Showing 21001 words to 24000 words out of 103469 words

Chapter 8 - GALADIMA FAMILY Complete Hausa novel

07 Sep 2024

6882

ta kafa daya kan daya tana duban tashar aljazeera, Abbie ne yayi sallama tare da shigowa a hankali tadago tadubesa dan murmushi tayi tace"Sannu da zuwa yallabai.
Murmushi Abbie yayi cike da zolaya yace"Yauwa yallabiya,zama yayi kusa da ita da yake cushion din two seater ne cike da gajiya yace"Am tired Madam.
Dan dariya tayi tace"Toh bari naje na hada maka ruwa kayi wanka zakaji dan dama then sai kaci abinci kadan kwanta stressed ne kwana biyu baka zauna ba yallabai gashi jibi zaka tafi Indonesia.
"Wallahi kuwa akan furnitures din su Mashahuda nakeso naje kinsan bikinsu 6 month akasa su ita da muneefa, shiyasa ma nakeso muje tare nida ke mu zabo musu kaya masu kyau,harda kayan kitchen.
Ummie tace"iyye lallai Abbien yara ya shirya to shikenan Allah ya kaimu amma bazamu kawo komai gida yanzu ba ko?
Abbie yace"to me za'a tsaya jira Bilkisou ai gwanda a kawo komai nasan kilama kayan su rigamu isowa. Kafin kuma na auta na yazo Allah yanuna min auren ta.
Da Ameen Ummie ta amsa a maqoshi.
Dan girgiza kai Abbie yayi yace"Bilkisou kenan Allah ya karkato da hankalin ki kan diyar ki.
Cike da kwarin gwiwa Ummie ta amsa da Ameen,da mamaki sosai Abbie yadube ta saboda jin ta amsa cike da confidence.
Ummie ta dubeshi murmushi kwance a fuskanta mai Kama da yaqe tace"kana mamaki koh?hmmm nima inason Zuhra sai dai tsanar da nake mata ya ninka son da nake mata,ina tsananin jin tausayin ta amma ya zanyi narasa meke damuna,takarisa maganar cikin raunin murya.
"Huhhhh!Abbie yasauke ajiyar zuciya yana dubanta,zuwa can yace"Bilkisou bana fatan zagin da yakeyi yazama gaskiya.
Cikin rashin fahimta Ummie ke dubansa.

"Ea ina zargi,alamu suna nuna kamar akwai sihiri tsakanin ki da Zuhra.
"Koh? Ummie tayi tambayar.
"Kwarai da gaske, bilkisou inaso kisani bana fatan na mutu banga kin daidaita da Zuhra ba.
Sosai gaban Ummie ya buga hankalinta yayi kololuwan tashi.
( _Duk da kin kasance Mai biyayya akan wannan abin kinkasa wa mahaifinki biyayyaaaaa._ _To bari kiji wallahi wallahi Ina sake jaddada miki muddin baki shiga hankalinki ba Bilkisou bazan taba yafemiki ba._ )
Kalaman Amma ne suka fara dawo mata a kwakwanta hankalin ta yasake tsananin tashi duban Abbie tayi idanuwan sa a rufe tace"Don Allah kadena fadamin haka kana tayar min da hankali na insha Allahu everything will be fine.
Mikewa yayi jikinsa sam babu kuzari yanufi stairs,hawaye ne masu dumi suka tsiyayo ma Ummie.

*_ADDU'AN DAI SHINAKE BUKATA NAGODE SOSAI MASOYA DA WADANDA SUKA KIRA DAMA WADANDA BASU KIRANI BA SON SO FISABILILLAH 🙏🏽 Happy birthday to you my rabin jiki baby Yusuf (Ãjmãl) Allah yaraya ka ya shiryaka yabaka ilimi Mai amfani da albarka ubangiji Allah ya albarkaci rayuwar ka Yusuf Imran Muhammad bature❤️🦋🔐_*

Xahratty CE🥰
Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️

07/3/23.
[3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳

Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now

*_GALADIMA FAMILY_*

Page 17-18

_Bismillahir-rahmanir-raheem._


______A kwana a tashi babu wuya after 1 month da satittika gashi zuhra jibi zata fara zuwa school(UNIMAID) sosai take jin dadi da annashuwa gashi gefe guda kuma suna tsananin mutumci ita da Shuraim da yake shi mutum ne mai barkwanci sosai duk da haka ZUHRA takasa sakemai ssai.
A bangaren Kareem kuwa hakan ba karamin sosa mai rai yake ba don yanason ZUHRA tun randa yayi tozali da ita suna zaune da Shuraim yaji yana tsananin kaunar ta,wannan kenan!

"Hajiya kefa kika ce zakiyi wani abu gashi wasa² anci 2months da saka ranar auren su yanzu saura fa 6 months, Rammat tayi maganar tana latso hawayen da suke gangaro mata.
Itakuwa banda girgiza kafa hajiya Biba babu abinda takeyi, Mom tadan mere baki tana duban Hjy Biba"Ni kam hajiya anya aikin malamin nan naki kuwa yanay........
"Ke...k..kke ke...keke kul! Meye haka rabi nema kike kidebomin tafasashen ruwa mai dafa duk taurin nama?ki rufamin asiri kinsan kuwa aikin dangudelle na yarda dashi na yarda da aikinsa,saboda shidin shedani neeeee takarisa maganar tana wani rimi dolen dole na hada zuri'ah da Galadima da wannan makirar tsohuwan Bodejo,inaso na bawa Laure mamaki tasan cewa ni nafita hatsabiban ci wallahi dani take zancen.
Duban Rammat tayi wacce take kukan cikin takaici tace"dallah ke kimin shiru,sai kace kema din ba mace ba?yanzu ke ba zaki iya jawo hankalin yaronnan gareki ba?meye amfanin macen da bata iya kissa ba kwata²n ta? hajiya Biba takarisa zancen tana huci tare da babban kada hanci.
"Hmmm aini Rammat wani takaici take bani hajiya,ga Akeela nan tanaji tana gani zata kwace mata shi.
Dan bata face Rammat tayi"Kai Aunty fatan tsiya haka?
Wani hararan Mom ta galla mata tare da mikewa ta dauki jakar ta duban hajiya Biba tayi"Hajiya zantafi bnson baban Aseef yadawo yaga bana a gida,Kinga ba'asan na fita ba.

Hajiya Biba tace"shikenan sai munyi waya,nan sukayi sallama tafita a ranta da qudurori kalakala,don ta dauki alwashin koda Rammat zata mutu ba zata yarda ta aure Sauban ba.

**** **** ****

Zaune take a cikin class din suna sauraren lecturer din English don da abinda aka fara tarbansu kenan sosai ta maida hankalinta akan lecture dinda ake musu,sanye take da Arabian gown coffee tayi rolling viel din sosai tayi kyau fatanta kalar half-caste yasake bayyana,duk da sanye take da facemask amma sosai taja hankalin 'yan class din.
Yadauki tsawon 20minutes yana musu bayani sannan yafita anan wani lecturer din yashigo yadauki 10 minute's kana yafita,na ukun ne yadauke fifteen minutes kuma daganan wajejen 11:30 suka fito daga lectures gabadaya, student's da dama sun sami bakin department dinnasu suna hira wasu na introducing kansu ga juna saboda asaba.
Zuhra kuwa kaitsaye gate tanufa don tafiya gida,tare da wasu daliban da qyar tasamu napep tahau dropped yakaita gida,cike da gajiya ta shiga gidan kaitsaye apartment din Ammi ta nufa.
Moryoyi ta fara jiyowa na 'yan mata koda tashiga parlon Aunty muneefa ne da Akeela,kan dinning kuma Aunty Mashahuda.
Cike da fari'a muneefa tace"A'ah students,yau UNIMAID sunyi sababbin dalibai.
Dan murmushi kawai Zuhra tayi tana karisawa wajen Mashahuda dake dinning,itama cike da zolaya tace"Wai yau 'yar gidan Ammi akwai rigima.
"Kai Aunty Mashahuda nifa ban gaji ba,dudu lecture's uku mukayi muka fito, takarisa maganar cikin shagwaba.
Ammi da saukowan ta kenan daga stairs tace"toh mene idan anmata tausar si auta ce,duk gidan nan itace auta yimata shine zaman lafiya.
Cike da tsananin jin nauyin Ammin zuhra ta duqar da Kai tana murmushi,dariya mashahuda ta saki tace"Ammi kinga zuhra wai kejin nauyinki.
Murmushi Ammi tayi dai-dai nan wayanta yasoma neman agaji, duban number tayi tare da sakin murmushi tayi picking.
"Assalamu alaikum Son.
Daga can bangaren Sauban ya lumshe ido cikin tsananin son Ammi yace"Sweetheart barka da rana.
Murmushi kwance akan fuskanta tace"barka dai yakake ya aiki?

Alhamdulillah Sweatheart jiya inata kiran number dinki yaqi shiga na Daddy ma haka nakira na Mash'huda kuma number busy tanata waya.
Ammi tayi dariya me sauti tace"itada taufeeq ne nasani to ya aikin?
Alhamdulillah,nima I think nanda sati biyu zan shigo zarian saboda branch dinmu na Abuja zanje naduba.

Cikin jindadi Ammi tace"Masha Allah son Allah yakawo min kai lafiya cikin aminci da yardarsa.
Cike da jin dadin addu'an ta ya lumshe ido yace"Ameen Sweatheart yasu Mom? don nayi waya dasu Bodejo.
Ammi tace"lafiya lou Mom dinku ya kamata kkrata koh?
"Ea Insha Allah haka za'ayi.
Kana waya dasu Ummien naku da Abbie?
Dariya mai sauti Sauban yayi wanda inba Ammi ko su Ummie dasu Bodejo ba bame ganin irinta yace.
"Ahhhh kaji Sweatheart sosai ma muna waya dasu.
"Yawwa son haka akeso Allah yamaka albarka.

"Ameen Ammi sai anjima a gaida yaran gidan.

"To Shikenan tafada tana me zare wayar daga kunnenta.

Cike da zumudi muneefa da Mashahuda ke tambayar ta ya tambayesu? Ammi tace"kowa ma ya tambaya ya kuma ce a gaida kowa don nanda sati biyu zaishigo kasar.

Akeela kuwa wani kululin bakin ciki dana takaici ne suka dirar mata ganin ko damuwa bai nunawa akan ta,kamar ma yamance da ranar wata akansa,hakan yasa cikin bacin rai ta tattara kwamatsanta tabar parlon,babu wanda ya lura da ita sai Zuhra,sai dai ita hakan ko a gyalen ta dan tabe mouth ma tayi.

*BAYAN SATI DAYA*

Zuhra ce zaune da ita da Shuraim suna hira cike da nishadi don Allah yabawa Shuraim nasarar samun Zuhra don sosai ta sake mishi.
Cikin muryan dariya tace"Yaya to idan kasamu balarabiya bazaka iya auren ta ba?
"Hmmm yarinya bazaki gane ba,nifa yarinyar da nakeso ko a larabawan ba lalai a masu mai kyanta da quality dinta ba,kedai kibari wataran zaki ganta.
Cike da shagwaba Zuhra tace"Lallai ma yayan nan naqi wayon,kawai dai kasa ma mana lokaci wataran kakaini naganta.
Zuhra tace"To shikenan Allah ya kaimu.

Da Ameen ya amsa yana mejin wani nishadi a ransa na yanda yaga yarinyar tayi bala'in sake masa.
Baba Mudi ne ya bude gate saboda horn din da aketa dokawa,ko gama bude gate din beyi ba aka shigo da motar a zafafe, cikin bacin rai ya balle murfin motar ya fito kaitsaye wajen Baba Mudi ya nufa,cikin rashin da'a yafara magana.
"Meyasa kake hakane tsohon nan?tunda nataso a gidan nan kai nake ganin matsayin me gadi gashi karfinka yafara karewa,don Allah katafi kabawa me jini a jika shima daman shigowa ya daddale arziqi mana, mtsewwww.
Yaja tsaki,shigo Baba mudi girgiza kai kawai yayi a zafafe ya nufi apartment dinsu.

Dan siririn tsaki zuhra taja.
"Yayadai?shikuma wancen wanene?

Zuhra tace"Hmmm barshi cousin dina ne haka yake duk gidannan shine Mara da'a shine wanda baiganin darajar talaka.
"Allah yakyauta ubangiji Kuma ya shiryeshi,da Ameen zuhra ta amsa,anan suka cigaba da hirarsu.

"Mom Wai dagaske ne?nifa bansamu labari ba sai shekaran jiya dana ga pic dinshi a IG yanda 'yan mata keta rushing akansa har fada wasu sunayi,baya kasarnan to waya sama masa aiki?
Mom tace"bansani ba,hmmm burika na biyu basu cika ba don haka bazanyi sake shima na ukun yaqi cika ba.
Aseef yace"wasu burika kenan?
Mom tace"naso ace ko Sauban ko taufeeq daya a ciki ya aure Muneefa amma gabadaya babu wanda yasamu,abin bakin cika wai Sauban yafika,nifa bana fatan rayuwar wanda zaifi dana ko wanene shi,shiyasa kota halin kaka sai ka aure Zuhra,takarisa maganar tana wani huci.

Wani irin sanyin dadi Aseef yaji a ransa.

"Ga sa ranar auren sa da akayi kasani ai koh?

"Nasani Mom sai dai hakan bedameni ba don sanin wacce zai aura ba kowa bace face bunsura,ai mom idan Sauban ya aure akeey beb ai yaci baya.
Mom tace"Toh meya shafeka da cin bayansa?idan yaso ma yaci uban baya,don kullum ni burina kenan dan iskan yaro.
Sallama Baba Hasheem yayi ya shigo.

Amsawa sukayi nan suka fara yimasa sannu da zuwa,sosai baba hasheem yaji dadin ganin Aseef"A'ah mutanen kaduna yaushe Kuma aka iso?
Dan sosa kai Aseef yayi yace"wallahi Baba yanzu bandane da shigowa ba.
"Ok to ya kabarsu Kuma?
"Lafiya lou wallahi Baba,dama nace Bari nazo na duba ku kwana biyu bamu shigo ba.

"Kashiga wajen su Galadima?
"A'ah yanzu zanshiga dai.
Alhaji kenan to inbanda abinka zaiki shiga ne?dole dai yafara gaisheni tunda nice na haifi abina.
"Gaskiya ne wannan,abinda Baba Hasheem yafada kenan yamike yashige corridor din bedroom dinsa.

Cikin farin ciki Aseef ya dubi Mom "Please Mom da gaske zan aure zuhra saboda gaskiya yarinyar tayi kota ina!
Mom tace"na taba maka wasa ne Aseef?
Girgiza kai yayi da sauri.

********
"Kai gaskiya naji dadi Allah yama Bashir albarka ubangiji yasake hada kawunan su, Bodejo ke mgn.

Daddy face dinshi dauke da murmushi yace"Ameen ai gabadaya kayan na 15 millions ne yahada musu babu abinda bai siya musu ba har kayan kitchen.
Baba hasheem yace"Allah dai yasaka ma Yaya da alkhairi.

Da Ameen gabadaya suka amsa, Galadima yace.
"To yaushe zasu dawo?

Daddy yace"insha Allah yace"kaitsaye ma gobe nan zai iso don yanason ganin Zuhra.
Dariya Bodejo tayi tace"Kai sadeeq na sangarta yarinyar nan matuka.

Dariya duk aka sanya.

Washegari wajejen bayan magrib Daddy ne da Ammi ke zaune sunayin lunch,wayar Daddy ya nemi neman agaji,da sauri ya dauka Yana murmushi saboda sunan Abbie da yagani,sallama yayi.

Nan aka fara magana tacan bangaren.
"Eah nine lafiya kuwa?Ina me wayar yake ne?daga can bangaren aka sake magana.
A gigice Daddy yamike yana furta" _INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN_,Ammi ma mikewa tayi tana Daddyn yara lafiya kuwa?

"Sadeeq!Sadeeq!! Aisha Sadeeq yayi hatsari shida bilkisou.
"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un a lokacin ne Baba Hasheem yashigo shima apartment din Daddy cikin rudu"Yaya!Yaya!! Dagaske ne?

Wani yunkurawa Daddy yayi cikin jarumta ya nufo Baba Hasheem,Kama hannunshi yayi.


_YANZU FA WASAN ZAI FARA MASOYA GALADIMA FAMILY_💃💃💃💃

Xahratty CE🥰
Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️

13/3/23.
[3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳

Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now

*_GALADIMA FAMILY_*

Page 19/20

_____A gigice suka nufi apartment din Galadima a dai-dai nan wayar Daddy yafara ringing, cikin rudewa ya dauki wayar,daga can bangaren aka fara magana.
"Alhaji Taufeeq majinyacin yana cikin wani hali don sai sunan ka yake ambata yana cewa kazo.
Bakin Daddy yana rawa ya dubi Baba Hasheem yace"Hashim mutafi asibitin ko kasan ko wane asibiti ne?
Baba Hashim yace"sun sanar dani muje kawai nan suka nufi motar Baba Hashim.

Tsananin rudewa kuwa Mashahuda tashiga don duk abinda ke faruwa akan idon tane da tsananin gigita tashiga apartment din Bodejo tana Kiran sunanta.
Bodejo dake zaune tana shafama Galadima man zafi a kafa ta dago tana cewa"ke kuwa Mashahuda wani irin Kira ne kikeyimin haka mai gigitar wa?

A rude takariso tara da durqushewa a gabansu tana sauke numfashi akai-akai.
"Bodejo Daddy sun tafi asibiti yanzu aka kira a waya Abbie da Ummie sunyi accident a hanyarsu ta tahowa daga airport.
"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un wane Abbie din? Bodejo tayi maganar tana gyara zanin ta da yake neman sabulewa.
Galadima yace"natsu Mashahuda kiyimana bayani.
Nan Mashahuda ta sanar musu da duk abinda ke faruwa a lokacin ne Kuma Ammi, Mom,muneefa da yaseer suka shigo parlon.
Cikin muryan tsawa Ammi tace"menene haka Mashahuda waya aikoki?haka ake fadan sako.

Daga musu hannu Galadima yayi cikin muryan dattaku yace"duk ku zazzauna.

"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un!!! Kalmar da Bodejo take ta fada kenan,hankalin ta yayi kololuwan tashi ga tsufa ga rudu,sai da Ammi da Mom suka kamata suka zaunar da ita.
GALADIMA wayansa yaciro yafara neman layin Daddy,sai dai ba'a daukan kiran,maida kiran yayi ga Baba Hashim ba'a dau lokaci ba tadauka,cikin kamewa Galadima yayi sallama.
Daga can Baba Hashim yadauka saboda a rude yake don muryansa har neman disashewa tayi saboda kuka.

"Hashim lafiya meke faruwa ne?

"Galadima ga munan dawowa yanzu,yakarisa maganar muryanshi na rawa.
"Mekefaruwa ne anan ina tamabayar ka meya same abubakar?fashewa da kuka Baba Hashim yayi yace"Allah yadauki rayuwansa wanda yafimu sonsa ya amshe abinsa Galadima.Runtse ido Galadima yayi batare da yasake magana ba yakashe wayan.

Cikin daburcewa Bodejo tace"malam meyasame abubakar din?
"Gasunan a hanyar dawowa gida,amsar da yabata kenan a takaice.
Dai-dai nan Zuhra tashigo parlon sai dai babu wanda ya lura da ita.
"Don Allah malam kamin bayanin meya same dana abubakar? Bodejo tafada tana me fashewa da kuka.
Sukansu su Ammi hankalinsu a tashe yake.

"Kuyi masa addu'ah Allah yakarbi rayuwarsa, Allah yamasa cikawa......wani irin kara da aka kwala ta bayansu yasasu gabadaya juyawa.

Zuhra ce a take anan tafadi sumammiya.

Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un!!!!shine kalmar da gabadaya 'yan parlon ke ambata cikin tsananin rudewa, Ammi dasu mashahuda suka nufo wajen zuhra.
Mom da Galadima suka nufi Bodejo saboda wani jiri da yadauke ta tanemi faduwa.

9:11
Kafin kace me gida yacika tam da jama'a bakajin komai sai tashin koke-koke na mata don ankawo Abbie gida,daga Daddy har Baba Hashim a gigice suke,me dauriyan ma Galadima ne.
Makota duk sun cika gidan,ana haka sai ga Abba dasu mommy tare dasu Laila duk sun iso saboda shima sanda sukayi accident din ankirashi kaitsaye asibitin yanufa yacidda ai dan uwanshi yarasu sun nufo gida.
Duk Wanda yaga ahalin nan a daren nan sai yayi musu kuka saboda tausayi, Zuhra kuwa tana apartment din Ammi ankira family doctor dinsu yaduba ta tare da samata drip da alluran bacci,saboda wasu sunbatu da mimmikewa da tafara.
Gawar Abbie kuwa a daren suka shiryashi tsaf sai gobe karfe tara na safe za'a kaisa(kwanan keso,ake cewa Koh?🤔).

Bodejo fifita su Mom ke mata saboda ta rude.

Su Daddy kwana sukayi suna ma Abbie karatun kur'ani, taufeeq shikan shi a gigice yake yafita daga hayyacinsa.

Washegari zuwa karfe takwas Galadima family yacika tam da jama'a dangi da masoya da makota,don abokan Abbie nanan Mai din da kaduna da yawa suna wajen, Maryam na Lagos ma ta iso abinka da jirgi itada mijinta da yaranta,labeeba dai suna hanya 'yan Canada.
Mahaifiyar Ummie da kannenta maza Suma sun iso da hajiya Zainab.

Duk Wanda yaga Zuhra sai ya tausaya mata saboda yanda takoma a kwana daya kawai ta gigice fuskarnan tayi jaa idanuwanta sunyi luhu luhu,mommy ce da Aunty Maryam rike da hannunta suka nufi babban parlon Galadima inda gawan Abbie take,mutane ne cike a parlon ana masa addu'ah,sallama sukayi suka shiga da ita,kowa hankalinsa yadawo gareta,dukar da ita Aunty Maryam tayi gaban gawar,dai-dai kunnenta ta mata magana"Banda kuka kinji? addu'ah zaki masa.
Hawaye ne masu zafi suke rige-rigen zubo mata,hannunta na rawa tadan bude fuskan Abbie.
Fuskan nan banda sheqi babu abinda yakeyi don zaka zata murmushi ma yakeyi kamar kace masa ya tashi.
"Allah yajikan ka Abbie, Allah yagafarta maka ubangiji yamaka rahama, Allah yasadaka da mala'ikun rahama Abbie,kaine uwana kaine ubana wanda yafini sonka yadauke ka a lokacin da nake tsananin bukatan ka, Allah ne gata na kaine gatanaa.....takarisa maganar tana fashewa da wani irin kuka.
"Abbie halinka nagari yab.....numfashinta ne yafara seezing da sauri Mommy ta kamata suka fita,kowa cike da tausayin ta yabita da kallo,anan aka fito da gawar.

Nan fa gida yasake haumutsewa da koke-koke na mata, Laila ma atake anan ta fadi ta Suma garau.
Guggo Laure da shigowan ta kenan da jiniyar kuka tafara"wayyo Allah mutuwa me yasa zaki Mana haka?me zesa kidaukar mana yaron kirki?ga sauran can,sai kika tafi mana da mai hakuri.
Takarisa maganar tana Jan majina.
Allahu akhbar kullu nafsin za'ikatul maut,duk Mai rai sai ya dandani dacin mutuwa Allah yajikan Abbie 🤧

Sai wajen la'asar ya taufeeq da Kareem da wani kanin Ummie suka daukota daga hospital sosai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login