Showing 45001 words to 48000 words out of 103469 words

Chapter 16 - GALADIMA FAMILY Complete Hausa novel

07 Sep 2024

6888

se ga abokan Sauban da suka zo daga abroad suma suna zubama Taufeeq da Zuhra manni,shima Shuraim tasowan yayi, Aunty safna ma haka tare dasu Aunty Maryam,su kansu amaren ba'a barsu a baya ba, Akeela kuwa zuciyar ta jitake kamar zata buga tsaban bakin ciki.
Haka atashi taro lami lafiya aka gama kowa na farin ciki wasu kuma akasinsa.

*****
Duk zaune suke a apartment dinsu na mazan,babban parlon ne da 3 bedrooms,firar dinner kawai sukeyi,daya daga cikin abokan Sauban mes suna Saif Ahmad Khan dan kasar India cikin muryan turanci ya dubi Taufeeq yace"Gaskiya Taufeeq kanwar nan taka tayimin matukar kyau nifa da zaku temaka ku bani ita na aura,wani me suna ishaq Adekunle mazaunin Canada yace"jibeka!taya zata aure wanda ba dan kasar ta ba?ai dani tafi dacewa Saif,harara Saif din ya gallamasa,shikuwa Taufeeq dariya kawai yake musu,mikewa yayi yana cemusu yana zuwa,don amso musu abincin su,duban Sauban Saif yayi yace"Oga magana nakeyi wallahi dagaske nake I love her so much"batare da yadago ba kuma be tanka ba ya cigaba da lallatse wayarsa,wani me suna Ashur shankeer ya kyalkyale da dariyan mugunta yace"lallai iska na wahal da me kayan kara sufa familyn su Oga da alama basu bama bare aure,auren zumunci sukeyi gabadaya,duban Sauban yayi yace"please Oga idan zakayi fighting din bamu ita nizaka mawa don ni nafi dacewa da wannan bby doll di.....dogon tsaki Sauban yayi tare da daure face babu alamun wasa ko kadan yace.

"Look niba dan iska bane da zanje na tare yaran ciki na da shirme,inbanda abinku ai ku yafi dacewa dakuje kuyi ma kanki fighting,babu wanda ya isa ya siyamin raini wajen yarinya,ya karisa maganar yana mikewa tamkar ba shine yayi maganar ba domin kuwa face dinsa ko alamun bacin rai babu,toilet ya shige ya barsu sai surutu sukeyi, Taufeeq ne yashigo tare da sallama bayansa,zuhra ce da katon basket a hannu,shima hannunsa basket ne da flask na ruwan zafi suna tafi suna hiran nishadi,shigowan su parloun yasata dan tsuke face,cike da girmamawa ta rissinawa tafara gaishesu da turanci,ko wanne na amsawa cikin nishadi suke amsawa,tana ajewa ta musu sai da safe tafita cikin sauri,kicibus tayi da Aseef rataye da hakan baya,cikin sauri taja baya,shikuwa marairaice fuska yayi yana duban ta,takowa yafara yi zuwa inda take yana kanne mata ido irin na cikakkun 'yan barikin nan.

Da wani irin gudu zuhra ta kwasa don harga Allah ita tana tsoron sa,tasan mummunan halinsa Wanda ba kow ya sani a family din ba,karasawa tayi apartment din Ammi don banda haki babu abinda takeyi.

Su Adda Zainab da hajiya Aliya ma sunzo,sashen Ummie sosai ya cika da 'yan uwa da abokan arziki,haka sauran sashisshikan.

*******

A gidan Guggo Laure kuwa shima gida yafara cika sosai da 'yan biki,Akeela sashin Baba sani ta koma da kawayen ta,inda banda hirar batsa babu abinda suke a tsakanin su,tare da kosawa gobe tayi domin kuwa an dauki buri a bikin nan musamman ma Akeela,banda dirkan magungunan mata dana matsi babu abinda takeyi,tagigita kanta a banza a wofi tana tsananin bukatan mijinta a cewar ta.

*๐‘จ๐‘บ๐‘จ๐‘ฉ๐‘จ๐‘น*

๐‘ฟ๐’‚๐’‰๐’“๐’‚๐’•๐’•๐’š ๐‘ช๐’†๐Ÿฅฐ
๐‘ณ๐’‚๐’๐’๐’‚๐’Š ๐‘จ๐’๐’’๐’‚๐’๐’‚๐’Ž๐’Š๐Ÿ–Š๏ธ๐’€๐’‚๐’‡๐’Š ๐’•๐’‚๐’Œ๐’๐’ƒ๐’Š.๐Ÿ—ก
๏ธ[6/9, 22:33] Xahratty (OUM AJMAL): ๐Ÿ‘จ๐Ÿฝโ€๐Ÿฆณ *_GALADIMA FAMILY_*๐Ÿ‘จ๐Ÿฝโ€๐Ÿฆณ

Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

Marubuciyarโคต๏ธ
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now

*_GALADIMA FAMILY_*

Page 45/46

______Allah yasani tatsani Aseef hakanan tarasa dalilin da yasa take kokarin shiga rayuwata ita tama mance dashi a shafin zuri'ar su,to ina ya shiga kwana biyu da ba'a ganin sa yabace bat?tambayar da tama kanta kenan batare da tana tunanin samun answer ba,ajiyan zuciya ta sauke mai karfi tana karisa shiga apartment din na Ammi.

*๐˜ˆ๐˜š๐˜ˆ??๐˜ˆ๐˜™*

Washe gari wajejen 11:30 babu abinda ke tashi sai muryoyin maroka suna sanar da daurin auren nasu Muhammad Taleeb Muhammad(Sauban) & Akeela Mansir,Taleeb Abubakar Muhammad(Taufeeq)&Mashhudat Taleeb Muhammad sai Ma'aruf Kabeer Mainaera&Habiba Hasheem Muhammad(Muneefa) sosai marokan nan suka saki makoshi asake,kafin kaceme sai guda shima kansa ya fara tashi,tsintar kanta tayi cikin wani irin bacin rai a hankali zazzabi yafara shiganta,fitowan ta kenan daga apartment din Ummie tana kokarin shiga apartment din Bodejo ne taji an fisgota,jitayi ta fada jikin mutum a tsananin rude tare da tashin hankali tadago,ido biyu tayi da Aseef,kirjinta ne ya shiga bugawa jikinta ya soma rawa,bude mouth tayi da niyyar sakin ihu,hannu yayi maza yadora a saman pink lips dinta yana furta"Shiiiii don't say anything baby,yakarisa maganar yana bin jikinta da wani irin mayetaccen kallo,karfin hali tayi na fusge jikinta sai dai ko kadan be bata damar hakan ba don ba rikon wasa ya mata ba,cikin rawar jiki tasake dagowa hawaye na sirnano mata cike da bacin rai da tsiwa tafara magana"ka sakeni please,niba 'yar iska bace wannan mummunan habits din da kake boyewa da yardan Allah wataran sai asirin ka ya tuno,murmushi yayi kamar ba dashi take magana ba yafara matso da bakinshi kan nata bakin,fusgewa tayi cikin karaji ta furta"ka sakeni la'ananne,kasakeni I hate you,natsaneka natsane halayen ka da yardan Allah nafi karfin ka bazaka taba samun galaba a kaina,yakarisa maganar tanajin wani mahaukacin karfi yazo mata lokaci guda,dagewa tayi ta turasa baya,aiko tasamu nasara don sai da yayi tagaยฒ zai fadi abinka da mashayi dama ba wani karfine a jikinsa ba,da gudu ta kwasa tana me sake zaginta.
Karkada kai Aseef yayi yana mebin jikinta da kallo,idanun sa sun kada sunyi jajir,yaji zafin zagin da ta masa,alkawari ya dauka duk bala'i sai ya dandana yarinyar kalmar da ya fada kenan yana me juyawa tare da wucewa,kaitsaye bedroom dinta apartment din Bodejo.

Kuka ta fashe dashi me tsuma zuciya tana sake me tsinewa halayyan Aseef"natsani gidan natsani kowa, Allah ya jikanka Abbiey na am always miss yhu,I love yhu lovely father da kananan da ka sharemin hawaye na,ina begenka da kauna me tsanani,wani ciwon kai taji me tsanani ya saukan mata,kukan ta tacigaba dayi tana fadawa kan gadon ta kwanta,tanajin sanyi na ratsa ko ina na jikinta.

Da kakalle fuskokin su angwayen zakasan lallai suna cikin farin ciki,hotuna aketa tayi dasu,kowacce budurwa burinta tayi pic da Sauban da abokansa musamman Saif da ishaq don sunfi kyau a bisa Ashur,shikuwa Taufeeq wurga idanuwa yake ko zaiga ta inda Zuhra zata fito amma sam be ganta ba,sosai yadan damu haka ya saki aka cigaba da hotunan,shima Shuraim yazo gidan sai laluben numbers dinta yake amma is not reachable ake cemasa, Aunty safeena ya tambaya tace bata ganta ba amma yabari zatasa a dubo mata ita,biki yayi biki taro yayi taro harga Allah Saif ya kamu da son Zuhra shiyasa ma yaketa wurga idanuwa ko zaiga gilmawar ta amma be ganta ba.

A can sashen Bodejo ko Zuhra taci kukanta har ta gode Allah,a take anan wahalallen bacci yayi awon gaba da ita,Saboda zazzabi da ciwon kai dake neman zautata.

Anci ansha anyi shagulgula karfe hudu aka Kai amare sashen Galadima inda suka hadu da Daddy, Abba, Baba Hasheem suka hadu suna ma amaren nasiha mai shiga jiki sosai,daganan aka kaiso sashen iyayen su mata, Mashahuda kadai za'a wuce da ita don haka tayi kuka sosai,gefenta Rammat ne keta lallashinta,nanfa motocin daukar amarya suka iso da ita da Mashahuda aka dauka don Mashahuda zata rakata gidanta.
Wajejen biyar angama kwashe duk wanda zashi gidan amarya anwuce dashi, Mashahuda kuma sai gobe za'a wuce da ita tare dasu Aunty Maryam, Aunty falmata(safeena)sai wasu 'yan uwan Ammi.
Dangin Ma'aruf sun tarbe amare da 'yan uwanta cikin mutumci da kulawa,kai tsaye sashen mahaifin Ma'aruf din aka kaita,babban mutum mai cike da dattaku nan fa yafara mata nasiha mai shiga jiki tare da Ma'aruf don babu kwana,daganan sashen mahaifiyar Ma'aruf din aka nufa da ita,itama tamata nata nasihar.

Bayan magrib akafara dawo da mutane,inda acan kuma masu kawo Akeela suma sun iso,ana tafe da amarya wanda babu abinda ke tashi sai kida a MP3,manyan mata wsu ma duk sun haifeta sune keta kwarkwasa,sai dai ba wanda ya fahimci wani abu,yan mahaifiyata kuwa mamaki yacika ta don bata sansu a dangi ba,ganin rashin da'an na neman yayi yawa tadaga murya"Meye haka?Wai wacece me mp nan da take cika gidan mutane da kida?haba bayin Allah meyasa muke hakane mutane? za'a fa kaita sasan sirikanta ne ba dakinta ba,yo ko dakinta nema ai be kamata a shiga da ita da mp ba,takarisa maganar cikin bacin rai,wacce mp ke hannunta ne tafara magana"wallahi mama hakan ba wani Abu bane,kawai mutanen mu na yanzu rashin wayewar kai ta musu yawa ne shiyasa,hajiya daharatu dake rike da hannun amarya tadubi yarinyar wata busasshiya da ita taci mai ta kwaile tace" 'Yar caras kashe mp nan mana.
Kashewa tayi suka shiga katon gidan wanda da damansu sai da suka raina kansu atake anan wasu hassada ya darsu musu sukaji inama ace sune suka shigo cikin wannan ahalin, lallai Akeela ta dace saurasu,wasu kuwa da yake ba auren ne a ransu ba hakan be wani damesu ba sai dai suma sunji sha'awar kasancewa a gidan.
Tundaga yanda Galadima family sukaga amarya da kawayenta sukeyi suka san lallai basuyi dace da sirikar kwarai ba amma ba anan gizo ke sakar ba kila tana da wasu halayyan, Ammi kuwa tayi bala'in jin kunyar kallon Akeela a matsayin sirika,don ko rufe fuska batayi ba,sai dai baka isa kagane hakan a face dinta ba Saboda murmushin da take tayi,tsakanin Rammat dasu Suby kuwa banda kallon banza babu abinda suke aikama juna,nan aka gama mata nasihohi aka fito da ita tare dasu Aunty Maryam don kaisu gidan amarya dake jikin nan gida,koda suka isa nanma mutanen Akeela sun raina kansu don ita da kanta ware ido tayi tana kashe kwarkwatan idanuwan ta.
Barosu su Aunty Safeena sukayi bakunan su cike da abubuwan mamaki tare da tausayin Sauban don da alama zasu wahala.
Bodejo ce tanufi dakin don dauko furar da ta'aje ma yallabai๐Ÿ˜‚Turus tayi saboda ganin mutum da tayi kan gado"Wanene nan?shiru taji,dan matsawa tayi cikin tsoro tasake cewa"Nace Wanene nan?ina magana ana jina eyye?mutum ko aljani?wallahi ko aljanuni sharri na yafi naku, hatsabibanci na yafi naku"takarisa maganar zuciyar ta fal tsoro shahada tayi ta yaye duvet din, Zuhra tagani banda rawar sanyi babu abinda jikinta ke mata,da sauri ta taba goshinta,gau haka taji shi da zafi sosai"Oh ni fatsima dama yarinyar nan kina sashin nan kikazo kika boye kina neman kashe kanki da ciwo?kinji jikin ki kuwa?tayi maganar tana bubbuga mata jiki.
A wahalce tadan bude idanuwan ta,tanajin wani irin azaba,sake lumshe idon tayi cikin tsananin azaban da takejin kanta na mata kamar zai rabe biyu.
"Ke Zuhra tashi kizauna lafiyanki kuwa?meke damunki ne haka?kinji yanda jikin ki yadauki zafi gau?gaskiya ba lafiya ba bari nazo,tayi maganar tana fita batare da tadauki abinda tazo daukan ba,ko minti goma bata kara ba tadawo ita da Taufeeq dasu Aunty Maryam,suka shigo,duk cikansu nufar gadon sukayi"Taba jikinta kaji Taleeb,zazzabi ne mezafi ya lullubeta"Bodejo tayi maganar,hannu yadora akan goshin nata,da sauri ya cire"Kai gaskiya kuwa, Aunty labeeba tace"Zuhra!Zuhra!!tayi maganar tana tabata.
A wahalce tadan bude ido tasake lumshewa,dagota Aunty Maryam tayi tasa kanta a cinyar ta tace"Zuhra bude idanuwanki, Zuhra"Uhum! Abinda tace kenan tana rufe idon ruffff "Ikon Allah jikin nata ya canza mata ne lokaci daya,duban Aunty Maryam Taufeeq yayi yace"Aunty ya kamata muje asibiti da itane ko?

Aunty labeeba tace"Gaskiya kam don wannan zazzabin ya bigeta gaskiya,dagata.Kamata sukayi suka mikar da ita,jikinta babu inda baya rawa saboda sanyin da takeji,face din har wani pink pink yake na wahala,wani mahaukacin amai ne taji yazo mata,ai kafin kace me tafara kelayarwa,haka jikinta ke cigaba da rawa,amai take sosai,sosai su ma hankalinsu yatashi,cikin muryan kuka take fadin"Abbie!Abbie!! Kamata sukayi ai ganin zata wahala ga jikinta yayi bala'in saki wani yaraf kawai take yasa Taufeeq cak yadauketa,biyosa sukayi,anan ma parlon ragowar 'yan biki suka taso ana tambayar lafiya?kowa yaganta yanda ta canza sai ya tausaya mata.

****
Daddy ne da Abba da Baba Hasheem suke farfajiyar gidan da alamun daga masallaci suke,gefensu Sauban ne kansa a tsaye,gani sukayi mutane duuuu sun fito daga apartment din Bodejo, Taufeeq dauke da mutum a hannu,cikin tashin hankali suka nufi wajen suna tambayar abinda ke faruwa,a rude Taufeeq ke tambayar ya Sauban akwai car key a hannunsa?batare da yabashi answer ba yayi saurin nufar motar sa yana mata key, banda bugawa babu abinda kirjinsa keyi,tambayar kansa yake me kuma ya sameta?batare da yasan maganar zucin da yayi tafito ba yaji Aunty Maryam na bashi answer"wallahi muma haka muka sameta a sashen Bodejo,sakata a motar Taufeeq yayi yana zaunar da ita kanta akan kafadar Aunty labeeba, Aunty Maryam ma tashiga,da sauri Ummie takariso a rude take sai tambayar inda zuhran take takeyi,tayi matukar rudewa,haka Ammi dasu Mom,nufar dayan motan tayi tana cewa Taufeeq ya tada"No Ummie ki zauna a gida insha Allah komai zaizo da sauki,wani kallo ta aika masa dashi jikinta yana rawa cikin rawar murya tace"Ace min ka dauko 'yata kamar gawa?shine kake tunanin zan iya samun natsuwa?lallai Taufeeq baka da hankali"cikin daga murya tace"kabudemin mota nace! Bude mata motar yayi Saboda ganin yanda ta canza lokaci daya,Ammi ma tashiga,Adda Zainab ne tabude bayan itama da sauri tafada banda salati babu abinda takeyi,nan fa kowa yayi jugumยฒ.
Su Laila kuwa sai kuka da kuka Saboda a yanayin da kowa yaga anfito da ita hankalinsa dole yatashi,a 360 Taufeeq ya figi motar,tuni securities din gidan suka wawwangale gate din.
"Ya Allah ya tayar da kafadunki Fatima, Amma ta fada hakan tana me juyawa,lallashin su Laila Rammat ta shiga yi tana yimusu fadan so suke su sake tayar ma da mutane hankali?su yahakuri insha Allah zata samu lafiya.
Koda labarin ya isa ga Akeela sosai tayi farin ciki da hakan don har addu'ah tayi kan Allah yasa kada ma ta tashi daganan ta mace kota huta da kallon ta tana kwasar takaici da haushi.


Xahratty Ce๐Ÿฅฐ
Lallai Alqalami ๐Ÿ–Š๏ธ yafi takobi๐Ÿ—ก๏ธ.
9/6/23.
[6/11, 12:36] Xahratty (OUM AJMAL): ๐Ÿ‘จ๐Ÿฝโ€๐Ÿฆณ *_GALADIMA FAMILY_*๐Ÿ‘จ๐Ÿฝโ€๐Ÿฆณ

Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

Marubuciyarโคต๏ธ
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now

*_GALADIMA FAMILY_*

Page 47/48

๐‘พ๐‘จ๐‘ต๐‘ต๐‘จ๐‘ต ๐‘ท๐‘จ๐‘ฎ๐‘ฌ ๐‘ซ๐‘ฐ๐‘ต ๐‘บ๐‘จ๐‘ซ๐‘จ๐‘ผ๐‘ฒ๐‘จ๐‘น๐‘พ๐‘จ ๐‘ต๐‘ฌ ๐‘ฎ๐‘จ ๐‘ด๐‘ผ๐‘ฏ๐‘จ๐‘ด๐‘ด๐‘จ๐‘ซ ๐‘ฒ๐‘จ๐‘น๐‘ฌ๐‘ฌ๐‘ด,๐‘ฎ๐‘ถ๐‘ซ๐‘ฐ๐’€๐‘จ ๐‘ด๐‘จ๐‘ฐ ๐‘ป๐‘จ๐‘น๐‘ฐ๐‘ต ๐’€๐‘จ๐‘พ๐‘จ ๐‘จ๐‘ณ๐‘ณ๐‘จ๐‘ฏ ๐’€๐‘จ๐‘ฉ๐‘ฐ๐’€๐‘จ ๐‘ด๐‘จ๐‘ฒ๐‘จ ๐‘ฉ๐‘ผ๐‘ฒ๐‘จ๐‘ป๐‘ผ๐‘ต ๐‘ฒ๐‘จ ๐‘จ๐‘ฒ๐‘จ๐‘ต ๐‘ต๐‘ผ๐‘ต?? ๐‘ฒ๐‘ถ๐‘ฒ๐‘จ๐‘น๐‘ฐ ๐‘ซ๐‘จ ๐‘ฒ๐‘ผ๐‘ณ๐‘จ๐‘พ๐‘จ ๐‘จ๐‘ฒ๐‘จ๐‘ต ๐‘ฉ๐‘ถ๐‘ถ๐‘ฒ ๐‘ซ๐‘ฐ๐‘ต.......๐‘จ๐‘ต๐‘ฎ๐‘ถ๐‘ต ๐‘น๐‘จ๐‘ฏ๐‘ด๐‘จ(๐‘น๐‘จ๐‘ด๐‘ด๐‘จ๐‘ป) ๐‘จ ๐‘ฉ๐‘ถ๐‘ถ๐‘ฒ ๐‘ซ๐‘ฐ๐‘ต ๐‘ฎ๐‘จ๐‘ณ๐‘จ๐‘ซ๐‘ฐ๐‘ด๐‘จ ๐‘ญ๐‘จ๐‘ด๐‘ฐ๐‘ณ๐’€๐Ÿ˜†

______wani Private hospital suka isa me kyau da tsada da alama nanne asibitin da ahalin suke hidimarsu,da isar su kuwa nurses din asibitin suka sanya ta akan gadon marasa lafiya kaitsaye emergency ward aka nufa da ita,likitoci uku ne suka tsaya akanta gefe guda kuma nurses biyu,su kuwa ahalin banda zarya babu abinda suke a dan dogon corridor din ward din sauran kuma duk sun zazzauna,idan ka kalle fuskokin su cike da alhini banda shi da yake zaune ya lumshi ido tare da jinginar da kai a jikin kujerar da yake zaune.
Sunanan dai zaune har 9:30 amma babu wani likita da ya fito bare a musu cikakkiyar bayani,dubansu Daddy yayi ya soma magana"Ku tashi kuje gida dare nayi muzamu jira har Doctors din su fito muji abinda ke wakana,matan ku koma gida"yakarisa maganar yana juyar dakai gefe daya.
Ummie ce tadago da niyyar yin magana amma sai takasa don Allah yasani tana tsananin girmama Daddy don musu bai taba hada ta dashi ba bare gaddama,cikin sanyin jiki suka mimmike,kallon Daddy Ammi tayi tace"Amma Daddyn su day kun bar daya a cikin mu ko kun manta cewa dole macece zata maida hankali wajen kula da ita?fuskan Daddy babu wani wasa yace"babu bukata zaku iya tafiya ga Sauban nan inma anbata gado zai zauna da ita ya kula da ita"Cikin mamaki suka dago suna dubansa,shima da sauri yabude idanuwan sa yana duban Daddyn nasa.Aunty Maryam tace"amma Yaya kamar hakan be kamata Saboda shidin ba muharraminta bane,kuma dole zata bukaci wani abu kamar shiga toilet da sauran su.
Wannan karan sake tamke fuska yayi yana maida duban shi gabadaya akansu yana kokarin magana, Abba ne yarigasa"Hakan ba matsala bane kawai kuje gida don muma munsan da hakan kuma munzauna a islamiya ba jahilai bane mu.
Babu wanda ya sake magana a cikinsu duk tashi sukayi suka fita ko wanne da tunanin da yake a cikin zuciyar sa, Ummie kuwa bataji dadi ba ko kadan sai dai bazata iya nunawa,cikin sanyin jiki suka nufi hanyar fita,duban Taufeeq Daddy yace"maza kaje ka maidasu gida dare nayi,amsa yayi cike da girmamawa yana me bin bayan su,muryan Sauban suka tsinkayo"Daddy taya zanyi jinyar ta?naga hakan sam be dace ba wallahi ni bansan ma yanda zan kula da ita ba.
Kafin wani yabashi answer doctor's din sun fito ko wanne na share zufa,karisowa Doctor Ahmad yayi Yana duban su Daddy"Alhaji idan babu damuwa zaku iya samu na a office,yana gama fadar haka yanufi office dinsa,kaitsaye rufa masa baya sukayi.
Waje yabasu suka zauna,nan suka shiga gaggaisawa da juna zuwa can ya sauke ajiyar zuciya yana duban fuskokin su"To Alhamdulillah munyi nasarar shawo kan matsalar tata ba wani abubane face damuwa wanda ya haddasa mata jinin ta yadan hau kadan tare da ciwon kai kunsan hawan jini ga zazzabi kuma a gefe daya,sai dai insha Allah munyi nasarar gano matsalar Allah yakara lafiya,amma gaskiya kuyi kokarin ganin kunji meye damuwar tata domin kuwa idan aka zuba mata ido a haka to akwai matsala,ajiyan zuciya suka sauke gabadaya Abba ne yayi karfin halin magana"insha Allah likita zamu kiyaye Allah yakara mata lafiya"Da Ameen gabadaya wajen aka amsa dashi suna me mikewa,rakasu Doctor Ahmad yayi yana tambayar me zama,duban shi yayi yace"ga Sauban nan shi zai zauna da ita yayi jinyar nata,da mamaki yake duban su don yasan alakar dake tsakanin Sauban da zuhra batare da nauyin baki ba yace"Amma Alhaji ina ganin da ansamo 'yar uwanta macece tayi jinyar ta idan ma babu sai mu duba muku a nurse's din mu.
Daddy ya danyi murmushi yace"Babu bukatan Doctor Ahmad don shidin mijinta ne......
Yana kare fadar hakan sukayi gaba abinsu, daga Sauban har Doctor Ahmad kamewa sukayi a tsaye kamar status saboda mamaki,wani murmushin jin dadi Doctor yayi,yana me

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login