Showing 96001 words to 99000 words out of 103469 words

Chapter 33 - GALADIMA FAMILY Complete Hausa novel

07 Sep 2024

6902

ta da jiki kada yasa ka mata kallon babba"tana ƙare faɗar hakan ta haye sama.
Ɗan sosai kai Sauban yayi tare da fita,gidan shi ya nufa,hango ta yayi a zaune a cikin ɗan rumfan,zuwa yayi ya buɗe ƙofan yana ƙoƙarin mata magana security ɗin gidan yazo wajen shi cikin sauri,magana ya fara masa koda ya juyo babu ita alamu sun nuna ta shige ciki,shima cikin ya shiga yana ƙoƙarin lallashin ta,koda ya shiga palour ta ta rufe bedroom ɗin da key, knocking yafara Mma Zuhra taƙi buɗewa sai ma kukan ta da yake ji nan ya shiga lallashin ta amma fir taƙi zuwa ta buɗe ƙofan,kai daga ƙarshe ma bathroom ta shige yana jin san da ta bugo ƙofan,kama kai Sauban yayi tare da juyawa ya koma kan sofa ya zauna,wasa² har 4 Zuhra taƙi buɗe ƙofan,hatta su Laila sun shigo taƙi buɗewa haka suka tafi,shima Sauban ɗin da ya gaji fitowa ya fice.
Jin fitan shi yasa ta fito cikin kwalliyar ta duk da batayi make up ba idanuwan nan a kumbure,kitchen ta shiga,ta buɗe friedge ta ɗauko naman dake ciki,nan tashiga tsince zallar tsoka,bayan ta gama ta wanke tasss sannan tasa a abin niƙa nama ta niƙa shi,gyaran kayan miya tayi sannan ta zauna tafara haɗa kayan girkin ta lokacin ma an kira magrib,komawa tayi tai sallah bayan ta idar ne ta koma kitchen ta ɗora dakakken naman ta, gabaɗaya ƙamshi ya buɗe gidan koda ya shigo wani lumshe ido yayi yana jin natsuwa har cikin zuciyar ta,tare da tausayin ta da soyayyar ta,kai tsaye kitchen ɗin ya shige,bata ji shigowan sa ba sai dai ji tayi anyi hugging ɗinta ta baya,ɗan fusge jikinta tayi tana nufar wajen gas ɗin ta buɗe tukunyar ta shiga motsa naman ta,nan ta zuba duk wani kayan ɗan ɗano,na ƙamshi da duk abin buƙata ta sake motsawa,sannan ta ɗauko ruwan kwakwan ta ta ɗan zuba ta rufe.
Sake matsowa yayi ya fisgota suna facing juna,da sauri ta sunkuyar da face, Sauban yace"Idan kin isa ki ɗago mana ƴar rainin wayo kinje kin haɗa ni da Ammi kinji daɗi?yayi maganar yana tsare ta da ido, Zuhra kuwa wasu hawaye ne suka taru mata batare da ta ɗago ba tafara magana"kada Allah ya nuna min ranar da zan haɗa ka da mahaifiyar ka yaya,amma ka yahaƙuri"tayi maganar voice nata na cracking,wani mugun tausayin ta yaci da wani irin son ta kamo haɓar ta yayi yace"Sorry Babyn Baby kiyahaƙuri nasan bazaki iya dama ji dani ba,hakan yasa na yanke wani hukunci"Zuhra bata saurare shi ba ta matsa taje ta cigaba da aikin ta,zama yayi a dinning ɗin dake kitchen ɗin me kujeru huɗu yana kallon ta,ganin yanda take komai cike da kulawa,jin da yayi an fara kiran isha'i yasa ya miƙe ya fita don zuwa sallah.
Zuhra kuwa a take anan ta haɗa lafiyayyar jollop ɗin cuscus wacce taji dakakken nama tare da Irish potatoe,tasa nasu a wani foodflask ɗin sannan tasa ma Galadima don shi mutum ne me son cuscus,gashi yaji kayan lambu,plantain ɗin da ta soya ta sa mishi a gefe, coslow kuma tasa mishi a wani ɗan glass bowl.
Nan ta fara shirya komai a dinning table ta kawo duk wani abin buƙata,sannan ta shige bedroom ɗin ta,wanka tashiga bayan ta fito ta tayar da sallah,nan ta shirya cikin wasu English wears,mini skirt tasa wacce ta tsaya mata iya kacin cinyoyin ta,sai wata bodyhug ta ɗora skirt ɗin a saman rigar tunda skirt ɗin dama me umbrella ne,banda wani sassanyan ƙamshi babu abinda takeyi, dai-dai tana fitowa dai-dai lokacin shima ya shigo,sosai tayi mishi kyau jiyayi kamar ya kamota ya dinga shilla ta sama,ɗan gyaran voice yayi yace"Nida Taufeeq ne"hakan yasa Zuhra komawa ta cire skirt ɗin ta ɗauki long trouser ta sanya tare da ɗaura P-cap a kanta,a dinning ta tarad dasu,cikin fara'a ta ƙariso.
"Yawwa yaya kamar kuwa kasan ina tunanin me kaiwa Galadima saƙo sai gaka"harara Taufeeq ya aika mata dashi sannan yace"idan har zaki iya aikena to wannan ma zaki iya aiken shi"yayi maganar tare da nuna Sauban.
Shiru Zuhra tayi tana ɗan murmushi, Sauban kuwa kallon ta yayi yana ɗan tsadadden murmushin sa yace"and so what?ai dama ni ɗan aiken ta ne,Please Baby ki aikeni duk inda kikeso kinji?murmushi Zuhra tayi, Taufeeq yaje"da dai yafi,nikam kiyi ki serving nawa kina ta yin namijin ki, ƙamshi ya cika min hanci"yayi maganar tare da ɗauko foodflask ɗin ya shiga serving ɗin kanshi.
Lafiyayyar jollop da taji dakakken nama ne da Irish,da carrot,grean beans,soyayyan plantain sai coslow da kowa ya ɗan kaɗan don dama kaɗan ɗin tayi gudun lalacewan ciki.
Gabaɗayan su suka fara cin abincin Sauban kuwa natsuwan shi kacokan ya maida ga Zuhra,ko yaya ta motsa sai ya bita da kallo,duk tana hankalce dashi.
[7/29, 00:20] 𝐎̃𝐔̂𝐌 𝐀̃𝐉𝐌𝐄̨𝐑𝐋💜🤍: 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_* 👨🏽‍🦳

Page:- 97/98

*~SECOND TO THE LAST PAGE~*

___Kwatsam Kuma sai labari ya canza inda mutuwar su Alhaji iliyasu da hajiya Aliya ya kasance shine,a sanda Hajiya talatu ƙanwar Alhaji Mansir taje gidan kai tsaye sashin Hajiya Aliya ta nufa batare da ko gate man yaga shigowar ta ba,aiko tana shiga ta ƙofan kitchen ɗin ta ta shiga nan ta hangota ta buɗe wani wammer tana ɓarɓaɗa garin wani abu,dakata wa tayi taƙi shiga sai da tabari ta gama sannan tayi wufff ta shige kitchen ɗin bayan Hajiya Aliya ta fice,aiko taɗau maganin ta ɓarɓaɗe a cikin tukunyar dake kan gas ɗin ta motsa ta ajiye ragowar sannan tayi wufff ta fice, don ita domin duk a tunanin ta maganin mallaka ne hakan yasa tayi haka.

Hajiya Aliya kuwa boka hatsabibi ne sukayi magana tace ya bata maganin da zata sama Alhaji yaci ya mutu tunda tana da ciki anyi scanning anga twince ne kuma duka maza so ita bata buƙatar cigaba da zama dashi kuma tana so taci gado,aiko nan boka hatsabibi ya bata inda ya sanar mata wannan maganin koba wanda yayi asirin bane yaci to shima fa zai mutu,sannan sai bayan awa goma sha biyu zaiyi aiki,aiko Hajiya Aliya tayi farin ciki ta amsa a ranar ta juyo don kada ya gane.
Shine washegari wajen ƙarfe 2 na rana ta zauna tayi musu girki ta ɓarɓaɗe masa a abinci bata sana angansa ba,koda ta kai mishi saman shi yayi yayi suci amma taƙi tace ita nata tayi mishi haɗi na daban ne na masu ciki ta cika yaji don dama tasan beson yaji,nan kuwa yaci abincin shi cikin natsuwa,itama taje ta zuba nata taci tana yi tana wani irin murmushin nasara.
Aiko ranar har anguwa zunje can babban family house ɗin su Alhaji iliyasu,daga can sukaje shopping ya haɗu ma babes ɗin shi kaya sosai suka dawo,a ranar Adda zainab har kuka sai da tayi,aiko cikin dare wajen ƙarfe biyu na dare cikin Alhaji iliyasu ya fara murɗawa,nan itama Hajiya Aliya nata cikin yafara nan fa suka dinga neman ɗauki,ai ko 5mnt basu haɗa ba rai yayi halinsa ba tare da kowa yasani ba.
Washegari da safe ita kuma Adda zainab nason fita ganin har wajen 9 bata ji motsin shi ba yasa ta nufi apartment ɗin nashi,nan ta cidda gawan su cikin bedroom ɗin sa,wannan abin ne ya firgita ta yasa ta fice da gudu tana faɗin Alhaji ya mutu,duk iya ƙoƙarin gate man na ya kamota ya kasa,hakan yasa yayi gaggawan kirar Ammar yazo suka nufi apartment ɗin Alhaji suka ci karo da mummunan abu,sannan gate man ya sanar masa Adda zainab ga yanayin da tafice,nan ya kira yayan Alhaji da ƙannen sa.
Shine Hajiya talatu na zuwa ta sake hargitse waje cewa Adda zainab ce ta kashe su don kullum iƙirarin ta kenan,kuma gashi ai ta gudu ya tabbata ita tayi kisan kenan?wannan dalilin yasa aka ɗora alaman question mark akan Adda zainab kenan har zuwa inda aka ganta da mutuwar ta.
To wannan CCTV camera footage shine ya bayyana komai tun dawowar su Hajiya Aliya garin har zuwa abinda ya faru,nan kuwa akayi ram da Hajiya talatu tare da kaita kotu koda akaje batayi ja ba sai dai tace ita arashin sani tayi duk a tunanin ta maganin mallaka ne,aiko kaitsaye aka yanke mata hukuncin shekaru hamsin a prison tare da horo me tsanani.
Hajiya talatu tayi kuka tayi nadama mara adadi.
Wannan kenan.
******
Sauban sam ya kasa gane kan Zuhra don da yayi mata magana sai ta masa banza idan ma ya matsa mata kuka take sa masa,sai dai muddin yazo amsar haƙƙinsa tana bashi,hakan ba ƙaramin tayar mishi da hankali yayi ba,haka dai suka cigaba da tafiya daƙyar da siɗin goshi ya shawo kanta komai ya dai-dai ta suka cigaba da shan soyayyan su ba sassauci.
Biki ya kama saura 5 day's hakan yasa shirye-shirye gidan suke babu kama hannun yaro,amare ana ta shiri inda ƙawayen su wasu duk sun shigo su shida,don haka a sashin Boɗejo suka sauka tsohon ɗakin Zuhra don nanne babu cikan jama'a,inda Ammi da Mommy ƴan uwa na jiki duk sun iso saboda events ɗin da za'ayi.
Yau ma kamar kullum zaune suke akan kujera 2 sitter kanta na cinyar shi sai wasa da gashin ta yakeyi zuwa can yace"Baby kamar jikin ki da fever fa ko?Zuhra tace"Something like that hub,cuz tun jiya nakejin hakan ga tashin zuciya sai dai ina haɗa hakan da ulcer dake tashi mun kwana biyu"
Sauban yace"Okey but ba kina Shan maganin ba? Zuhra tace"Yesss.
"To kodai zamuje hospital ne?Sauban yayi tambayar,zumbur Zuhra ta miƙa tana kwaɓe face,cikin shagwaɓa tace"Ni..Ni..dai gaskiya A'ah nifa ba sosai nake jinsa ba yaya,ni kasan abinda nake son ci yanzu?girgiza mata kai yayi tare da shafo face ɗin ta, Zuhra tace"Gullisuwa me daɗi Please"
Sauban yace"Eweee this girl na kwaɗayayya,kinga mouth ɗin nan naki?so ni ina zan samu gullisuwa?
Zuhra tace"Nidai shi zanci katashi muje munema Please"tayi maganar tana bubbuga ƙafa, miƙewa yayi yace"Okay to tashi muje,muje na shiryaki,"yayi maganar yana kamo hannunta.

Fita sukayi don nemo gullisuwa sosai Zuhra tabawa Sauban wahala don kuka sosai tasa masa da sukaje trade biyu basu samu ba,ƙarshen shi wani getto area suka nufa anan suka,don Sauban da kanshi ya fita suyo mata ya hanata fitowa saboda masu zaman majalisar da ya gani a layin group group hakan yasa yaji wani masifar kishinta ga idanuwa da duk yadawo kan motar nasa,yana zuwa 1k ya miƙa ma yarinyar ya tambaye ta na nawa ne?nan take ce masa na 650 ne,cewa yayi ta juye masa,ledar ta baƙa me kyau ta zube masa gullisuwar sannan ta shiga laluben canji,ce mata yayi ta barshi,sosai ta shiga godiya.
Shikuwa tuni yaja motar,mamakin ta yakeyi yan da take shan gullisuwar hannu baka hannu ƙwarya tare da lumshe idanuwa tana jingina kanta a sit ɗin.
"Sai kuma mene bayan wannan?ta tsinkayo voice nasa.
Zuhra ta dubeshi tare da murmushi tace"Allah yaya sai agwaluma,but nasan ba za'a samu ba cuz ba lokacin shi bane yanzu".
Sauban yace"lallai ma yarinyar nan yau da kwaɗayi ma kika tashi kenan?,bata tankasa ba ta cigaba da shan agwalumar ta har suka isa gida,koda suka koma farfesun kayan ciki kawai yace mata yanaso ya ɗan yi yaji saboda muran da yakeji.
Amsa masa tayi sannan ya fice shima saida suka tattake waje ya cema ta Daddy ke neman sa sannan ta barshi ya tafi.
A lokacin kusan ana gabda magrib ne hakan yasa ta shiga kitchen ɗin tafara ɗora masa bata bar kitchen ɗin ba sai da aka kira magrib,ga wani mahaukacin bacci da ya sakota gaba sai dai bata son yi sai ta gama masa pepper soup ɗin,shiga bedroom tayi ta wuce toilet ta watsa ruwa sannan ta ɗauro alwala,sallah ta tayar tana idar wa ta shige kitchen nanfa ta zauna anan cuz bata so ta koma bacci ya kwashe ta,ɗan rage gas ɗin tayi, dai-dai ana kiran isha'i ta sauke don tasan shi yafi son ta tayi laushi,plaintain guda ɗaya da ta yanka ta soya masa,sannan ta shirya su, plaintain ɗin tasa a plates ta rufe, pepper soup ɗin kuma ta sa a wani bowl ta rufe abinka da kayan tangaras riƙe zafi,a tray ta haɗa masa tare da spoon da pork sannan ta ɗauko ta fito,komawa tayi ta haɗo masa fresh milk nd Fairless a wani tray ɗin,glass cup nd bottle water ta fito dasu ta ajiye,palour ta koma ta cigaba da shan gullisuwar ta babu jimawa bacci yayi awon gaba da ita.
Babu jimawa kuwa ya shigo yagan ta tana barci,aiko peck ya bata a kumatu ya wuce dinning ya fara dinner ɗin shi,yana gamawa yakai komai kitchen sannan cak ya ɗauke ta,ya ɗau mata gullisuwar ta ya haye da ita upstairs, bedroom din shi ya wuce da ita sannan yayi mata addu'a yaja mata duvet tare da ƙara mata A.C don ita mejin zafi ne,toilet ya faɗa yayi wanka be wani jima ba ya fito yayi duk abinda ya kasance al'adar sa,aiko ya haye gadon a buƙace yake,hakan yasa shikaɗai ya fara kaɗan sa da rawar sa sai dai wani gigice wa yayi saboda wani daɗi da yaji ta sake,a bacci takejin komai sai dai sam takasa tashi,don sam Sauban be san ko isha'i batayi ba.

Bayan ya kammala komai yaje yayi wanka tare da dawowa ya rungume ta sai bacci.
Zuhra ko wajejen uku da rabi a yanayin jikinta kawai tasan yaya yayi aiki murmushi kawai tayi da ƙyar ta miƙe ta shiga toilet,wanka tayi sannan ta ɗauro alwala tazo ta tayar da isha'in ta,a daddafe ta koma ta sake kwanciyar ta.
*********
Bayan kwana huɗu yau ta kasance ana gobe biki,events an yishi babu magana,yau kuma dinner za'ayi duk yanda Zuhra taso zuwa Sauban ya hanata saboda zazzaɓin da takeyi,itama bata wani damu can ba,fita yayi saboda zasu kama ma mijin da zai aure Nihal hotel don yanzu haka suna hanya, shida Taufeeq da Kareem suka fice.
A can Ummie da Mom su suke abincin tarba,babu abinda kakeji na tashi sai hayaniya a Galadima house, Zuhra tana zaune ta jiyo motoci anzo ɗaukar mutane don tafiya dinner,hakan yasa Zuhra taji wani iri kamar ta ƙwala ihu.
Haka dai suka tafi sauban kam be wani jima ba ya shigo lokacin Zuhra tayi baccin ta abinta shi kam yana mamakin wannan baccin na kwana biyu da takeyi yauma har ɗaki ya kaita,haka ya cigaba da rainon ta like baby.
Washe gari kuwa da wani azababben zazzaɓi ta tashi da mugun ciwon kai duk da kuwa taƙi yarda ya gane,sa mata abin wuya yakeyi ta jikin mirror yana kallon ta.
"Baby kinyi balai'n kyau kinganki?har naji wani kishi"ɗan shagwaɓa face Zuhra tayi tace"kai yaya nidai ka barni na shiga cikin ƴan uwa na Please".
"But Baby kamar baki da lafiya right?
Cikin sauri Zuhra tace"Nop yaya mene kagani kuma?Ni lafiya ta ƙalau"
Murmushi Sauban yayi yace"Okay to muje,anko sukayi duk da ita lace tasa doguwar riga blue Black ta sanya veil white takalmi high heel white da ƴar hand bag ɗin ta white tayi kyau ainun.
Shima shadda ɗanya yasa sai maiƙo take blue Black,hulan kansa light blue haka halfcover ɗin ƙafarsa,hannun ta ya kamo suka fito,anan masallacin Alhaji Mai Deribe aka ɗaura auren sosai mutane suka halarta tare da sheda auren.
Muhammad Shuraim & Lailah Taleeb Muhammad,Aliyu Abdulhakeem& Barakah Haroun Muhammad (Nihal).
Aiko gida ya cika tanƙam da ƴan uwa da abokan arziƙi, Zuhra tana sashin Mom don acan su Aunty Mashahuda suke,itadai tunda ta ƙyallare ido taga wannnan jollop ɗin shinkafar da yaji curry hankalin ta ya tashi,wani mugun amai taji ya taho mata,duk iya ƙoƙarin ta na ganin ta danne ina,da masifar gudu ta shige toilet.
Gabaɗaya su Aunty Safeena suka bita suna lafiya?sai dai Zuhra amai takeyi sosai don jikinta har wani irin rawa yakeyi,cikin sauri Aunty Safeena ta kamota daƙyar ta gama aman nan,haka tatafi luuuuuuuu.
Yaraf! Ta zube a jikin Safeena,salatin suka sanya suna tattaɓa ta sai dai babu numfashi babu alamun sam babu numfashi a jikinta.
Gabaɗaya sun gigice, Mom ma ta taho,ruwa aka ɗauko a fridge aka shafa mata sai dai ko ajiyan numfashi batayi ba, Mom ta dubi Aunty Safeena cikin ruɗewa"Me yafaru da ita ne haka Safeena?
Aunty Safeena taba ma Mom labarin komai.
Mom tace"To ai zama be ganmu ba,maza² kikira Sauban"nan Safeena ta lalubo Number sa tahau kira,har 2 times beyi picking ba,tana shirin sake kira ya kira ta.
"Hello yaya kana inane?daga can Sauban ya amsa mata, gamu nan a apartment ɗin Mom don Allah idan babu damuwa kazo"cikin sauri ya Sauban yace"What is happening Safeena? where's her Zuhra?
In Ina Aunty Safeena tafara,ko kafin tayi magana ya yanke don a lokacin fitowan shi kenan daga apartment ɗin Ammi yaje gaida ƴan uwan ta,cikin zafin nama ya shigo palour ko bi takan mutanen palour beyi ba,ya danna ma Safeena kira,hakan ya tabbatar mata da ya shigo palour.
Mom tace"bari ni naje.
Aiko babu jimawa sai gashi sun taho da ita,tambaya ya shiga yi meya same ta?hankalin shi tashe ya ɗauke ta ya fito,nan duk suka biyo shi.
Mutanen palour suka mimmiƙe Hajiya Biba tace"Subhanallah meya sameta ne haka?nan duk mutane suka fiffito,Mom da Hajiya Biba sai Aunty Safeena suka bishi don motar shi dake bakin gate ya ɗauka gabaɗaya hankula ya dawo kansu kafin kace me magana ya zagaye gida.
Aiko Mommy itama shiryawa tayi tare da yayar Ammi suka bi bayan su Taufeeq da Kareem suka kaisu,duk da kuwa jama'an da Mommy keda su haka ta tsallake su.
Kaitsaye hospital ɗin su Dr Ahmad suka nufa cuz sun fi zaton suna can.
********
Sauban kuwa suna isa a take anan aka nufi VIP da ita Doctor's sukayo kanta cuz gabaɗaya Sauban ya ruɗe ganin ko motsi batayi ga jikinta ya saki gabaɗaya.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login