Showing 48001 words to 51000 words out of 103469 words

Chapter 17 - GALADIMA FAMILY Complete Hausa novel

07 Sep 2024

6893

dafe kafadar Sauban wanda yayi suman tsaye banda bugawa babu abinda zuciyan sa ke masa yarasa me yakeji a zuciyar sa,farin ciki yake ko bakin ciki?baisani ba,cikin tsananin murna Doctor yace"Na taya ka murna oga Sauban Ashe auren gata aka maka? congratulation!wucewa yayi yana cigaba da mamaki don shima yaso ace ya mallake Zuhra a matsayin matarsa,yana tsaye jikinsa na sake sanyi,ganin tsayuwar babu abinda zai masa yasa ya juya,direct dakin yanufa cikin tafiyar da na izza da kasaita,a hankali yaka ma handle din ya murda,a makoshi yayi sallama tare da kutsa kai cikin dakin da aka canza mata (VIP) idanuwan sa kuri akan kyakkyawar fuskan ta wanda yini guda kawai yasa ya yamutse saboda ciwo,kallonta yakeyi kawai yakeyi jikinsa na sake sanyi a gefe guda yana jin taya shi zai iya rayuwa da mata har biyu?to ta inama shi zaifara?tambayar da yayi ma kansa kenan.Haka ya samu kan kujerar dake gefen gadon nata ya zauna batare da ya dena kallon ta ba yana kissima abubuwa da dama akanta,duban agogo yayi yaga sha daya da kusan rabi ne ma na dare,lumshe ido yayi batare da yanajin dadin zaman kujerar ba.

A can gida kuwa duk da mamakin su Daddy suka dawo tare da tambayar kawunan su a zuciyoyi mezesa suyi haka?shi kanshi Taufeeq mamaki ne fal ransa,sai dai rashin samun me Basu amsa yasa kowa yakasa furta komai,koda su Aunty Maryam suka isa apartment din Galadima tambayan su me jiki sukayi tare da me kwana da ita,cikin alhini suka basu amsa da wai Sauban ne zaiyi jinyar ta,ganin fuskokin tsofaffin sukayi normal babu wani alhini, Galadima yace"Hakan ma yayi Allah yabata lafiya ya kuma tada kafadun ta,da Ameen suka amsa jikinsu nasake sanyi da lamarin ahalin nasu masu cike da abubuwan mamaki.A sashin Ummie kuwa sun tadda Amma har tayi bacci abinta don dama kafa ya matsa mata, Adda Zainab ne keta sababi akan mezesa su Daddy suyi hakan?ita kuma Ummie takasa magana kan abinda yake faruwa,ajiyar zuciya Ummie tayi tace"bazan iya tambaya ba Adda domin koni dana haife Zuhra bankai bayin Allah nan sonta da kaunar ta,ni ina tunanin suna da kwakkwaran dalilin su nayin haka don dai haka kawai bazasu yanke wannan hukuncin ba.
Adda Zainab tace"Hmm to ai shikenan Allah ya kyauta meson dangin miji ke dama sam bakison a fadi lefinsu koma dai menene?ai hakan dai bedace haba jama'a sai kace ana garin ga6a²,shiru ita dai Ummie tayi bata tanka ba.Hajiya Aliya ce tadubi Adda Zainab tace"Niko aminiya yaushe Alhaji iliyasu zai dawo ne?saboda munada biki acan gombe inaso da muje tare da kene,kinsan hajara na zata aurar da 'ya next week,cikin mamaki Adda Zainab ke duban hajiya Aliya tana sakin dariya"Eyye aminiya kina nufin hajara har zata aurar mu muna zaune?lallai aiko ya kamata muje ma hajara biki ai komai zaizo da sauki nima gobe zan koma nafara tarban dawowar shi don jibi zai dawo yace jirgin 4:00 zai biyo, cikin farin ciki hajiya Aliya tace"Kai naji dadi ai nida kaina ma zan tambaye shi domin nasan zaiji dadin hakan sosai,dariya Adda Zainab tayi tace"gaskiya kam zaiji dadi sosai Allah yadawo min dashi dai lafiya kinsan yatafi yana fushi danine don naki binsa sai a waya muka shirya,hajiya Aliya tace"Ai tafiye²n nan irin nasu ba kowace mace bace zata jura kinji kiyi zamanki anan wallahi, Adda Zainab tace"yanda kikajin nan.

Ummie najinsu sai dai bata tanka ba don asanin kanta duk abinda za'a cema hajiya Zainab akan hajiya Aliya ba yarda zatayi ba saboda son da take mata,tasani yanda takeson hajiya Aliya bata mata irin wannan son tun suna secondry school,sabanin ita da take tsananin son yayar tata,mikewa tayi don nufan dayan sashin nata don duba sauran jama'ar nata nan tabarsu suna cigaba da hirar su,da wani irin mugun kallo Adda Zainab tabita dashi tanajin kamar tatashi ta makure ta tahuta.
Bayan fitanta cikin dacin murya Adda Zainab tafara magana"Aminiya boka hatsabibi bai kyauta minba,ba haka kukayi dashi ba nidai duk aikin da yabani nayi nayi amma kina ganin ma idon ki babu abinda yayi aiki ni garas ma naga takari,gaskiya zan canza wani bokan ki samo min wani nikam bazan iyaba wallahi so ake ciwon zuciya da bakin ciki su kashe nine ko mene?Hajiya Aliya tace"Kash!Kash!! Dadina dake Aminiya gajin hakuri,munyi magana dashi nayi masa korafi sai dai yace lefin ki ne wallahi domin kuwa duk aikin da kikayi sun lalace sai dai besanar dani yanda akayi suka lalace ba,amma kinsan idan kika fadi wani magana mara dadi akan boka hatsabibi kema baki masa adalci ba,shekara nawa yana miki aiki kuma anga dacewa don kawai wannan anyi kuskuren da kecema kikaja sai kifada haka?wallahi banji dadi ba idan yajiki kuma babu ruwana.Adda Zainab tace"gaskiya ne idan nafada wani abu nayi butulci aikam zanje nane mesa da kaina domin magance matsala ta.
Hajiya Aliya tace"Da dai yafi kam,haka suka cigaba da tattaunawa akan matsalolin su har suka raba dare.

*********
Wajen karfe 2:40 ta farka a hankali tashiga bude ido still tanajin kan na mata ciwo sai dai baikai na farko ba,kwata² babu karfi a jikinta ga wani masifaffen fitsari da takejin ya matseta,muryan ta da babu wani kwari ta bude tafara magana"Ummie! Ummie!! Ummie!!! Zanyi fitsari"kamar a mafarki yakejin muryan nata don shi mutum ne wanda beda nauyin bacci,bude ido yayi ya zubanya mata batare da yayi magana ba,magana tasake still"Ummie zan shiga toilet,mikewa yayi yana me kunna switch din,room din ya gauraye da haske,ido biyu tayi dashi wani irin kamewa tayi akan bed din duk da kuwa wani irin fitsari da takeji ga rashin karfin da bata dashi ko kadan jinta take kamar a wani duniyar,tamke fuska yayi ganin yanda ta kura masa ido alamun ta tsorata dashi,bata fuska yayi da kyar ya bude baki ya soma magana"Zaki tashi narakaki toilet dinne ko zakiyi a zaunenne?yayi maganar yana tsura mata dakwa-dakwan idanuwan nan nasa,cikin rawar jiki ta mike sai dai ko second biyu batayi ba tatafi luuu zata fadi,cikin hanzari yakarisa yana me tallabo ta jikinsa,duk cikansu sunjisu a yanayi na daban a dalilin hakan,kamata yayi suka nufi toilet din wanda yakejinsa fess kamar ba'a hospital ba sai kamshin Toilet freshener yake Dana hypo,kokarin sakinta yake amma sai yaga tatafi luuu,ita kuma ga azababben fitsari tanaji kuma yaki matsuwan mata,rasa yanda zaiyi da ita yayi a hankali yake jan kananun tsaki saboda takaici shi sam bema san yanda zai mata ba,ganin haka yasa Zuhra fashewa da kuka tanajin wani irin takaici don dai ba'a kyauta mata ba da aka barta a daki daga ita sai shi,tafada a cikin ranta,ita batasan tana hospital ba,karfin hali yayi ya jingina ta da bango tare da dukawa,doguwar gown din dake jikinta ya fara dagawa,jikinta babu inda baya rawa kafafuwan ta naneman gaza daukan ta don ita abune wanda be taba faruwa da ita ba,a hankali ya cire mata pant din face dinsa babu walwala yace" Oya yikiyi, am waiting for you.
Ganin da tayi bata da wani mafita yasa tafara kokarin yin fitsari ai babu zato bare tsammani tafara sakin shi a tsayen,runtse idanuwa tayi da karfi tana mejin wani irin mahaukacin kunya tare da takaici,shima takaicin a gefensa yake ji don ma anci sa'a bata fallatso mai da fitsarin ba da ya kafa mata mari acewar sa,idanunta a rufe,bude tap taji yayi nan ya jinginar da ita daga jikin bangon sosai yana me matsawa tare da kauda kai yace"Yi tsarki mufita,duk kincika ma mutane toilet da zarnin fitsarin ki,mtsewwww! Yaja siririn tsaki.
Zuhra kamar kuwa babu zato taji hawaye na sirnano mata,cikin rashin abin yi tayi tsarkin ta gama,kamata yayi suka fito yana zaunar da ita akan gadon,idanuwan ta arufe ta kwanta tana jin kanta na juya mata.
Kashe switch din shima yayi yana me komawa yazauna kan plastic chair din,kowanne da abinda yake sakawa a ransa,babu jimawa bacci yayi awon gaba da ita saboda alluran da aka sa mata a drip din harda na bacci,jin yanda take sauke numfashi cikin natsuwa ya tabbatar mata da tayi bacci don haka yamike ya shiga toilet din don dauro alwala.

*~DA ALAMA BA KARAMIN CAKWAKIYA BANE ZAI AFKU GABA,NINAGA LABARIN NATA TSAYINE ANYA KUWA ???~* 😂😂

Xahratty CE🥰
Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️.
11/6/23.
[6/14, 10:59] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳

Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now

*_GALADIMA FAMILY_*

Page 49/50

*_KUYAHAKURI PLEASE DUK DANI NA TSARA LABARINA NAKE KUMA RUBUTA ABINA SAI DAI WANNAN KARAN LABARIN SHIKE TSARANI YAKE KUMA JANA😂FATAN KUN GANE ABINDA NAKE NUFI?INA KOKARIN INJA BURKI,SHI KUMA YANA WASKEWA🤣*
*PLEASE FORGIVE ME MAKARANTA🙏🏽GABADAYA LABARIN SADAUKARWA NE GA MASOYA BOOK DIN GALADIMA FAMILY.*


______Shi mutum ne me kyankyami gashi babu abin sallah don haka yabude kawai app din complete Qur'an dake wayan sa na Alaramma Ahmad Sulieman yafara karatun,itakuwa bancin ta takeyi cike da natsuwa,haka Sauban ya cigaba da karatun sa har aka kira sallar asuba,toilet yakoma yadauro alwala yafita don neman masallacin asibitin ya gabatar da sallah.

*******
A can kuwa washegari haka suka tashi jiki a sassalube sai dai hakan be hana hidiman na bikin kawatuwa ba,cikin sauri su Aunty Maryam ke hada abin breakfast din 'yan asibiti su Laila na tayasu don bada su za'a koma Zaria ba, Rammat ma said tayasu aikin takeyi ta saje a cikinsu sosa,'yan aikin Ammi kuma suna na amare Akeela,sai wajen tara suka gama hada breakfast din.
Da mommy dasu Aunty Maryam su Nihal sune suka nufi asibitin,don Abba, Daddy, Baba Hashim tun safe sukaje asibitin amma bata farka ba,haka suka dawo akan anjima zasu sake lekowa,Koda suka isa baya dakin sun ciddata tana zaune bayan ta pillow ne an jingina mata,ganinsu ba karamin murna tayi ba sai dai kallo daya zaka mata kasan tanajin jiki, basket din duk suka aje suna Isa bakin gadon suna mata ya jiki,shimfina dan babban carpet din da sukazo dashi sukayi,nan wasu suka zazzauna,mommy dafa kanta tayi tace"Sannu my baby ciwon nan naki na jiya ya tsorata mu sosai,ke Kinga yanda kikayi zuru-zuru kwana daya kawai,dan lumshe ido tayi cikin karfin hali tace"mommy nama ji sauki fa,duban su Aunty Maryam tayi tace"Mommy Maryam,mommy labeeba ina kwana?amsa mata sukayi cikin sakin fuska tare da tambayar ta ya karfin jikin nata?amsa tabasu da Alhamdulillah.Cikin tsokana Nihal tace"mufa munzata shekawa zakiyi har munfara tanadin gumba,duka akasa dariya,cikin karfin hali Zuhra tace"ai idan na sheka ku kanku bazakuji dadin zama a family dinba wallahi,cikin Wasa Laila tace"injiwa ya gaya Miki?lallai mudai kinmana bakin cikin cin gumba,kwafa tayi"hahaha kubari na warke zakuga yanda ake rashin mutumci.Duka 'yan dakin dariya suka sanya,dai dai sukayi sallama suka shigo dakin,shida Taufeeq ne,kallo daya ta masa ta kauda kai da sauri don harga Allah batason hada ido dashi,hada ido sukayi da Taufeeq wanda Kai tsaye yanufo inda take,langabar dakai tayi cikin muryan shagwaba tace"Yayaaaa sai yanzu ko?
Murmushi dauke a face din taufeeq yace"sorry kanwaty aike dince kin tadama kowa hankali jiya kowa ya rude,tana kokarin magana aka turo kofar aka shigo.
Shuraim ne da wasu 'yan mata biyu sai wata 'yar dai babban mace kamar su Aunty Maryam sallama dauke a bakunan su,hanayen 'yan matan kuma rike da ledoji riki-riki sai basket,cikin mutumtawa da girmamawa mommy dasu Aunty Maryam suka tarbesu,nuna musu wajen zama sukayi.
Koda suka zauna gaisawa suka farayi da juna,shiko kaitsaye wajenta ya nufa face dinsa dauke da damuwa,tsira mata idanuwa yayi kamar zai lasheta cikin tausayin da wani irin murya yace"just one day?jibi yanda kikayi?gaskiya koban gani ba nasan kin wahala,yakarisa maganar kaman besan da mutane a dakin ba,duk sauraran sa sukeyi cike da mamaki.
Dukar dakai tayi yashiga wasa da 'yan yatsunta masu daukar hankali da sukasha jan lalle,dan murmushi Shuraim yayi yace"kidago face mana nine kikejin kunya?ya karfin jikin naki?
Ahankali tace"naji sauki Alhamdulillah.

Cikin jindadi yace"Alhamdulillah to ga Aunty na, aunty safiyya wadancan kannena ne,khairat da khausar su din twins ne,yayi maganar yana nunasu,duk ya jiki sukayi mata,maida hankali yayi yashiga gaishe da 'yan dakin inda su kuma su Sauban musabaha sukayi,jiyake kamar ya shake yaron saboda wani mugun tsanar da da yaji da haushin sa lokaci daya,kawai yazo yanama mutane wani rawar kai,mommy ce tadube Sauban tace"Son ya kamata fa kazo kayi breakfast itama yanzu za'a Sanya mata,duban Aunty labeeba tayi tace"please labeeba zuba ma Sauban abinci.
"No mommy kinsan wallahi bazan iya cin abinci a hospital ba yanzu ma zan wuce gida nayi wanka sai nayi breakfast.
Da yake mommy Sarai tasan halinsa shiyasa bata jaba tace"To shikenan amma yakamata ka hanzarta don kada kayi ta zama da yunwa ko?cikin kamewa yace"insha Allah mommy yanzu zamu tashi.

Duban zuhra tayi tace"Baby meza'a zuba miki?akwai Chip's nd eggs sai samosa,akwai faten Irish da hanta sai kuma doughnut wanne zakici,cikin sanyin murya tace"mommy nikam nakoshi mouth dina babu appetite ko kadan shiyasa,mommy tace"to da yunwa kike tunanin za'a barki?kitashi kici abinci ko Yaya ne sai kisha magungunanki,nannarke murya tashiga yi tana neman botsarewa,wani kallo ya aika mata dashi cikin sa'a kuwa suka hada ido.
Mommy ki zuba mata abincin za'a tsaya jin tabakin ta ne?kamar bashine yayi maganar ba saboda ko dagowa beyi ba daga daddana wayan da yakeyi,kamar zatayi kuka take dubansa.

Mommy tace"wanne zakici a ciki?

Cikin sanyin murya tace"faten Irish din,zuba mata akayi dai-dai,dayake jikinta din ba wani kwari bane dashi, matsowa Aunty labeeba tayi ta shige bata abincin a baki,duk da bakinta babu dadi amma taji dadin faten ainun,dakyar aka lallabata ta gama shan faten shima saboda Sauban ne daya tsareta da idon dina.Shuraim kuwa jiyake tamkar yayi kuka don Allah yasani yana tsananin masifar son zuhran,duk abinda yake Sauban na ankare dashi shys gabadaya ya nemi walwalar sa yarasa jiyake kaman yaje ya kama yaron da duka.
Duk suna zaune zuwa can sister's din Shuraim suka mike kan zasu wuce,'yan matan nan kuwa sun mutu akan Sauban,mommy tace"Haba kukuwa har zaku wuce da wuri haka?yarshi tadanyi murmushi tace"Ai mommy Shuraim dinne wallahi zanje gdn bikin wata cousin's dinmu but Saboda shidai nayi squeezing din time muka wuto,kinsan yanda yake son zuhra kamar ya maida ta cikin ciki yasake haifota"duk cikan 'yan dakin dariya suka Sanya har taufeeq,shikuwa ogan yasake cudu² da face sam babu walwala, Shuraim kuwa sosa kai yaketa tayi cike da kunya.Mommy tace"Allah sarki ai dama hakane,mungode sosai domin a haka ma mune da godiya matuka Allah yabar zumunci,da Ameen duk suka amsa,duban shi Aunty safiyyan tayi cikin zolaya tace"Ouncle Romeo oya let's go! Nan ma dariyar aka sanya,dan susa kai yayi yace"Aunty muje nadai taka muku don bazan iya barin ta ita kadai ba wallahi look at her Aunty gaskiya muje na taka muku,duk da mamaki ake duban sa wannan karan Sauban tsaban mamaki daskarewa yayi don ko dago face ya kasayi,yana mamakin rashin kunyar yaron,a ransa yace _Lallai dole ne yaron yayi nasarar sace zuciyar kanwar tasa,dole ya Mike tsaye._
Fita sukayi Mommy kuwa sai dariya suke, Aunty Maryam tace"Lallai zuhra wannan yaron yana matukar son ki gashi kunyi masifar dacewa don shima kyakkyawa ne,ga natsuwa da alama idan kika aure shi zakiji dadi don bai boye irin son da yake miki, Laila tace"wallahi kuwa Aunty Yaya Shuraim na matukar sonta sosai, cousin's din su ya Asheer din Aunty safeena ne,hada baki sukayi wajen fadin dagaske?Nihal tace"Allah kuwa yace mata shi idan ma akace yaturo yanzu Allah zai turo don hajiyan su da kowa nasu suma sunason hadin musamman da sukaji kanwar Aunty safeena CE, Mommy tace"Kai Nihal duk a'ina kikejin wannan labaran? Laila tace"wallahi Mommy dagaske ne ya Asheer ke fadama Aunty safeena da mukaje gidan,ai gaskiya wallahi.....batare data karisa ba ya Sauban yadaka mata tsawa yana diddilo mata wannan idanuwan da suka koma jajaye,tsit tayi daga ita har Nihal jikinsu babu inda baya rawa,ita kanta Zuhra banda rawa babu abinda jikinta keyi ganin haka yasa ta zamiye ta juya tana me rintse idanuwan ta.Maida duban sa yayi ga Mommy yace"haba Mommy meye amfanin ku tasa yaran nan a gaba ana firar samari?dudu shekaran su nawa da suke hirar samari?wato ana ma sane tana karatu take kula wasu 'yan iskan yara?cikin bacin rai da karaji yake magana,cigaba yayi"Lallai zaki zaba kodai auren ko karatu cikin daya kizaba daya ki aje daya,mtsewww! Yana kare fadan haka yafita yana mejin zuciyar sa na wani irin bugawa,Taufeeq ne yabi bayansa.
Duk cikan su day kallon mamaki suka bisa har yafita,ajiyan zuciya Mommy ta sauke,a ranta tana ayyana abubuwa ita kadai, Aunty Maryam da Aunty labeeba suka mike suna duban mommy"Aunty Hauwa'u mu zamu wuce kinsan tafiya kaduna zamuyi akai Mashahuda gidan ta,kafin keda Ummie ku karaso, Mommy tace"Ea nasani babu damuwa ai Labeeba Allah yatsare don Allah ki tabbata tasha magunguna nan,muneefa ma na aika mata da nata,can gidan ta zamu wuce mu"Aunty Maryam tace"Insha Allah.zumbur Zuhra ta mike duk da kana ganin yanayinta kasan karfin hali take face dinta babu wani walwala kamar tayi kuka tace"Mommy!juyowa Mommy tayi tana duban ta,cikin rashin abinyi da damuwa tace"Mommy nifa inason karatu na kibawa ya Sauban hakuri nazabi karatun Amma wallahi inason ya Shuraim,duk da mamaki suke dubanta,su Laila kuwa sai guntse dariya suke.
Aunty Labeeba tace"ke Zuhra ki rufama kanki asiri kibar maganar nan a yadda naga Sauban yafita a fusace ai idan kika cigaba d maganar nan zai kassara kine a banza,kuma wannnan abin tun zamanimmu ne ba kukadai ba,duk wacce karatu zatayi to bata aure sai tagama degree,bakiga su Mashahuda da muneefa bane?mu kanmu sai da muka gama diploma mukayi aure,wallahi ki rufama kanki asiri kada kikawo wani sabon tsari, Aunty Maryam tace"Ah to kidai fada mata.
Mommy cike da tausayin ta take duban ta,batare da tayi magana ba suka fita ita dasu Aunty Maryam,cikin raunin murya mommy tace"wallahi Maryam inajin tausayin Zuhra,soyayya tayi gaggawan shigowa rayuwar ta da wuri duk da farin jinine ma yasake ruruta wutar wani abu,inajin tsoron abinda zaije yadawo kinsan yayyen nan naku?ita kanta tana son yaron haka zalika shima da baya iya boye sonta ko gaban wanene,a gefe daya Zuhra na matukar son karatu yana daya daga cikin abinda yasa sam tatsani wani ya mata maganar soyayya kenan to Amma kinga yaron nan yaci galaba a kanta?Suma ajiyan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login