Showing 87001 words to 90000 words out of 103469 words
ƙofan palour Guggo Laure sai mita takeyi,cikin ɓacin rai da muryan kuka Akeela ta fara magana"Wai ya kuke so nayi ne da rayuwa ta?nace nayi nadama ina kuma neman yafiya na a wajen Allah to meyasa za'a tasa ni da cin zarafi? Guggo Laure tace"dole aci zarafin ki domin kin daɗe kina cin amanar mu tare da ɓata mana sunan ahali,ashe ba karya da sharri su A'isha suka miki ba amma kika zo kika faɗamin ƙarya da gaskiya kika sa naje na ma ɗan uwa na tujara har takai shi da samun mutuwar ɓarin jiki?wallahi Akeela ke sheɗaniya ce"sosai kalaman Guggo Laure ya ɓata ma Akeela rai,tana kuka ta fara magana"Kada ki mance Guggo kece kika fara tusa min son ya Sauban a raina tun bansan menene so ba,kece kika samin kwaɗayin son sa,wallahi Guggo har yanzu ina son ya Sauban banjin akwai na mijin da zanso bayan shi,don Allah Guggo kije ki roƙa min gafarar sa ya maidani"wani kallo Guggo Laure ta mata na baki da hankali sannan ta miƙe ta shige cikin uwar ɗakin ta tana jin baƙin cikin abinda tama yayan nata,tarasa da wani idon zata je duban sa.
Kuka sosai Akeela keyi tana Allah wadai da irin rayuwar ta,ga kunyar duniya bata isa ta fita waje ba,aci zarafin ta iyayen ta da basu ji ba basu gani ba suma a zage su,share hawayen ta tayi tana miƙewa ta nufi apartment ɗin su.
A tsakanin Bana sani da Alhaji Mansir kuwa sun yanke hukuncin zuwa su bama GALADIMA da su Daddy haƙuri akan abinda ya faru,don haka suka fito cikin shirin su suka nufi wajen Guggo yi mata sallama,anan suka ci karo da Akeela da ke tafe tana sharɓen kuka,wani dogon tsaki Alhaji Mansir yaja sannan yana nuna ta da yatsa cikin ɓacin rai yace"Ai inhar duniya ce Akeela baki ga komai ba"girgiza kai kawai Baba sani yayi harga Allah yana jin zafin abinda Akeela ta aikata ga tsananin tausayin ta.
Koda suka shiga wajen Guggo Laure sanar mata sukayi da inda zasu nanfa ta tubure kan itama zataje,duk yanda suka so lallaɓata taƙi hakan yasa babu yanda suka iya suka ce to ta shirya suje.
Fitowan su kenan daga apartment ɗin Zuhran Rammat tana ƴar dariya ta dubi Muneefa tace"wallahi kidai kula da amanar da yaya ya danƙa miki idan ba haka ba kuma babu ruwa na"duban Zuhra Muneefa tayi tace"wa? aidole na kulan ma yaya da wannan amanar tashi domin idan nasake wani abu yafaru hukunta ni zaiyi duk da yau saura kwana uku biki,ni fa banga wani wurin da akayi na zuwa saloon ba.
Rammat tace"Gaskiya kam,suna ƙoƙarin fita second gate sai gashi anturo,su Guggo Laure ne,aiko cikin girmamawa su Zuhra suka shiga gaishesu,sosai suka amsa cikin kulawa inda Guggo Laure keta nuna kulawa akan Zuhra fiye da kowa,domin ko gausuwar Rammat ma bata amsa ba,sai su Baba Sani ne ke tambayar ta Hajiya Uban da shirye-shiryen bikin?(kunsan dama su ɗin ƴan uwa ne da Hajiya Biba da mahaifin su Baba Sani.)
Wucewa sukayi inda Muneefa tace"To me kuma yakawo Guggo gidan nan?ita da ta nuna bata babu ahalin nan sannan sai wani basar damu takeyi"Rammat tace"mtseeww! Can ta matse mata ganina ne yasa take ta wannan abin ke bakisan sunje family ɗin su Hajiya sunyi tujara ba ita da Ouncle Mansir?suna cewa Hajiya ce ta kashe ma Akeela Aure tunda dama taso nine na aure Sauban?sai da ashirin Akeela ya tonu sannan da Hajiya ta wanku,anan kuma aka samu masu zuwa jin gulma,idan kika lura Ouncle Mansir ma cikin kunya ta ai yake tunda dama shine mataimakin ta idan tana tujara.
Zuhra tace"Allah dai ya kyauta"Duk da Ameen suka amsa,inda suka isa bakin ƙofan motar, Zuhra ta fara shiga backseat ɗin sannan Rammat, Muneefa kuma tashiga gaba,dama Mus'ab mijin ta ne zaikaisu saloon ɗin.
Acan ƙofan palour Boɗejo kam sallama suke ta dokawa, Boɗejo ta fito tana amsawa tare da bada izinin shigowa,sallama sukayi suka shiga da mamaki take binsu da kallo musamman Guggo Laure tamke face tayi don sometimes Boɗejo bata da dama,gaisawa suka fara yi,sannan shiru ya ɗan gifta, Guggo Laure tace"yaya Boɗejo yaya Muhammadun ko nanan? Boɗejo ta sake tsuke face sannan tace"Yana nan dame kuma yau akazo masa?don bazan yarda yau a kuma tayar masa da hankali ba"tayi maganar tana ɗauko cup ɗin goron ta ta ɗauraye ta ɓantara,cikin damuwa Guggo Laure tace"Wallahi ko kusa hasalima nazo na bashi haƙuri ne akan duk abinda yafaru,tabbas nayi kuskure wanda gashinan nazo ina nadama"Boɗejo tace"Ikon Allah to madallah bari na mishi magana ya fito nan,miƙewa Boɗejo tayi zuwa can sai gashi sun fito GALADIMA ne a gaba yana tafe yana dogara sandar me shegen kyau da tsada,bayan sa Boɗejo ce ta fito.
Samun waje yayi ya zauna cikin kulawa GALADIMA ya dubi Guggo Laure yace"Laure kece a gidan?cike da jin nauyi Guggo Laure tace"ina wunin mu yaya?ya ƙarfin jikin naka?cikin fara'a GALADIMA yace"alhamdulillah jiki yayi sauƙi sosai,nan su Baba Sani suka shiga gaishe shi cike da girmamawa tare da tsananin jin nauyi,kunya da nadama.
"Hanne!!! Boɗejo ta shiga ƙwala ma maid ɗinta kira,babu jimawa ta iso hango baƙin da tayi ya fahimtar da ita abinda zatayi,komawa kitchen tayi ta haɗo abin motsa baki a tray sannan ta iso ta ajiye tana gaishe dasu Guggo Laure,a lokacin da yake da la'asar ne sai Galadima ya ɗau waya ya kira su Daddy,babu jimawa suka iso shida Baba Hasheem sunyi mamaki ƙwarai,inda Baba Hasheem ya ƙudurta a ransa idan sunzo da niyyar cin wani mutumcin ne to shi zai sauke musu.
Saɓanin haka domin kuwa sosai suka nemi yafiya inda Guggo Laure har kuka tayi, Baba Hasheem yace"ai Guggo an aikata abin kunya ne zalla,be kamata yara su haɗaki da Galadima ba,yana ɗaya daga cikin abinda a yanzu haka naji auren zumunci ya fita kaina,amma wannan ba komai bane face rubutaccen ƙaddara, Allah ya tsare gaba"da Ameen duk aka amsa,sannan Daddy ya dubi Guggo Laure yace"to meze hana ita Akeela ta dawo nan gidan da zama tunda kince acan babu halin ta fita sai hantara da ƙyamar?ta dawo nan kaw.....wani tsalle Boɗejo tayi ta dire cikin masifa tafara zazzaga ruwan bala'i"wallahi Taleeb zanci mutumcin ka duk abinda ya faru be isheku ishara ba ko?to wallahi ba zata dawo nan ɗin ba babu ruwan ka,aikin banza kawai aikin wofi"gabaɗaya palour shiru akayi kowa na sauraran masifan da takeyi, Guggo Laure tace"ai komai ma mai wucewa ne Taleeb mungode sosai muma a yanzu ba zamu tabbatar da nadamar Akeelan ba sai a dalilin zama a gaban mu tukuna zamu gane"taƙarisa maganar tana sharɓen ƙwalla da gefen mayafin ta, Baba Sani yace"Gaskiya ne wannan yaya gwara ta zauna acan gaban namu zafi, miƙewa Boɗejo tayi tare da mere da baki kamar ba tsohuwa ba tace"Da dai yafi ku gaida gida"tana gama faɗar hakan bata jira amsar su ba tanufi corridor ɗin da zai sadata da jerin ɗakunan ta sai ƙananan surutai takeyi tanaji kamar ta faffallama Daddy mari.
Anan aka fahimci juna tsakanin Guggo Laure da Galadima sannan sukayi musu sallama suka miƙe,suma su Daddy miƙewan sukayi don taka musu.
Wajejen magrib Suby da Zuleey ne aka tsinci gawar su a wani hotel room inda suke tsirarar su an musu yankan rago, wannan abin ba ƙaramin girgiza Akeela yayi ba don kamar zatayi hauka da ta samu wannan mummunan labarin,kuka take kamar ranta zai bita,cikin tashin hankali Alhaji Mansir ke magana"Kin gani?sune manya²n ƙawayen ki baki da ƙawaye sama dasu to wallahi Akeela Allah na Son ki da rahama domin kuwa ya miki da kyau abisa su,ki dage da istigfari da roƙon Allah yafiya,ki kalla ita wancan yarinyar suwaiba uban ta ƙin ɗaukar gawan ta ma yayi sai da ƴan uwa suka suturta,wannan kuwa"yayi maganar yana nuna Zuleey"Iyayen ta kuka suke kan ammata sharri ne, saboda bata taɓa ɓarin wata ƙofa da zakayi mata kallon mutumiyar banza ba,kullum cikin suturta jikinta takeyi,ina me baki shawara da kiyi tuba irin tuban taubatun nasuha,idan ba haka ba ƙarshen ki sai yafi nasu muni"cikin muryan kuka Hajiya maimuna tace"haba haba mana Alhaji kadena jifan yarinyar nan da mugayen kalamai haka,kune kukayi silar komai nata Akeela tun tana da 16 yrs ta nuna maka aure takeso amma kai da Guggo kuka nace sai tayi boko"taƙarisa maganar cikin kuka.
Zira takalmi Alhaji Mansir yayi yana fita yace"kyadai daiji dashi,nidai gaskiya nake faɗama ta ( _Nikuwa nace gaskiyar ka ta banza Alhaji Mansir?sai da Akeela ta lalace kake faɗa mata gaskiyar?kana ina sanda take kwana a waje?kana ina sanda ƙasashen banza ke zuwa wajen ta?baka taɓa bincike ƙawayen ta ba,kuskuren da iyaye da dama keyi kenan a wannan zamanin, Allah yasa mudace alfarman Annabi da Alkur'ani._)
[7/25, 09:30] 𝐎̃𝐔̂𝐌 𝐀̃𝐉𝐌𝐄̨𝐑𝐋💜🤍: 👨🏽🦳 *_GALADIMA FAMILY_* 👨🏽🦳
Page: 89/90
____Sosai Sauban ke nuna ma Akeela soyayya da kulawa wanda be jin kunyar uban kowa,su Laila ma an sakko da bikin su nan da six months don har ga Allah yayi nesa a ce sai sun gama School tunda dududu 2000l yanzu suke,dama Zuhra ce dai bata shiga da wuri ba,yau ta kama Tuesday kuma yau ne ake event na Kanuri day,amarya tasha kyau ko ta ko ina.
Zuhra sosai take kuka a dalilin hanata zuwa wajen event ɗin da ya Sauban yayi,har yau takasa sabawa dashi tun wajen 1 yake abu ɗaya har yanzu da ake neman 4 azaba ya ishe ta duk da ma juriyar da Allah ya saka mata amma tayi kuka har ta gaji,gabaɗaya a wahale take ko hannun ta bata iya ɗagawa,sai yanzu ya sarara mata,ɗaukan ta yayi ya shiga da ita toilet ya musu wanka,inda ita kuwa sai ƙananun koke² take masa da complain ɗin ciwon jiki,shiyasa suna fitowa daga toilet sallah yaja su sannan yafara aikin yi mata massage,a haka wani wahalallen bacci kuwa ya ɗauke ta,cike da wani irin ƙaunar ta yake kallon ta yana ji kamar ya haɗiye ta,peck ya bata a kunci sannan ya shirya cikin wata kaftani ɗinkin half jamfa me laushi tare da tsada,kwantancen gashinta a gyara suɓul sai sheƙi yakeyi batare da yasa hula ba yaɗau car key ɗinsa yabar gidan,kai tsaye wani lafiyayyen eatry ya nufa,shiga yayi ya haɗo musu take away na Burger sannan yadawo, ko a lokacin bata tashi ba hakan yasa kaitsaye ya faɗa kitchen inada ya feraye Irish nan ya haɗa musu chips nd egg,komai jera shi ya shiga yi akan dinning,batare da ya sake hawa upstairs ɗin ba,toilet ɗin palour ta ya shiga ya daura alwala ya tafi masallaci.
Bashi ya shigo ba sai wuraren 8:30 don har isshan shi yayi,hayewa saman yayi nan yaje ya fara tashin Zuhra cikin kulawa,shafa mata kai ya shiga yi yana hura mata iska a kunne,cikin wani irin shagwaɓa ta tashi,cikin muryan shagwaɓa tace"Kai yaya nifa baccin be isheni ba sam"tayi maganar tana turo mouth gaba,rungumo ta Sauban yayi cikin kulawa yace"to ai dole ki tashi I know yanzu haka kinajin yunwa ga sallolin ki,Please wake up"yayi maganar yana kamo hannunta tare da miƙar da ita,kukan shagwaɓa ta saka masa,be sake ta ba,har toilet ɗin ya kaita tayi alwala sannan ya shimfiɗa mata praymat ta tayar da sallah, hakan yasa ya fita yaje ya haɗo komai a tray ya kawo saman anan palour ya ajiye.
Waya yakeyi da ƴan office ɗin su sai iskanci suke masa kan yaƙi dawowa,fitowa tayi tana ɗan nesa dashi don har ga Allah wannan jarabar nasa tsoro yake bata,miƙewa yayi ya kamo ta ya zaunar tare da hanging call ɗin,cikin shagwaɓa ta dubesa"Shine bazaka jira na tashi nayi komai ba?ni nafi son kana cin abinci na sam bana son kana cin na eatry"kumatun ta Sauban yaja yana maimaita maganar nata,throw pillow ta ɗauka ta jefa masa tana sakin kukan shagwaɓa, kamota yayi ya ya shiga lallashin ta,hakan ya sata lafewa a jikinsa,shida kan shi yayi feeding ɗin ta sai da taci ta ƙoshi sannan ya ƙyale ta.
Haka rayuwar su ta kasance gunin ban sha'awa da burgewa Sauban bashi da wata matsala sai na kishi,yana da zazzafan kishi sosai.
********
Ranar juma'a su Laila suka diro harda su ya Taufeeq,mommy ce kawai bata biyo su ba,sai ta haɗa su dasu Ateeq da maimoon a dalilin kukan da maimoon ta dinga yi kan sai tazo wajen Zuhra,gabaɗaya Zuhra ta tare acan da yake Sauban ranar yana busy saboda suna shirye-shiryen tarban abokan su waɗanda sukayi school,wasu ba'a state ɗin suke ba,wasu kuma suna can daga waje zasu shigo, Zuhra na zaune wayar ta tafara ruri, Nihal ce ta miƙa mata,ganin sunan Sauban ne yasa ta ɗanji sanyi a ranta don tunda ya fita be nemeta ba,duk da taso kiran shi amma sai hayaniyar ƴan uwan ta ya hana ta zuwa, picking tayi,daga can ɓangaren Sauban yake ce mata don Allah gashi nan zai turo da saƙo idan babu damuwa yana so ta haɗa ma baƙin su dinner da zasu iso yau ɗinnan.
ZUHRa cikin sanyin murya tace"Tom babu komai tana jiran shi"sanar mata yayi da taje gida zai aiko da komai,miƙa tayi tana faɗin"Tom bari naje"kashewa yayi,ada yaso suyi Oder ne ta hotel sai yaga rashin dacewan hakan,shiyasa ya yanke wannan hukuncin,sun kama musu hotel rooms wanda sai da suka kama ɗakunan goma sha biyu,duk Sauban ya biya komai.
Duban Nihal da Laila Zuhra tayi tace"kuzo muje ku taya ni aiki yaya zai aiko saƙo zamuyi ma baƙin su girki,cikin murna kuwa suka tashi suka tafi,maimoon kuwa tana biye dasu,don Ateeq na can wajen su Daddy.
Su Laila sai sake santin apartment ɗin suke yi,wai kamar ya sake kyau, Zuhra ta basu amsa da Ea an ƙara wasu kayayyakin.
Nihal ta riƙe waist tare da duban Zuhra tace"Matar nan nifa naga sai wani glowing kike ƙarawa me yaya ke baki ne haka?hararar wasa Zuhra ta galla mata tace"munafuka bari idan ya dawo ki tambaye sa"kama baki Nihal tayi tace"Wa? Rufamin asiri in mutu maza su kaini salin alin"Laila dariya tayi tace"kenan da wani tambaya kike Nihal,aiko abinda yaya ke bata da ya wuce rufaida yoghurt"da yake Zuhra ta fahimce lailai aiko ta maka mata duka tana kaucewa, Zuhra tace"ai kam zakiyi masa bayani bari ya dawo"kafin lailai ta bata answer door bell yafara ƙara,Nihal ce taje ta buɗe,aiko wani ɗan matashin ne ya sauke bako biyu na kaya,nan Nihal ta ɗau ɗaya, Laila ma tazo taɗau ɗayan.
Kai tsaye kitchen suka dire komai da komai, Zuhra ce ta bisu kitchen ɗin,leda ta farko kayan miya ne sai kayan salad,sai egusi da owgun,sai ɗayar leda kaji ne daƙwa² guda huɗu sai saidin kifi,shiru Zuhra tayi tana tsura ma kayan,aiko nan abinda zatayi ya faɗo mata,ɗaya ke gashin a gyare ne, ɗauraye wa kawai tayi sannan ta dubi Nihal tace ta gyara kayan miyan,ta fara niƙa tomatoes daban sai kayan yajin daban,Laila kuma ta wanke kifin ta tsane a basket sannan ta barbaɗe kayan spices.
Kowa kama aikin sa yayi, Zuhra koda ta ɗauraye kajin,kwaso kayan spices ɗin da Ammi duk ta kawo mata tayi tasa komai yanda ya kamata,ginger,cloves,gerlic tasa kaɗan,sai ɗiyar miya,ta ɗau ko ganyen parsley ta ɗan ɗora a sama tasa Curry bata sa tyme ba, seasoning ta kwaso, Maggi star 4, Maggi know 4,rayco 4 sai onga chicken flavour tasa biyu ta rufe, store ɗin da ke cikin kitchen ɗin ta ta shiga,ta ɗauko semovita guda biyu ta fito.
Ɗauraye peas ɗin tayi da carrot ta fara gyarawa bayan ta ɗora ruwa a wata tukunya,bayan ta ɗora ruwan,komai dai tayi shi cikin natsuwa wanda su Laila suke mamakin inda Zuhra ta koya girki,komai daki² takeyin sa,perboiled ɗin shinkafar ta tayi ga ƴar souce na kayan yaji da tasa ma Nihal komai,gefe guda kuma Laila na soya kajin,acan kuma kuma ga peas nan nata nuna a ruwan da tayi sanwa ɗan dai-dai,tuwon ta fara tuƙawa dama tayi talge tun ɗazu, duban Nihal tayi tace ta zuba mata shinkafar koda ta zuba lokacin ta gama tuƙin hakan yasa tazo ta fara motsa shinkafar,gabaɗaya wani ƙamshi me shegen daɗi ya game apartment ɗin,bayan ta motsa shinkafar ne ta ɗan rufe ya ɗan turara,abinka da nonestick pot.
Laila na gama suyan kajin dama tun ɗazu an sauke source ɗin da ɗan ruwa kaɗan a jikinta,kifin aka ɗora Nihal itama ta cigaba da kula da shi gabaɗaya hankalin ta nakan Zuhra don ganin komai Allah yasa ni cike take da mamakin komai, haɗa kajin nan Zuhra tayi aɗan bawo me balance sannan ta ɗauko source ɗin nan tafara haɗa komai,cikin natsuwa take komai, Laila ganin kamar ta gaji ne yasa ta amsa ta cigaba da motsawa,cikin natsuwa tace"naga ma kamar ya haɗu,ki buɗe wancan drower ki ɗauko set ɗin wasu foodflask mugani,miƙewa Laila tayi inda Zuhra kuma ta rage wutan tuwon don yanzu zata kwashe,kashe wutan shinkafar tayi,da yake kulolin babu lefi suna da ɗan girma duk da kuwa kyan su ana biyun ta juye shinkafa,na farkon kuma ta juye pepper chicken ɗin,kwashe sauran tayi ta maida carbenet ɗin,sannan ta fito da wasu set ɗin.
Suma 4set ne sai ta cire biyu da babban dana ukun, babban suka fara ƙulla tuwo suna sakawa sai da suka ƙulla malmala goma ƴan dai-dai,sauran tabada wani foodflask ɗin tace a zuba shima malmala goman yaci,babu abinda ya rage akan gas sai miyan tuwon da kuma cooslow, already an goge kayan cooslow ɗin haɗi kawai yake jira,sauke miyar tayi wacce sai tashin ƙamshi takeyi sannan ta zuzzuba anasu foodflask ɗin sauran ta zuɓa a ɗayan foodflask ɗin shima,sannan ta ɗauko soyayyen kifin ta zuba a kowane kulan miya wada tacce,ragowar ta saka cikin fridge.
"Ikon Allah nifa ina mamakin inda kika iya girki ne haka Zuhra musamman me yawa,kinji yanda ƙamshi ya game apartment ɗinn nan?Nihal tayi maganar tana kama haɓa,murmushi Zuhra tayi cikin zolaya tace"idan za'a ɗauki Course sai azo tunda bikin naku ma ya gabato"Laila tace"yanda kika jin nan" sauran jollop ɗin shikafan tukunyar tabasu foodflask tace su sake musu,fito musu da komai tayi harda su masarar gwangwanj,bama,waken gwangwani,babu egg dai tace su haɗa cooslow ɗin,ita kuma