Showing 30001 words to 33000 words out of 103469 words

Chapter 11 - GALADIMA FAMILY Complete Hausa novel

07 Sep 2024

6881

su huci zuciyarka yakai mebiya mana bukatun matsalolin mu( _wa iyazubillah_)

"Ya isa hajiya Aliya kunfi kowa sanin abinda kukamin kun batamin aikinda tunda nake babu aikin da nasha wuya akansa sama da wannan,me kuke zaton yafaru?yayi maganar yana zaro musu mummunan idanun saasu kama da attarugu saboda ja.

Kunsan aljanu nawa aka konamin a aikin nan?tabbas wadanda sukayi aikin nan ba kananun bane,duk sharrin dan dagiya da masanu sai da aka konamin su,duk cikin aljanuna babu jajirtattu irin su.

"Wallahi bazan kyale ko waye ba sai na dauki fansa akan abinda akayi musu koba yanzu ba.

Su dai su hajiya Aliya sun kasa magana banda rawar jiki ba abind sukeyi.
Duban dayan yayi yace"yanzu me kikeso a musu?don shiryawa sun ruga sunyi itada diyar ta sai dai wani zancen ba wannan ba.

Jikinta na rawa tafara magana cikin rawar murya.

"Duk da 'yar uwata ce ubanmu daya amma nayi mata wani irin tsana mafi muni, duk da cewa mahaifiyar ta tafifitani akanta tanuna min soyayyar da bata nuna mata ba amma inajin muguwar tsanar ta a zuciya ta, takasance ta taso da soyayyar mutane da dama ne a zuri'ah mu harda mahaifinmu,wallahi boka hatsabibi bana sonta kuma ba zan taba sonta ba,inason ka sabauta min bilkisou yanda ba zata moruba.

"Hhhhhhhh boka hatsabibi ya shiga qyalyqala dariya,zuwa can ya daure face.
"Aikin ki sai na sake nemo wasu aljanun kuma shedanu saboda kinsanta da rukon addini bata wasa da azkar to zanyi shiri na musamman akanta,don yanzu haka tana kwance a asibiti jinita ya hau a dalilin karya sihiri nan da akay .........

"Allah dai yakashe ta ma kihuta aminiya,cewar hajiya Aliya.

Wani kallo boka ya watsa mata.

"Ba Amin ba nine nan ajalinta,mutuwar ta a hannu na take,sai dai wannan aikin ba kamar ko wanne bane don inada tabbacin duk me zatayi se yaci,amma kema zakiyi wani aikin daga bangaren wasu ayyukan.

"Ni Kuma?tayi tambayar tana zaro idanuwa.

"Eah ke!wannan karan mata biyu zasuyi amfani dake,bi ma'ana zasu mu'amalance ki.

"Kamarya yaya boka?
Duban hajiya Aliya yayi yace"kiyi mata cikakken bayani.

Nan hajiya Aliya tashiga yima aminiyar ta bayani yanda zata fahimta,ai bata bari rakarisa ba tadafe kirji tace.

"Ni Zainab bantaba madigo ba kuma banjin zan iya aikatawa.

Daga hajiya Aliya har boka daure fuska sukayi.
Boka yace"to duk inda zaki babu me yimiki maganin matsalar ki muddin baki aikata wannan abin da nace ba.

"Mtsewwww!hajiya Aliya taja tsaki tace kika ma aikata wadanda sukafi wannnan muni da sabo wannan ne bazaki iya aikatawa ba lallai baki shirya ganin nasara ba.

"A'ah ba haka bane aminiya da girma na da komai aganni ina madigo?
"Waye zai ganki?cewar hajiya Aliya.

"Boka hatsabibi yace a gabansa za'ayi fah 😥

"Mtseww Kinga idan bazaki iya ba tashi mu tafi makwancin mu zuwa safe mu tafi gida.
"A'ah matsalata dake saurin fushi aminiya,cewar hajiya Zainab.

"Toh ai ke dince da kayan haushi,idan kin shirya kiyi magana.
Da sauri ta daga kai alamun ta amince.

Nan boka hatsabibi ya rufe ido yana wasu yare kafin kace wani abu wasu katta kattan mata biyu bakake sun shigo ta kofan,babu sutturan arziki a jikinsu.

Ba hajiya Zainab kadaiba,hatta hajiya Aliya sai da ta hadiye wani irin miyau na firgita.

***** *KADUNA* ****

Ansamu Ummie ta farfado tana tare dasu mommy, Amma da kannen ta maza, Abba ma yana asibitin don su Daddy ance suna hanya.
Hawaye kawai takeyi tana ambatan sunan Zuhra.

"Amma na manta da Zuhra a babin rayuwata wallahi ni naman ce wai bayan Taufeeq inada wata diyar,meyasa na aikata mata hakane fisabilillah?

Takarisa maganar tana zubar da hawaye masu dumi da zafi.

"Ba laifinki bane Ummie wannan duk wanda yagani ko yaji labari yasan aikine na sihiri akwai farraqu a lamarinku,ba gashi ba yanzu da akayi magani komai ya warware?

Mommyn yara bazaki gane me nake nufi ba,Abbie ya rasu batare da na cika mishi burin shi ba naganin naja diyata a jiki,ya rasu yana tausayin diyar shi da fargaban halinda zata shiga na kiyayyata bayan bashi,kuma hakan baitaba shafan zaman mu ba.
"Allah yasani duk wanda da sa hannunshi akan wannan lamarin ban yafe ba kuma sai Allah ya bimin hakki na.

"Wallahi kuwa bazamu yafe ba, Amma tafada tana kuka.
Dai-dai nan ne kuma su Daddy, Galadima, Bodejo, Ammi, Mom, Sauban, Zuhra suka shigo dakin bakunan su dauke da sallama.
Ummie jikinta har rawa yake ta sauko daga bed din ta nufosu,zazzaro idanuwa takeyi kawai tana laluben ta inda zata ga Zuhra.

Zuhra kuwa ganin ta nufo inda take ne yasa jikinta kama rawa ta runtse ido tare ruqunqume kwankwason Sauban gam,fadi take.

"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un don Allah Ummie kiyahakuri babu abinda na miki please bazan kara ba,na hadaki da Allah please kiyahakuri wallahi.

Shesshekan kukan da tadinga ji daga maban bantan bakuna ne ya sata bude ido.
Ummie tagani a durqushe tana kuka mai sauti, Amma ma da Bodejo kukan sukeyi.

Duk da haka jikinta rawa yakeyi takasa sakin Sauban don ita batasan tama rikeshi haka ba,Ammi ne ta matso tare da kamota tazo da ita har gaban Ummie inda take durkushe.

"Zuhra Ummien ki tadawo gareki, Ummien ki mai sonki tadawo gareki dama banace miki ba?kidena jin tsoro kinga kinsata kuka koh?
Kamar wawuya haka zuhra takoma tana kallon Ummie tana kallon Ammi.

Kamo hannunta Ummie tayi wanda gabadaya ilahirin jikinta yashiga rawa tafara magana.
"Zuhra diyata kiyafemin bansan abubuwan da nake mikiba a baya hasalima nina mance ma na haihu tun washegarin sunan na manta ki a shafin rayuwa ta,don Allah kiyafemin.
"Ni maisonki ne,ni me kaunar kine,ina tsananin begenki,please diyata forgive me my babe.


Xahratty CE🥰
Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️
14/4/23.
[5/4, 14:37] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳

Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now

*_GALADIMA FAMILY_*

Page 29/30

_Bismillahir-rahmanir-raheem._

*BARKAN KU DA SALLA MASOYA FATAN ANYI SALLAH LAFIYA,WADANDA SUKA RIGAYEMU GIDAN GAAKIYA ALLAH YAJIKANSU.....YAWWA NACE BA GORON SALLAH KADA A MANTA DUK WANDA ZAI BADA YAZO A BASHI ACCOUNT NUMBER😁HAR NAMAN SALLAH DA CIN-CIN ZA'A IYA TUROWA TA ACCOUNT.*

*DUBUN GAISUWA A GAREKU MAMAN ASLAM,MMN TAUFEEQ,UMMU MEE'AD,GODIYA DA TARIN KULAWA.*


________Gabadaya dakin daga masu tayasu kuka sai masu juriya haka suka kasance, Zuhra kuwa wani irin nishadi takeji wanda tunda take bata tabajin irin sa ba.
Nan Galadima yake sanar dasu abinda yafaru,babu wanda baishiga shocked ba, Ummie haka ta taso ta rungume Sauban tana me sake zubda hawaye cikin muryan kuka tace.
"Nagode son Allah ya saka maka da mafificin alherinsa bazan taba manta kaba a rayuwa ta, Allah ya dafa maka a lamuran ka.
Amma tace"ubangii Allah ya baka mata tagari me kula dakai Allah ya daukaka duniya da lahira.
Gabadaya dakin sai amsawa akeyi da amin,ita kuwa Mom takaicin irin addu'o'in da ake kwaranyo ma Sauban takeji,domin ji take kamar ta shake shi ya mutu kowa ma ya huta,banda yaqe babu abinda takeyi.
Anan suka sake godiya ga Allah akayi addu'o'i suka dunguma kuma jabi road don Ummie sarai ta warke, Zuhra na maqale a gefenta.

Ko kafin su iso Abba yasa anyimusu oder lafiyayyun kalolin abinci,tuwon shinkafa miyan egusi,jollop din shinkafa,sakwara da miyan alayyahu sai snack's da drink's.

A babban sashen Galadima suka zauna wanda idan yashigo da kaduna yake zama,matan kuma suka nufi sashen Ummie.
Amma tace"Niko lafiya hajiya Zainab gabadaya number ta baishiga?nakirata ban sameta ba nakira number farida tace batanan tayi tafiya.
Ummie tace"toh ina Adda Zainab taje ne?tayi tafiya kuma takasa sanar dake Amma? gaskiya da mamaki.
"To nima dai shi nagani,ita takanta taci burin zuwan wannan ranar shiyasa nake nemanta fa, Allah ya kyauta bari zuwa anjima nasake gwada kiranta.
******
Hajiya Aliya da hajiya Zainab kuwa basu da wani choice da yawuce amsan bukatan boka,haka hajiya Zainab tanaji tana gani wadannan kattin matan sukayi amfani da ita sannan a gaban boka hatsabibi yana watsa musu wani irin ruwa yana cigaba da surkullen sa.
Sai da suka shafe awa daya suna abu guda zuwa can suka kyale ta,boka yace suje zuwa anjima tazo ta amsa saqon magungunanta,su kuma matan suka zauna anan.
Banda dariyar keta babu abinda hajiya Aliya keyi ganin yanda aminiyar ta ke tafiya a tattale,sosai hajiya Zainab ta kulu ta dubeta da niyyar tayi magana amma sai ta rigata.
"Kada kice komai don tun kafin ayi hakan dake akayi dani fin sau goma,ke nifa idan har akan biyan bukata ne zan iya komai,ke ko boka hatsabibi ne yace yana son kaina zanbashi,ke ko dan mutum yace nakawo zankawo.
Takarisa maganar tana taunar chwengum"kas kas kas".
Sai yau hajiya Zainab tasake yarda lallai aminiyata hatsabibancin ta ko shedan tsoron ta yakeyi.
"Nikam mu amsa maganin nan mutafi don wallahi Alhaji baisan da fitana ba kuma kowane lokaci zai iya dawowa,gashi layina ba za'a iya samu ba.
Hajiya Aliya tace"toh mukoma mu gaya masa mukam tafiya zamuyi yanzu.

Haka suka sake komawa inda babu abinda ke tashi a dakin sai hayaqi da wani irin wari,sun dauki minti biyar a tsaye kafin boka hatsabibi cikin muryan tsawa yace.
"Tsayuwar me kuke musu a hanya alhalin zasu wuce,wallahi duk Wacce aka gurgunta babu ruwa na,duk cikansu jikinsu na rawa suka fada dakin.
Zama sukayi a kasa,wani bakin kwarya boka hatsabibi ya dauko tare da yin wasu yare sai ga kullin magani guda biyu sun bayyana,hannu yasa ya dauka inda yadaure face tare da duban hajiya Zainab yace"Kinga wannan hajiya,kije kisamu dai-dai kan inda 'yar uwanki ke kwanciya ki barbada wannan garin maganin,babu wanda zai gane kinsa wani abu,ni kuma ina tabbatar miki da muddin anyi aikin yanda ya kamata to fa 'yar uwanki zata kamu da mummunan ciwon barin jiki(paralysis)wanda har tabar gidan duniya babu maganin shi.
Sai kuma wannan kisamu abincinda kikasan shine abincinda tafiso duk cikin abinci ki barbada mata hhhhhhhhhhh....daga zarar kika barbada mata taci kowa gudunta zai dingayi harta 'yan uwanta da uwanta ke da kowama nata,don zata dinga magana ne bakinta na wani irin aman wari tare da fitar da wasu tsutsotsi.
Wani irin dariya hajiya Aliya da hajiya Zainab suka sanya najin dadi.
"Idan wadannan basuyi ba to dole sai munyi mummunan aiki akansu.
"Ayi boka hatsabibi ka kasheta inaso ta mutu natsani in daga ido naga bilkisou.


"Hhhhhhhhh kisa a ranki aikinki ya kammala gashi kutafi yanzunnan.
Da sauri suka mike ko gidan da suke sauka basu koma ba don dama bawai sunzo da kayan canji bane,hand bags ne shima suka tura driver hjy Aliya yaje ya dauki musu,nanfa suka fafaro hanyar dawowa lajeria🤪

______ *NIGERIA*______

Haka wadannan ahalin suka kasance cikin farin ciki inda a washegari Sauban zai koma Malaysia,ummie ma tace zataje maidugri kusa da diyarta ta kwana biyu ta dawo.
Tunda babu daman ita ta zauna kodan school dinta,inda Amma itama atake anan tace zata bisu taje sosai sukaji dadi babu bata lokaci Abba da Daddy suka fita nema musu jirgi Wanda zaije borno kona 5:00 pm ne.
Cikin yardan Allah kuwa suka samu jirgin inda nan suka tafi suka bar su mommy da Abba da kewarsu,maimoon ma sai rigima suke kan sai sun bi Ummie.

Washegari tun 7:00 am Kareem yadauki Sauban don kaishi airport,jirgin 7:30 zaibi hakan yasa basu wani jima da isaba aka fara neman matafiya aiko nan Sauban yatafi suna ma juna waving hannu shida Kareem.

Anan ma wani sabon kwarkwaryan walima aka hada don su Mashahuda sunyi farin ciki haka su nihal saboda babu wanda besan 'yar tsaman dake tsakanin Ummie da Zuhra ba.

Duk da tasan yatafi Amma sai ta nemi walwalarta tarasa tunda taji labarin shine mutumin da yayi aikin haqo asirin da aka mata itada Ummien ta sai taji wani kiman sa da darajar sa a zuciyar ta,musamman da taji irin kasada da hadarirrikan dake cikin aikin tare da wahalar da yasha sai mutumcin sa ya ninku a idon ta,duk da tasan bawai yinsa take ba hasalima ba birgeta yake yaba yasata jan tsaki akasar ranta ta furta " _to meye abin damuwa da tafiyar nasa?kekam wawuya ce._"

Yinin ranar kwanan farin ciki wadannan ahalin keyi,don saura kiris Zuhra tayi lattin School ko wanka batayi ba ta sulale tatafi gashi suna da test.

*MALAYSIA*

Yauma kamar kullum sanye yake cikin suit gray sosai yayi kyau duk da fuskar sa babu alamun fari'a ko kadan amma hakan 'yan matan company din nan keta binshi da mayataccen kallo,dan tsaki yayi kasa² tare da sake tamke fuskar a hankali ya isa office dinsa.

Nan aka fara shigowa yimasa barka da zuwa maza da mata.
Aiki yakeda shi sosai akan wani designer shoe da yafito wanda sam bema bayyana ba shine take su hada don ko babu komai a fara gani a company nasu shysa take so busy yaudin kam,don duk wanda yazo nemanshi ma baya ma samunsa saboda ya gayama secretary dinsa cewa duk wanda yazo tace yana aiki.
Bashi yabar office ba sai kusa to 6:18 na yamma kaitsaye wani shagon coffee yanufa saboda wata hardaddiyar yunwar da yake jinsa.

****** *NIGERIA* ******

"Ni gaskiya yau zan dawo kanme zakice nakara lokaci?kinsan kuwa irin takurar da nake anan?ni da wallahi nasan yau zai jiya zai wuce da tun shekaran jiya na dawo gida,ganinan dawowa yanzu.
Akeela takarisa maganar tare da datse kiran tana jan dan siririn tsaki a fili tace"mutum sai shegen taurin kan tsiya,yama kulani baikulani ba hasalima kamar besan da wanzuwa ta ba.
"Lallai iska na wahal dame kayan kara! Taji an bata amsa ta bayanta.
Juyowa tayi don ganin ko wace isasshiyar ce.
Rammat ce zaune kan 2sitter din daya daga cikin set din kujerun guda biyu dake farlon,ta daura kafa daya kan daya sai girgiza su takeyi bakinta dauke da chwengum tana tauna,dagowa tayi akaro na biyu tasake watsama Akeela wani banzan kallo tare da cewa.
"Ko mara aji nason mace me aji,ko wawan namiji nasan mace me aji kisama ranki cewa keda ya Sauban tazarar ku tamkar sama da kasa ne yayi Miki nisan da baki isa ki cimmasa sai dai kizo a 'yar aikinsa".Sosai kalaman Rammat suka batama Akeela rai wanda har yasata kasa control din kanta cikin tsantsan hargagi da masifa tataso ma Rammat"karya kikeyi karamar karuwa karamar kilaka,karya kike kice tazarar dake tsakanina da ya Sauban tamkar sama da kasa ne don ko babu komai nidin jininsa ce kuma dan gaba kadan zan zama uwar 'yayansa"takarisa maganar tana zabgama Rammat harara.
"Ahayye cassss! Lallai saifa su jininsa su jininsa an wahala,shiyasa ai naga yana tattalaki tare da riritaki ko?ko kina tunanin bansan irin shige da fice da gwagwarmayan da kike bane don samu soyayyan sa?wallahi ba baki nake miki ba Akeela keda samun soyayyar ya Sauban sai Allah,muddin baki natsu ba kinsan Allah ya faku,maganar karuwan ci kuwa ke har kinda bakin magana akan wannan?ke wani irin badala da ta'asa ne bakiyi?kunna datan ki,kishiga cikin IG naki kiga abinda na wallafa.
Tana kare faden hakan tadauki handbag dinta tare da barin farlon zuciyar ta fal farin ciki duk da taji zafin maganganun da Akeela ta fada mata amma tasan ko babu komai nata martanin yafi zafi.
Da sauri Akeela ta dauki wayar ta da niyyar shiga IG dinta sai ganin kiran Suby tayi,da sauri tayi picking call din.
Jin abinda Suby ke karanta mata tacan bangaren yasa zuciyar ta sake tsinkewa batare da tabari takai aya ba takatse kiran,babu zato sai ga Kiran zuleey itama.Dogon tsaki Akeela taja tare da rejecting call din tana meshiga cikin IG dinta inda tafara cin karo da sakon ni ta DM dinta,shiga tayi tafara duddubawa inda banda dakan lugude babu abinda zuciyar ta keyi,kaitsaye wall din Rammat tanufa nan taci karo da wani post da Rammat dintayi wai.
_Wai Wanda akasa ma Rana da Akeela ba sonta yakeyi ba hasalima itace tashiga tafita tare da bin malaman tsubbu da matsafa aka shawo mata kansa har akasa rana,a hakan ma shidin baya sonta don yanzu haka tana gidan su don farauto soyayyar sa,inbanda karuwa ma jahila ce taya zatayi tunanin kamilin mutum irin wannan zai so karya kamanta? Tabbas ta yaudare kanta da bata tantance dai-dai da akasin hakan,mudai namu ido Allah yakaimu lokaci musha biki._

Abinka da celebrities kafin wani lokaci magana nata trending a social media wasu har screenshot sukeyi,wani kwallan takaici ne yazo ma Akeela a makoshi cilli tayi da wayar kan kujera tare da fita daga apartment din Ammi,kaitsaye apartment din Mom tanufa.
Mashahuda da fitowan ta kenan daga apartment din Abbie don kaima su Ummie abinci taganta,dan tabe mouth tayi.

Itakuwa koda tashiga ta cimmusu sunata aikin hira da shewa,ai tana Isa batayi wata wata ba cikake tassssssssssss!


_KUYIMIN AFWA MAKARANTA MUNA FAMA DA MATSALAR WUTAN NEPA NE DON BA SAMU MUKE BA,SHIYASA NAKETA ASUSUN NA'URAN NAN NAYIN CAJI🤧, XAHRATTY MAI KAUNAR KUCE🥰._

XAHRATTY CE🥰
Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️
1/5/23.
[5/4, 14:37] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳

Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now

*_GALADIMA FAMILY_*

Page:- 31/32

_Bismillahir-rahmanir-raheem._

_______Duk cikansu mikewa tsaye sukayi Mom,muneefa,banda Rammat dake zaune dafe da kunci baki a sake,aiko minti biyar ba'a kara ba itama tamike batayi wata wata ba tasauke ma Akeela tagwayen maruka dama da hagu wanda har sai da yasata yin taga² zata fadi,cakumo ta tayi tare da fara magana.
"Ni sa'ar kice ko ko ancemiki ni irin yaran da kuka raina ne kuje har inda suke ku dakesu,tayi maganar tana me wujijjiga akeelar abinda da dama ba kiba.
"To bari kiji idan kina cin kasa kikiyaye ta shori wallahi duk randa kika sakemin wannan jakan cin sai nabiki abinda a kungiyar kuma babu wanda zaiganeki usless kawai.Sosai Akeela tayi mmkin abinda Rammat tayi mata kuma bazata iya ramawa ba don tasan tafi karfinta amma tadau alwashin sai tasa anrama mata ko badane ko bajima,haka tamike jiki a sabule tana fadin"wallahi ki rubuta ki ajeyi sai nabaki mamaki sai namiki abinda baki zata ba....
"Kindade bakiyi ba don abu kaza naki ina jiranki",takarisa maganar tana me nufo Akeela,ai dagudu tabar farlon tana cigaba da zage².
Mom da muneefa kuwa mezasuyi banda dariya saboda yanda Akeela tabasu dariyar.
Koda nufar ta apartment din Ammi cikin sa'a tacidda babu kowa a farlon haka ta isa bedroom dinda tasauka tashiga hada kayanta,babu bata lokaci ta jawo trolley bag dinta nanma bata ci karo da kowa ba kaitsaye fita tayi daga farlon.
Haka tafita gidan tare dajan dan akwatinta don barin layin,saboda a layin ba'a samun adaidaita sahu sai anfita don ma suna farkon layine.
Haka tabar layin cike

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login