Showing 99001 words to 102000 words out of 103469 words

Chapter 34 - GALADIMA FAMILY Complete Hausa novel

07 Sep 2024

6906

Aiko nan aka ɗebi jininta tare da nasarar dai-dai ta numfashin ta,alluran bacci aka mata tare da sa mata drip suka fito,nan Dr Ahmad ke sanar dasu su kwantar da hankalin su insha Allah jikin da sauƙi ya bada jini aje lab a gwada su ɗan jira akawo result,yayi maganar yana dafa kafaɗar Sauban ganin yanda ya susuce lokaci guda.
Babu jimawa su Mommy suka ƙariso tare da tambayar meyasame Zuhra sannan wani hali take ciki?
Nan Mom ta shiga basu labari,can babu daɗewa Daddy, Abba, Baba Hasheem, Boɗejo, GALADIMA, Guggo Laure duk sun ƙariso suna neman cika asibitin.
Wata nurse ta dubi abokiyar aikin ta tace"Oh sis su kuwa waɗannan wasu ahali ne suna neman tarewa a hospital? murmushi wancan nurse tayi tace"Galadima family kenan,kinga wancan tsohon to shine Galadiman"tayi maganar tana nuna Galadima, ɗayan tace"Wow but familyn so nice sunyi ko ta ina ga kyau"dariya wancan nurse ɗin tasa tace"ke duk wata mace zata so ta shiga family ɗin nan da sunan aure don a yanda ake bada labarin family ɗin komai sun haɗa Masha Allah"wancan nurse tace"kuma fa patient ɗin nasu ba wani ciwo bane me damuwa,don Allah ki kalli kayan alfarman dake jikinsu"wancan nurse ta sake cewa"Galadima family aka ce miki fa,I think wancan ne mijin me blue Black ɗin shaddan can,kinsan yanda ƴan mata ke rushing guy ɗin can?sai dai ance ɗan wulaƙanci ne gashi yana bala'in son matar shi,ance ma fa yarinya ce ƙarama don baza ta wuce 19yrs ba,yana son ta sosai"ko kafin wancan tayi magana Boɗejo ta katse su"kai kuwa waɗannan yara da tsinannen gulma kuke,duk a ina kukaji wannan?domin basuyi tunanin suna jin hirar su ba, gabaɗaya hankalinsu ya koma kan nurse's ɗin,su ko tsitsitsi suka shiga yi da idanuwa.
Dr Ahmad ne ya leƙo tare da kiran Sauban,jikin shi na rawa ya shiga office wani mahaukacin bugu ƙirjinsa keyi.
Dr Ahmad yace"bismillah Malam Sauban have a sit"zama Sauban yayi tare da ƙosawa yaji me zaice mishi,wani takadda Dr Ahmad ya miƙo masa yace"take this result nd da abinda ya ƙunsa.
Ɗagowa Sauban yayi ya dubi face ɗin Dr Ahmad.
[7/30, 14:53] 𝐎̃𝐔̂𝐌 𝐀̃𝐉𝐌𝐄̨𝐑𝐋💜🤍: 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*

*~LAST PAGE~*

___Hannu ya miƙa masa sannan yace"Congratulation Mr Sauban Madam ɗin ka na ɗauke da juna biyu na tsawon 2weeks Allah ya sa albarka"Wani mugun farin ciki ne ya kama ya Sauban wanda ya sashi rungume Dr Ahmad babu shiri,sakin sa yayi tare da yin sujudur shukur,babu ɓata lokaci Sauban ya fice da result a hannu sai a sa ilin da ya hango su Daddy ne yaji wani irin nauyi da kunya,hakan yasa shi babu shiri ya kame kansa duk da kallo suka bisa tare da tambayar shi me Dr ɗin yace,saboda har ga Allah hankulan su a tashe yake, Sauban cikin kamewa yace"sunce da sauƙi sai dai ga results ɗin"yayi maganar yana miƙawa Mommy da tafi kusa dashi,aiko ta warware don dubawa,inda wasu suka shiga tambayar me result ɗin yace,ai kafin abada answer Mommy ta daddage ta saki guɗa wanda ya jawo hankulan mutane da dama, Mom itama ta amsa result ɗin cikin farin ciki ya shiga furta"Alhamdulillah Allah mungode maka"Boɗejo ta mere baki tace"dama sai da jiki na ya bani yanzu haka ciki ya shiga ne tunda akace tayi amai,to Allah ya ƙara lafiya,don ciwon me ciki sai haƙuri,kai Abdulkarim kuzo ku sauke ni a gida mun bar jama'a"duk dariya aka sanya,su Daddy duk wanda ka kalla fara'a ne a face ɗin sa,haka zalika Ammi wani farin ciki ne ya ziyarce ta wanda ko a cikin Mashahuda da Safeena ba taji hakan ba,a ranta tashiga gode ma Allah.
Don haka yasa duk suka shiga ɗakin har lokacin tana bacci sosai,lokaci ɗaya tayi wani fayau ta faɗa,nan suka dudduba jikin ta inda duk suka tafi aka bar Sauban da Mom don su Taufeeq sunyi² ya taso suje yaƙi.
Acan gidan biki kuwa anbar jama'a da jimami,koda suka koma nan suka cema mutane jikin nata da sauƙi, Ummie ce kawai aka sanar da ita abinda ke faruwa,nan fa su Mashahuda suka dasa chapter tsegumi wai dama ai wannan haske kwana biyu da tayi ga ƙirjin ta daya cika,nan dai suka dinga.
A hospital kuwa Zuhra bata farka ba sai wajejen magrib,shima tana farkawa aman tafara ga cikinta da babu komai da ka kalleta kasan a matuƙar wahale take, Sauban kuwa gabaɗaya ya ruɗe har sai da yabawa Mom tausayi,da ƙyar aman ya tsaya,anan Mom ta kamata suka shiga toilet tayi alwala tayi sallah la'asar,sannan aka ɗan jinginar da ita saboda complain ɗin da takeyi na jiri da take gani.
"Yaya yunwa nakeji"ta furta cikin wahalallen murya wanda daka ji kasan na marasa lafiya ne, Sauban cikin kulawa yace"mezaki cine baby?Girgiza kai Zuhra tayi tace"ina jin yunwa amma banjin cin komai"Mom tace"A'ah Zuhra ai dole kici wani abu ba zai yiwu ki zauna da yunwa ba fa gaskiya"ZUHRa wani wahalallen ƙwalla ne ya ziraro mata daƙyar tace"Mom idan naci amai zanyi na sani Kum.....ai bata ƙarisa ba aman kuwa ya taho ga uban wahala,don cikinta babu komai sai kakarin aman da takeyi,a lokacin nurse's ɗin ɗazu dake ta gulma ne suka shigo,nan suka shiga yi ma Zuhra ya jiki,a gefe guda suna satar kallon Sauban wanda ya tsuke face,ya tattare gabaɗaya hankalin shi ya koma kan matar sa.
"Yaya nidai a maida ni gida bansan warin asibitin nan amai yake saka ni"tayi maganar a wahale, miƙewa Sauban yayi yace"Okay so bari nama Dr Ahmad magana gaskiya"sannan yasa kai ya fice,daga Mom har nurse's ɗin da kallo suka bita,kamo kafaɗun ta mom tayi tace"Zuhra kidaure kici wani abu koda zakiyi amai saboda idan cikin ki da akwai wani abu bazaki wahala kamar irin wanda kikeyi da cikin ki babu komai ba"ɗaga ma Mom kai Zuhra tayi,a dai-dai lokacin ne kuma Sauban suka shigo shida Dr Ahmad,hakan yasa nurses ɗin ficewa.
Dariya Dr Ahmad yakeyi ya dubi Zuhra"Madam kinfi dai son komawa gida right? ɗaga mishi kai Zuhra tayi don har ga Allah warin asibitin damun ta yakeyi,a take anan kuwa ya rubuta mata sallama,inda Dr jamila zata dinga zuwa dubata, sannan sai ruwan hannun ta yaƙare zasu wuce.
Godiya Sauban yama Dr Ahmad a kuma take anan ya tura masa 250,000 tukwicin sanar da wannan daddaɗan albishir ɗin,wani baccin Zuhra ta koma sai wajen magrib lokacin ma Sauban na masallaci, Mom ma sallan takeyi sannan Zuhra ta farka,yunƙurin miƙewa take yi amma jirin dake nema kada ta ne yasa takoma ta jingina tare da rintse idanuwan ta gam.
Muryan Mom taji"Ya yadai Zuhra?jikin ne? ɗaga ma Mom kai tayi tace"jiri ne ke neman wahalar dani Mom,ga aman da nakeji har yanzu nina rasa meke samun jin aman? Mom tace"Ai haƙuri zakiyi Zuhra yanzu keda jin dai-dai kuma sai Allah ya sauke ki lafiya"wani kallo Zuhra ta ma Mom na rashin fahimta don har ga Allah bata son abinda ke faruwa ba,dariya Mom kawai tayi a lokacin Sauban yayi sallama ya shigo duk cikan su suka amsa,nufo su yayi tare da zama gefen Zuhra yace"Mom Yaya jikin nata?ta sake aman ne?? Mom tace"Jiki alhamdulillah Sauban complain ɗin ta ɗaya jirin da take gani ne kuma Dr Ahmad yace insha Allah zaiyi sauƙi a hankali tunda Dr jamila zata dinga zuwa gida kula da ita,don bayan fitan ka ma ta shigo mun daɗe da ita lokacin ma Zuhran tana barci".
"Masha Allah, Allah ya ƙara lafiya,to ai sai muyi shirin tafiya ko Mom? Mom tace"Okay muje Toh.
Duban Zuhra Sauban yayi yace"hey beb zaki iya tafiya?Zuhra tace"ka mance nace ma ina ganin jiri kawai kama ni zakayi muje"kama ta yayi Mom ta gyara mata mayafin ta sannan suka fice,har mota ya saka ta don yaso shiga office ɗin Dr Ahmad but ya tashi.

Haka ya ɗauko su,suna tafiya da yake hanyoyin akwai street light hakan yasa duk inda ka wuce haske ƙau,har zasu wuce ya jiyo muryan ta,da yake suna baya ne kanta na kan kafaɗar Mom"Yaya ga me balango can"dakata wa yayi yace"zaki ci ne? ɗaga masa kai Zuhra tayi,samun waje yayi yai parking sannan yafice, yaɗau almost 4mint sannan ya shigo,hannunsa ɗauke da ledoji uku ɗaya madaidaici, ɗaya ya fishi, ɗayan kuma duk ya fisu yawa,haka suka ƙarisa, dai-dai wani shagon da ake saida yoghurt ya tsaya ya sai manyan robobi huɗu sannan ya dawo ya shiga motan ya tayar.
A haka suka isa kaitsaye Galadima family ya wuce da ita sashin Ammi,kama ta yayi ya kaita, Mom kuwa apartment ɗin ta tawuce saboda Hajiya Biba tana nan,don biyo su Ammi sukayi suka dawo ɗazu.
********
Kowa tambayar jikin nata yakeyi,haka amare duk sun shisshigo sun tasa ta a bedroom ɗin da aka sauke ta,su Aunty Maryam da Aunty labeeba duk suna tare da ita sai sannu ake mata masu sharri nayi,ita dai Zuhra kunya ta saka ta a gaba duk bakin ta takasa furta komai.
Sauban da kanshi ya kaima Mom na manta har apartment ɗin ta da yoghurt,godiya sosai tayi masa,inda shida Kareem suka ɗauki Hajiya Biba don maida ta gida,suna zaune har kusan 9:00 sannnan ya shigo,hakan yasa siɗif² suka fara ficewa cikin su na ɗuran ruwa,turo mouth gaba, Zuhra tayi tace"ƙarfi da yaji ka zama kaman wani mala'ikan mutuwa da angan ka sai a shiga taitayi"harara Sauban ya galla mata yace"kema ai saboda kin ganni tsirara ne shiyasa kika rainani haka,kuma zanyi maganin ki"dariya Zuhra tasa tace"Sorry Babyn Baby".
"Kinci abinci?yayi mata tambayar tare da jawo ledojin, Zuhra tace"ai baka zo ka bani balangon ba"ɗan murmushi Sauban yayi sannan ya buɗe komai ya shiga bata tana amsa idanuwan ta akan shi tana jin wani soyayyan shi,sai da yabata yaga taci ta ƙoshi sannan ya ƙyale ta suka cigaba hira,wanda rabi da kwata duk romance ɗin junan su sukayi,har sai da Zuhra ta mishi abinda ya samu natsuwa( Su Sauban manya😁🙄).
Sai wajen 11:43 ya tashi shima sai Ammi ta shigo ta kora sa sannan wanda Zuhra kuwa a lokacin amai ta dinga sheƙawa,basuyi wani kwanan daɗi ba daga ƙarshe bedroom ɗin Ammi ta koma.

*WASHEGARIN BIKI*

Nihal da Laila kuka kawai sukeyi kamar ransu zai fita don sai da suka tayar ma da mutane da dama hankali sun saba komai tare gashi aure zai raba su duk da Laila after 2weeks zata koma saboda school hakan yasa Shuraim ya sama mata gidan haya a can,duk weekend zai dinga shiga kaduna, Nihal ita ta raka Laila gidan ta wanda yayi kyau ɗan dai-dai kasha Allah,wajen 10 aka kaita,ana dawowa ƴan k.d suma suka ɗauki amarya tare da duk wanda zai tafi motoci bakwai suka wuce.
Zuhra dai nata ido don Sauban wayo ya mata anfito tafiya da amarya yaja ta gidan su,yaci karen sa babu babbaka,wanda sosai zubar ke kuka don wani mugun tsanar abin ta tsinci kanta daji duk da kuwa itama ta samu natsuwa,ko kaɗan bata so taji ya....a ciki,shiyasa ya koma yi a waje.
Sai wajejen magrib sannan ya maido ta gida,hararar kawai Ammi ta masa inda tace"to lallai Zuhra ta koma ɗakin ta don ba za'ayi abin kunya a sashin ya ba.
Laulayin cikin na damun ta don ma ta samu sauƙin jirin sannan Dr jamila tana iya ƙoƙarin ta wajen bata kulawa,ranar Laraba Sauban yayi mata kyautar motar ta ƙirar MERCEDES_BENZ
G - CLASS G500
MODEL 2022,babu wanda beyi farin ciki ba don motar babu ƙarya ta haɗu iya haɗuwa,ƴan uwa hakan suke kira suna taya Zuhra murya,da yake su Aunty labeeba duk basu tafi ba,kai kowa da murna yake, Zuhra kuwa jitayi kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta shiga,don koda wasa bata taɓa kawo za'a siya mata mota nan kusa ba,ba wai don babu ba a'ah sai don ko maganar sam basuyi dashi,ya bata a matsayin tukwici akan abubuwa da dama a cewar sa ma harda baiwar da Allah ya mata.
*******
After one week gidan kamar ba'ayi sha'ani ba don duk sun wawwatse,inda Sauban shi ya cigaba da rainon cikin Zuhra tare da yimata duk abinda takeso,aikin gida ma kuwa tare sukeyi,shi yake kai ta school ya ɗauko inda da haka yake mata dubarin koya driving,weekend kuwa me gasken sukeyi, sosai Sauban ya dage da koya ma Zuhra driving Kuma lokaci guda ta iya,duk wanda ya gansu sai yaso kasancewa tare dasu,ranar da zata dawo daga school haka suka ci karo da Akeela inda wani me daidai ta sahu ke ta mata rashin mutumci kan kuɗin da tabashi be kai ba,har yana kiran ta ƴar maɗigo sai wulaƙata ta yake mutane har sun fara taruwa.
Akeela kuwa sosai take kuka,idan ka ganta duk tayi laushi tunda bata rame ba,kawai da ka kalle ta zakasan lallai Akeela ta tuba tayi nadama,long hijjab ne a jikinta , gabaɗaya tayi sanyi, Zuhra da kanta tafita taje ta ƙwato Akeela don Sauban hanata yayi ita kuma taƙi, a motar tazo ta sanya ta,inda kuka sosai Akeela keyi, ta buɗe hand bag ɗinta takaima me adaidaita kuɗin da ita kanta bata san ko nawa bane, sannan tazo ta shiga sai lallashi Akeela take, sauvan ko yayi kicin kicin da face,babu alamun rahama ko kaɗan,nan Zuhra ta shiga bata baki har gida suka kaita, Zuhra na ƙoƙarin fita Sauban ya galla mata uban harara hakan yasa dole ta haƙura, Akeela buɗe motar tayi sannan ta zagayo ta dubi Sauban tace"Don Allah Sauban ka yafemin nasan ni mai lefi ce a gare ka,naci amanar ka amma Allah sheda ne na tuba,tuba irin na taubatun-nasuha don Allah ka yafemin"tayi maganar tana fashewa da kuka, Sauban yace"Allah ya yafe mana,ai ke yanzu duniya ma ta isheki"yana gama faɗar hakan ya zuge glass's ɗin motar ya mata key,beyi wata² ba ya fisgeta ya bar layin,wani irin kuka Akeela keyi don harga Allah tasan cewa lallai ta cuce kanta rashin Sauban matsayin miji asarar ne.
1months Sauban yayi suna zuba soayyayn su daga ƙarshe ya tattara yana shi ya nashi ya koma,wanda Zuhra taji kamar tayi ta kururuwa.
____________

Sauban koda ya koma sau biyu ya dawo a lokacin har anyi azumi har anyi babban salla don lokacin Zuhra cikin ta kusan six months ne dawowar da yayi na farko,cikin yayi girma na hankali duk wanda ya gani sai yayi magana,a lokacin da ya cika seven months wani kumburi Zuhra tayi kota ko ina,ga damuwa da ta sanya ma ranta na mutuwa,ita a kullum gani takeyi mutuwa zata yi hakan yasa lokaci guda jininta ya hau,sosai su Daddy ke mata faɗa don ransu ya ɓaci,gashi wannan karan da yake sun samu hutu har na wata guda hakan yasa duk inda ta zauna sai ta tsaya ma kowa a rai kowa na jinta,ita kanta Boɗejo wani nan nan takeyi da ita,haka Ummie itama sosai ke nuna mata kulawa, ɗaki guda suka cika da kayan baby unisex,don Sauban duk kayan da akasaa ɗakin daga abrod ne.
A lokacin Mashahuda ta haihu baby boy ne hakan yasa yaci sunan Abbie suna kiran sa da Ashraf, hakan yasa tadawo gida bayan anyi suna acan,don ko sunan Zuhra bata je ba Sauban ya hanata,shiyasa bata da aiki kullum sai na tambayar Mashahuda yaya haihuwa yake da zafi ko kuwa?
Sometimes Mashahuda murmushi takan mata tace"kada ta damu idan lokaci yayi zataji don shi haihuwa ba lallai wahala da wancan ya sha ba shi wannan ke sha,wani yana zuwa masa da sauƙi"kowa cikin tattalin ta da nuna mata kulawa.
Sai alokacin Muneefa ta samu ciki na wata huɗu,inda daga Laila har Nihal ke ƙunshe da cikin su ɗan wata bibbiyu.
Rammat itama haihuwa yau ko gobe.
Haka rayuwa ta cigaba da daɗi babu daɗi har Rammat ta haifi Baby boy inda mahaifin Kareem ya sanya masa sunan Daddy suna kiran sa Aslam.
********
Bayan wata biyu lokacin Sauban ya dawo gida gabaɗaya saboda Zuhra cikin ta ya shiga watan haihuwa,sosai ta sake kumbura sai dai anci Sa'a jinin ya sauka,kullum da la'asar sai Sauban ya jata zuwa struggling hakan yasa yake ɗan jin dama dama.
Wata ranar Lahadi ƙarfe 11 na dare naƙuda ya sako ta gaba,tun tana abinta ita kaɗai har Sauban dai ya tashi dama baccin sa rabi da rabi ne hankalin sa na kanta always.
"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un"ta furta tana yarfe hannu tare da duƙewa,cikin azama Sauban ya diro daga kan gadon a gigice ya nufeta yana faɗar haihuwa ce Baby? ɗaga masa kai Zuhra tayi ta kasa magana saboda azaba.
Hakan yasa a gigice Sauban ya fice daga gidan ƙoƙarin fita yake but ya kasa hakan, gabaɗaya ya gama ruɗewa da gigice wa lokaci guda.
Wayan shi ya ɗauka ya lalubo number Ammi,kusan 2misscall sannan ta ɗauka muryan ta da alamun bacci tace"Assalamu alaikum Sauban ya akayi?
"Ammi Zuhra kizo don Allah"cikin sauri Ammi ta miƙe tace"haihuwar ce? Sauban yace"i think cuz tana shan wahala"Ammi ce tayi hanging call ɗin, Daddy ma tashi yayi,hakan yasa cikin sauri ta nufi apartment ɗin Mom ita da Daddy, Daddy da kanshi ya kira Baba Hasheem a waya ya sanar dashi,babu jimawa suka fito shida Mom ko wacce zani ɗaure akan kayan bacci tasa hijjab.
Wayan Ammi ne yayi ringing cikin sauri ta ɗaga Sauban yace"Ammi ganinan a mota a waje".
Amsa mishi tayi sannan suka fice wajen su suka shiga inda su Daddy suka ce duk halin da ake ciki su sanar dasu.
Sauban kiran Dr Ahmad ya sanar dashi,inda akayi Sa'a Dr yana asibitin cuz night duty zaiyi.
Suna Isa cikin hanzari aka karɓe ta sai labour ward.
Nan fa aka shiga bata kulawa gabaɗaya Sauban ya ruɗe,cikin yardan Allah wajejen 3:00 ta sunkutu yaran ta biyu mace da namiji,ihun su ne ya cika ward ɗin.
Aifa nan su Ammi sukaji sanyi ya ratsa musu,babu jimawa Dr jamila ta ƙarisu hannun ta ɗauke da Baby wata nurse ma ɗauke da Baby,atake anan Sauban yayi sujudur shukur,inda banda hamdala babu abinda su Ammi keyi, Sauban cikin sauri yace"yaya take?zan iya shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login