Showing 27001 words to 30000 words out of 103469 words

Chapter 10 - GALADIMA FAMILY Complete Hausa novel

07 Sep 2024

6884

da mikewa.
"Dakata!!! Inazaki a haka?Akeela dai kika kawo ta zauna koh?to Shikenan kidauke ta kikaita wajen Aishan.
Guggo Laure tamike inda Akeela kuwa tuni taja trolley dinta tafice cikin jindadi.

*******KADUNA*******

Sosai Ummie taji dadin ganinsu ya Sauban tarasa inda zata Sanya kanta don murna,haka tasa me aikinta takawo musu breakfast don wajen 9:30 suka iso shikuwa Aseef kaitsaye BQ yanufa batare da yaje gaida Ummie ko Mommy ba,koda yashiga wanka yasakeyi yacanja kaya,don sunyi da wata yarinya zasu hadu zai kama mata daki daga adamawa.
Gidan tsohon governor jahar kaduna sukaje shida Taufeeq wajen abokinsa Hamid anyi biki Sauban baisamu zuwa ba kuma sosai ran Hamid yabaci,don ko zuwan baisan dashi ba.

Basu suka shigo gidan ba sai wajejen Tara nadare shiyasa Ummie tarufe ido yadinga yimusu fada sosai,abinci tace suje dinning suci ita tawuce bangaren Abbie don tunda tadawo acan take kwana.

Sunji dadin hakan sosai,sai da suka jira dare yayi nisa sosai misalin karfe sha daya sannan suka nufi bedroom din Ummie kaitsaye, Taufeeq yamiko ma Sauban man da su Daddy suka bayar sukace wanda zai dakko da hannunshi a cikinsu yashafa.
Ansa Sauban yayi ya shafa tare dayin wasu addu'o'i sosai kana yaduka yakai hannunshi.
Jikinsa ne yakama rawa saboda damko tukunyar kasan da yayi,kokarin fadi takeyi daga hannunshi kuma tabbas idan tafadi da matsala,jikinsa kuwa jiyake tamkar anjona mishi shock kota ko ina.
Taufeeq bakaramin tsorata yayi ba saboda yanda yaga Sauban nayi,gashi duk wata jijiya dake kansa tafito banda zufa babu abinda yakeyi.
Sauban kuwa jikinsa jiyake kamar ana yankan naman sa,jiyake kamar yasaki tukunyar amma taurin zuciyar shi bazaisa yayi hakan ba.
Cikin yardan Allah dai yajawo tukunyar yadaukota,wani irin hayaki ne ke fita daga tukunyar,cikin sauri Taufeeq ya watsa garin maganin da malama Baba yabada a watsa,zuwa can kuma hayakin yafara raguwa,haka rawar da jikin Sauban keyi shima yafara raguwa,a hankali kuma komai ya lafa.

Da sauri Taufeeq ya nannade tukunyar da wata bakar kyalle da aka basu, Sauban kuwa kamar jira yake a amsa yazube kan gadon,kansa namasa wani azababben sarawa.

Ruwa Taufeeq yadauko masa anan fridge din Ummie dake dakin,da qyar Sauban ya iya tashi hannunsa dafe da kansa,idanuwansa sun kada sunyi jazur,sai da Taufeeq yatsorata daganin idanuwan Sauban.
A haka Taufeeq yakamasa suka nufi bq yakaishi dakinsa don kowa da nashi dakin,sannan yace zai kwana anan don bazai iya tafiya yabarshi a yanayin da yake ciki ba.

A haka dai suka kwana jikin Sauban gabadaya babu dadi abin kama da jarumi don sosai yakeda dauriya acewar Taufeeq.
Koda safiya tayi dakyar ya iya shiga toilet ya watsa ruwa yafito,wannan man shi yashafa a jikinsa tare da kundundunewa cikin duvet saboda zazzabin daya rufesa,shidai Taufeeq hankalinsa yayi kololuwan tashi don haka yafara neman layin Daddy.

*OLD MAIDUGRI*

"Lallaima yarinyar nan ni akeey babe zata yaudara?wallahi bata Isa tabar kunya ba kuma dole itadin mallakina ce ko tanaso ko bataso kubarni da ita dole nakira boka na yayimin aiki akanta ni zata ci amana?hajiya daharatu tayi maganar cikin fusata.
Zuleey ta tabe mouth"hmm mommy kenan ai Akeela ta mutu akan gayen nan kumafa bason ta yakeyi ba da ita da wannan kwadayayyar kakan tatace suke wahalar da kawunan su.
Murmushin jin dadi daharatu tasaki tace"kice akeey 'yar wahala ce,yo metake nema anjikin da namiji?me zata tsinta?wallahi saina bata mamaki saina hanata jindadin rayuwa.

"Ai mommy saikinyi tsaye fa don bikin baiwuce saura six month ba,inji zuleey.

"Hmm kisha kuruminki dani take zancen wallahi.Tayi maganar tare da sakin kwafan bacin Rai don sosai ranta yabaci.

*GALADIMA HOUSE*


Xahratty CEπŸ₯°
πΏπ‘Žπ‘™π‘™π‘Žπ‘– π΄π‘™π‘žπ‘Žπ‘™π‘Žπ‘šπ‘–πŸ–ŠοΈπ‘Œπ‘Žπ‘“π‘– π‘‡π‘Žπ‘˜π‘œπ‘π‘–πŸ—‘οΈ
20/3/23.
[5/4, 14:36] Xahratty (OUM AJMAL): πŸ‘¨πŸ½β€πŸ¦³ *_GALADIMA FAMILY_*πŸ‘¨πŸ½β€πŸ¦³

Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

Marubuciyar‡️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now

*_GALADIMA FAMILY_*

Page:- 25/26

_Bismillahir-rahmanir-raheem._

β€ŽΨ§Ω„Ω„Ω‡Ω… Ψ¨Ω„ΨΊΩ†Ψ§ Ψ±Ω…ΨΆΨ§Ω†

Welcome Ramadan πŸŒ™

Wishing all our Muslim brothers and sisters good health, luck and wealth on its moon sighting tonight March 22, 2023 before fasting commences. Ramadan Kareem, may Allah bless you with happiness and grace your home with happiness & peace and may all your good deeds, prayers and devotions get acceptance by Allah Almighty during this blessed month of Ramadan.

π•πˆπ“π€π‹ π‹πˆππŠ ππ”πˆπ‹πƒπ„π‘π’ 𝐀𝐍𝐃 πƒπ„π•π„π‹πŽππ„π‘π’.

______Sosai hankalinsu yatashi musamman Bodejo tunda taji halin da akace Sauban na ciki, Ammi ma yashiga sai dai sam bata bayyana damuwar da take ciki ba addu'ah tadinga yimasa a cikin ransa tare da rokon Allah yabashi nasara.

Akeela na zaune a parlo kusa da Ammi don Mashahuda tunda taji ance wai tazo ta zauna ne tabar parlon takoma bedroom dinta.
Wayarta ce tafara ringing ganin sunan mommy wato hjy daharatu yasa da sauri tamike tanufi kitchen,da kallo Ammi tabita batare da takawo komai a ranta ba.
"Hello my sweet mommy....
"Dallah can rufemin baki munafuka,mukike kokari ki munafurta Akeela?to bari kiji wallahi Koda zanyi yawo tsirara baki isa kibar kungiya ba kuma baki isa kice zakiyi aure ba,sannan duk abinda kikeyi kizo inason ganin ki tana kare fadar hakan tadatse kiran.
"Mtsewwww nikam wallahi babu wanda ya isa yace zai hanani aure kuma da mijin da nake burin aure mijin da kowace mace zataso kasance wa dashi haka kawai bazai yuwu ba.
Komawa cikin parlon tayi fuskar ta cike da tsantsar damuwa ta isa ga Ammi cike da bariki tace"Ammi zantafi gidan su kawata Suby yanzu akakira ni wai tafadi tayi targade a hannu shine zanje naduba ta"takarisa maganar cikin marairaice fuska.
"Subhanallah gaskiya ya kamata kuwa kije amma don Allah kiyi sauri don bayan la'asar kiyi maza kidawo don Daddyn ku kinsan baison fitan dare.
Sake marairaice face Akeela tayi tace"Insha Allah Ammi nace please kibani number dear nakirashi na sanar dashi fitata.
Ammi tace"wanene Kuma dear ni Aisha?
"Oh ya Sauban nake nufi Ammi.

Ammi tace ok to bari nabaki,daukan tsadaddiyar wayar ta tayi tabawa Akeela tasaka number,zuciyar ta cike da tsantsar farin cikin tasamu number mafarkinta,mikewa tayi babu jimawa tafito tare dama Ammi sallama tafita zuciyar ta cike da tsantsar farin ciki.
Tazo dai-dai fita gate dinne kuma saiga muneefa da Rammat zasu shigo, wani banzan kallo duk cikansu su biyun suka watsama juna ,dogontsaki Rammat taja tana me tofar da miyau,da mamaki muneefa ke dubansu gabadaya.
Akeela kwafa tayi tare da yima Rammat gargadi da yatsu taraba au tawuce tana karkada shafaffen boom boom dinta.

"Useless kawai"Rammat tafada cike da bacin rai.

"Aunty rahama meke faruwa ne tsakanin ki da Akeela?meyayi zafi haka?
"Natsani wancan 'yar iskan yarinyar duk duniya bani da babban makiyiya sama da ita kuma wallahi sai nayi maganin ta ahankali.
Muneefa tace"kiyahakuri mushiga daga ciki kawai banji dadin banzan kallon da tayi miki bane don ko babu komai wata kusan tafi wata mushiga ciki.

******
Daka kalleta kasan a fusace take zaune take akan wata dakakkiyar kujera banda karkada kafafuwa babu abinda takeyi tana huci,gefen daman ta matane masu irin shekarunta,daya gefen kuma 'yan mata ne ciki harda zuleey da Suby.
Shigowa tayi parlon ganin fuskokin kowa yasa jikinta yin sanyi kaitsaye wajenta ta isa.
"Mommy kiyahakuri nasan nayi lattin zuwa wallahi bansamu dan adaidaita bane da wuri,sorry my sweet mommy,tayi maganar tana shasshafa mata face.
Da sauri hajiya daharatu tabige hannun tare da mikewa tadubi Akeela ido cikin ido tana huci tace.
"Nizaki yaudara Akeela nizaki ci amana?to bari kiji wallahi baki isa kici amanata ba kisanni sarai kaf cikin wadannan,tayi maganar tana nuna mutanen dake wajen da yatsa tace"Babu wanda yasanni a cikinsu sama dake kinsan ni nasanki kinsan abinda zan iya da wanda bazan iyaba wallahi wallahi kinji na rantse muddin kika ce zaki bijirewa umarni na to saina illataki.
Sosai gaban Akeela ke bugawa don tabbas tasan halinta matukar sani ta kuma San batada Imani ko kadan,muryan ta yana rawa tafara magana.
"Mommy kiyahakuri walahi bazan taba barinki ba inanan tare dake babu abinda zai rabamu nida ke,inason ya Sauban amma son da nake masa baikai wanda nake Miki ba,idan babu damuwa zanso nayi magana ta sirri nidake.
Banda harara babu abinda momy ke zubama Akeela,zuleey kuwa burinta kawai hajiya daharatu ta kore Akeela daga kungiya ita kuma tazaga tayi cuku-cukun rabata da Sauban din ita ta auresa.
Daya daga cikin manyan matar ne tafara magana fuskar ta dauke da murmushi tace"haba baby kibata dama mana.
"Auntyn kayan dadi bazaki gane bane Akeela ta gama kaini makura tasan duk cikin yaran nan babu wanda nakeso da kishinsa sama da ita amma shine ita take kokarin ganin taci amanata.

"A'ah kifa dena saurin cewa cin amana kedai kuje bakisan mezata ce miki ba.
"Hmmm shikenan muje,hajiya dahara tayi maganar tana fara fita,cikin nishadi Akeela tabi bayanta,da wanj banzan kallo zuleey tabisu tana sake jin matsananciyar tsanar Akeela a ranta.

Samun wani lungu sukayi suka labe,anan Akeela tashiga shasshafe jikin hjy dahara,cikin muryan da takeyi najawo hankalinta tafara magana"sorry momy na kinsan koda zanyi aure ba'a son raina bane don babu harkan danafi so sama da wannan"takarisa maganar tana cusa hannunta cikin kirjin hjy dahara.
Momy aure na da Sauban nasan na manufa ne shiyasa Guggo Laure tadage ayi shi,daga ni harke kinsan munada burin mallakar kudi banda wannan harkan,na amince da auren sa ne kawai badon komai ba sai don nadinga tara mana kudi nidake,sannan kwadayin Guggo ma nasan baiwuce akan kudin bane sam banason nayi maganar agaban wasu ne.
Lullumshe idanuwa hjy dahara tafara saboda abinda Akeela take mata,bude idanuwa tayi tasaka cikin na Akeela tare da tsuke fuska tace"bakison auren shine harkina rawa da murna a shafinki na IG da tiktok?
"A'ah wallahi momy nayi haka ne saboda mahassada na kinsan suna zagaye damu a duk inda muke.
Dan murmushi hjy dahara tayi tace"Ok na fahimta to kikiyaye gaba maganar gaskiya kuma kada ki rufa a sonsa da yawa na fada miki.
"Insha Allah momy"Akeela tayi maganar tana rungumo hjy dahara zuwa jikinta.

** *GALADIMA HOUSE* **
Zuhra cike da gajiya tadawo daga makaranta kaitsaye apartment din Ammi tanufa,babu kowa a parlon don haka tanufi dakin Aunty Mashahuda,koda ta isa tacidda ta tana waya kuma da alama da ya Taufeeq take wayan saboda yanda take maganar.
"Shikenan Darling T bari zankira ka zuwa anjima ka gaishe da ya Sauban din Allah yakara sauki.
Nan takatse kiran tana duban Zuhra.
"Yanzu kika dawo?
"Ea wallahi Aunty ai nadawo da matsananciyar gajiya ne a jikina shiyasa.

"Ok toh kisamu ki watsa ruwa zakiji normal insha Allah.
Zuhra tace"insha Allah yanzu kuwa Aunty,takarisa maganar tana zare turkey gown dinda tasanya kallon ruwan powder wanda yayi mata kyau sosai,towel din Aunty Mashahuda dake kofan bathroom tadauka tasanya.
Dan murmushi kadan Aunty Mashahuda tayi bayan Zuhra tashige toilet a hankali tace"zuhra duk namijin da ya aure ke yamure, Allah ya hadaki da miji nagari.

*KADUNA JABI ROAD*

Daqyar yatashi yayi sallan la'asar shima da temakon Abba don mommy batanan taje gidansu suna,tare sukaje da Nihal da Laila,kuma sai gobe zata dawo.
Zuwa wajen sallar magrib jikin nashi yadanyi dama sosai don haka bayan sallar isha'i yafara haka inda malam Baba yayi masa kwatance, Taufeeq na tayashi shidai Abba yana tsaye yana kallon wannan abin al'ajabin abu kamar a mafarki,suna cikin hakin ne hayaki yafara tashi sosai bakinkirin,sannan sai akafara wasu maganganu da wani irin yare wanda sam sunkasa fahimtar abinda ake cewa,jikin Sauban ne yafara rawa saboda jawo wani bakin tsumma daya farajawo wa daga ramin.
"La'iala ha illalllahu muhammadan rasulillah"kalman da yaketa ambata kenan shikadai yasan azaban da yakeji gashi yaki sakin kyallen,yana gama jawo wa atake anan yafadi sumamme,daga Abba har ya Taufeeq wajensa suka runtuma suna ambatan sunan sa.
Abba kuwa banda salati babu abinda yakeyi,a dai-dai kuma wannan lokacin ne itama Ummie tayanke jiki tafadi sumammiya don haka cikin rudewa Baba sa'a metayata zama kawar Amma ne tanufe ta tana ambatan sunanta tana girgizata.

Da gudu tafito inda ta taradda wani tashin hankalin ma nufar su Abba tayi tana cewa"innalillahi wa Inna ilaihirraji'un haruna wannan wani irin musiba ne yau ya tunkaromu a gidan?ga Bilkisou can itama rai a hannun Allah ta yanke jiki tafadi.....ai ko gama magana batayi ba Taufeeq yanufi cikin sashin Ummie cikin tsananin rudu.

Abba kuwa banda salati babu abinda yakeyi megadi yashiga kwala ma kira"safiyanu!safiyanu!!!kana inane?shima cikin rudu ya iso yace.
"Ranka shidade gani,maza kamamin Sauban munufi dakinsa dashi,aiko nan suka ciccibeshi sukayi na dakin don dama Aseef baya gidan,number Galadima yashiga nema.
Aiko babu jimawa yadauki wayar.

"Assalamu alaikum, Galadima barka da rana?nace don Allah meza'a baiwa Sauban yaciro dayan abin ne gashi jikin yafi bayama rikicewa ance Bilkisou ma tayanke jiki tafadi kuma ina zargin duk sanadin Ciro abinne.
Cike da dattaku da jarumta a muryan tsoho yasanar dashi cewa bari yakira Malam Baba yaji mezaice.
Katse Kiran yayi ko minti goma ba'ayi ba yakira Abba nan yashiga sanar dashi abinda zaiyi wato zaihada garin maganin nan da wannan man nacikin kwalba ya cakuda tare da karanta suratu ikhlas,falaq,nass sai yashiga shafa mishi Yana durza mishi a goshinsa,da toh Abba ya amsa tare da fara shafama Sauban maganin.

*****

Banda sintiri babu abinda takeyi tare da duban kawarta tsoro karara bayyane a fuskar ta tace"nashiga uku hajiya Aliya inatsoron tonuwan asiri na 'yan uwana sun yarda dani gashi kince boka yayi fushi dani.

"Hmmm aminiyata cewa fah yayi kinja anata Kona masa aljanunsa gashinan sunyi mummunan fushi dashi don haka nema yace"gobe da sassafe yana neman mu a dajin katamu inba haka ba duk abinda yafaru kiyi kuka da kanki.

Dora hannu aka tayi tafara kuka rurus tamkar wata karamar yarinya"innalillahi wa Inna ilaihirraji'un yazanyi hajiya Aliya?wani karya zanyi har Alhaji yabarni naje nijar?nashiga uku wallahi da nasan wannan tsinannen tsohon zai iya gano Shirin mu da dajin da babu wanda zai iya zuwa zansa abinne,
"Sannan wayaje har karkashin gadon Bilkisou yaciro wannan tukunyar?kadafa kimance boka yace"duk Wanda ya koda taba tukunyar ne mutuwa zaiyi balle ace wai andauko shi kacokar?

Xahratty CEπŸ₯°
Lallai Alqalami πŸ–ŠοΈ yafi takobiπŸ—‘οΈ.
22/3/23.
[5/4, 14:36] Xahratty (OUM AJMAL): πŸ‘¨πŸ½β€πŸ¦³ *_GALADIMA FAMILY_*πŸ‘¨πŸ½β€πŸ¦³

Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

Marubuciyar‡️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now

*_GALADIMA FAMILY_*

Page:- 27/28

_Bismillahir-rahmanir-raheem._

_____kamar yanda aka shafama Sauban maganin haka Baba sa'a ta shafawa Ummie,cikin hukuncin Allah Sauban yasamu dan dama sosai a jikin nashi,itakuwa Ummie da azababben ciwon kai tatashi dole tasa su Abba suka garzaya da ita asibitin giwa hospital ba'a dau wani lokaci ba aka bata gado saboda yanda Doctor din yasanar da Abba cewa jinin ummien yahau sosai.
Don haka Abba yakira Daddy yasanar dashi, Baba sa'a itace tayi zaman jinyar inda su Abba basu bar hospital dinba har kusan 10:30.

*****

Tunda Alhaji yakirata cewa bazai samu dawowa ba sai jibi yana da meeting aiko taji dadi don a daren gidan hajiya Aliya ta kwana.
Washegari kuwa da sassafe driver dinta yajasu a mota suka nufi nijar duk da tafiya ce me tsaho kuma da alama za'a wahala hakan bata shafesu ba sudai burinsu susami biyan bukata.

Haka yadinga falfala uban gudu dasu a hanya.

*OLD MAIDUGRI*

A washegari Sauban yadawo batare da taufeeq ba don shi yana tare da Ummie shima don saboda sakonin ne,koda yadawo babu jimawa suka kama hanya,Galadima, Daddy, Baba Hashim,Sauban suka nufi kauye don ganin malama Baba.

Basu wani jima ba suka kariso,tarba na mutumci malam Baba yayi ma aminin nasa,don zabi guda biyar yasa aka gasa musu shi sai madarar shanu mai dumi wanda banda maiko babu abinda yakeyi.
Sai da suka natsu gabadaya don har sallan azahar sukayi kafin malam Baba yayi musu ison shiga wani daki a cikin zauren nashi,ba wani wadataccen haske bane a dakin.
Duban Sauban yayi yace"malam muhammadu kawo sakonnin,yakarisa mahanar cike da raha.
Hannun Sauban na rawa yamika masa,aiko wannan kyallen yafara hayaqi inda akafara magana cikin wani yare,babu bata lokaci malam Baba yasaka kyallen cikin wata qatuwar kwalba,tare da rufe kwalban da murfinsa.
Aiko abin al'ajabi kyallen ne kewani irin girgiza a cikin kwalban,inda hayaki ya turnuke cikin kwalbar.

Tukunyar nan yadibo wani ruwa a kwarya yakafa baki alamun addu'o'i yakeyi kafin kuma yafara watsa ruwa a jikin tukunyar kasan,aiko nan tashiga daddarewa ko ina yana tsagewa a jikinta har yafashe dakansa inda wadu kulle-kullen layoyi suka shiga bayyana.
Hankalinsu Daddy ne yayi kololuwan tashi saboda cin karo da sukayi da hoton Ummie da zuhra ranar suna fuskar ta dauke da murmushi a kasa an rubuta,
_Mummunan farraqu,har subar gidan duniya basu babu juna wutar kiyayyar diyarta shi zai cigaba da wanzuwa a zuciyar ta._

"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un!!! Kalmar dasu Daddy suka shiga maimaitawa kenan, Baba Hashim yashare ruwan hawayen da yakawo masa, Galadima dukar dakai yayi Daddy da Sauban kuwa jijiyoyin kan nan tayi baro-baro.

"Ya Salam hasbunallah wa ni'imal wakeel,malam baba wannan wane irin musifa ne haka?wane mara imanin ne ya aikata haka?tabbas ko waye wannan yacika cikakken mara imani.
Galadima yayi maganar.

"Huhhh Sauban yafitar da wani huci idanuwan nan sunyi jajazur,kansa har wani irin sara masa yakeyi.

Haka malam baba ya cigaba da aikinsa.
Zuwa can yadubi galadima yace"Alhamdulillah malam Muhammad nayi nasarar magance matsalar nan sannan na hada musu wani dafa'i wanda insha Allah babu abinda zai sake faruwa a tsakanin su,komin tsafin me tsafi kuwa da yardan Allah.
"Sannan akwai wasu addu'o'i da zan basu da ita da 'yan wanda zasu lazumci yinsa da yardan bi'iznillah babu abinda zaifaru.

Duban Sauban yayi yace"Shima takwaran ka na hada mishi wasu zan bashi domin tabbas za'ayi kokarin bibiyar wanda ya lalata aikin koda kuwa ba'a gano shiba sai sunyi kokarin sabauta ko wanene.

"Mungode malam baba Allah yasaka da alkhairi ubangiji yaja kwana Allah yayima rayuwa albarka.

Cewar Daddy kenan cike da tsananin jin dadin yadda malam baban ya warware musu komai da yardan Allah da temakon sa.

Godiya sukayi sosai inda Galadima yake cemai ga sadakan abinci nan yayi ma almajiran sa sannan anbiya mishi kujeran hajji.

Nan yashiga godiya duk da ya nuna musu sunfi karfin haka a wajenshi Amma ina.

*********

Sai yamma lis suka isa qauyen wajen bokan inda shima driver hajiya Aliya dan gari ne don suna shiri sosai ita dashi don har aikoshi tanayi wajensa a sirrince.
Gidan da suka saba sauka a dan quyen gefen gidan boka nan suka sauka,zuwa bayan sallan isha'i suka shiga wajenshi.

Da wani banzan kallo ya tarbe su,nan danan hajiya Aliya tasha jinin jikinta,a dan tulluwan kasan da suka saba zama suka nufa zasu zauna.

"Kulllll! Ahirrr dinku Aliya ka kasa nan ku zauna.
Jikisu har tsuma yakeyi saboda yanda yayi maganar.

"Aljanu su huci zuciyar ka,shedanu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login