Showing 90001 words to 93000 words out of 103469 words
a gurguje ta haɗa musu lafiyayyen cucumber juice nd tamarind juice ta saka cikin fridge, duban su tayi tace"bari naje nayi sallolina gamunan babu magrib bare isha'i,sai na shirya,don ma yanzu aka kira isha'i,tana fita dai-dai lokacin kuma Sauban yakira ta,kan nan da 8:30 zasu shigo,amsa mishi tayi da to tana duban agogo,lokacin 8:06 cikin sauri tafaɗa bathroom tayi wanka tayi alwala,a gurguje tazo tafara sallolinta,a lokacin da ta idar 8:20 cikin sauri ta shirya cikin wata haɗaɗɗiyar lutfaya golden yellow,wanda ya mata kyau ainun,powder da kwalli kawai tasa sai ɗan kunne,agogo da sauran su,lalle nan ya fito tare da yin kyau sosai,high heel shoe me igiyoyi ta saka brown sannan tafice,shiga kitchen ɗin tayi da sauri tace su fito da kayan a fara shirya dinning,aiko cikin hanzari suka fara shirya dinning ɗin,komai suka jera sa a muhallin da,plates,glass cup's,spoons duk dai komai na buƙata,a dai-dai lokacin taji door bell,nufar ƙofan tayi tana buɗewa,babu zato taji ya wani rungomu to,nan ya shiga bata kisses kota ko ina,su Laila ganin hakan yasa cikin sauri suma suka fice suka nufi personal palour ɗin ta don gabatar da sallolin su.
"Uhum kai yaya Please stop,tayi maganar tana maƙalƙale jiki"cak ya ɗauke ta ya shige da ita palour yana dariya,kukan shagwaɓa tasa mishi wai ya sauketa,dire ta yayi yace"Eyye kin ganki kuwa Mrs MS?kinyi 100% babu makusa dressing me kyau me kuma mutumci,tunda muka shigo ƙamshi ya buɗaɗe gidan nan"Zuhra ta rufe ido tace"kai yaya,to ina abokan naka? Sauban yace"yanzu zan shigo dasu,wai Taufeeq har dashi ya tsaya wai sai na bashi izini?ɗan rainin wayo"hararar wasa Zuhra ta zabga mishi sannan tace"ai gaskiyan shine ni banga lefin shi ba,yaya ya san ka da kishi ne shiyasa"Sauban yace"to kinga lefina?ke bakisan irin kyan da Allah ya miki bane shiyasa,ga diri na jan hankali dole na dinga taka tsantsan dake"yana faɗar hakan ya juya,itama Zuhra murmushi tayi ta koma kitchen,ɗauko juice ɗin da ta haɗa tayi,glass jug biyu ta fito dashi,suma a lokacin ta taradda su zazzaune sai hayaniyar fira sukeyi,ajiye komai tayi sannan ta koma ta shaƙu tray da bottle water shima ta ajiye ta koma ta ɗauko cooslow ɗin da sukayi ɗanɗane,ta ajiye wani tray ɗin ta ɗauko inda su samosa,spring rolls nd cake ke kai ta ajiye, Sauban ne ya ƙariso kamar zai rungume ta yana kallon dinning ɗin yace"yanzu duk wannan aikin Babyn Baby ce tayi shi?lallai yau da rigima"dukan wasa ta kaima chest ɗin sa tace"mun kammala bari naje palour su Laila na can"Sauban yace"Okay love yhu"Zuhra ta watsa hannu ba tare da ta jiyo ba tace"me too love".
"Guys bismillah fa ku ƙariso"ya faɗa nan kuwa suka tattaso da yake dinning ɗin me cin mutane goma sha biyu ne,su kuma su goma sha ɗaya ne akwai ya Taufeeq da ango Kareem,sauran ne dai baƙin su,waɗanda in ka kallesu kasan kuɗi da sun zauna babu ƙarya, Kareem yace"Kai oga ƙarfi da yaji kasa Aunty Zuhra irin wannan aikin? murmushi Kareem yayi wani daga cikin su yayi carab yace"Nima idan zanyi baƙi Nihla nake sawa tayi komai,to ga iyalin ka ta iya mezesa kaje waje ci? Please Taufeeq yi ka serving ɗina"gabaɗaya dariya aka sanya harda Taufeeq kowa ya ƙagu ya fara cin abinci,inda kowa ya shiga zaɓan abinda zaici,sai dai daga ƙarshe ko wannensu sai da yaci komai dake wajen,babu abinda ke tashi sai muryoyin su da suke zuba santi
[7/25, 21:43] 𝐎̃𝐔̂𝐌 𝐀̃𝐉𝐌𝐄̨𝐑𝐋💜🤍: 👨🏽🦳 *_GALADIMA FAMILY_* 👨🏽🦳
[7/26, 10:39] 𝐎̃𝐔̂𝐌 𝐀̃𝐉𝐌𝐄̨𝐑𝐋💜🤍: 👨🏽🦳 *_GALADIMA FAMILY_* 👨🏽🦳
Page: 91/92
____Sun zuɓa santi,zuwa can Kareem yace"Allah Sarki Aure Aure me daɗi oga kaifa naka yayi kyau saura mu ƴan baya don wallahi Aunty Zuhra ta iya girki, shiyasa lokacin da suke Kaduna Taufeeq idan yazo nan yayi ta ɗafe-ɗafen yunwa ashe ashe"dukan wasa Taufeeq ya kai masa gabaɗaya suka saki dariya,wani a cikin su me sunan kabeer ɗan Gombe suna ce mishi kb ya dubi Sauban yace"Wallahi da a garin nan muke sai haseena tazo wajen yarinyar nan koyon girki"harara Sauban ya galla masa sannan yace"Matar rawa ce yarinya?Kb yace"Ea mana yarinya ce akan su haseena,a shegen girman kan haseena ma nasan ba zata taɓa zuwa ba"haka dai suka cigaba da tattauna wa domin sun ji daɗin abincin matuƙa.
Basu suka bar gidan ba sai wajen 9:30 lokacin su Laila ma sun tafi,tare da tuwon Galadima, Daddy da Ammi, Ummie sai na Baba Hasheem,suma dai acan hakan ce don santi suka dingayi,sannan su Laila suka sanar dasu Zuhra tayi girkin ta abinta,don su shinkafar su da kajin su suka ce, Aunty Mashahuda kuwa kiran Zuhra tayi ta sanar da ita idan akwai ragowan tuwo ta bama ya Taufeeq ya kawo mata,da yake a wajen ta malmala ɗaya ya ragu kuma tana so taci don bata jin cin shinkafar,ce mata tayi bari su tafi idan sun rage zata bashi ya kawo mata,cike da farin ciki Mashahuda ta kashe wayar,abinka da me kitchen.
Sauban ne ya shigo ɗakin yana aika mata da wani kallo me tafiya da zuciyar mutum,idanuwan sa sun koma so sexy yace"Wifey taso muje kuyi sallama"yayi maganar yana gyara mata lutfayar ta,hannun ta ya kamo ya miƙar da ita sannan suka tafi ajere.
Nan Zuhra ta shiga gaishe su,cikin kulawa suke amsawa,wani me suna Kamal yace"Gaskiya Madam oga beyi zaɓen tumbin dare ba shiyasa yake ta sake zama young Alhaji ashe kulawa yake samu,wannan delicious haka"murmushi Zuhra tayi tana sunnar dakai,nan dai duk suka gaggaisa suna miƙewa don tafiya tare da mata sallama suna godiya,hannun Kb ɗin riƙe da tray ɗin snack's ɗin don sunce sai sunje otel zasu ci, Zuhra tace"babu komai ai,fita sukayi ya Taufeeq na jinjina mata hannu, Sauban ya bata wani peck a kumatu"ina alfahari dake matata kin fitar dani kunya Allah ya miki albarka,yasa ki haifa min Baby girl me kama dake sak!👌🏼yayi maganar yana ƙale yatsu,dukan wasa Zuhra ta kaima chest ɗin shi sannan ta nufi dinning ɗin tace"Kaga dare ya fara bari na fara kai kayan nan kitchen,kun rage tuwo? Sauban ya dube ta cikin kulawa yace"baki ci bane? Zuhra tace"Ea ban ci ba ina da ragowan malmala ɗaya a kitchen dama Aunty Mashahuda ce ta kira tana so"Sauban yace"Caɓ anya sun rage tuwon nan bari mugani"yayi maganar yana buɗe foodflask ɗin,ragowar malmala ɗaya ne ya rage,yace"kinga abinda ya ragu ki kira ta ki sanar da ita babu"Zuhra tace"Haba yaya a'ah gwara na bata ni naci jollop ɗin hakanan"Sauban ya wurga mata harara yana tamke face"wai kina nufin ki zauna da yunwa?to baze yiwu ba keda aiki wasu da lamushe daɗi ki kirata kice mata babu"marairaice face Zuhra tayi sannan tace"yaya ita fa me ciki ce inada ragowar miyan gobe da safe sai na tuƙa wani yanzu zanci jollop ɗin ka bari a bata"Sauban ya sake tsuke face yace"kika sani ko kema cikin ne dake?dariya Zuhra tasa kawai batare da tayi masa reply ba saboda kiran wayar sa da akayi.
Batare da yayi picking ba yace"bari naje suna jira na zamu kaisu otel ɗin da suka sauka sai mu dawo,cikin sauri Zuhra tace"Please yaya ku sauke ni cikin gida sai na kaima Aunty Mashahuda tuwon"wannan karan tamke face ɗin yayi gabaɗaya Sannan yace"ba zaki kai mata ba a daren nan,idan ta buƙatu tazo ta amsa"yana gama faɗar haka yayi wucewar sa,ɗaga murya tayi tace"safe journey"juyaowo wa yayi cikin jin daɗi yace"tnx love"ya fice,kaya kayen kayan Zuhra tayi tana harhaɗa plates ɗin,kuɗi ta gani kashi da kashi kusan biyar,zato ido tayi cikin mamaki,wato ihsani sukayi mata kenan,ɗaukan kuɗin tayi ta irga na farko 10,000 na biyu 5000,na uku 10,000,na huɗu 15,000,na biyar 7000,cike da mamaki Zuhra ke kallon kuɗin lokaci ɗaya sun haɗa mata 45,000k kenan sun biya ta kuɗin aikin ta,hakan yasa sai taji bata wani murna da ganin kuɗin ba,ajesu tayi anan side ɗin dinning ɗin ta cigaba da gyaran wajen.
Basu jima ba suka shigo shida ya Taufeeq,a lokacin ta shirya cikin wasu shegun night gown,sanin ƙila Taufeeq ya shigo yasa ta zunduma long hijjab abin ta, Taufeeq yace"Malama ina tuwon Madam ɗina? Zuhra na murmushi ta miƙe ta nufi kitchen,bata jima ba tafito hannun ta ɗauke da foodflask tare da wani ɗan take away tace"gashi tunda abin bin bashi ne,kada Babyn mu ya fito da taɓo yaya"Sauban yace"a samu hujjan yi mana aharri ba? Taufeeq ya amsa foodflask ɗin yana dariya yace"wallahi kuwa don haka kun fanshi kawunan ku,gud night"Yana ƙare faɗar hakan ya fice, Sauban na biye dashi ya sama ƙafan key,tare da juyowa ya rungume Zuhra a jikin shi,cikin kulawa yace"kinci abinci? ɗaga masa kai tayi,yana rungume da ita suka haye stairs yana cewa"shine za'ayi wankan ba za'a jirani ba?so wallahi sai kinyi sabon wanka don ke zaki tayani"bubbuga ƙafa Zuhra ta fara cikin shagwaɓa,don harga Allah idan aka ce dare yayi to always cikin fargaba takeyi,don tutur federal government ɗin ta a matse yake duk da ruwan ni'iman da yake shiyasa take wahaluwa,duk da ko kaɗan bata nuna masa gazawan ta,hakan ke ƙara masa son ta da ƙaunar ta,kamar yasan tunanin da takeyi ya matso dai-dai kunnen ta cikin muryan raɗa yace" sai kinyi haƙuri da yayan ki, cuz bana gajiya dake keɗin ta daban ce Babyn Baby"yayi maganar tare da ɗaukar ta cak ya shige da ita toilet.
********
Dama akace duk abinda ake sama rana sai idan lokaci beyi ba,domin kuwa yau ne ake shirin ɗaurin auren su Kareem.
Zuhra tayi kyau har ta gaji,ankon colour sukayi da Sauban kayan da ya siyan musu,wani straight gown aka yima Zuhra me ɗaukar hankali,don ma veil ɗin babba ne,daga ita har Sauban ɗin duk wanda ya kallesu sai ya kuma, ga high heel ɗin ta da ga henna gaskiya Zuhra tayi kyau wanda me karatu ne kawai zai ƙiyasta irin kyan da tayi a zuciyar sa,saura five minutes daurin auren don daurin auren 2:30 ne gabaɗaya 'yan gidan su tun ɗazu suka fice, Ammi na gidan su Kareem, Ummie dasu Mashahuda dasu Laila suna gidan su Mom,sai da Sauban ya samu natsuwa sannan ya shirya Zuhra a bala'in gajiye take ƙarfin hali kawai takeyi duk abinda takeyi,da kanshi ya kamata ya shiga da ita gidan,nan fa maroƙa suka shiga roƙo,duk inda suka gifta kuwa kallon su akeyi ƴan jaridu ma na ɗaukan pic,haka zalika wasu daga cikin mutane,don Sauban yayi fice matuƙa kuma bikinsu da Zuhra duk da ba'ayi wani events ba amma hotunan da akayi yasa sosai sukayi trending a lokacin.
Mom sosai ta tarbesu cikin kulawa ta kamo Zuhra,palour da aka kai Ummie nan Mom ta nufa da ita,Hajiya Biba ma cikin kulawa ta tarbe Zuhra,ita kuwa cikin girmamawa take gaida su, Zuhra tace"kai Mom kin ganki kuwa? Baba yaga kwalliyar nan?daƙuwa Mom ta mata tace"ƴar nema da har ina cewa Sauban ya rufe miki baki ashe be rufu ba"dariya Zuhra tayi tana ɗan rissinawa wajen Ummie tana gaishe ta, hararar Ummie ta kai mata tace"hamshaƙiya ai nayi tunanin bazaki zo ba"don har aiko su Nihal nayi tunda wayar ki kin kashe"Zuhra tace"Ummie fa yaya ne ya tsayar dani"Ummie tace"Okay to kije wajen amaren mana"Zuhra tace"ai bansan inda suke ba"dai-dai lokacin Muneefa ta shigo tasha kyau cikin lace me tsada ganin Zuhra yasa ta ƙarisu da sauri,kamo ta tayi taja sai da suka fita tace"Masha Allah maganar ku ya yaɗa ko ina ance kunyi anko da yaya kun haɗo shine nazo neman ki muje"Zuhra tayi murmushi kawai,a dai-dai lokacin ne kuma maroƙa suka shiga shela
"An ɗaura auren Abdulkarim Usman Shugaba tare da amaryar sa Rahma Ahmad lakadan ba ajalan ba,nan fa mata suka shiga zazzaga ruwan guɗa.
Sosai biki yayi armashi, Zuhra ta bawa Rammat gudummawar bikin ta da yaya ya bata ta bayar 50k Cass haka ta bata,tabawa Hajiya Biba 20k sosai sukayi farin ciki don Ummie ma 20k ta bawa Hajiya Biba Mom taji daɗin karan da suka mata.
Ƙarfe huɗu akazo ɗaukar amarya a masu ɗaukar amarya kuwa harda Ammi,anan itama ta bawa Hajiya Biba 30k, Zuhra Sauban da Taufeeq suka ɗauke su ita da Mashahuda dasu Laila,aiko aka nufi new g r a maidugri da amarya,gida fa yayi kyau sosai ɗan dai-dai sama da ƙasa ne,sosai fa wajen yayi kyau Masha Allah,sannan babu lefi su Mom sunyi ƙoƙari wajen haɗa wajen,duk da saman Kareem da kanshi shi ya sanya komai,shima yayi kyau sai dai ko rabin rabin na Sauban be kamo ba, dai-dai ƙurji dai, dai-dai tsaki,haka kowa yafito cike da sanyi aka watse aka bar amarya don babu ƴan kwana, Zuhra kuwa daurewa takeyi saboda zazzaɓin da yake ta cin ta a tsattsaye.
Cike da gajiya suka isa gida.
Washe gari ya kama Sunday,koda Zuhra ta tashi wajen 9 bata ga Sauban ba tunda komawa bacci tayi abinda,gyara ko ina tayi sannan ta shiga kitchen,tuwon ta ta tuƙa malmala huɗu sannan shi kuma ta haɗa mishi lafiyayyar sandwich da coffee,ta shiga toilet tayi wanka sanda tafito lokacin taji motsin shi ya shigo gidan tunda ga ƙarar motar sa nan.
A gurguje ta sakko cikin wata haɗaɗɗiyar turkey gown tayi mata kyau peach colour me hannun vest,sannan har ƙasa,sai hulan gown ɗin da ta saka,cikin da jin daɗi yayi hugging ɗinta tare da shinshina ko ina na jikinta yana lumshe ido,cikin wata kasalalliyar murya yace"shine zakiyi wankan kibarni?jin haka yasa Zuhra cikin zafin nama ta fusge jikinta da gudu ta ƙarisa wajen dinning tace"Allah ba zaka sani yin wani wankan ba"cikin muryan dariya tayi maganar, Sauban yace"hmmm yarinya zaki shigo hannuna ne"hayewa stairs yayi be daɗe ba ya fito cikin kaftani black anyi mishi ɗinkin halfjamfa yayi kyau ainun,gyararren baƙin gashin nan nashi sai sheƙi ya keyi,zama yayi nan Zuhra ta fara serving nashi tana cewa"Gud morning Babyn baby"murmushin jin daɗi Sauban yayi yace"morning to my everything,hope kintashi lafiya?Zuhra tace alhamdulillah, duban plate ɗin ta yayi yace"nima fa zanci tuwon"yayi maganar idanuwan sa ƙur akanta,murmushi Zuhra tayi tasa mishi malmala guda,nan suka fara breakfast ɗin su cike da soyayya tare da ƙaunar juna.
********
A ranar su Ummie suka koma, Zuhra kuwa kasuwa tasa Sauban ya wuce da ita tunda gobe shima zai tafi,sam bata son tafiyar nasa haka kawai taji damuwa inda ta alaƙan ta hakan a matsayin shaƙuwa.
Koda ta dawo,dambun kaza ta shiga haɗa masa da doughnut sai cin-cin,tare sukeyin aikin don sosai ya sake yana taya ta suna komai cikin soyayya juna,basu kammala ba sai wajen 6:00,aiko Sauban bebi takan gajiyar da sukayi ba,ya nemi haƙƙinsa ya sauke,ita kuwa Zuhra sai ƙananun kukan shagwaɓa take masa,wanka ya musu sannan suka ɗauro alwala,kaitsaye masjid ya wuce,ita kuma ta tayar da sallan ta anan.
Text ya turo mata kan yana wajen su Daddy kada tayi girki,reply ta masa cewa"Okay ka gaishe su"nan ya turo mata alamar sumba😘, murmushi kawai Zuhra tayi sannan ta miƙe,itama gobe suna da class sai dai wajen 11 zasu shiga,shiko Sauban 9 zai wuce,cike da gajiya ta kwanta ba ita tafar ka sai sanda taji anata shafa ta,cikin sauri ta buɗe idanuwa,a kyakkyawar fuskar mijinta ya sauke,murmushi tayi ta miƙe tare dukan chest ɗinsa"Kai Yaya shine kaje ka daɗe ko? Sauban yace"Sorry love Ammi tace na tsaya na taho miki da masa"yayi maganar yana kamo ta,cikin farin ciki Zuhra ta taso ta biyo shi,da yake anan palour saman nashi ya ɗauki duk wani abin buƙata,nan yayi serving nasu tare da feeding ɗin ta don yaga bacci ne sosai a idanuwan ta,koda suka kammala da kanshi yaje ya kwantar da ita yaja mata duvet,shi kuma ya dawo palour don yin aiki a laptop ɗin sa.
Zuhra tunda ta farka da asuba basu koma ba nan ta tayashi haɗa duk wani abin buƙatan sa,inda shima ya nemi haƙƙinsa,(oga Sauban kenan sam ba'a ɗaga ƙafa,kana so Zuhra itama ka koya mata......ba)
Lokacin har 9 ɗin yayi sosai Zuhra ke kuka don ko kunyar su Daddy bata ji ba,kuka takeyi sosai,shi kanshi Sauban daurewa yakeyi,ganin taƙi shiru ne yasa Baba Hasheem cewa to idan batayi shiru ba bazata rakasa airport ba,dole kuwa ta haɗiye kukan ta, Kareem da kanshi shida Rammat suka zo kaisa airport,sai Zuhra da Yasir,haka suka tafi Ammi da Boɗejo su Galadima na ɗaga masa hannu.
Basu baro airport ɗin ba sai da suka ga tashin sa inda ya nuna mata soyayya a gaban mutane don rungume ta yayi ya bata sumba a goshi tare da mata magana a kunne yana shafa cikinta"Insha Allah nasan nayi ajiya anan,ko don dagewan da na dinga yi kwana biyu"sosai Zuhra ta saki murmushi tana faɗa wa jikinsa,cike da ƙaunar juna suka rabu.
Har gida su Kareem suka kawo Zuhra suka ajiyesu ita da Yasir, apartment ɗin Ammi ta wuce,bata wani jima ba tayi shirin school 10:30 ta fita inda driver zai sauke ta.
[7/26, 21:02] 𝐎̃𝐔̂𝐌 𝐀̃𝐉𝐌𝐄̨𝐑𝐋💜🤍: 👨🏽🦳 *_GALADIMA FAMILY_* 👨🏽🦳
Page: 93/94
_____Zuhra ta cigaba da resuming school ɗin ta duk da bawani daɗi takeji ba amma a haka take maida hankalin ta sosai akan karatun ta,duk tsananin kewar mijinta da takeyi ko da yaushe sai dai sam taƙi bada ƙofar da za'a fahimci hakan har shi don suna waya sosai tare da video call don ya aiko mata da tsadaddiyar laptop ɗin ta Apple.
*AFTER 4 MONTHS*
Abubuwa da dama sun faru na farin ciki,ciki kuwa harda ƙarin matsayin da Sauban ya samu aka maida shi Malaysia sosai yaji daɗin hakan don yafison ƙasar da Canada,ƴan uwa kowa ya taya shi murna da farin ciki, Zuhra kuma suna exam na shiga 200l inda bikin su Laila yayi saura 2 months,shirye-shirye duk sukeyi ta kowa ce ɓangarori haka aketa shiri.
Akeela duniya ta ladabtar da ita duk da kuwa matsanancin Son da take ma Sauban nanan daram dam don babu abinda ya ragu sai ma ƙaruwa,kullum ka ganta a ɗaki cikin zubda hawaye takeyi tare da tsanan kanta da kanta,ta bayan fage kuma mommy(hajiya daharatu) nata ƙoƙarin ta dawo da ita ruwa tsundum.
********
Su Zuhra sai da sukayi 2 weaks suna exam sannan suka kammala a lokacin tafara shirye-shiryen zuwa kaduna don haka ta kira Sauban take sanar dashi sai dai duk ƙoƙarin ta na yabari