Showing 60001 words to 63000 words out of 103469 words

Chapter 21 - GALADIMA FAMILY Complete Hausa novel

07 Sep 2024

6890

din,kokarin binta Shuraim yakeyi sai dai rikon da ya Asher shima ya masa ya hanasa bintan.
Duk wanda ke parlour sai da suka basu tausayi harta shikanshi Sauban din,daqyar Daddy ya lallabashi suka tafi a mota kuwa ko magana ya kasa lokaci daya zazza6i ya rufeshi,wajen 9:26 pm suka isa gidan su Shuraim din.

******
Sosai ciwo ya kwantar da Shuraim wanda sai da takai takawo ga anbashi gado,ya rame yayi baki inban da kuka babu abinda yakeyi, daga mahaifinsa har mahaifiyar sa da kannensa basu da natsuwa Saboda banda sumbatu babu abinda yakeyi.

A bangaren Shuraim da Akeela kuwa sun dinke duk da ba wani zama yake suna hira ba sai dai yana kula da ita sosai tunda mutum ne mai yawan bukata, Akeela tun tanajin dadi idan akafara haryazo da kuka take kosawa a gama,son shi kuwa sake ninkuwa yayi a ranta,shirye²n tafiya yakeyi gobe da safe.

Zaune suke shida Kareem a parlour sa suna kallon tashar aljazeera,duban shi Kareem yayi yace"Kai oga aini nashiga rudu dajin wannan labarin, gaskiya kai me sa'a ne don kuwa nima har ina shirin sulalowa nazo na kama kafa ta bangaren ka gudun kada wani yamin wuffff Ashe kadade dayin wuf din da ita?yayi magana yana sakin dariya,dan tsaki Sauban yaja yana kaima kafadun Kareem duka"kaifa matsalata da kai dan iska ne,nima bansan meke faruwa ba sai randa aka kaita hospital din nan,don su Daddy dagewa sukayi kan dole wai nice zan kwana da ita,aiko hakanan na kwana da ita,to sai akan wannan yaron shine sanadin da magana mafa ta fasu"yakarisa maganar yana picking call,magana akayi masa ta can bangaren,amsawa yayi da "okay gani nan zuwa Daddy, hanging call din yayi yana duban Kareem yace"Daddy na kirana tashi muje.
Mikewa sukayi suka bar gidan gabadaya kaitsaye cikin GALADIMA house suka nufa,da yake Abba ya iso shida Mommy.

Bayan sun hadu yagaishe da iyayen nasa nan Abba yake cemasa ya maganar tarewar na zuhra?domin shi bayason abinda zaisa ayita jan magana ana sake tada fitina,cikin girmamawa Shuraim yace"Abba ai tarewar nan ba yanzu ba,a bari komai yasake warwarewa tukuna,dan dariya Abba yayi yace"shikenan,mommynku ma kiri² tace ba yanzu zata tare ba da ita da Ammin ku,dariya Shuraim yayi yace"Abba ai gaskiyan su ne, Abba yace"To Masha Allah! Allah ya tabbatar da alkhairi,muzamu je gidansu Rabi tukuna",duban Kareem yayi yace"Muhammad Kareem kai ya maganar naka auren ne?naji shiru ya kamata kafin tarewar abokin ka kafito da mata idan kuma ba haka ba zan nema maka fulanin ruga",Kareem yace"Insha Allah Abba munkusa asamu a addu'ah kafin dai oga ya tare da.....shiru yayi yakasa karisawa,dariya sosai Abba yayi da yake shi din mutum ne mai barkwanci sai dai duk cikinsu yafisu fada sosai.

******
Mommy sosai tashiga bawa zuhra baki tana lallashinta,cikin muryan kuka zuhra tace"Mommy ya Shuraim ance yana kwance a asibiti anbashi gado,meyasa ba'a yima kowa auren dole ba sai ni?ko wacce fa ita takawo wanda takeso to taya ni za'a ce dole sai ya......bige mata baki mommy tayi batare da tabari takai aya ba,cike da takaicin wautan ta tace"Wai don Allah zuhra yaushe ne zakiyi hankali?to bari kiji wannan tamkar kinaja da maganar Abbie ne,bari kiji abinda yace a ranar"Nan Mommy tasaka mata recording din, tabbas muryan abbien ta ne sanda yake barin wasiyyar auren ta dana ya Sauban,kuka sosai ta kece dashi cikin muryan kuka tace"tabbas Abbie zanbi maganar ka,zan amince da abinda kskeso, kayafemun Abbie"takarisa maganar tana kece wa da kuka tare da fadawa jikin toilet,sosai tabasu tausayi matuka gaya.

Washegari ta kama Monday a ranar su Abba zasu koma domin tun jiya sun dawo da Mom tayi nadama matuka, Sauban shima ranar zai koma Canada,sosai Akeela tasa rigimar sai yaje da ita dadai taga sam hakan bamai yuwuwa bane sai ta hakura,zuhra kuwa a ranta tsattsaye take ta ciwon ta na rabuwa da masoyinta,abin sam babu dadi.
Alhaji iliyasu ma a ranar aka daura aurenshi da hjy Aliya,hauka ne kawai Adda Zainab batayi ba amma hankalin kuwa sai da yatashi haka rayuka sun 6aci,don a ranar da hajiya Aliya zata tare sai Alhaji iliyasu yace ta dakata idan yadawo daga tafiyan da zauyi sa tare,cikin dibara kuwa Hajiya Aliya taja hankalin shi tafiyan nan da zaiyi to dole tare sukayi shi ita da shi, jirgin su yadaga sai kasar Argentina,duk wanda yaga Adda Zainab sai ya tausaya mata sosai.

Rayuwa kenan a kwana antashi babu wuya yau gareka gobe ga wanin haka,yanzu gashi anci wata hudu da bikin amare, inda Shuraim ya sake gogewa a cikin Galadima family ya zama dan gida don sun hada kansu da Laila harda ranar aure inda itama da ta gama degree dinta sai biki,ta bangaren Nihal ma haka wani yaron kanwar Mommy dake aiki a cotonou shima yafito ansa rana,ta bangaren Rammat itama Kareem yafito kan tabbas shifa yake son ta,to su ansa rana don biki bairi sauran 2 months ba,sosai zuhra ta maida hankali akan karatun ta,gashi ta bangare guda tasake cika da wani irin kyau na daukar magana,don haka samari suka sanyo ta gaba domin kuwa muddun tafita sai anbiyo ta kuma manyan mutane haka ake sintirin zuwa neman aurenta.Sosai hankalin su ya tashi a dalilin hakan yasa suka nemi Sauban ya samu lokaci ya shigo musamman ma don iyalinsa da suke ganin kwana biyu mata suna suntiri a gidan nata.

*** *KADUNA* ***

Zaune take a leadeseat din dake parloun glass cup ne a hannunta fresh milk ne a ciki,idanunta sanye da medical glass,kafa daya akan daya ta dora tana cigaba da kallon ta,waya takeyi hankali kwanci tana dariya"wallahi Yaya kinganni nan jiyama muka dawo kasan da Alhaji ina tunanin nan da 2 weaks ma zamu sake barin kasar"saurara tayi don da alamu daga can bangaren magana ake mata,dariya ta kyalkyale dashi tana taunar chwengum tace"Ai Yaya bamu gama honeymoon ba kinga Alhaji mutum ne me son kulawa sam baya son gidadanci to shiyasa nake zagewa nake basa kula"magana aka mata tacan barin,dariya ta kuma saki tace"Ah to kinga lefina?ai yama fada yace yanzu ne yasan yayi aure"takarisa maganar tana duban wajen dinning din da Adda Zainab ke zaune tana cin abinci.
Adda zainab tsaban takaici da 6acin rai kasa cin abinci tayi tana sauraran ta ga zuciyar ta da take lugude,cikin zafin rai saboda jin irin maganganun da hajiya Aliya keyi yasata mikewa a zafafe ta nufeta, dai-dai ita kuma ta aje wayar,tana isa tatsaya a gabanta cikin 6acin rai tafara magana"Hajiya Aliya tsakanina dake wallahi Allah ya isa,banta6a tunanin ke mayaudariya bace sai da kika aure mijina,ke maciyiya amana ce daga ke har boka hatsabibi bazan ta6a yafe muku ba domin nasan da saka hannun sa azzaluma kawai karuwa"tana gama fadar haka yajuya zuciyar ta na mata wani irin rawa,muryan hajiya Aliya tajiyo tana kyalkyale dariya tace"Hmm Aminiyata kenan kace babban maciyiya amana domin kece ke cin amanar 'yar uwarki,babu babban maciyiya amana kamar ki,kuma ki rubuta ki ajiye wallahi wallahi wannan sakon da kika bani tamkar a kunnen boka kika fada"dogon tsaki Adda Zainab tayi tace"ki sanar masa don ubanku ke dashi"tana kare fadar hakan tajuya ta haye stairs,daga murya Hajiya Aliya tayi tana dariya tace"Oho kishin banza mijine dai na mallakesa.
Koda Adda Zainab tashiga daki a tsorace take hankalin ta yayi kololuwar tashi da wani tunani da ya fado mata rai akan kada hajiya Aliya ta tona mata asiri, tabbas tana nan akan bakanta na kin 'yar uwanta sannan tana son kauda ta a doron kasa,sosai takejin 6acin rai.

A can maidugri kuwa da yake Ummie ta gama iddarta shirye-shiryen komawa kaduna takeyi sosai hankalin zuhra ya tashi tadinga rokonta kan tazauna anan amma taki da yake jirgi zata bi ,don su Laila sun dade da komawa saboda school,da Ammi da Mom ne zasu rakata sai yaseer da zuhra don ita ke driving din ma motar,sun rakata airport tayi duk abinda zatayi basu baro can dinba sai da sukaga jirgin su Mom yatashi sannan suka nufi gida cike da gajiya wajejen karfe 8:07pm.


A haka rayuwa take ta tafiya bayan kwana biyar,adalilin rashin napep da ake fama dashi yasa ta tafara takawa a kasa, motocin da suka tsaya yimata lift sunkai amma zuhra taki sauraran su sai wani wanda a yanzu sai binta yake yana rokonta kan tazo ta hau sosai gayen ba lefe kyakkyawane nd gently daka kallesa kasan dan gidan manya,sai binta yake ana cikin hakan ne taga wata motar tasha gabanta a zafafe kirar Benz G wagon duk cikan su tsayawa sukayi batare da ya fito ba yayi zipping tinted window motar tare da bude front door,hada ido sukayi ita dashi duk dashi kallo daya ya mata amma ita takasa dena dubansa saboda abune biyu ne suka darsu mata a rai,na farko yasake zama wani arrogant and sexy boss kyansa kullum sake fitowa yake ga tsoron sa da kwarjinin sa daya darsu mata a zuciya,bata da wani za6i dole tanufi motar ta shiga,ganin hakan yasa gayen nan juyawa.
A motar babu Wanda m yace da wani kanzil,itadai banda wasa da finger's dinta babu abinda takeyi, duk yana kallon ta ta wutsiyar ido,sosai ta masa kyau sannan yaji dadin ganinta da wannan gown din da be kama mata jiki ba sam nd tayi rolling mai kyau gunin sha'awa,ga wani cika da yaga takara da kyau,wani numfashi yaja saboda wani abu da yaji ya taso masa,zuwa can face dinsa babu alamun walwala yace"Da auren nawa akanki ne kike kula kulan samari?kinsan lefin hakan kuwa?"yakarisa maganar cikin rausayar da kai,sosai mamaki ya kamata wanda har yagaza 6oyuwa,gabadaya sakin baki tayi kamar wawuya tana dubansa saboda taji alamar mutumin nan yana son yayi mata sharri,sassauta face dinsa yayi yana dubanta,da sauri Zuhra takau da fuskanta cikin sanyin muryanta da wani dadi da ya kara tace"Ba haka bane yaya,niban kula kowa ba ko suma din naci sukeyi amma ban kulasu"takarisa maganar tana sunkuyar dakanta kasa.
"Amma wannan gayen da alama da banzo ba kila da yayi nasara akanki don naganshi yana da masifar naci sam baya sassauta wa"tajiyo muryar sa yana fadar hakan,ajiyan zuciya ta sauke me karfi batare da tayi magana ba,shima be sake magana ba suka cigaba da tafiya,kaitsaye gate din gidan sa yanufa yana danna Horn,da sauri ta dubesa,shiko ko kallon ta beyi ba,babu jimawa akazo aka bude gate.

Xahratty CE🥰
Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️.
[7/2, 23:53] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳

Page:- 61/62

______Gama parking yayi tare da fitowa babu abinda ke tashi a gidan sai karar kida na waqar Ado Gwanja mai taken "chass" sosai Sauban ransa ya 6aci kaitsaye apartment din Akeela ya shiga,da yake batasan da dawowan sa ba shiyasa,ransa yayi kololuwan 6aci ganin yanda mata manya wasu ma sunyi 'yar ciki da Akeelan amma haka suka tike sai rawa sukeyi suna rungume da junayen su,duk cikan su ba kayan arziqi bane a jikinsu.Ji sukayi sautin wakar ya tsaya cak,wata hajiya ce tafara jiyowa ganin Sauban yasa tayi mutuwar tsaye don ba karamin kyau yaron yayi mata,tabbas a haife ya haifeta,ganin irin kallon da take masa yasa cikin bala'i ya qanqantar da idanuwa,muryan Akeela ne yafara tashi"Oh honey barka,hope kadawo lafiya?tayi maganar tana nufarsa tare da kokarin fadawa jikinsa,cikin zafin nama ya tureta side,tare da kololuwan 6acin rai ya nunata tare da fara magana"kafin nadawo sashen nan,ki tattara min wadannan 'yan iskan kazaman su barmin gida,if not nadawo wallahi sai na rufe kofan parlourn na muku dukan mutuwa"yana kare fadar hakan yajuya kamar wani zaki,cikin 6acin rai ya isa sashen shi,kaitsaye bathroom ya isa ya sakin ma kansa shower yana sauke ajiyar zuciya,face dinsa a runtse,idanuwan ta yafara haskowa da yanda tasake wani cika da tsananin kyau,murmushi kawai yasaki,a gurguje yafito ya shirya cikin kananun kaya wadanda suka masa matukar kyau.

Fita yayi, dai-dai lokacin su kuma matan wadanda sunkai biyar suka fice daga gidan,yana mamakin yanda Akeela ke tara masa mata a gida musamman wadanda ma sun haifeta sun juya sannan daka kallesu kasan shedanu ne,sam baya son tabbatar da zargin da yake akanta hakan yasa ya saki dogon tsaki, Galadima house ya nufa direct apartment din Bodejo ya isa yana waya da Taufeeq akan rashin lafiyar da Mashahuda keyi,sai tsiya Sauban yake masa wai ko ciki ne.
Sam basu kula da juna ba saboda saurin da take taje sashen Mom,sanye take da wata gown wacce tadan bude gabadaya iya gwiwwa ta tsaya mata rigar,sai dai duk da haka be hada tudun saman ta bayyana ba,haka kuma be hana tudun bom bom dinta bayyana.
Garam!karar bugewar su ta bayyana,da sauri zuhra tadan dafe goshinta tare da cewa"ouch! Matsawa gefe tayi da sauri saboda kallon da taga Sauban na mata sosai tasha jinin jikinta,sake hade rai yayi dama da ragowar 6acin ran da Akeela ta hada masa yake,cikin tsukakkiyar fuska yace"Ina zaki da wannan dressing din haka?in ina Zuhra tafara"dama..d...dama leqawa zanyi nadubo abu shine,cikin muryan tsawa yace"Dallah go back my friend,wallahi akan ire-iren wadannan banzayen dressing din da kike a gidan nan sai na baki mamaki,yayi maganar yana ra6ata ya wuce, Bodejo da fitowan ta kenan daga palour Galadima tace"To sarkin kwarwa kadawo kenan,yanzu kuma ba zata samu wani sakewa ba,haba jama'a wai meyasa duk idan kashigo da masifar fadan ka baka saukewa kan matarka sai ita? Sauban fuska a daure yace"to ai itama matar tawa ce Bodejo,idan ki kaga na mata fada itama lefi tayi, Bodejo tace"to sannu me mata ai saika cigaba.
Mikewa yayi yanufi parlourn Galadima batare da yasake bin ta Bodejo ba.

Bayan kwana biyu,gabadaya Zuhra time din kanta ma wahala yake mata cuz exam da suke ta shirye-shiryen farawa sam lokacin ta na karatu ne,sai dai kullum tana shiga kowane apartment da safe gaishesu,a bangaren Ammi kuwa sosai take samun kalawa,don sam Ammi bata dauke ta wata surika ba,sunyi kusan kwana biyu basu hadu dashi ba hakan ba karamin faranta mata rai yayi ba saboda ta fahimci a duk sa'in da zasu hadu sai ya nemi lefi ya liqamata ya hauta da fada,Yau ma kamar kullum da wuri suka gama Exam dalilin hakan yasa kawai ta nufi gidan muneefa,sosai Muneefa tayi murnan ganinta ta dade sosai a gidan sai bayan isha'i sannan Mus'ab yadauko ta yadawo da ita,bude motan tafito tana dan rissinawa tace"to Yaya Mus'ab nagode sosai Allah yabar zumunci, murmushi yayi yace"Ameen kanwar mu kicema rigimammiyar tsohuwan nan bazan samu leqowa ba amma ga wannan ki bata"yayi maganar yana miko mata wani leader bag me kyau sannan sukayi sallama yazuge tinted window dinshi yaja motar,cikin natsuwar ta tashiga gidan,harta gota first gate sai taji kamar ana binta a baya ko kafin tayi yunkurin juyowa taji anfisgota,a gigice ta bude baki da niyyar ihu sai dai jitayi andane bakin da yatsu,sosai taji wani azababben zafi, face dinsa ta kalla sosai ya canza jikinta ne yadauki wani irin rawa da tsuma,bakinsa har rawa yake tsaban masifar dake cinsa fuskar nan tayi jajawur,hadata da jikin gate din yayi,da karfi Zuhra ta rintse ido domin kuwa ta sadakar yau me kwatar ta sai Allah,muryan shi tajiyo cikin amo yana magana"Wancan wane dan iska ne ya ajeki a mota?Fateema da aure na a kanki kike kula wasu mazan?da aurena akanki kike cin amanata?wai halan kina mance ke din matar aure CE koh?yayi maganar cikin muryan tsawa yana me matse mata hannu gam kamar zai balla,wani irin kuka Zuhra ta saki jikinta kuwa banda tsuma babu abinda yakeyi"Am talking to you teemah!!!yayi maganar yana daka wani tsawa wanda yasa Ammi fitowa ita da Daddy don apartment dinsu tadan fi farko duk da kuwa tazarar su,cikin muryan kuka Zuhra tace"wallahi ba wani na kula ba kuma ba wani ne yakawo ni....bata karisa ba yace"To uban waye ya sauke ki a mota?karya zanmiki?
"Kai Sauban lafiyan ka kalau kuwa?Wai menene kakeyi haka ne?sakin mata hannu kafin ranka yayi mummunar 6aci wallahi a gidannan"Ammi tayi maganar cikin 6acin rai,yakasa sakin ta saboda bala'in kishin da ke cinsa a ransa, Daddy yace"Wai bada kai ake magana ba?sakinta yayi Yana me kafa mata idanuwan sa da sukayi jawur,itakuwa kanta na kasa banda kuka babu abinda take rusawa.
"Meke faruwa ne Sauban? Daddy yayi maganar yana karisowa cikin kamewa,itako zuhra kamata Ammi tayi tare da maidata gefenta,yanaso yayi magana yakasa saboda ruwan kwallan da ya taru masa a idanuwa,juyawa kawai yayi yanajin kansa na sara masa yafita daga gate din, Daddy bece masa komai ba don yaga yanayin mode dinsa,"kamata muje ciki muji meyafaru"kamata Ammi sukayi har parlour ta ajeta kan carpet duk suka zauna,nan Daddy yake tambayanta abinda ke faruwa"Wai saboda yaga an sauke ni a mota shine yashigo yafara fada"tayi maganar cikin sanyin murya, Daddy yace"wanene ya ajeki a motar? Zuhra tace"Yaya Mus'ab din Aunty Muneefa ne"Daddy yace"A'ina kuka hadu dashi har ya dauko ki?nan Zuhra tafara in ina alamun rashin gaskiya"da...dag...daga gidan su naje wajen Aunty Muneefa daga school na wuce"Daddy yace"okay to karfe nawa ya saukeki?zuhra tace"wajen 8:17 kayahakuri Daddy"Daddy yace"wakika tambaya? Zuhra cikin tsananin tashin hankali tace"Bodejo kawai tasani.
Girgiza kai kawai Daddy yayi yace"tashi kije da safe zan nemeku kedashi"cikin muryan kuka Zuhra ta mike tafita,da kallon tausayi Ammi tabita tana takaicin abinda Sauban kema Zuhra,duban Daddy Ammi tayi zatayi magana,hannu yadaga mata tare da cewa"Hmmmmm!"dole Ammi taja bakinta ta tsuke.

Duk da ya fita apartment din da 6acin rai amma hakan be hanashi soyewa da matarsa ba,duk da bawai wani dadi da gamsuwa yake ba amma haka yake hakuri don gudun fadawa halaka.

**********
"A gaskiya Alhaji nagaji da rashin adalcin da ake gwadamin a gidannan kada fa kamanta nima fa matarka ce,akan me tunda kazo duk inda zaka sai da hajiya Aliya kake zuwa?dame tafini?kyau ko kuwa ilimin addini dana boko?dan murmushi Alhaji iliyasu yayi yana girgiza kafa tare da sipping coffee"Alhaji magana fa nake maka"Adda Zainab tayi maganar damuwa tattare da a face dinta,ajiye cup din Alhaji iliyasu yayi yana duban Adda Zainab"Bata fiki da komai hasalima ke kika fita dashi,amma fa kuma ada,domin kuwa a yanzu tafimin ke sau dubun dubata,kin manta ada lokacin da kika fifita ta akan kowa naki,hatta ni mijina?sai nace miki kizo muyi tafiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login