Showing 9001 words to 12000 words out of 103469 words

Chapter 4 - GALADIMA FAMILY Complete Hausa novel

07 Sep 2024

6880

da plate guda biyu.Da toh Laila ta amsa.
Tuni yaran parlon suka fara murna.

Laila batajima ba tafito hannunta da wani dan leda baqa medan girma,tare da plates uku babba guda da madaidaita biyu,akan babban plates din tadora ledan.
Galadima yace"hajiya bodejo azo akasa abawa kowa nashi.

Bodejo takama baki tace"wa? Ai idan zuhra na waje bodejo bata tasiri ga tagaban goshi?
Murmushi Galadima yayi yace"Toh ko nihal ta raba ne?nihal zoki raba mana.

Tasowa nihal tayi aiko ta raba kashi uku kamar yanda Galadima yace tayi,shida bodejo kashi daya itada da Laila da zuhra Kashi daya sai su maimoon ma kashi daya.
"Allah yasaka da alkhairi granny ubangiji yaqara budi, Allah yaqara daukaka GALADIMA FAMILY,zuhra tayi addu'an cikin muryanta mai sanyi.

Da Ameen su Laila suka amsa.

Sosai Galadima da bodejo sukaji dadin addu'an na zuhra,wanda a kullum suna yabawa da hankalinta.

_SU WAYE GALADIMA FAMILY?_

Cikakken sunansa Muhammad Taleeb Muhammad haifaffen garin MAIDUGRI sai dai mahaifiyar sa ce 'yar nan wacce take shuwaarab,shi kuwa mahaifinsa buzaye ne irin masu tashin nan,adalilin haka Allah yakawo mahaifinsa da mahaifiyar sa garin MAIDUGRI inda wata rana suna kwance da daddare wata takama Wanda ba'asan daga inda wutar yafito ba.
Mutane suka fara kawo dauki,a lokacin Muhammad nada shekara a duniya,atake anan Allah yayiwa mahaifinsa rasuwa garin ganin ya cece matansa da dansa maisuna Muhammad,don sosai yayi wani irin mummunan kuna,mahaifiyar Muhammad kuwa itama kokari take takare Muhammad tare da abinda ke cikinta.

Asibiti aka kai mahaifiyar Muhammad,inda likitoci suka dukufa akanta,koda suka duba sai sukaga cikinta yana watan haihuwa ne babu bata lokaci suka yanke hukuncin ciro abinda ke cikinta,suna shirye²n yimata aikin ne Allah yadau rayuwanta,ganin haka yasa suka hanzarta yimata aikin.

Aiko suka Ciro yarinya kyakkyawa mace, Muhammad kuwa sai kuka yakeyi,nan suka tattara akayi abubuwan da za'ayi aka amsa gawar Muhammad.

A lokacin hakimin garin shine kakan bodejo don haka shine yayi komai,suka koma suka sallaci gawa biyu,babu bata lokaci hakimi da sauran dattawan anguwa suka yanke hukuncin baiwa hakimi su Muhammad,inda shi kuma hakimi yadamqasu a hannun danshi tilo namiji Harun mahaifin bodejo.

A lokacin bodejo nada shekara bakwai mahaifiyar ta daga kanta bata sake haihuwa ba Allah yamata rasuwa,a lokacin matan baban bodejo na aure da kanin bodejo yakub sai aka bata jaririyar ta hadasu tana shayar dasu.

Kamar yanda al'ada yazo ranar suna aka radama yarinya suna Lauratu inda mutane ke kiranta da Laure,sosai mahaifin bodejo da kakanta suka bawa su Muhammad gata,hakimi yasa aka tattaro masa raquman su Muhammad guda goma Sha biyar yabawa wani abokinsa dake cikin gari ajiyansu ana cigaba da kula dasu.

A haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya har akasa Muhammad a makaranta inda shakuwa mai karfi tashiga tsakaninshi da bodejo,a gefe guda kuma hakimi na cigaba da kula mishi da dukiyanshi shida mahaifin bodejo.

Xahratty CE🥰
Lallai Alqalami🖊️yafi takobi🗡️

16/2/23.
[3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳

Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now

*_GALADIMA FAMILY_*

Page 07

_Bismillahir-rahmanir-raheem._

_____A lokacin da Muhammad yagama secondry school lokacin Allah yadauki rayuwan hakimi,inda anan harun mahaifin bodejo yatura Muhammad cikin garin MAIDUGRI gidan aminin mahaifinsa inda gadon su Muhammad yake anan yaciga ba da karatunsa na gaba da sakandiri,a gefe guda kuma shakuwa sosai tasake dinkewa tsakanin bodejo da Muhammad lokacin tagama aji uku na sakandiri sai aka cireta, Laure ma tana samun kula sai dai takasance tun tana karama take da wasu dabi'u sam marasa kyau.

A kwana a tashi babu wuya Muhammad yasamu kwalin diploma dinshi,a lokacin ne Kuma harun ya aura masa bodejo inda suka tare anan gefen gidansu bodejo din, Muhammad yataso mutum ne mai tsananin hazaqa da kokari uwa uba kuma kyau,auren su da wata uku yakoma makaranta.

Lokacin da yagama Digree dinshi na farko a lokacin harun yadamqa mishi gadon su wanda tuni ansai da raqumayen,anjuya musu kudadensu inda ya habaka sosai,lokacin bodejo ta haifi danta mai santalele namiji kyakkyawa aka sanya masa Taleeb sunan mahaifin Muhammad,sai dai kiri² Muhammad ya hana a boye sunan,bayan bodejo tagama wanka Muhammad yadauke ta ya maidata cikin gari inda yayi musu gini, Laure Kuma tana zaune wajen harun da matarsa.

Bayan shekaru 28 aiki ya maida Muhammad garin kaduna inda yake zaune a zaria akuma lokacin yaran Muhammad su shidda ne maza hudu mata biyu,Taleeb ne babba sai Sadeeq,Haroun,Labeeba, Maryam sai auta Hasheem.
A lokacin anyi auren Taleeb da Sadeeq don rana daya akayi bikinsu.

Taleeb ya aure matansa 'yar maidugri ne don shuwa ce itadin gaba da bayanta,inda Sadeeq ya aure 'yar zaria wajen fada,duk cikansu Allah ya hadasu da mata nagari.
Matar Taleeb sunanta Aisha,matan Sadeeq kuma bilkisou.
Shekarar da suka cika shekara guda da aure Allah yabaiwa Taleeb karuwar da namiji inda yaci sunan Muhammad Taleeb Muhammad,waton sunan kakansa inda ake cemasa Sauban,bayan cikin Sauban suka sake haihuwar mace inda aka sanya mata sunan mahaifiyar Aisha Safeena suna cemata falmata wacce take sa'a da Dan wajen Sadeeq wato Ahmad ake masa laqabi da Taufeeq.

Wasa Wasa sai da Aisha tayi haihuwa hudu, Sauban,falmata, Mashahuda, Laila.
Amma bilkisou tundaga kan Taufeeq bata sake haihuwa ba.

A lokacin shima abba yayi aure sai dai matansa shima bata haihu da wuri ba 'yar kaduna mai suna hauwa'u.
Hasheem yayi aure inda yake aure da 'yar wan mijin Guggo Laure, me suna Rabi.Yaransa uku,babban Bashir ana cemasa Aseef sai muneefa inda takeda ciki a lokacin itama bilkisou tasamu cikin nabiyu.

Anyi bikin Labeeba da Maryam, Labeeba tana zaune a Canada tare da mijinta yaransu biyu muhsin da musaddiq.Inda Maryam ke Lagos sai dai ita bata haihu ba.

Rabi ta haifi yaronta namiji Mai suna yassir tsakaninshi da Laila wata daya,inda itama hauwa'u ta haifi diyar ta mace akasanya mata Nihal.
Alokacin da cikin jikin bilkisou itama ya bayyana sosai ahalin Muhammad suka shiga farin ciki kowa yaqosa ace tahaihu,sosai akayi zumudin cikin,lokacin haihuwa tayi ta haifi yarinyar ta kyakkyawa Masha Allah anan ne fa akashiga turka turka inda bilkisou tace sunan mahaifiyar ta za'a saka mata,shikuma Sadeeq yace sunan mahaifiyar sa zai saka Fatima.

A lokacin rashin kawaicin bilkisou yafito muraratan inda tace to muddin yasa sunan bodejo to bazatayi farin cki ba,sosai ran Sadeeq yabaci dana ahalinsa sai dai su suka danne,bodejo kuwa duk bakinta haka tazuba ma bilkisou Ido, Guggo Laure kuwa tasamu bilkisou tayi mata tijara tundaga lokacin ta tsani bilkisou.
Aiko aka sanya sunan bodejo wato fateematuz zahra'u suke cemata zuhra.
Da farko bilkisou tace bazata shayar da jaririyar ba,sai da mahaifinta da mahaifiyar ta sukazo har gida sukayi mata tatas inda mahaifinta yace muddin Bata shayar da zuhra ba sai yayi mata baki,sannan yatasa ta taje tabaiwa bodejo hakuri da Muhammad da mijinta Sadeeq.

MUHAMMAD kafin kace mene yayi fice saboda kudinsa da kuma ilimi irin na 'yayansa ga uwa uba kyau,don alokacin Taleeb Yana aiki a NNPC inda yaran gidan ke kiransa da Daddy,Sadeeq kuma yana aiki a wani company a Lagos inda yaran gidan kekiransa da Abbie sunan da Sauban yasa masa, Harun wanda suke cema Abba kuma yana lecturing a KASU ne,shima Hasheem wanda suke Kira da Baba yana lecturing ne a ABU zaria.

Allah yarufama iyalensa Muhammad asiri da shi kansa dai² gwargwado,sosai sunanshi yayi fice inda a wancan lokacin zamanin sarkin lokacin ya nada masa sarautar galadiman zazzau shikenan kuma sai sunan yabisa,an nada masa sarautar babu jimawa kuma don ba'a wuce shekaru uku ba yakoma MAIDUGRI gabadaya da iyalensa,banda Abba da Abbie inda Baba Hasheem yakoma University of maidugri yacigaba da lecturing dinsa.

Zuhra kuwa sosai tasha wahala a hannun mahaifiyar ta bilkisou vwacce suke kira da Ummie,duk da kuwa tataso 'yar gatace Amma sam batajij dadi ta wajen Ummie yana daya daga cikin dalilan da yasa Abbie yake tsananin son ta kenan,tunda yayi fadar har yagaji yasama Ummie Ido,mommy ce a kaduna tamaye mata gurbin mahaifiyar ta.

Inda sosai mommy ke tsananin tausaya ma zuhra tare da bata cikakkiyar kular da tadace komai tare take musu ita da Nihal har Allah yabata ciki tasake haihuwar junior yasir,takuma sake haihuwan mace maimoon.
Dalilin dayasa zuhra tataso da tsoron Ummie kenan tare da shakkar ta,idan kuwa ace Abbie baya gari zama takeyi kamar mara lafiya.

Wannan kenan.

_Cigaban labarin._

Ji kake tassss!
Jikinta babu inda baya shaking tsaban rudun da take ciki hawaye ne kawai ke tsiyayowa daga idanuwanta,dafe kuncinta tayi don sosai Marin ya shige ta.

Lokaci daya parlon yadauki shiru sosai Taufeeq, Mashahuda, Laila, Nihal jikin su yayi sanyi ganin irin marin da Ummie ta zabga ma zuhra,cikin kakkausar murya tayi pointin dinta tare da cewa.

"Karyan rashin hankali kikeyi zankoya miki natsuwa ne,stupid kawai.

Takarisa maganar tare da jan tsaki cikin muryan tsawa tace"Get out !!!
Da wani irin sassarfa zuhra tafita inda jikinta babu inda baya rawa, Taleeb kuwa sunkuyar dakanshi yayi idanuwan shi sunyi jajazur.
Kaitsaye apartment din Ammi zuhra ta wuce,kicibus tayi da Ammi a kofar hawa stairs din Daddy, fadawa tayi jikin Ammi tare da fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciyar duk wani mai sauraro,cikin rawar murya tace.

"Ammi...Am...Ammi don Allah Ummie ne mama na? Ummie ne ta haifeni?meyasa Ummie tatsaneni?please kuje kubata hakuri kuce tasoniiii...taja kalmar saboda wani irin kuka da yazo mata.

A hankali Ammi takai hannu tana shafa kan zuhra cikin tsananin tausayin ta wani kwalla taji ya taru mata a idanuwan ta,kama hannunta tayi tanufi hanyar wani corridor inda zai sadata da parlon ta,zaunar da zuhra tayi akan sofa.

Facing dinta tayi tare da kakalo murmushi takira sunan zuhra, dago dara²n idanuwan ta tayi wanda suka tasa saboda kuka ta zubawa Ammi.
"Kiyahakuri kinji?kidauki duk wani abu da zaifaru dake a matsayin kaddara da kuma jarabawa kinji?Allah Yana sane dake Koda wasa kuma kada nasake ji kinkuma fadar maganar nan,watarana fah sai labari kinji zuhra na?
Daga kai kawai tayi tare da amsawa Ammi,murmushi Ammi tayi tace"kinci abinci?
Cikin sanyin muryan ta tace"A'ah yanzu zanje wajen Mommy na amsa alale na.

Ammi tace"yawwa to taaji kije Allah yamiki albarka.
Mikewa tayi cikin sanyin ta tafita,kaitsaye apartment din mommy tanufa dai² dan lungun shuke shuke tsakanin apartment din Mom dana mommy taji anfisgo ta tafada jikin mutum.

A tsananin gigice ta dago tare da kokarin sanya ihu,Ido biyu sukayi da Aseef inda yake binta da wani irin matsiyacin kallo Yana lashe lips.
Jikin zuhra ne yatsananta kadawa,kirjinta na tsananin bugawa,baki yakai da zummar yimata sumba Allah kuwa yabata sa'a ta dunkule hannu takaimasa punch a hanci.

Ai tuni yasaketa yana me dafe hancinsa,itakuwa zuhra dagudu ta falla bata tsaya ko inaba sai apartment din Mom banda nishi babu abinda takeyi,hawaye kuwa anan ya tsananta ambaliya.

Gefe ta samu tafashe da kuka a fili ta furta"wa zankaiwa kuka na?wa zanfadama halinda nake ciki don ya magancemin?
A hankali maganar wata 'yar ajinsu yafado mata inda suke fira dawasu can daban a cikin firar tace.
_Fauziyya duk duniyar nan banda mahaifiyarka babu Wanda zaka fadama magana ya fahimceka sama da mahaifiyarka shiyasa Allah yakara ma iyayenmu mata lafiya da nisan kwana._

A fili tasake fashewa da kuka tace"banda nawa Ummien.
Dafata taji anyi,da sauri tadago sai sukayi ido biyu da Taufeeq dan murmushi ya sakin mata yana kallon yanda hawayen idanunta kowanne yake rige²n sauka,zama yayi a dan gefenta tare da daukan kanta yadora akan kafadarsa.
Sai dai ko wannensu yakasa cewa komai,katse shirun da cewa.

"Tashi muje mommy na nemanki,yayi maganar yana miqar da ita tsaye,a hankali ya miqar da ita.

Apartment din mommy suka nufa.
********
"Daddyn Sauban bazaka gane abinda nake nufi bane wallahi bilkisou sam bata kyautawa rayuwar ta,ni kaina bacin agaban mu bilkisou ta haifi zuhra sai nace ba itace ta haifeta saboda wannan dan kankanin matsalar amma ace bilkisou tadauki tsanar duniya tadorawa zuhra,anyi anyi anyi?iyayenta sunyi rokon har sun gaji wannan wane irin musifa ne?
Daddy yace"Aisha nikaina hankalina na tashi, muddin zamu hadu da Sadeeq to maganar da zaifara yimin kenan, yarinyar tana shiga tsananin damuwa,ni tsoro na kada wani larura ya kamata.
Ammi tace"narasa meya shiga kan bilkisou,bilkisou meson yarane kaduba fa,kuma sanda tasamu cikin zuhra ta dauki son duniya ta dorawa cikin don ko cikin Taufeeq batanuna zumudi haka ba,ko a sanda tahaifeta kamar ta hadiye abarta sai daga baya zancen ya canza.
Daddy yace"Allah ya kyauta,ita kuma Allah yakara mata hakuri da juriya ubangiji ya bata ikon cinye jarabawarta.

*MALAYSIA*

Sosai Sauban yake cike da farin ciki saboda kaitsaye anamasa interview akace za'a daukeshi aiki a company kuma hazaka da kokari nashi sun burgesu sosai,inda sauran goma sha biyar din akace zasuji bayani daga baya.
Anan suke sanardashi nanda 2 weeks zaifara shiga office,sosai yayi godiya inda yafara shirye shiryen dawowa gida Nigeria.
Kwananshi biyar a Malaysia yafara shirin dawowa.

A MAIDUGRI kuwa gabadaya yaran 'yan matan gidan suna cikin din Ammi inda suke aiki,zuhra ce kehada couslow don aikin da aka bata kenan.
Cike da sanyin ta take aikin sai dai sam fuskanta babu walwala ko kadan,cike da barkwanci Mashahuda tace"Aunty zuhra kiyi kigama hadamana couslow dinnanfa don nasan yau akwai santi akan dinning.
Dariya duk sukayi muneefa tace"Ai sis shiyasa Ammi tabata hadin couslow din.
Dan murmushin gefen baki zuhra tayi tace"kai Aunty's.

Xahratty CE🥰
Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️
17/2/23.
[3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳

Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now

*_GALADIMA FAMILY_*

Page 09

_Bismillahir-rahmanir-raheem._

*This page is dedicated to my lovely son Ãjmãl,much love 😘 my rabin jiki*

_____Wannan saurayin ne da suka hadu dashi a super market dazu,mirmushi ya sakar ma zuhra cikin sauri ta kawar dakai tare da basarwa.
Maida dubansa yayi ga Aunty Mashahuda wacce batadena yimishi kallon mamaki ba,dan murmushi yamata yace"Auntymmu dama nan kukazo?
Mashahuda tace"aiko nan mukazo sannu dai.

Aunty Safeena tace"kunsan junane Shuraim?dan sosa kai yayi tare da murmushi yace"Ea Aunty munsan juna.

Zuhra ce tadubi Abban inteey tace"Yaya Asheer sannu da zuwa, inayini?
Fuskarshi cike da fari'a ya amsa da lafiya lou autan Abbie yaushe kuka shigo garin?
Zuhra tace"yau sati daya.

Yace"Masha Allah yasu Ummie da Abbie?

Zuhra tace"duk suna nan lafiya lou harma sun koma yau kwana biyar da komawansu.
Shiko wannan saurayin ke suna Shuraim tuni zuhra tatafi da imaninsa gabadaya hankalinsa yakoma kanta.

Dubanshi Aunty Safeena tayi"Shuraim lafiya kuwa?firgigit yayi tare da maida dubansa wajen Aunty Safeena,daga Abban inteey har zuhra suma dubansu sukayi.
Abincin Aunty Mashahuda tadauka tare da duban zuhra tace"Sis zo muje dinning muba su Yaya Asheer waje.

Mikewa zuhra tayi don dama a takure take hannunta riqe da hannun inteey suka nufi dinning din zama sukayi inda zuhra tajuyama parlon baya.
Cikin kasa kasa da murya Aunty Mashahuda tace"kinsan wancan mutumin ke yabiyo anya ba sonki yake ba zuhra?
Sosai zuhra taji gabanta ya fadi amma sai ta basar tace"hmmm Aunty ni babu ruwa na dasu Daddy wallahi yaje can yaqarata,takarisa maganar tana kai lomar spaghetti din bakinta wanda yaji dakakken naman kaza.
Itama bata sake magana ba mashahudan, can wayar Mashahuda yafara Ringing,hannu takai tare da dauka sunan ammi ne ya bayyana akan screen din wayar.
"Assalamu alaikum ammi,bansan me akace mata daga can bangaren ba sai dai tazaro idanuwa gabadaya,ta marairace face tace"please ammi kice masa muna hanya yanzu zamu dawo,magana aka sake mata tacan bangaren.
Sake marairaice face tayi"please ammi muna zuwa fah.

Itakuwa zuhra tuni ta aje spoon din a cikin plate din taja tissue tagoge mouth dinta sannan tamike,itama Mashahuda mikewar tayi bayan ta aje wayar tadubi zuhra tace.
"Wai Daddy ne yadawo yake tambayar inda muke,shine tace munje supermarket shine fa yafara fada.

Tafiya zuhra tafara suka dawo parlon,mikewa Abban inteey yayi yace"Shuraim kamaidasu gida zanshiga inwatsa ruwa ne don yanzu za'a kira magrib,cike da girmamawa ya amsa key din yace"nima gida zan tafi yaya dagacan.
Abban inteey yace"tohm shikenan ka gaida mutan gidan kacema Alhaji gobe zanshigo.

Aunty Safeena tace"muje toh kutafi don nasan kuna wuce magrib sai sunyi fada musamman ma Baba Hasheem,fita sukayi suna yiwa Abban inteey sallama.

Parking space suka isa nan suka shisshiga cikin motocin,shima Shuraim sallama yama Aunty Safeena sannan yashiga yatayar da motan,nan gate man yabude masa gate din yafita.

Aunty Safeena kuwa sosai take farin ciki don idan harsashen ta ya tabbata to tabbas sai tafi kowa murna( _Ji wannan safeenan zaki hadu da bodejo ai_ )🤔

Suna cikin motar babu wanda yace da wani qala sai dai time to time Shuraim na duban mirror kuma cikin rashin sa'a su hada idanu,itako zuhra ta galla masa harara tare da murguda baki.

Sai dai kawai yayi murmushi don shi masifar burgesa tsiwan nata keyi,a haka dai suka kariso anguwan su,kwatance Aunty Mashahuda tashiga yimishi,nankuwa yakawosu kofar gidan yadanna horn,da sauri Aunty Mashahuda tace.
"Kada kadamu Baba mudi ma bayanan suna cikin masallaci ka ajemu anan ma ya isa,bude murfin motar sukayi suka fito, shima fitowan yayi yadan tsaya a setin zuhra duk da suna da tazara face nasa dauke da smile yadubi Aunty Mashahuda cikin zolaya yace"shikenan Auntymmu gashi dai a bonus naga gida da alama kuma tafiyar tawa akwai nasara,yakarisa maganar yana duban zuhra.

Tunda yashigo layin idanunsa ya sauka akan kofan gate dinsu don gidan Galadima yana daya daga cikin manyan gidajen da akeji dasu a layin,a hankali yarage speed din motar,idanuwansa ne yafara sauka akan na wannan saurayin dayake wani irin murmushi,da sauri yaduba don ganin wanda yake ma murmushin,nandanan yaji kirjinsa yabuga ransa yayi kololuwan baci yamaida dubansa ga Mashahuda wacce take ta murnushi.

Kara speed din motar yayi gefen su yafaka motar yaballe murfin motar yafito,daga Zuhra har Mashahuda gwalo idanuwa sukayi waje,ai kamar hadin baki su biyun da sassarfa duka shige cikin gate din.
Da mamaki Shuraim yadubi inda yaga sun kalla har yasasu wannan razanar sai dai abin mamaki baiga kowa ba awajen.
Abinda Shuraim baisani ba kuwa shine koda Sauban yafito daga motan ko kallon inda suke beyi ba ya shige cikin masjid din,amma su da take sun ganshi shine fah.
Yadade sosai a bakin gate din daga karshe yashiga motan ya gyara parking din agefe yanufi masjid din yayi alwala yashiga ciki.
Su kuwa daga Mashahuda har zuhra kowacce takanta tayi don kaitsaye apartment din bodejo zuhra

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login