Showing 42001 words to 45000 words out of 103469 words
jerin ahalin karuna ba idan har abinda nayi niyyar basu bazai musu ba sai dai subar hidimar da zasuyi.
"Calm down! Friend abin bana daukan zafi bane haka,please kabisu a sannu nisam banason abinda zai sanya kabata ma kanka rai ka bata mata ita.... wayar ce aka kara Kira, Sauban ko kalla beyiba duk da face dinsa bazaka ga mahaukacin fushin nan ba,Kareem ne yayi picking call din.
Cikin muryan shagwaba tare da karairaye murya,gyaran murya Kareem yayi yace"bashi bane amarya,barka da Rana amaryan bakya lefi koda kin kashe dan masu gida.
Batare da gaisuwa ba Akeela tace"uhum Kareem kenan,nace please sweetheart din baya kusane kadauki phone din?dan murmushi Kareem yayi ta hanyar danne bacin ransa yace"aiko baya kusa yabar wayan a dakina ne kafin yaje yadawo but insha Allah idan yadawo zan sanar masa kinkirani"Da sauri Akeela tace"no ba wani abu bane dama tuni akan maganar hidimar kawaye naje haryanzu baku nemesu bane kuma time na tafiya ya kamata abasu abinda kikace.
Kareem sosai yasan abokin sa magana daya yakeyi daganan baya canjawa"kingani Akeela abinda yasa bamu nemeku ba maganar gaskiya Sauban yace bazai iya bada 10 millions ba,idan kuma kum matsa sai hakan tofa sai dai ku fasa hidimar taku.
Wani kululin bakin ciki da takaici Akeela taji ya ziyarce ta lokaci guda,tanaso tayi rashin kunya amma tsoro ya hanata,cikin karfin hali"Yanzu fisabilillah a ganinka Kareem ya kamata Sweatheart yace bazai bani wannan kudin ba?me akayi akai 10 millions please?meyasa yakeso yamaidani wata karamar yarinya wajen friend's dina?alhalin ansan wanda zan aura Muhammad Taleeb Muhammad nefa haba haba,dage kafada Kareem yayi tamkar tana gabansa yace"to kinji nidai abinda yacemin kenan kije kiyi shawara don yace daga 3 millions bazai kara wani abu b.....batare da yakarisa abinda zaice ba daga bangaren Akeela yaje tace"Kutumar uban can!!! Atake anan kuma wayar ta gimtse alamun ta gane katobarar da tayi kenan.Wani dariya Kareem ya kunshe saboda tabbas tasan Akeela ba irin tsarin macen da abokinsa yakeso bane,dogon tsaki Sauban yayi tare dayin kwafa batare da yace komai ba yamike ya shiga toilet.
Acan kuwa gidansu Akeela tabotsare sai masifa take zazzagawa a dakin Guggo Laure tare da kuka,tana fadin itafa Sauban baya sonta,sosai hankalin Guggo Laure ya tashi ranta ya baci matuka amma haka ta danne gudun abinda zaije yadawo taja Akeela cikin dakinta tare da fara kwantar mata da hankali,nan fa tafara lallashinta magana tafara mata kamar haka"inaso ki saurare ni kiji da kyau, ni babban matasalata dake wutan ciki taya bikinki saura kwanaki kifara bacin rai da hayaniya? Cikin muryan kuka Akeela tace"Haba Guggo ni sam abinda guy dinnan yakemin sam baya min dadi,haka sauran mazan suke?koko don yaga ina son shi shiyasa yake min haka?nikawai Guggo kisa mallakemin shi sai abinda nakeso za'ayi"Ajiyan zuciya Guggo Laure ta sauke tace"Ai wannan dole ne kisha kurumin ki dama kina tunanin zamu barshi haka ne?ai wallahi bazai yuwu ba,gashi yaro Yana neman zama mante malloniya,dole ya zama na yana tafin hannu mu mune muke juyasa wanda ko Aisha sai tarasa kwanciyar hankalin ta,cikin tsananin farin ciki Akeela tasaki dariya"yawwa Guggo na shiyasa nake matukar son ki nufa kin fimun Mom wallahi,domin Mom bata damu da damuwa ta ba"... Mtsewwww! Don Allah dena tadin wannan shashan wake maganar ta?cewan Guggo Laure.
Wayan Akeela ne yayi ringin cikin sauri tadauka"hello baby's ya akayi ne?daga can bangaren aka amsa"ok to bari nazo dama ina sasan Guggo ne amma ganinan fitowa,takarisa maganar tana mikewa wayar kare a kunnenta tana fita,cikin jin dadi Guggo Laure ke duban ta don ko babu komai tana mata murnan shiga ahalin GALADIMA FAMILY,a fili tace"Wane Mujaheed?ai Akeela ba tsarar ka bace,kuma ba sa'ar ka bace,duk da nice nan na haifi iyayen ku amma kuma da banbanci"Guggo Laure tayi maganar tana wurgama iska harara.
Dai-dai sanda ta isa wajen su Suby alokacin wayar ta tadanyi kara alamar message yashigo cikin wayar,cikin zumud ta dago wayar tana dubawa,sai dai abinda taci karo dashi yasa murmushin nata gushewa,da karfi ta furta"kan ubancan,lallai ma mutanen nan nizasu maida wata 'yar iska wai ko mene?jibi don Allah Suby,tayi maganar tana mika mata wayar ta.
"Wai iya kacin abinda suka turo kenan?Suby tayi maganar tana duban wayar,cikin hasala Akeela tace"Gashi kuwa kina gani,amma gaskiya ba'a mun adalci ba,inada hidima fa sosai,ga event din gobe,ranar Friday Kuma kamu haba!tayi maganar tana yatsine fuska.
"Ai shikenan sai kiyi maleji da abinda yasamu kawai muma abamu kasammu,wani banzan kallo ta aika mata dashi"bangane me kike nufi ba,abaku kasanku kamar Yaya kenan?bata fuska Suby tayi tare da kura mata ido.
"Ea mana ko kinmanta ana bawa kawaye wani abune?aka idama kudin nan bata account dinki ya kamata a turo ba, account din daya daga cikin mu zaki bayar mukuma muyi yanda mukeso da kudin"Zuleey tayi maganar tana tamke fuska"kwarai kuwa zuleey amma kinji abinda yarinyar nan ke cewa, Akeela wai me kika maida mu wawaye ko menene?
Sauke ajiyan zuciya Akeela tayi tana kokarin danne bacin ranta"A tunanina million 3 bazai hadani da ku ba amma tunda kun matasa zanbaku 200,000 naira shikenan?
"A'ah wallahi bazamu amsa ba ya mana kadan,inama lefin kibamu 1 million mu biyu?
"Wallahi bazan iyaba,inama lefin 500,000?da wanne zqnji ga Kama hall da sauran su, Zuleey tana kokarin magana Suby ta hanata ta hanyar yi mata magana da ido,badon ranta yaso ba haka tadannne.
"Okey to kuzo muje mufara tsare-tsaren yanda komai zai wakana,don inaso muje gidan mommy ne ko kuwa?dukka amsa mata sukayi da hakane.
********
Tarasa dalilin da yasa take tsintar kanta cikin bacin rai a duk sa'ilin da taji anyi maganar auren Sauban din,hakanan takejin wani kunci na ziyartarta tare da tsanar Akeela matuka a ranta,shikuwa mugun haushinsa takeji,a kullum cewa take bacin hadene dana su Aunty Mashahuda da wallahi bazata zauna ayi bikin ba,kai ita duk wanda taga yana rawar kafa akan lamarin na Sauban shima haushinsa takeji.
Shigowa Laila tayi don bata jitaba,zama tayi tare da makama cinyar ta duka,da firgici tadago tana dubanta, ajiyar zuciya ta sauke"zuwa nayi nace miki kitashi muje mu amso dinkin mu,gasu ya Taufeeq zasu sauke mu a shagon"bata fuska tayi"Gaskiya nibazan bisu ba idan ku zaku bisu ku bisu amma ni adaidaita zan samu,takarisa maganar tana mikewa don shiga bathroom"Ummie tace nazo na fada miki idan kuma naje nabata amsar hakan to,tayi maganar tana mikewa tsaye.Cikin sauri Zuhra ta dawo tana shan gaban Laila tare da tsuke fuska"ni ban aikeki ba kice mata ganinan nashiga wanka ne,tayi maganar tana juyawa cikin sanyin jiki, dariya Laila ta kunshe tana me fita.
Bata wani jima a toilet dinba ta fito ta shirya a gurguje don tasan basu fiye son delayed ba yayyen nasu,ba wani kwalliya tayi ba a fuskar ta,Dubai gown Army Green ta sanya sai sneaker black tayi Rolling kanta,dan karamin hand bag dinta baki tadauka tafita da sauri,ilai kuwa tana fita ta hango Laila da nihal a parking space jikin motar ya Sauban,wani kululin bakin ciki da bacin rai taji ya taso mata lokaci daya,harara Laila ta aikamata tace"Zaki gamu dasu Yaya wallahi babu ruwan mu kin bata musu lokaci,bata kulata ba suka bude motar suka shiga, Taufeeq ne ke driving,shikuwa Sauban laptop ne akan cinyar sa yaketa sarrafata,gaishesu sukayi duk suka amsa,cikin barkwancin sa yadube su"Allah yasa telan be mata muku dinki ba,don nasan teloli sai addu'ah,cikin raha Laila tace"Ai Yaya Ameer ya iya dinki sosai,tun daga Zaria yazo yima su Aunty Mashahuda dinkin biki,namune be gama ba yace sai munzo da kanmu,jinjina kai Taufeeq yayi yace"Ah gaskiya ne tunda aka dauko tun daga Zaria to lallai nima na sheda,don nasan gimbiyar tawa bata za6en tumin dare ko gimbiya?yayi maganar yana duban Zuhra ta jikin mirror motan,dariya Zuhra tayi wanda sai da point nata ya loma,sannan Gap teeth dinta suma suka samu damar bayyana,lankwasar dakai tayi cikin shagwaba tace"To yaya maganar saloon din bamuje bafa, gashi gobe mother's day,kuma mu a goben ne zamu henna ko?tayi maganar tana duban su nihal,daga mata kai sukayi gabadayansu,nihal tace"Kuma ranar Friday kamu ba! Zuhra tasake shagwabe muryan"Yes yaya and kamu.
Tun sanda ta fara magana tatafi da duk wani kuzarinsa lokaci daya yaji wani kasala ta kamashi,banda bugawa babu abinda zuciyar sa keyi,shekara da shekaru kenan yake karya ta abinda zuciyar sa ke raya masa,sam takasa tunkarar wani da maganar balle yasamu sassauci,lumshe idanuwa yayi cikin natsuwa wanda mutum bai isa yagane ya yanayin sa ba.
Cikin taushe tare da basarwa yafara ma Taufeeq magana batare da ya dubesa ba"inada baki da zasuzo,wasu daga maleysia wasu kuma daga Canada so ina bukatan hotel me kyau sosa and sai dai niban san kan hotel's din garin nan ba,jinjina kai Taufeeq yayi yace"Gaskiya nima bansan kan hotel's din garin ba sai dai mukira Kareem kan ya bincika mana,let me call him"yayi maganar yana jawo wayar sa daga aljihu,jinjina kai Sauban yayi batare da yayi magana ba.
Zuhra kuwa ajiyar zuciya take ta sauke wa a boye batare da kowa ya fahimta ba,dai-dai lokacin da suka iso shagon dinki me tsananin kyau don dama yasan shagon shida kanshi yake dauko Mashahuda ya kawo ta.
Bude kofan sukayi suka fito tare da rufo musu kofan,tsayawa Zuhra tayi gefen Taufeeq duban ta yayi yace"to yanzu maganar saloon din zaku wuce ne, idan mundawo zamu biyu ta shagon mu dauke ku,jijjaga masa kai Zuhra tayi,kudi yaciro a aljihu wanda shi kansa besan ko nawa bane yamika mata,godiya suka masa gabadaya suka shiga shagon.
Ta wutsiyar ido yake hankalce da duk wani motsinta da wani babbasar wan da takeyi.
Kai tsaye shagon suka shiga,basu jima ba suka fito dauke da kayan su Ghana most go guda medium,an dinka a goge duk da sunso dudduba kayan amma ganin mutanen dake cikin shagon yasa suka hakura,don Zuhra a takure take abinda ta tsana kenan a rayuwar ta,har bakin titi Ameer ya rakosu suka samu napep sannan yajuya,kaitsaye shagon saloon din suka isa me suna saleema hair beauty saloon matar tana da matukar kirki,gashi tana tsananin son Zuhra,basu jima ba bayan magrib suka gama ana Shirin Kiran isha'i,turama da Taufeeq address din Zuhra tayi,babu kuwa bata lokaci yadawo,wannan karan shi kadai kuma ta map ya dinga bin address din.
Kudin saloon din yabiya sannan tadauki kayansu yasanya musu a cikin boot,kaitsaye suka isa gida.
_________
Washe gari
Biki yayi biki inda labarin event din su Akeela kawai akeyi,maisuna suger mommy's day,sosai suka kashe kudi a event din wanda akayi a gidan hajiya daharatu,wato mommy, sosai ranar 'yan less sukayi iskancin da suke so, Akeela kuwa a daren mutane uku sukayi masha'arsu da ita,sun cancare matuka gaya,sai karfe ukun dare suka watse.
A dai-dai kuma wannan lokacin aka tura ma da Sauban video.
Xahratty CE🥰
Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️
7/6/23.
[6/8, 21:41] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽🦳
Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*
Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now
*_GALADIMA FAMILY_*
Page 43/44
_______Ganin bakuwar number ce yasa yadanja siririn tsaki tare da kin bude message din a fili yafurta"Trash! Yana takaicin 'yan matan dake bibiyan sa wadanda sam basu da aji balle ayi maganar kamun kai,wayar ya ajiye a side yana mikewa tare da shiga toilet don dauro alwala,saboda Sauban mutum ne mai rukon addini tsantsa shiyasa lokuta da dama yake jin dan sanyi a zuciyar sa.
Washegari da safe GALADIMA family suka tashi da shirye-shiryen mother's day,Ammi,Ummie,Mom,Mommy sunyi kyau sosai don babu wacce bakinta basu zoba musamman Ummie don da kawayen ta na kaduna da Zaria,haka ma Ammi kowa dai yatara mutanen sa,kanofi uku aka kakkafa,duk wannan shagalin su ZUHRA basa gidan suna can wajen henna,sun hada mother's day dinsu yayi masifar kyau,duk da iya kacinsu ne don ko maza basu shigo gidan ba, security ma suna can gate 1,haka zalika sunsa police mata kan su kula duk wacce tayi video Koda waya ne to aka mata,duk da cewa ba badala sukayi ba,sunyi wanka mahaukatan lace hadaddu,da Ammi da Ummie lace dinsu iri daya white,sai Mom da Mommy kuma orange sunyi kyau abinsu matuka,bodejo da Amma ma sunyi kyau cikin lace dinsu suma,inda Aunty Maryam da Aunty labeeba suma suka sanya coffe din lace, Adda zainab dai tana hanya tare da matan yayyen Ummie biyu basu kariso ba.
Haka aka gama shagali lafiya inda kowa yatashi yana tsananin farin ciki tare da kyaututtuka.
Sukansu amare sunyi matukar kyau inda acan company taje gidan ko wacce tayi mata danki,gidan muneefa Masha Allah kamar yanda na Mashahuda kuma baya faduwa ya kawatu,kananun magana ne yafara tashi saboda ba'a ga anyi dankin Akeela ba sai yau zasuje suyi.
********
"Hmmm suby kina kallon abinda Akeela take mana? kuma mu zuba mata ido?sauke ajiyar zuciya Suby tayi tace"To zuleey me kikeso ayi?zubanya mata ido zamuyi komai zai wuce by the grace of God cuz ayi komai agama lafiya.
"Shikenan Suby yanda kika ce haka za'ayi,muje mu cigaba da shirye-shiryen mu kinga kudin ma a siyayyan kayan daki na kyale kyale ya kare,sai dai tabar 1 million na dinner gobe da tarban jama'ar mu duk da nasan wannan abune me sauki mommy tace zataji da wannan.
Haka suka cigaba da zantukan su inda zaka fahimci zuleey tana cikin matukar damuwa tare da bacin rai don bini-bini kadan sai ta duba wayar ta,sai dai gnin babu alamlun message yasa ta basar tare da saka wayar a jaka,anje anyi dankin gidan Akeela,wanda ya gaji iya gajiya,tsaruwa da haduwa kuwa ba'a magana,anan jikin gidan akayi gidan,kayan dankin ne dai basu dace da gidan ba,don ma apartment din Sauban dabanne da abin kunyar yafi yawa,domin apartment din shi yayi balai'n haduwa komai oder ne, itakuwa Mashahuda a j
K.d akaje akayi danki waje yayi balai'n haduwa, muneefa ma gidan ta yayi kyau sosai.
Yau ta kama Friday kamu aka shirya guda narwa a Galadima family,amare sunyi kyau matuka gaya,anan ne su Aunty Maryam suka tura su Laila gidan su Akeela akaimata kayan kamun,don dama an amsa majorment nata,Anko sukayi su uku inda,angwayen ma sukayi ankon arniyar danyen shadda sky blue,su kuma amaren net ne sky blue su Aunty labeeba suka musu dinkunan.
Wajen ya kawatu matukar kawatuwa,baka tatan su Suby suka tsinta maganar don su sun zata zasuyi abinsu daban ne,abinka da waje babba fili ne dake bayan gidan Galadima wanda yake mallakinsa,an katangeshi tare da zuba interlock da shuke shuke,lokaci guda masu decoration suka canza masa kamanni yakara wani masifar kyau da tsaruwa,kawayen Akeela da 'yan uwanta guda goma aka bukata,kamar yanda aka bukaci na ma'aruf saurayin muneefa,sukuwa sauran abinka da abu nasu ba'a maganar 'yan uwa,su Suby suma sunyi shigansu na tatattun 'yan duniya itada Zuleey anko sukayi.
Waje fa ya hadu ya tsaru matuka gaya babu abinda kakeji na tashi sai sautin kidan wakar namej me taken "dama".
*****
Kwance take akan gadon Ummien sam bata da alamun tashi ta shirya balle ayi maganar fita,su nihal sunyi maganar har sungaji sun wuce tare da wasu cousin's dinsu agemate, Ummie ce tashigo tana sanye da wata lace maroon tayi matukar kyau face nata dauke da tsantsar fari'a,turus tayi taja tatsaya tana duban ZUHRA cike da mamaki tace"Zuhra zaman me kikeyi anan?kowa yanacan yana watsa idanuwan ganinki ke kina nan kina kwance.Turu mouth gaba tayi tace"Ummie kaina na ciwo ne shiyasa ma banfita ba kuma bazanje ba,takarisa maganar tana sake gyara kwanciyar ta"Lallai to wallahi baki isa ba shashancin banza,yayanki sai kirana yake akan be ganki ba ke kuma kinzo kinrashe?maza² kitashi ki shirya kiwuce tun kafin raina yabaci,haba babyn Ummie kinaso ki batama sweat broo din naki rai ne ranar farin cikinsa?
Girgiza kai Zuhra tayi tana me mikewa badon ranta yaso ba,nan Ummie ta cigaba da lallabata da lallashinta don ta fahimci tunda bikin gidan yakarato take cikin kunci da damuwa,a gurguje tafito ta shirya cikin wani hadadden yadin rose white sai net dinsa wanda Ameer ya zauna ya tsattsafa mata wani street gown me daukan magana,abinka dame kirar cikakkiyar halitta,shape dinta yayi balai'n fita,light make-up tama kanta,tashirya tayi matukar kyau,takalmin high heel shoe me siraran igiya tasanya a 'yar karamar kafanta wanda yaji jan lallen salatep,fitowa tayi cikin takunta me daukan hankali,nan tanufi sashin taron,duk da kowa zaune yake a mazaunin sa amma shigowan ta yasa da yawa hankulan su ya koma kanta,haka abokan angwaye ma, half-caste skin dinta shima yasamu damar sake fito mata da ainahin kyanta,kananun magana ne yadan fara tashi.
Akeela kuwa ganin Zuhra ba karamin baci taji zuciyar ta tayi ba,jitayi kamar ta tashi ta shaqe ta don wallahi ita kanta da take amarya tasan yarinyar tayi bala'in finta kyau nesa bama kusa ba,wani banza kallo tashiga aika mata dashi zuciyar ta na tsananin tatarfasa, Zuhra kuwa ko kallon inda amare da angwaye suke batayi ba babu zato taji sallama ta gefen kujeran da take zaune,duk da kujeru uku ne table a tsakiya amma ita kadaice,dagowa tayi don jin muryar sa,murmushi suka sakin ma juna one time,da ido ya mata alama da ya zauna?cikin cool nd sexy voice dinta kamar me rada tace"yep have a sit,murmushi suka sake sakinma juna,shima yayi kyau sosai Shuraim don babban rigan ta masa kyau gaya.
Wani bacin rai yake tsintar kansa a ciki amma haka yaketa dannewa har aka fara Kiran angwaye da amare su fito suyi rawa,duk da a takure yake jinsa sai dai hakanan yadaure yakamo hannunta suka sauko suma filin,dai-dai yadago idanunsa itama ta dago,ido cikin ido yasan ya mata musamman ganin yanda take hira cikin nishadi da kwanciyar hankali,basarwa tayi ta hanyar dena duban ta tana sake maida hankalinta ga Shuraim dake ta bata dariya.
Tunowa tqyi da Taufeeq cikin hantsari ta dubi Shuraim,excuse me! just give me five minute"daga mata kai yayi masu ma amare manni sun ragu,a dai dai lokacin da aka saki sautin wakar "luwaiiii" na Ado gwanja,tafiya tafara tana karkada jikinta cike da jan aji da basarwa tabude pos dinta ta ciro 'yan dubu-dubun da Daddy yabata tafara manni,aiko nan aka saki tafi tare da shewa,rike hannunta Taufeeq yayi suna rawar cike da natsuwa tare,ai nan danan Nihal da Laila suma suka fito,sun burge mutane da dama,don shi kanshi ya Sauban sun matukar burgesa.
Akeela kuwa face dinnan ansake cureshi lokaci guda,kafin kace me