Showing 72001 words to 75000 words out of 103469 words
ciki,kikkimtsawa yayi sannan yadauro alwala yayi sallah raka'a hudu sannan ya kwanta,duban ta yayi yana shafa face dinta yanajin wani sanyi,abinda yadinga mafarkin zuwan shi kenan,tun sanda aka haifeta yake da burin kasancewa da ita,murmushi ya saki sannan ya jawota jikinsa yana manna mata kiss a forehead dinta"I love you so much my life"ya furta kaman wani me rada,babu jimawa shima bacci ya suresa.
Ita tafara farkawa wajejen 5:30 jinta tayi kamar ammata daurin goro cikin sauri ta bude idanuwan ta,a hankali ya sauka kan face dinsa,diddilo idanuwa tayi cike da mamaki cikin sauri ta yunkura zata tashi,batare da ya bude ido ba yace"were re you going?cikin muryan bacci,kallon sa tayi still taga bacci yakeyi seriously,batare da tayi magana ba tasake kokarin mikewa,amma sai taji yaki sakinta"uhm am talking to you"yafada,wani kuka Zuhra ta kece dashi wanda yasa cikin sauri Sauban ware idanuwan shi akanta yana sakin ta,mamaki fal ransa,ganin ya saketa yasa ta mike da sauri tare da sauka daga bed din taje can gefe tayi tsaye tana cigaba dakai,dafe kai Sauban yayi yace"kaga takanka Sauban"tamke face yayi yana mikewa,toilet ya shiga ya barta nan tsaye,ruwa tafara jiyo zuban sa,hakan ya tabbatar mata da wanka yakeyi a gurguje yafito saboda lattin da yayi be samu asuba ba,jallabiya yasaka fara tas sannan yafita a gaggauce.
Wani ajiyan zuciya ta sauke tana share hawayen ta,toilet din tashiga tana wani irin lumshe ido saboda tsaruwan sa,cikin sauri tayi wanka itama tayi alwala,koda tafito lutfaya dinta ta dauka ta nada,tare da tayar da sallah,koda ta idar azkar tayi sannan tafara rera karatun alqur'an,Suratul Yusuf,daka takeyi cuz wayanta bata gani a saman ba,a haka har bacci yasake awon gaba da ita akan dadduman.
Sauban wajejen 7:00am yadawo gidan, kaitsaye sashen da yake gyming ya wuce,be fito ba sai wuraren 9:00 a lokacin Zuhra ta farka ta gyara bedroom din sannan ta sakko kasa shima tadan gyaggyara duk da bawani datti.
Knocking tajiyo duk a tunanin ta Sauban ne hakan yasata rudewa sannan kamar wacce aka dasa takasa mikewa,kusan minti biyar sannan tajiyo muryan sa,ku shiga mana I think tana bacci ne,tsuru tayi ganinsa da tayi batare da ya dubeta ba yahaye stairs, bayan sa Mashahuda ne da Muneefa, Muneefa dauke da basket a hannu,nufota sukayi Mashahuda na dariya kasa-kasa tace"morning Aunty amarya"haka kannen miji ke cewa ko Muneefa? Muneefa da tanufi dinning cikin muryan dariya tace"kwarai kuwa yanzu biyayya dole don matan Yaya ne, Zuhra da idanuwan ta yayi luhu luhu muryan ta na rawa tace"kai Aunty Muneefa"Muneefa tace"wani kai Aunty Muneefa gaskiya ne ai, Mashahuda tace"kinyi wanka ne? Zuhra tace"nayi sai dai bani da kayan canji"Mashahuda tajawo wani dan akwati dake gefen ta tace"ga wannan kije ki shirya kafin su Laila anjima su kawo miki kayanki,amsawa Zuhra tayi da to tana mikewa,dayan parloun ta nufa anan kasa inda taga bedroom har biyu,nan tashiga daya,shima sosai yayi kyau, biyo ta sukayi a baya,anan suka fito mata da kayan da zata sanya,wani arnen lace silver suka fito mata dashi Wanda akayi masa dinkin half bubu da street skirt yayi bala'in kyau,sai Muneefa tace tadaura dan kwalin da kanta don sun santa gwana ce akan dauri,bayan ta gama daurin tadan shafa powder kwalli nd lipstick,ta dan tace girar ta,tayi kyau sosai,takalmin ta golden high heel shoe ta sanya sai mayafinta gold shima,dan kunne da abin wuya silver,tayi kyau sosai-sosai.
"Wow Masha Allah wallahi kinyi bala'in kyau little sis"cewan Mashahuda tana zuba mata hotuna,kamo hannunta Muneefa tayi duk suka fito bedroom din.
Sauban ne yafito sanye da wata danyen shadda fara tasss babu aiki ko dis a jiki,daka kalle shaddan kasan naira dai tayi kururuwa bama kuka ba,sai half cover shoe blue,hulansa ma blue,yayi kyau har yagaji sajen nan tasaka zama baki sidik akan farar fatar nasa sai sheki takeyi,gefen sa abokan sa ne Taufeeq, Kareem, Aseef,sai wasu guda uku 'yan nan maidugrin,ga Mommy da Mom,kannen Ummie,sai na Ammi,sannan Rammat.
Sosai yake sakin murmushi saboda ganin Zuhra da yayi,a hankali ya fara takawa babu abinda ke tashi sai wakar ciza dani,manni kawai ake musu,yana zuwa ya rungumo ta gabadaya yana sakin wani irin ajiyar zuciya,goshinta yakai ma sumba,nan akasa ihu,kamo habar ta yayi yana laluban idanuwan ta wanda ta runtse su sosai,dukawa Sauban yayi yana ciro wani dan box a pocket dinsa,atake anan wani abun wuya na gold ya bayyana,aiko nan aka sake sa tafi da ihu,matsawa yayi yana Sanya mata abin wuyan, cikin wani irin murya ya furta"I love yhu Fateema Zuhra,I can't live without you,I love you so much,yafada yana kai mata kiss a baki,ai wannan karan daga mommy,mom har sauran iyaye rufe Ido sukayi.
Zuhra kuwa sandarewa tayi saboda jin abinda yace mata,haka aka cigaba da shagali,hotuna kawai akeyi a parloun inda kowa na cikin farin ciki,zuwa la'asar kowa ya watse.
Xahratty CEπ₯°
Lallai Alqalami ποΈ yafi takobiπ‘οΈ.
[7/14, 16:21] πππ‘π«π πππ‘π«ππππ²π₯°: π¨π½β𦳠*_GALADIMA FAMILY_* π¨π½βπ¦³
Page:-73/74
https://chat.whatsapp.com/Cz6pFHyd9N68OmqNx3Vpqs
_____Acan angano Adda Zainab wacce sai sunbatu take saki,nacewa ba ita takashesu ba kalmar da taketa ambata kenan kamar karatu tana kuka,duban ta wani police yayi cikin natsuwa yace"hajiya ki nutsu ki sanar damu asalin alakanki da hajiya Aliya har zuwa sanda ta rasu,kuka sosai Adda Zainab tasaki nan tashiga basu labari tun daga haduwar su na secondry school,daganan ta dakata,sannan cikin muryan kuka tace"officer don Allah ku kiramun 'yar uwata bilkisou tare da Amma nafiso duk labarin da zan bayar yazama suna wajen,sannan a hadani da hajiya kareema kanwar mijina suma duk suzo tare da yarana.
Haka kuwa akayi a ranar aka kira Ummie tafiyan urgent sukayi ita da Amma da Taufeeq,don mota ma suka biyo, Mashahuda kuwa dasu Mommy zata dawo,don ita kanta Zuhra bata son Ummien ta wuce ba.
Bayan komawar su kaitsaye gidan Adda Zainab suka isa sannan duk 'yan sanda ne a bakin gate din gidan,cikin gidan,kofan parloun da cikin palour,dama or ready family din Alhaji iliyasu sun hadu,su Ummie kawai ake jira,aiko nan police din ya dubi Adda Zainab"Hajiya ke muke sauraro,nan Adda Zainab ta cigaba da bada labarin sannan tace"babban sake dinkewar alaqar mu da Hajiya Aliya shine sanadin bilkisou,kowa kallon Ummie yayi nan ta cigaba tana duban Ummie"tunda na mallake hankalina nafara jin tsanar bilkisou a dalilin komai da tafini yasa nakejin tsanan ta,tsanan ta besake nunkuwa ba sai da tasamu miji daga ahalin da suka fi nawa sannan nasake jin wata iriyar tsanar ta,alhalin mahaifiyar ta bata ta6a nuna cewa ba itace ta haifeni ba,hasalima ta fifitani akan bilkisou,daya ke bilkisou ta rigani aure a lokacin hankalina yatashi wanda har Amma taso a fasa bikin Bilkisou abari nima na samu miji ko kuma Sadeeq ya aure ni ya hakura da bilkisou, Allah yajikan baban mu shine ya hana hakan a lokacin naji matsanancin haushin sa,ana haka ne na hadu da Hajiya Aliya inda ta hadani da wani boka da yake nijar,salati aka Sanya gabadaya palourn, Ummie kuwa kuka kawai takeyi.
Ta cigaba da cewa"Nice nasa akayi miki farraqu da Zuhra nayi amfani da kyallen jininki na kaiwa boka akayi asiri,tun daga lokacin kika tsane Zuhra,nan fa Adda Zainab tadinga bada labarin irin abinda suka dinga kullawa da hajiya Aliya har asirin da tasake yi mata da wancan ya karye,har zuwa sanda hajiya Aliya ta aure Alhaji iliyasu,da irin rigimar da sukeyi sannan tayi shiru tana jan shasshekan kuka, Ummie ma kuka takeyi tare dasu Amma,cikin kuka Amma tace"Zainab dama kece duk kike musu wannan farraqun?mahaifinku ya mutu da fushin bilkisou akan haka, fisabilillah kin kyauta kenan?cikin tu ajjabi hajiya kareema tace"lallai Zainab shedancin ki yakai inda yakai,yo wanda yayi wannan aikin ai kisa bazai mishi wahala ba,domn tuni aka cire miki imaninki"Adda Zainab cikin dasasshiyar muryan ta tana kuka tace"wallahi bani ce na kashe su Alhaji ba, wallahi"Ammar cikin muryan kuka yace"idan bake bace wanene Mom?please wanene?yayi maganar cikin muryan tsawa,islaha da kuka yaci karfin ta tace"why?why Mom?kinja mana abin fade Mom innalillahi wa Inna ilaihirraji'un ya Allah,babu 6ata lokaci aka sanya ma Adda zainab ankwa a hannunta wata mace,kuka sosai takeyi haka yaranta dasu Amma, Ummie ta dubi police din tace"Please yalla6ai yanzu ina zaku kaita?dan sandan yace"hajiya kaitsaye daganan state CID zamu wuce da ita domin gudanar da bincike yanda ya kamata,munyi muku alqawari muddin babu saka hannunta zamu saketa,idan dasa hannunta kuma zamu turata court a yanke mata hukunci"yana gama fadar haka aka tisa keyan Adda Zainab akayi waje da ita,kowa kaganshi bashi da kwanciyar hankali.
********
Yau a bedroom dinta ta kwana domin kuwa tayi alqawari bata sake kwana daki daya da Sauban,hakanne ma yasa tun kafin yadawo ta koma dayan palour kasa tare da shigewa daya daga cikin bedroom din ta kwana,hakan kuwa sosai ya sosa ma Sauban rai tare da yanke hukuncin yau da la'asar zaibi flight,ta online yasai ticket da komai nasa ya gama batare da tasani ba,da safe tana tashi ta shirya musu lafiyayyen breakfast,babu abinda ke tashi sai na room freshener da turaren rushi,gefe guda kuma ga kamshin girki,tasan Sauban ma'abocin son macaroni ne,dalilin hakan yasa tahada masa lafiyayyen macaronin sa da yaji dakakken nama yayi kyau da dadi,sannan ta dama masa kunun gyada, Ammi ma ta aiko da breakfast din kosai da custard sai wainan kwai,shiryawa tayi cikin riga straight gown,wanda ya fito mata da cikakken surar ta ko ina yacika Masha Allah, tayi kyau sosai,abinka da atamfa me dan duhu sai tayi kyau kwarai,daurin Aisha buhari ta murza mai kyau,kafarta sanye da high heel shoe brown, fitowan ta kenan daga kitchen hannunta dauke da plates taji alamun tafiyan sa,turaren sa me kamshi Arabian Oud ya buge hancin ta,dan lumshe ido tayi tanajin faduwar gaba,daurewa tayi ta cigaba da shirya dinning din.
Karisowa yayi yaja kujera ya zauna,sanye yake da wata yadi me kyau tare da maiko brown colour,daka ganta kasan lallai anyi fitan nera wajen siyan ta,kansa murzazziyan kube ce,wacce kudinta zasukai dubu 35 face dinsa babu wani walwala kamar koda yaushe, Zuhra kuwa gabanta ne ya cigaba da faduwa,a hankali tayi karfin halin furta"Ina kwana Yaya"kura mata ido yayi babu ko kiftawa,almost 5 minutes sannan ya girgiza kai kawai,ajiyan zuciya Zuhra ta sauke kirjinta na cigaba da bugawa daurewa tayi tace"Yaya meza'a zuba maka?hannunsa dauke da wayar sa yana latsawa batare da yadago ba yace"meda menene akwai?Zuhra tace"akwai jallop din macaroni with kunun gyada nama nd custard wih kosai,sai wainan kwai.Dagowa Sauban yayi yana zuba idanuwan sa akan warmers din dake kan dinning din,duk da a rufe suke yace"kisamun macaroni nd kunun gyada kadan inci tukuna"yanada tabbacin itace tayi wannan, cikin nutsuwan ta take serving dinta,gabadaya ya tsareta da idanuwan sa jinta kawai take a takure, shikuwa Sauban baiki yaji Zuhra akan cinyar sa ba, wani irin shaukin son ta kawai yakeji,batare da ya ankare ba yaji maganar ta"bismillah Yaya"dan sake hade face yayi yana daukan spoon din tare da duban plate din,lumshe ido yayi yanajin wani sanyi da dadi a ransa don dakakken mama yaji a cikin macaronin Masha Allah,hadiye miyau yayi, bismillah yayi yafara cin abincin cikin mutsuwa,jiyayi wani dadi ya ratsa masa har kwakwalwan kansa,sosai yake daurewa gudun kada yayi santi,ganin ta zauna tatasa kosai da yaji tanaci yasa ya dubeta"bazaki kiyayi kanki da cin yaji haka ba?wallahi idan kikazo kina min complain din basir da ulcer ko?sai kawai yayi shiru ya cigaba da cin abincin, Zuhra kuwa dagowa tayi cikin marairaice face,tare da wata shagwa6a66iyan murya wanda ita kanta bata ta6a sanin tana da ita ba tace"kai Yaya kosai fa idan babu yaji babu dadi"wani tsam!yaji a dalilin yanda tayi maganar,batare da yayi magana ba yadaga mata kai kawai,atake anan ya cinye plate din,gyaran murya yayi mata, dagowa tayi ta kallesa,da ido yayi mata alamun akara,kara mishi tayi ba da yawa ba,itako kosan biyar taci ta basshi cuz takasa sakin jiki taci yana wajen,shiko ko a jikinsa sakin jiki yayi yaci abincin sa yayi katt,yana gamawa yadau kunun gyadan sa yafara sipping,lumshe ido yayi domin har ga Allah yaji dadin kudun sosai,be yadda yabiye ma dadin ba yadaka,don a haka ma jin cikinsa yake ya cika don dama shi ba ma'abocin cin abinci bane,tissue yadauka yafara goge bakin sa,ji sukayi anwani daka kofan palour.
Da sauri suka mike, Akeela ce tashigo jikinta sanye da wata doguwar riga fitted sai dai ko kadan batayi mata kyau,sai taunar chwengum takeyi tana kare ma palour kallo,ganin canja wasu abubuwa da akayi tare da kara gyara sa,ta6e mouth tayi tana jan tsaki,nan tashiga takowa a gaban Sauban ta tsaya idanuwan ta cike tafff da hawaye tafara magana"Kaine na mijin dana fara so a rayuwa ta wanda akansa nasan menene so,amma munafukai sunyi nasarar rabani dakai a lokacin da muka kasance tare,inaso kasani wallahi bazan ta6a rabuwa dakai ba koda kuwa zanyi yawo tsirara ne sai na farauto soyayyar ka,sai nadawo cikin gidan nan matsayin mata"takarisa maganar hawayen na zubowa,duban ta ta maida ga Zuhra tana nuna ta,ke kuma inaso na Miki wata zazzafan gargani duk sanda kikasan mijina a matsayin miji wallahi babu ke babu kwanciyar hankali,banza kawai jak.....ai bata karisa ba taji saukar gigitaccen mari Sauban ya shimfida mata a fuska,sannan yana huci ya nufi wajen extension wear ya ciro cabel din caja,ai Akeela na ganin haka ta nufi kofan palour tana fita da gudu,aiko binta Sauban yayi cikin zafin nama, Zuhra kuwa da taga ma tsorata da kalaman Akeela binsa tayi jikinta na wani irin rawa.Wallahi babu macen da ta isa ta haifa maka yara saini,ke kuma kijira kiga abinda zai sameki"tana kare fadan haka tafice kamar wata zararriya, Zuhra kuwa kuka ta fashe dashi tana juyawa don ta tsorata da kalaman Akeela gani takeyi tabbas kamar wani zai farun,babu zato taji Sauban ya mata wani irin runguma,ai a haukace ta fisge jikinta tanaja baya,tsayawa kawai yayi yana kallon ta,jiyayi ta saki kuka tana hade hannayen ta waje guda,kuka yasa ta gaza furta komai,nufota Sauban yayi da mugun sauri ta kuma jan baya,tsayawa yayi kawai yana kallonta"Naroke ka da Allah yaya ka sakeni,ni bazan iya auren nan ba inajin tsoro please kasakeni nac..... batare da taji sanda yakariso ba kawai saukan mari taji a kuncin ta me azaban zugi,wani ihu tasa tana dafe kumatun tare da duban sa,jikinsa ne ke wani irin shaking,idanuwan nan nashi sunyi jajawur bakinsa na rawa"Du....dduk..duk ranar da kika sake cewa na saki wallahi sai nayi miki dukan mutuwa"yana kare fadar hakan yajuya yana maida kwallan dake kokarin zubo masa,tabbas a yanzu ya tabbatar da yarinyar nan bata son sa, kaitsaye palour yafice jikinsa na cigaba da rawa,ita kuwa Zuhra inda yabarta nan ta zube tana sake fashewa da wani irin kuka( _Nikaina Zuhra kinfara bani haushi akan kalmar sakin nan da kike fada,da mene zaiji?_ ).
Tana bedroom tana sallah taji shigowan sa yahaye upstairs,har taji sanda yake sakkowa da alaman ana jan trolley bag,cikin sauri ta mike tafito,shi tagani sanye da kananun kaya, security dinsa na daukan akwatin yana fita,kafadun shi dauke da wani jakan, Zuhra lokaci guda zuciyar ta tatsinke taji kuka kawai yataho mata,a hankali ya tako har inda take,face dinsa kadaran kadahan,hannunta ya kamo duka biyun tare da sumbatan goshinta"Zan tafi insha Allah zandawo nan bada jimawa ba,Zaki koma wajen Ammi before nadawo,ina miki fatan alheri"yana kare fadar hakan yajuya yafice,sai a lokacin makalallen hawayen da Zuhra ke makalewa suka samu damar sirnano mata,tana me zama kan sofa din sharaf,tana fashewa da kuka.
Shiko Sauban a tunanin sa Zuhra zata biyo sa a baya amma sai yaga akasin haka,girgiza kai yayi yana sake yarda da lallai Zuhra bata son shi,mota yashiga driver yaja,dama ya masu Ammi sallama kaitsaye sai airport, Zuhra kuwa tasha kukan ta ta koshi sannan ta mike tashiga tayi wanka sosai ta kwanta atake wahalallen bacci yayi awon gaba da ita,sai wajejen biyar ta farka tasake wanka ta shirya cikin turkey gown me yankakken hannu,tadau hijjab tasanya,abubuwan bukatan ta tadauka,dama ba komai aka kawo mata ba na kayanta,fita tayi ta kashe kowane socket nd switch na sashen har saman shi sai da tahau ta kashe komai sannan ta rufe ko ina tafito tanufi Galadima house.
Cikin sanyi tashiga sashen Bodejo tafara nufa,suka gaisa nan Bodejo tafara mata tsiya tana cewa ta canza lokaci daya saboda mijinta yayi tafiya sam babu walwala tattare da ita, Zuhra kuwa da baki be iya shiru tace"Cab Allah ya kyauta,ni wannan har nayi irin wannan shakuwan dashi ne? Allah yatsare a gayas,dariya Bodejo tayi tace"hmmm yaro yaro ne koma me zakice ba yarda zanyi ba.
Nan suka ta6a hira ta mike ta nufi sashen Mom,tagaishe ta aiko nan ta cidda Rammat ai zama sukayi suka sha hirarar su sosai,duk da Rammat sa'an su Aunty Mashahuda ce amma akwai saukin kai gashi nasu ya hadu da Zuhra,ba ita tashiga wajen Ammi ba sai after magrib,aiko nan Ammi tafara nan-nan da ita,duk kulawar da take bata ada sai yakaru, Ammi kuwa sai taga kamar Zuhra na cikin damuwa ne na tafiyan mijinta yasa tace"ki kwantar da hankalin ki Zuhra, yayan ki baze dade ba zaidawo kuma idan zaidawo dake zai koma gaskiya"Zuhra tace"a'ah Ammi nifa ba komai,kawai dama Akeela ne..sai kuma tayi shiru,kallon ta Ammi tayi tace"dama Akeela mene?me Akeelan tayi miki? Zuhra tayi raurau,hawaye na silalowa,nan taba Ammi labarin abinda yafaru dazu da safe,sannan cikin muryan kuka ta cigaba"ni Ammi inajin tsoron abinda zatayi mun ne,tace"idan nasan shi,duk da ban fahimci me kalmar take nufi ba,kuma ninasan shi,ba Yaya na bane? Ammi ta sauke ajiyar zuciya don ta fahimci tabbas Zuhra bata gane me hausar idan kika sanshi yake nufi ba hakan yasa taji natsuwa tace"ki kwantar da hankalinki,kinfa je islamiya Akeela ke saukakkiya ce,kinsan bawa baya wuce kaddarar sa, Akeela bata isa ta miki abinda Allah be miki ba,kisa hakan a ranki, sannan kuskure ne Wanda kema kinsa ni nacewa miji ya sakeki,kinsan zunubin hakan,sannan kinsan wani irin so Sauban ke miki?
Zuhra tace"Ammi wallahi Yaya beso na kawai ya aure ni ne.
Xahratty CEπ₯°
Lallai Alqalami ποΈ yafi takobiπ‘οΈ.
[7/15, 10:35] πππ‘π«π πππ‘π«ππππ²π₯°: π¨π½β𦳠*_GALADIMA FAMILY_* π¨π½βπ¦³
https://chat.whatsapp.com/Cz6pFHyd9N68OmqNx3Vpqs
Page:75/76
____Ammi murmushi kawai tayi tana jinjina ma yarintar Zuhra,haka Zuhra ta cigaba da zaman ta a apartment din Ammi tama mance da wani Sauban sai idan taji suna waya da Ammi take tunawa dashi,sannan tasake yarda da baya sonta tunda ko kiran