra,kuma Allah inaso cinshi sosai.
Kama baki hajiya zainab tayi"cabb!gaskiya shekarun da yawa,Anya kuwa wannan ko kingani zaki iya ci kuwa ma?
Dariya ummie tayi tace"ci kuwa sosai,inafa son shi don kawai bansamu bane,kai duk da haka ma nina mance da wani abu wai dan gauda.
"Aikuwa insha Allah gobe da sassafe zan dauki driver muje kasuwa munemo garin dan gauda don acan zan siya masara ta kuma nabada nika a hada min komai da komai sai dai dana tashi nazo nayi miki,yajin ma musamu wanda yaji tafarnuwa don nasanki da son tafarnuwa,takarisa maganar tana dariya zuciyar ta fal nishadi.
Nan ko suka cigaba da hirarsu suna dinner abin gunin sha'awa.
Washegari kuwa kamar yanda hajiya zainab ta alkwaranta haka ne tafaru don wajen karfe sha daya na safe tafara kwabin dan gaudan ta tayi na ummie daban sannan ta kwaba nata dasu Bodejo daduk dai me sha'awan ci, zuhra na tayata,babu bata lokaci ta cewa zuhra tacigaba da zuba dan gaudan da wannan yayi za'a zuba na ummie ne.
_____________
"Tab ai wallahi kinbani kunya Akeela kitsaya wannan yarinyar ta farfada miki magana haka?babu abinda ke cinta sai bakin ciki da hassada dole tasan kika mallaki guy dinnan kin mata fintinkau,na gaba yayi gaba na baya ai sai tsintar hula,aike dai kibari kawai zamuyi maganin tane karamar 'yar iska"Suby tayi maganar tana karkada kafafuwa.
Akeela tasauke wani ajiyan zuciya tace"ni ba wannan nake tsoro ba kada watarana tace zata tonamin asiri kunsan fa tasammu farin sani ta kuma san abinda muke aikatawa.
Tabe mouth zuleey tai tace"to sai mene?su da babu abinda suka sani sai Shan minti da samari fa?abi wannan saurayi abi wancan.
"To ai inaso kisan nata me sauki ne akan namu namu yafi nata muni,wallahi ni da ace wani a cikinsu zaiji wannan labarin to nida shiga GALADIMA FAMILY matsayin mata wallahi sai gani sai hange don bazasu taba bari na aure ya Sauban ba,shiyasa nakeso Allah nadena wannan harkan fa don ni duk abinda zai shiga tsakanin aurena da ya sauban gudunsa nakeyi don rasa sa wallahi babban asara ne kuma bazan jura ba,wallahi na rasasa zan iya mutuwa.
Wani harara zuleey ta watsa mata a ranta tace" _Hmmm indai ina raye bazaki taba auren saurayin da nake mafarkin aura ba tunda nataso nasan waye Muhammad Taleeb Muhammad Sauban yatafi da imanina,muddin bazan sameshi ba wallahi kema bazaki taba samun saba._
Suby tace"Lallai Akeela keko wani irin so kike ma Sauban haka?kinmance ba'a hada soyayyar mommy data kowa?ina guje miki randa zaki juyama mommy baya don kuwa kinsan sai kinshiga cikin gagaruman matsala.
"Huhhhh! Suby don Allah kukasance koda yaushe cikin yimin fatan alheri ba fatan tsiya ba,meyasa kuke kokarin fasamin kwanya ne?inaso kugane cewa ko wanne da matsayinsa a waje na,amma banaso Kuna hada soyayyar ya Sauban data kowa please"takarisa zancen tana bata face.
Da mamaki duk suka dubeta,zuleey tace"harda ta mommy?wani banzan kallo Akeela ta watsa mata tace"bansaniba mtsewwww,wallahi zuleey kwana biyu kaman kina neman zama munafuka ce,inafa lure dake kina kokarin shiga tsakanina da Mommy wallahi shiru kawai na miki,hmm kicigaba.
"A'ah dakata mana Akeela"zuleey tayi maganar tana mikewa"akan me zakice min munafuka?menamiki na munafunci?kidubi tsaban ido na kicemin munafuka?ko a girme na girmeki kibar ganin ina binki kamar rakumi da akala wallahi bashi zaisa na dauki cin zarafi ba.
Itama Akeela a fusace ta hayayyako mata"kada Allah yasa kidauk......
"Guys!guys!! Haba meye haka?kun manta mudin suwaye?meyasa kuke kokarin bawa haters damar shiga tsakaninmu?gaskiya banji dadi ba,gaskiya banson haka inkuwa ba haka ba sai atafi wajen mommy.
"Bama sai anje ba!!duk su biyun suka hade baki,murmushi Akeela tasaki tace"Shikenan kiyahakuri zuleey,fuskan zuleey kadaran kadahan itama tace"Allah yabaki hakuri tana kare fadar haka tamike tare da daukan jakanta tadubi Suby tace"ni zan wuce gida yanzu Suby.
Murmushi Suby tayi"Lallai zuleey Ashe baki huce ba?babban matsalata dake dama riko,meye amfanin hakan a tsakaninmu?
"Ba maganar riko bane Suby zanje gida don nasan hajiya zatayi ta zuba idon ganina yanzu.
"Shikenan kigaida gida sai munyi waya,Suby tafada.
Akeela tace"adai yayyafewa juna akara hakuri,ko tankata zuleey batayi ba tafice tanajin zuciyarta namata wani irin tukuki.
Tabe baki Suby tayi"banziya munafuka ainaji dadin abinda kika mata don yanzu Suby karfi da yaji takoyi munafunci da hassada" Akeela ta dubi Suby tace"Ashe kema kin fahimta?ai sainayi maganinta batasan ina raga mata bane saboda hater's kiris suke jira.
Anan dai suka shige daki tare da rufo kofar rufff!
*GALADIMA FAMILY*
Sosai Ummie tadinga santin dan gaudan mai da yaji don yayi dadi sosai,suma su Bodejo kadan suka dan tsakura.
Washegari su Adda zainab da Amma suka tattara komatsan su tare da Sha tara na arziki drivern Daddy yadaukesu don maidasu gida, Amma zata sauka gidan hajiya zainab ta kwana biyu sai takoma Zaria.
Haka rayuwa yadinga tafiya tun ana abu saura kwanaki satittika watanni har takai dai yau saura 1month da 3 week's biki,indai aikin ya Sauban kuma yakoma Canada,aka bashi matsayin chairman na branch dinsu na Canada saboda sam basu fatan abinda zaisa su rasa sa matsayin ma'aikacin su jajirtacce mai amana, kafin kace me har ya Sauban yasake zama celebrity,kudi kuwa sun zauna masa sosai su Daddy ke alfahari dashi,shima ya taufeeq yasamu aiki a Abuja yana aiki a CBN, Aseef nedai har yanzu yake lecturing din a ABU wanda hakan sosai yake taba zuciyar Mom,kuma haryanzu bin malaman suke daga ita har hajiya Biba amma babu nasara don Sauban din ma baidawo kasar ba ballanta na aikin yatafi yanda akeso.
A dai-dai wannan lokacin ne Kuma akatafi yajin aiki wanda yasa su Laila da nihal dawowa maidugri,su tattaro kayansu gabadaya a sashen Ummie suka tare saboda yanda gabadaya take sangarta 'yan matan.
Mom tunda ta fahimci muneefa zata shiga gidan masu arziki kuma manyan mutane sai ta dora ma ranta salama tadena maganar wani hadin Sauban da muneefa kamar yanda ita takeso,don a zahirance iyayen yaron Suma sunada kudi sosai ga asali da nasaba.
________
"Hajiya don Allah kidena wahalar da kanki akan Sauban shidin yafi karfina wallahi ba ajina bane nasani kema