Showing 39001 words to 42000 words out of 103469 words

Chapter 14 - GALADIMA FAMILY Complete Hausa novel

07 Sep 2024

6889

yaranki duk maza ne ba mata ba balle ace suzo a amshe kayan dasu.
"Amma Yaya Bodejo duk da maza ne ai naga suna da matayensu ko?ko babu komai ai ace ko su maimuna da uwar mujaheed ne a turo,ammaai babu komai dama idan ba'a dauke ka da muhimmanci ba babu abinda bazaka gani ba.

"Guggo wallahi ko daya ba haka bane,kayan ma ba mata ne suka kawo ba mazane suka kawo kayan.
Guggo Laure tace"Maryam to tunda mazane suka kawo,ba sai akira ko mansir bane?

Aunty Maryam tace"To shikenan Guggo kiyahakuri ai akwai na wasu 'yan matan har guda uku bayan wadannan kibari idan za'ayi nasu zakiji komai mun amsa lefinmu dai wannan.
Ture kaga tsiya Guggo Laure tayiwa dan kwalinta tare da hura hanci tace"da dai yafi kam.
Bodejo kuwa tun sanda taji Guggo Laure tafara korafi ta yunkura tabar wajen.
"To shi Sauban nashi lefen be isone kuwa ba?
Dan murmushi Aunty Maryam tayi tace"Ea to ina tunanin sai next week zai iso dasu 'yan Dubai ba,kinsan shi acan yake hada lefensa"murmushi Guggo laure tayi cike da jindadi tace.
"Ah Masha Allah, Allah dai ya iso mana dashi lafiya,da Ameen aka amsa gabadaya.
Akeela sosai taji dadi a ranta,sai lokacin ta tuna bata gaishe da Aunty Maryam ba,cikin kissa tashiga gaisheta, Aunty Maryam itama ta amsa cike da kulawar don batasan itace Akeelan ba itadai taji ana cewa jikar Guggo Laure ce.

A kwana atashi babu wuya yau biki yarage saura sati guda kuma ayau Sauban zai diro don taufeeq yatafi daukosa tare da wasu abokansa su hudu,don kayan kwana biyu kenan da isowar su yana hannun wata kawar Ammi an aje a gidan.Itama Aunty labeeba anjima zasu kariso,gida fa yacika yayi tam,a gefe daya kuma Guggo Laure ranta a jagule yake saboda rashin ganin ba'a kawo lefe ba don kuka Akeela ta tasata tafara mata,aiko ana cikin hakane baba sani yayi sallama yashigo farlon.

Gaida Guggo yayi cikin kulawa face dinsa dauke da raha yafara magana"Guggo dama maganar kayan lefen Akeela ne ankawo sunzo bayan la'asar don yanzu suka taf......ai be karasa magana ba Guggo Laure tamike tare da sakin wani guda.
"Ayyyiirirrrriiiii!Allah nagode ma,sani ina suke masu kawo kayan?.
"Sun tafi tun dazu Guggo.

Shigowa Alhaji mansir yayi, ya gaida Guggo,nanfa ta amsa baki a yage tsananin murna.
"Sani to ina kayan suke yanzu?
Baba sani yace"Suna farlona.
Hade rai tayi tace"a sashen ka Wai kake nufi?

Sake tsuke fuska tayi tare da dubansa tace"A'ah magana ta Allah niban yarda ba akan wane dalili za'a ajiye kaya a sashenka ga sashin uban 'ya?gaskiya ayi maza-maza adawo dashi sashin mansir,daga baba sani har baba mansir,mujaheed sakin baki sukayi suna duban Guggo laure,cikin bacin rai Baba mansir yadago zaiyi magana,katsesa Baba Sanj yayi ta hanyar daga masa hannu sannan yadubi mujaheed wanda ranshi yakai kololuwar baci yace"Mujaheed maza kaje parlo na ga key din ka kwaso kayan lefen kanwar ka kakawo dakin Guggo,cikin ladabi Mujaheed yasa hannu ya amsa key din tare da juyawa yatafi,da harara Guggo laure tabishi tana Jan tsaki kasa².
Baijima ba yafara zhigowa da akwatunan,aifa nan Guggo laure tashiga guda daga Mom din Akeela har hajiya zainab murna sukeyi baki har kunne,kafin kace me gida yafara cika da makota zuwa ganin kayan lefe,sosai kayan sukayi kyau Masha Allah don Sauban yakashe kudi musamman hand bag da shoes nd Dubai gowns,kaya dai sunyi kyau sai dai makiyi akwatuna takwas yayi.
Nanfa kafin kace me kawayen Akeela sunfara watsawa a duniya.

Washegari ya Sauban yaturo mata da message kan yananan shigowa,murna Akeela tayi saboda aganinta yafara son tane da kula da ita a fili ta furta"Lallai bokan Guggo yasan aikin shi, hehehehe ya Sauban kenan ai kashigo hannu na kagama,takare maganar tana mikewa tare da fadawa toilet,sabulan ta na dilka dana bleaching da ake hada mata tafara muttsike jikinta dshi before tashiga wanka.

Aiko washegari su Suby da Zuleey suka zo gidan inda suka je wani restaurant suka siyo musu snack's lafiyayyu,tare da shiryawa ala dole zakace su ne suka hada.
Sai wajen 5:30 su ya Sauban suka iso dashi da Taufeeq da Kareem duk cikan su sunyi kyau musamman Sauban da Taufeeq duk da cewa manyan kaya suka sanya,shadda ya Sauban yasanya me ruwan kanwa inda aka mata dinki half jamfa sai hannun ma gajere hulan kanshi ya murzata brown sai cover shoe da ya Sanya brown,agogon hannun shi kirar Gucci me ruwan kanwa,inda farin fatan shi yafito yayi masifan kyau,face dinshi sanye da shade fuskar nan babu annuri ko kadan,shima ya Taufeeq shaddar ya sanya dark blue shima half jamfa amma shi besa hula ba takalmin shi da agogon sa bakake shima yayi kyau duk da daka gansu shida Sauban zaka san jini daya ne, malam Kareem kuwa kananun kaya yasanya jeans da t shirt sai dai yayi kyau don duk cikansu badai iya wanka ba,gabadaya sun rude da ganin zaratan mazan,sosai Zuleey da Suby suka hadiye miyau don gabadaya sunyi mutuwan tsaye da ganinsu musamman Sauban.
"Hello sannun ku da zuwa,please have a sit, zuleey tayi karfin fada tana nunawa Sauban inda zai zauna,cike da karairaya ita da Suby suka samu 2 seater suka zauna,inda su Sauban ke zaune a 3 seater,cikin kissa Suby tasa wayar s kunne tare da fara magana"hello kawata wai mekikeyi ne?kifito mana haka gasu angon namu fa yazo,takarisa maganar tana lankwasa muryan ka,ta wutsiyar ido Zuleey ta gallamata harara tana me mikewa.
Yake tasaki tana saka idonta kan na Taufeeq don sam kwarjinin da Sauban ya mata yasa takasa hada Ido dashi tace"excuse me!tayi maganar tana watsa yatsu wadanda suka sha kunbunan kanti,sanye take da wani riga da skirt na atamfa sunyi bala'in matseta duk da ba bayan ne da itaba amma karfi da yaji ake jujjuya su.
Ko kallonta Sauban beyi ba don shi hankalin sa Yana ma kan wayan dayake daddanawa ne, Taufeeq ne da Kareem sukayi karfin halin amsa mata, Suby tace"ya shirye-shirye guy's?munji ku shiru Ashe yau dinma kuna tafe?shiru kowannen su ya mata yana danna wayansa,da mamaki Suby ta dubesu amma sai wata zuciyar ta bata amsa da kila basu jita bane.
"Oyoyo sweetheart"Akeela tashigo farlon da gudu tare da nufar Sauban sai dai ganin face dinsa da rayi yasa dole ta ajiye duk wani kissa da bariki da taso aiwatar wa,cikin rawar jiki tashiga gaishesu,cike da kulawa Taufeeq da Kareem suka amsata amma gogan ko dagowa beyi ba balle tasa ran ze amsata,"amarya kina lafiya?karem yayi maganar yana dan murmushi, Akeela ma murmushin tayi tace"lafiya lou munjiku shiru ga events da zamu fara gudanar wa tun jiya amma baku iso ba sai yau.
"Aikam kinsan ogan be gama wattaakewa da tafiya ba so munjira ya huta sai mu shigo agaisa, Akeela tace"eyya babu komai,duban Sauban tayi tare da langabar dakai tace"Baby inata magana amma kayi shiru, dagowa Sauban yayi tare da Kura mata ido duk da bata ganin eye ball nashi amma sai da kallon yasata taji babu dadi,agogon hannun sa ya kalla tare da duban su yace"please Taufeeq kuyi abinda yakawo mu cuz time yana tafiya, Taufeeq yace"Ok.

Dagowa yayi cike da basarwa yadubi Akeela yace"amarya nawa kuke da bukata ne?na hidima nd everything?

"10 millions naira!
Sukaji ambasu amsa,duk cikansu suka dubi inda maganar yafito har shi gogan sai da yadago.

Xahratty CE🥰
Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️
[5/28, 11:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳

Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now

*_GALADIMA FAMILY_*

Page 39/40


______Sosai maganganun hajiya Aliya suka tsaya ma Adda zainab a ranta domin tashiga fargaba tare da tsananin tashin hankali,lallai tasan wacece hajiya Aliya duk abinda ta sama gaba to tabbas sai ta cimma nasara,hankalinta a tashe yake sosai take safa da marwa a cikin dakin nata,a gefe guda kuma damuwar ta daya shine haryanzu bataji sakamako akan bilkisou ba,a koda yaushe cikin jiran tsammanin kira take amma shiru ga biki ya gabato saura kwana biyar kuma can maidugrin zasu nufa don acan ne ake taron biki,sosai hankalinta yakasu gida biyu,wani tunani ne yafado mata cikin rai don haka da sauri tadauki wayarta tafara laluban layin hajiya Aliya,sai dai kash!sanar da ita ake wayan fa haryanzu a kashe take alamu ya nuna tabbas bata dawo daga kasar nijar dinba.

******

Sanye takeda doguwar riga mai hannun armless,roba ce tasamu waje ta lafe a jikinta wanda har tayi sanadin bayyanan duk wani halittun ta saboda shape duk ya bayyana,musamman kugunta wanda yake a tsuke sai hips daya nemi waje ya baje ga tudun bom bom,hankalinta a kwance take tafiya da alamu video call takeyi don murmushi takeyi da surutai.Kallo daya ya mata tare da kauda fuskan shi cikin basarwa,idanunshi ne suka sauka akan wani security dake bakin gate ya kurawa mata idanuwa ko kiftawa bayayi like maye,maida dubanshi yayi gareta yaga tabbas ita yaron yake kallo,ranshi ne yayi kololuwan baci wanda har sai da yakasa control din kansa,idanuwan sa sun kankanci cikin bacin rai yanufo inda take gadan²,babu zato taji an fusgota tare da yarfa mata mari.

Lokaci guda tanemi jinta da ganinta tarasa don sun dauki batasan sanda tasaki wani ihu ba tare da dafe kunci don rabon da ayi mata irin wannan marin ta manta,da sauri Ammi ta futo daga apartment dinta don yafi kusa saisu Mashahuda da suka fito daga apartment din Mom suma a guje saboda karar ihun nata,nunata yashiga yi da hannu bakinsa har wani rawa² yake amma yakasa furta komai."Menene haka Son?me ta maka lafiyan ka lau kuwa?gabadaya yakasa magana,da sauri yajuya kai tsaye gate din yanufa,koda yaje beyi wata² ba ya zabga ma security dinnan mari,a gigice ya dafe kuncin jikinsa babu inda baya rawa,cakumo kwalar rigansa yayi tare da diddilo masa idanuwa yace"idan nasake kama ka kana ma wata mace a gidannan irin kallon da kama wannan yarinyar yau,wallahi sai kabar aiki a gidan nan tare da tsarabar nakasa ka don sai na nakasa naga uban da ya tsaya maka,stupid son of a bitch!! Yakarasa maganar tare da hankada sa baya,a gigice security dinnan yanufi kofan gate yafice jikinsa na wani irin rawa,juyowa yayi kaitsaye yanufi parking space, Ammi ce tayi saurin isa garesa"Son wai ba magana nake maka ba kana jina meta maka da zaka mata irin wannan marin?kaga yanda shatin yatsunka suka fito a kumatun ta kuwa?bakinsa na rawa yace"Saboda rashin kamun kai na yarinyar nan haka taga sauran 'yan uwanta ke dressing a cikin gidan?ta fito tana karkada ma security jiki tana shaking body?ko kunya bataji?wallahi daga yau nasake kamata da makamancin dressing dinnan sai na lahira yafita jindadi"yakarisa shiga motar tare da kunnata yayi reverse yana dannan wani azababben horn.
Juyawa Ammi tayi taga dressing din jikin Zuhra,babu wani aibu a shiganta amma yamata wannan marin?girgiza kai Ammi tayi tare da nufar Zuhra wacce banda kuka babu abinda takeyi gashi bakinta yakasa shiru cikin muryan kuka take magana"Ni me dressing dina yayi?kawai saboda cin zali zemun wannan marin wallahi sai Allah yasaka min tun ina karama yatsaneni saboda kawai yatsaneni shine zaizo yamin marin nan Allah nagani,kuma ban......"Zuhra!!! Bata karisa maganar ba taji ankirata cikin daga murya, Ummie ce,karisowa tayi fuskar ta babu wani walwala tace"mekike so kice?cewa zakiyi da baki yafe ba?shidin sa'an kine?kull kada nasake ji,meyasa bema sauran ba sai ke kidubi shigan su mana,amma ai basu fito ba suna killace a daki bari har idon security yakai kansu.
Cikin muryan kuka Zuhra tace"amma Ummi aini shiga ta duk tafi tasu mutumci.
Ummie tace"naki yaga yafi muni sai ki gyara gaba inba haka ba zakisha wahalar sa kuma niba zan hanashi hukunta ki ba,tana kare fadan hakan tajuya,kamota Ammi tayi tanufi apartment dinta da ita"Why? Why?dani kadai yasama ido a gidan nan baga su Aunty Mashahuda ba wallahi Ammi nima aurena zanyi na huta kawai ranar bikinsu Aunty Mashahuda a dauramin aure tare da nasu nima na huta"takarisa maganar cikin muryan kuka,dubanta Aunty Maryam tayi tace"Oh really?to a'ina kika samo mana mijin naki?sai ama Daddy magana idan yadawo.Duk dariya 'yan parlon suka sanya,Ammi tace"gaskiya kam Maryam ya kamata bari muji Koda wa za'a samata ranar.
Shiru Zuhra tayi kamar ruwa yacita sai yanzu ta fanimci baran baramar da tayi,rufe fuska tayi da sauri, Mashahuda tace"kila da Shuraim ne Ammi, Ammi tace"wanene haka? Mashahuda tace"Shuraim fa cousin din su ya Asheer din Aunty falmata, Ammi tace"wannan yaron?lallai na ganesa kuma sosai na yaba da halayensa don yayi his very innocent,murmushi Zuhra tayi tare da nufar hanyar bedroom din Aunty Mashahuda cikin daga murya tace"wallahi Ammi niba da gaske nakeyi ba da wasa nakeyi wallahi niba yanzu zanyi aure ba sai na kammala degree dina tukuna.
Duk cikansu dariya suka sanya.

*** *NIJAR* ***

Sosai ya kura mata idanuwa saboda yaji dadin maganarta,cigaba da magana tayi"nifa boka hatsabibi babu cin amana a cikin lamarin nan naga tana wasa da aurenta shiyasa ninakeso na aure Alhaji iliyasu zanyi tattalin sa tare da basa kulawa tunda ita tazama ballagaza,duk fa cin amanar da zanyi bekai Wanda takeyi,wallahi har gwara nawa raya sunna nakeson aikatawa ita kuma fa?wani irin dariya boka hatsabibi ya kyalkyale da ita tare da tsuke face yace"kisa a ranki aikinki yama yiwu ya gama,dole kishiga gidan Alhaji iliyasu matsayin matansa ta aure,domin nima hajiya Zainab tayi min lefin da dole namata mugayen hukuncin da bata taba zato ba,tasa nayi asaran aljanu bila adadin kuma sune sojoji duk ciki wallahi sai ta girbi abinda ta shuka,zaro idanuwa hajiya Aliya tayi bakinta na rawa tace"b..bo..boka wai shima wannan aikin ba'ayi nasara bane?juyowa yayi a fusace ya watsa mata idanuwan sa cikin daga murya yace"kada kija lefinta ya shafeki duk da cewa harda ke amma nata yafi naki domin aikinda akayi gabadaya babu wanda akayi nasara.
Dafe kirji hajiya Aliya tayi da karfi tace"Nashiga uku ni Aliya,amma ya akayi aikin beyiba,wallahi boka da hannuna nataya ta barbada maganin a shimfidar ta kuma ta kwanta akan shimfidar,wani banzan kallo boka hatsabibi yama Aliya cikin muryan tsawa yace"shine nace miki beyi ba don asirin ya karye,kekuma ga wannan kwalin ki sanya a idanuwan ki,a ranar da kikaji Alhaji iliyasu zai dawo kafin yafara kallon kowa ki tabbatar da kece yafara kalla,sannan kada ki kuskura ki hada idanu da wani idan ba haka ba to tabbas wanda kika fara hada idanu dashi shine zaki aura"ya karasa maganar yana mika mata kullin maganin,jikin hajiya Aliya na rawa ta amsa tare da cewa"da yardan boka hatsabibi sai na mallaki Alhaji iliyasu,kuma aikina baza'a samu kuskure ba.
Anan sukayi sallama inda sai da wadannan kattan munanan mata suka biya bukata da ita.

____*NIGERIA*____

Sosai shirye²n biki ya kankama ranar laraba su Mashahuda sukayi bridel shower,sosai events din ya hadu,don suyi kyau matuka, Shuraim yazo gidan don shine yakawo Aunty safeena,sosai yakema zuhra wani irin so wanda shikansa mamakin kansa yakeyi,fuskansa dauke da murmushi ya zubanya mata idanuwa,dan cuno mouth tayi cike da shagwaba tafara bubbuga kafa"To wai ni ya Shuraim kallon na menene?tayi maganar cikin shagwababbiyan murya tare da zaki da sanyi,"zakasa Allah nakoma ciki,tunda tasani zakayi kamar wata television kana kallo,sosai yanayin nata yakara rikitar dashi har ya rasa lissafin sa ajiyan zuciya ya sauke"Huh bazaki gane bane ina imagine ne wai na mallakeki,huhhh da ranar sai anyi sadaka na abinci,kudade, everything,yakarisa maganar cikin shauki,dariya Zuhra ta sanya"I am still young,dudu shekaruna 18 ne fa,why not?na gama degree na daura B8? Wani banzan kallo ya Shuraim ya mata cikin sigar Wasa yace"wa kike tunanin zai tsaya jiranki har wannan shekarun?ai malama kawai kya cigaba a gidana,dariya sosai ya bata don haka tasake tafara dariyar ta wanda dimple, Gap teeth dinta duk suka bayyana a kuma dai dai wannan lokacin ne motar su ya Sauban ta danno kai cikin gidan,fitowa sukayi su duka ukun,sai dai shi gogan face nasa a dore,ba kamar taufeeq da kareem ba,duk da shi Kareem na ciki na ciki.
Cikin sauri Zuhra ta nufi inda suke sai dai kaitsaye ta wuce Sauban ko kallon sa batayi ba ta nufi wajen taufeeq,kamo hannunsa tayi,"yawwa Yaya ga ya Shuraim can kazo ku gaisa, bata jira mezece ba tafara jansa.
Tun kafin su kariso Shuraim ya karisu,cike da girmamawa yadan rissina kadan tare da mikawa Taufeeq hannu yace"Yaya sannu da zuwa,shima Taufeeq face dinsa babu yabo ba fallasa yamika masa yace"sannu ko malam Shuraim ya mutanen gidan? Shuraim yace"kowa lafiya lou Yaya,dubansa Taufeeq yayi sannan yadubi Zuhra,sake maida duban sa yayi ga Shuraim din yace"Ko zan iya sanin matsayin ka a wajen kanwata malam Shuraim? Shuraim na kokarin magana cikin sauri Zuhra tace"he's my friend...tayi maganar tana sakin murmushi,gyada kai Shuraim yayi yace"yes Yaya,murmushi Taufeeq yayi yace"Ok nice to meet yhu malam Shuraim,insha Allah zansa mana lokaci musake gaisawa da kyau,dariya Shuraim yayi cikin jindadi yace"babu damuwa Yaya a shirye nake don amsa kiranka.
Taufeeq yace"Ok ka gaida mutan gidan.
"Insha Allah zasuji Yaya.
Wucewa yayi a ransa yana kissima abubuwa da dama inda lokaci guda ya fahimci inda Shuraim ya dosa,kaitsaye apartment din Ummie ya nufa.

"Kingani ba?tun yanzu nafara samun shiga a family naki ko?to dana fito da maitata nasan za'a amince,dariya Zuhra tayi tana kokarin yin magana ne ta hango Laila ta doso inda suke kaitsaye,nuna ma Shuraim Laila tayi tace"kaganta ko?duban inda tanuna masa yayi yace"who is she?dariya Zuhra tayi tace"her name is Laila, she's my lovely sister nd my abokiyar fada,dariya Shuraim yayi itama Laila dariyar tayi don taji amsar da zuhran ta bada,duban Shuraim tayi tace"Barka da zuwa!
Dariyq Shuraim yayi yace"Barka dai fatan kina lafiya?ya shirye-shiryen biki? Laila tace"Alhamdulillah shiri ananan anayi sai dai mujira ranar daurin aure,maida dubanta tayi ga Zuhra tace"Ummie na kiranki, Zuhra tace"Okay to bari naje tayi magnan tana duban Shuraim"Ya Shuraim nizan wuce please don Allah kagaishe da mutanen gidan.
Takarisa maganar tana me wucewa tabarsu tare da Laila yana janta da hira.

Xahratty CE🥰
Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️
26/5/23.
[6/7, 15:49] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳

Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now

*_GALADIMA FAMILY_*

Page 41/42


______Kareem ne yadubi Sauban yace"Ango kiran kafa akeyi da alama kawayen amarya ne,kuma nasa akan maganar kudinsu ne"Cikin bacin rai Sauban yace"I don't have time for wadannan 'yan iskan ladies din masu fama da hayakin kai,nine zanbasu 10 millions naira na hidimar biki?to ai banfito a cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login