Showing 3001 words to 6000 words out of 103469 words

Chapter 2 - GALADIMA FAMILY Complete Hausa novel

07 Sep 2024

6876

Alhaji mansir.
Shiga dakin sukayi bakunansu dauke da sallama, bodejo ce ta amsa tana zaune akan kujera,tsohuwa me shakaru sai dai dayake tanada kyan jiki ga kuma arziqi yasa tsufan yamata kyau,itakuwa guggo Laure sallah take Amma tsaban farin ciki ko lazimi bata idar ba tajuyo ta sallame sallar tace"Yaya muhammadu yau Kaine a gidannan?tayi maganar tana dariya, a'ah a'ah a'ah gaskiya naji dadi gaka gasu taleeb da Alhaji sadeeq maraban ku sannu da zuwa.
Gaisheta su Daddy sukayi cike da dattaku da muntuntawa suka mata ya jiki,sannan aka shiga gaida bodejo wacce murna da dadi yakasheta a zaune ganin zaratan yaran nata.
"Yaya muhammadu nace magana akan akilan kazo ayi koh?dama nace najika shiru ai wallahi da nasan zakazo da banbari yau taje bikin nan ba!Guggo Laure tayi maganar.
Galadima yace"wacece kuma haka Laure?ninazo duba jikinki ne,tun sassafe yaronnan sani takirani kan bakijin dadi shiyasa ma bodejo tamatsa zatazo duk da itama ba dadin jikin nata takeyi ba.
Guggo Laure tadan tamke fuska tace"a'ah Yaya kamanta ne yarinyar wajen mansir dana maka magana kan inaso a hada aurenta da Sauban ko don zumuncinmu yaqara karfi!
Kallon kallo akafara tsakanin Daddy da Abbie da Abba da baba hasheem cike da mamaki,bodejo kuwa hangame baki tayi tana duban guggo Laure.

_TOFA🤔 WATA SABUWA INJI DAN CACA,ANYA TSOHUWAN NAN BA RIGIMAMMIYAR TSOHUWA BACE?DA ALAMA GALADIMA DA IYALENSA BASUYI AMANNA DA WANNAN MAGANAR BA._

Xahratty Ce🥰
Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️
[3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳

Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now

*_GALADIMA FAMILY_*

Page 03

_please idan kunga kurakurai na typing ba'ayi editing bane so kuyahakuri._🙏🏽

Gyaran murya Galadima yayi tare da duban guggo Laure yace"Laure kenan keda baki da lafiya wani magana ne za'ayi yanzu data wuce ta samun lafiyarki?nikinga su taleeb ko tuntubar su ma banyi da zancen ba a inda mukayi zancen anan nabarshi.
Da mamaki sosai a fuskan guggo Laure take duban Galadima.
"Au Yaya kana nufin zancen nawa ma bashi da darajar da za'ayi ta?nifa Yaya so nake mu karfafa zumuncinmu tunda bamu samu hadawa ta hanyar 'yaya ba sai muhada ta hanyar jikoki,idan kacire rabi datake aure da Aliyu(Abba) waye nahada ?wannan kuwa jininmu da tsokar mune zamu hada.
Galadima cike dattaku irin na tsofaffin mutumci yace"Laure kibari kisake samun sauqi sai ayi maganar sannan muji ta bakin yaran idan sun amince da juna.
Salati guggo Laure tasanya tana tafa hannu tace"Yaya muhammadu!kada dai ace yaran zamanin nan sunaso su maidaka kaima dan zamani?bodejo da takasa haquri tuntuni tace"aiko Laure yanzu zamani yazo ba'a ma yara auren dole,to shi saudan dinne yace muku baida wacce yakeso?
Cike da takaici guggo Laure tace" A'ah Yaya bodejo ko Sauban nason Akeela ko baya sonta dole ya aure ta tunda 'yar uwanshi ne,murmushi bodejo tayi tace"A'ah Laure kice Allah kin tuba don babu wanda ya isa yama Saudan auren dole?wayayyan yaro yaron da yayi gogayya da turawa ne za'a ce za'a masa wani auren dole?bazaiyuwu ba ahto.
Tayi maganar tana Ciro gutsiran goronta ta bangala.

Fashewa da kuka guggo Laure tayi,cikin muryan kuka tafara magana.
"Wallahi Yaya bodejo tuntuni na lura dama kinamun wani gani-gani sam bakison a hada zuri'ah da talakawa,yo menene Sauban zai nunama Akeela?kyau ko mene?wallahi babu Kuma Akeela wayayyar yarinya ce itama don samari da dama ruhubin ta sukeyi.
Wani shewa bodejo tasaka tadubi guggo Laure Ido cikin Ido tace"Laure tunda hakane ta aure mana masu rububin nata daidai ita.

Daddy ne yayi gyaran murya ganin guggo Laure ta harzuqa tana Shirin maida martani yace"guggo don Allah kiyahakuri,bodejo kema kiyi shiru insha Allah za'a zauna asamu lokaci ayi maganar.
Guggo Laure tace"kada Allah yasama ayi taleeb dolene Sauban ya aure Akeela muddin munfito ciki guda da Yaya muhammadu!tana qare fadan haka takauda fuska gefe tana huhhura hanci,bodejo kuwa goranta take ta bangala tare da karkada kafafuwa.
Abbie ne yayi ajiyar zuciya yace"insha Allah za'a ma bullowa lamuran komai zai daidaita.
Cike da masifa guggo Laure tataso mishi kamar zata dakeshi tace"toh karere kayahakuri badakai ake magana ba tukuna, Kuma bamaga ake akan danka taufeeq ba.
Da mamaki duk suka dago suna dubanta,bodejo ce tabude baki da niyyar magana Amma sai Galadima yakatseta ta hanyar fara magana"Laure kenan har yanzu rashin iya maganarki yananan,kinada shekaru sittin da wani abu kina shirin cika saba'in Amma ace baki iya kalamai masu dadi ba?ai abubakar yafi karfin karere tunda jinina ne nine nan nahaifeshi kuma Sauban danshi ne tunda dan Dan uwanshi ne kingako yafi karfin karere a ciki.
Yayi maganar yana me miqewa tare da gyaran sandar sa,duk miqewa sukayi harda bodejo ta gyara mayafinta tace"ai kafata kafarfu don nima zan wuce Laure dai taji sauqi,tayi maganar tana aikama da guggo Laure harara,inda itama akaikaice ta rama sam bazakace su din tsofaffi ne ba.
Duqawa su Daddy sukayi har qasa tare da mata sallama Kuma kowannensu sai da ya ajemata kudi, murmushi tafara tare da samusu albarka tana memikewa.
Harara bodejo ta aika mata dashi a fili tace"daso samune kadama a amsa na karere,duk cikansu sun fahimci abinda bodejo ke nufi amma kowanne ya basar.
Guggo Laure kuwa tace"ai dadin abin ma na 'yayan Dan uwa nane.

Ko wanne a cikinsu dariya suka sanya banda bodejo wacce dama duk ta rigasu fita,sai da akazo tafiya ne sukaga cewa motar bazai ishesu ba duk da cewa ba wani girma ne dasu ba Amma ko babu komai zasu so mutumta iyayen su susakasu a wake guda,motan Alhaji sani ne tashigo farfajiyan gidan da sauri ya fito daga cikin motan cike da muntuntawa,domin Daddy da Abbie da Abba duk sun girme mishi.
Kai tsaye wajensu yafito fuskansa dauke da tsantsar fari'ah,cike da ladabi yaduqa yana gaishe da bodejo da Galadima,sukuwa sauran mazan hannu yamiqa musu tare da musabaha yana dan tsokanar su abinka da abokan wasa.

Duban Galadima da bodejo yayi yace"Kawo ku shigo na maidaku gida a cikin tawa motar.Haka kuwa akayi don Kai tsaye suka shiga motocin biyu suka nufi old maidugri don ba wani nisane dasu tsakaninsu da gidan direbi ba.

A garin kaduna kuwa zuhra ce tsaye a bakin kofan shiga farlon nasu sai dai ta kakire a tsaye ita bata shiga ba kuma ita bata juyawa ba inda ka kalli fuskanta kuwa zaka sha mamakin irin mugun kallon da take watsama wanda ke tsaye a bakin kofar.
"Please ya Aseef ka kama mutumcinka don ina ganin mutumcinka ba kuma zan iya maka rashin kunya ba Amma inaso kasani nisam ba irin watsattsun matan da kake tunani bane.Tayi maganar cike da fusata.
Matsowa Aseef yayi inda take tare da fara lasan labba yace"zuhra kenan 'yar kakkyawan kanwata kina tunanin bansan irin sheqe ayar da kikeyi bane?duk gidannan anhanaki saka English wears Amma kinki ji,idan zakisa kisa na mutumci mana irin wanda su Laila ke sawa Amma kinasa abu jiki a dame kiyi tunanin ire-ire na bazamu bibiyeka?
Wani dogon tsaki taja saboda yanda ranta yayi qololuwan back,wanda kuma yayi dai² da isowar Ummie wajen zata wuce.
Da sauri Ummie ta juyo tana duban zuhra cike da mamaki tace"zuhra!Ashe dama rashin kunyar taki har takai haka?kidubi idon Aseef kiyimasa irin wannan tsakin?saboda yace yana sonki?so hauka ne da har haka zai baki damar yimasa rashin kunya?to bari kiji zaki sha wuya a cikin gidannan muddin bazaki dena rashin kunya ba.
Kai kuma kada son da kake mata ya rufe maka Ido ka kasa hukunta ta ka zaneta to nonsense ni nasa,mara kunyan banza kawai.Taqarisa maganar tare da gyara zaman medical glass dinta tana wucewa apartment dinta kaitsaye.

Wani kuka ne ya tahoma zuhra saboda tsananin takaici tarasa menene tayiwa Ummie take nuna mata irin wannan tsaanar sam bata jawota a jiki irin na uwa da da,anya kuwa Ummie ce tahaifeta?a ranta tayiwa kanta wannan tambayar.
Shiko Aseef cike da murna yayi wani irin murmushin gefen lebe yajuya yanufi BQ nasu kaitsaye.
A haka ya taufeep yashigo ya iske zuhra da sauri yayi parking din motar sa yafito tare da karisowa inda take,miqar da ita yayi yace"me akamiki zuhra ke da wanene?bude baki tayi da niyyar masa bayani Amma ina?tuni kuka yaci karfinta.
Lallashinta yashiga yi har yasamo tayi shiru banda ajiyar zuciya babu abinda takeyi.
Kaitsaye apertment din Ummie yanufa cikin disasshiyar murya zuhra tace"zanje bangaren mommy ne.
Ya taufeeq yace"Ok muje,shiga farlon sukayi sallama dauke a bakin taufeeq,sun cidda mommy dasu Laila,gefe guda kuma ateek ne ke wasa shida maimoon,da gudu yaran suka taso suna hugging din zuhra da taufeeq,daga ateek ya taufeeq yayi sama yaron na qyalyqalewa da dariya.
Jikin mommy zuhra tafada tare da kara fashewa da kuka,a hargitse mommy tafara tambaya"A'ah taufeeq meyasameta daga dawowan ta jamb class dinnan?
Murmushi ya taufeeq yayi yace"shagwaba gurl! Mommy kenan nafa rarrashe ta tun a wake kafin munshigo dama nasan shagwaban nata akanki zai kare.
Hararan wasa mommy ta wurga masa tace"Allah taufeeq ka kiyayeni me aka mata kuma? Yace"ai kinsan halin 'yar mulkin taki ko nima rarrashin ta nayi batare da nasan ko dawaye neba don na tambaye ta bata fadamun ba.
Dariyar qasa² Laila tayi tace"ko dai ita da Ummie ne?
Zuhra kuwa kaman antsikare ta tadago tafara zayyane ma mommy abinda yafaru a waje tanayi tana kuka tace"Kuma wallahi ya Aseef dinnan dan iska ne gwara na konawa na gidan Galadima saboda nagaji.
Gabadaya dariya suka saka,nihal tace"chabdi saboda wani nabar gidan mu gaskiya I can't kema fah kamar harda rashin fahimta da yashiga tsakaninku kedashi.
Mommy kuwa tace"tabbas nihal ninarasa gabadaya irin wannan abu haka tsakaninsu gaskiya taufeeq kayima Aseef magana matsayinka na wansa nisam banga amfanin hakan ba.
Ya taufeeq tace"sudai suka sani ai idan ma bazasu dena ba sai aje wajen Ummie don itace zata bulloma lamarin.
Zuhra ta zunburo mouth gaba tace"ni bazanje wajen Ummie ba,Ummien ma da goyon bayansa take ni kullum cikin lefi nayi mata,wallahi Abbie zai dawo shizan fadawa don ma wayana babu credit ne kuma bani da kudi a ccount dina bare na siya dana kirasa na fada masa.
Ya kabani wayarka nakira shi kaji?
Harara ya taufeeq ya zabga mata yace"ni?lallai yarinyar nan bada wayata ba,sai akace miki nima mara hankalin ne irinki koh?ga dai mommynki nan ki amsa tata...da sauri mommy tace"wah don Allah taufeeq ka rufamin asiri sai kuma akace bamu da tunani gabadaya?
Dariya su Laila suka sanya,zuhra kuwa a fusace tamike tafita daga farlon.
Gabadaya dariya suka bita dashi.

Koda tashiga farlon su bata samu Ummie ba don haka kaitsaye bedroom dinta tashiga tare da fadawa akan kayataccen gadon ta tafashe da kuka,itasam takan rasa abinda ke mata dadi sam ita da gidan su da mahaifiyar ta araye amma kamar wacce take mara uwa(niko nace hmmm zuhra kenan nibanga abinda akai miki nakaman rashin uwa ba.)


Xahratty Ce 🥰
Lallai Alqalami🖊️ yafi takobi🗡️
[3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳

Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now

*_GALADIMA FAMILY_*

Page 04

_Bismillahir-rahmanir-raheem._

_____Haka zuhra takarisa tunane tunaneta tamiqe tashiga toilet ta dauro alwalan sallan magrib kaman yanda taji anata kiran sallar harma wasu masallatan sun tayar.
Babu bata lokaci itama tazo tafara gabatar da sallan ta.

Bayan sallar isha'i Sauban yasamu su Daddy a farfajiyar gidan don a ka'ida nan suke dawowa su cigaba da hira abinsu cike da qaunar juna,sallama yayi cike da mutumci irin na hadadden yaron tare da kamewa yaduqa yafara gaishesu.
Suma cike da jin dadi suke amsawa saboda natsuwar Sauban da Kuma kamewarsa,wanda wannan dalilin ne yasa yakeda jama'a da dama a cikin family din nasu.
Abba ya dubeshi yace"Sauban ya akayi ne?dan murmushi yayi tare da sake sunkuyar dakai yace"Abba dama sako ne dazu aka turomin daga can maleyshia kan suna son muje za'ayi mana interview mu goma Sha shida 'yan Nigeria,nanda 4days shine nace bari nazo nasanar daku.
Ko wannensu cike da farin ciki Daddy yace"Masha Allah! Abbiel kuwa murna sosai kwance akan fuskar sa yace"Sadauki Masha Allah, congrats my son! na tayaka murna sosai,yayi maganar yana masa musabaha.
Inda sabo Sauban yasaba da halin Abbie don tun yana yaro yake tare dashi,murna sosai sukayi.
Daddy yace"ka fadama su Ammin naka?

"A'ah Abba yanzu nakeso nashiga wajenta na fada mata sannan na fadama mom itama.
Sake mishi fatan alkhairi sukayi,miqewa yayi cike da qasaita duk da cewa hakan halittarsa ce domin Sauban tsayayyen namiji ne a cike wanda dai² da maza ma 'yan uwansa yana musu kwarjini balle kuma mata.

"Yanzu Sauban kasar maleyshia zakaje yin aikin?Koda Allah yasa hakan shine yafi zama alkhairi nidai abinda nakeso dakai kada ka kawomin wata 'yar qasan kacemin aurenta zakayi don magana ta gaskiya ba lamunce maka zanyi ba,don ga 'yan uwanka nan cike da dangi.
Dan guntun murmushi yayi yace"sweetheart ko aikin ma ba'a samu ba kinfara kawo korafi?

Ammi ta sake tsuke fuska tace"ai gaskiya ce na fada saboda nasanku ku maza shiyasa tun yanzu ma nake gaggawan taka maka birki kada naji ko nagani Koda kuwa andace ne.
"Shikenan sweetheart hakama sam bazai faru ba gobe nakeso naje gidan Aunty falmata.
Ammi tace"Allah yakaimu!da ameen Sauban ya amsa nan suka cigaba da hirarsu.

Washegari da safe wajejen goma saura sai ga Guggo Laure itada Akeela,tsayawa nayi naqare mata kallo tasss,kyakkyawa ce sai dai ko kusa bata kamo kafar yaran gidan ba duk da cewa a ciki akwai qalilan da tafi kyau,sanye take da lutfaya baki mai ratsin jan flowers sai kafanta sanye da halfcover ja,hannunta riqe da handbag shima ja fara ce tass wanda a farin ma akedan karawa da man bleaching daga gani zatayi sa'a dasu mashahuda.
Baba mansir mahaifin Akeela shine Guggo Laure tasa ya kawo su don baisamu shigowa gidan bane saboda ana jiransa ujila.
Kaitsaye bangaren su bodejo suka nufa, Akeela kuwa tamkar bazata take kasa ba,Koda suka shiga sun cidda bodejo da Galadima,bodejo tana hada masa brabusko da miyar kuka Wanda yaji nama zallan tsoka daga bangaren Daddy aka kawo.
"Assalamu alaikum!ga bakin sassafe fa.
Guggo Laure tana fada fuskanta dauke da tsananin fari'ah saboda ganin motocin yaran gidan da alamu ma basu fitaba hakan ne yasata sake fari'arta.
Galadima yace"Laure!kece a gidan?lallai jiki yayi sauqi sosai tunda gashi kin iya fitowa yayi maganar fuskansa kadaran kadahan.
A inda Akeela take tsaye ta gaishesu ko rissinawa babu qiqam ta gaidasu.
Cike da mamaki su bodejo ke duban ta, Galadima yace"ke haka akace miki mata na gaida mijinta?duqawa akeyi har qasa bawai atsaya a tsaye kerere ba kinji?
Akeela ta wayance ta hanyar cewa"toh ai saboda bana auren tsoho irinka yasa na gaisheka a haka saboda kada tsohuwar matanka ta huramin hanci.
Bodejo kuwa Sarai ta ganeta sai cewa tayi"to ai tunda kikama wannan angon haka babu irin angon da bazakiyi wa ba.
Guggo Laure tace"musake gaisawa kundawo lafiya?ya gajiya Yaya bodejo?
Bodejo tace"ai gajiya tabi jiki Laure Kuma marasa lafiya kun fito balle kumamu?
Guggo Laure tace"wallahi fah kedai Bari jiya najuya yafi sau nawa? narasa gabadaya abinda kemun dadi a gidan duniya naqosa gari ya waye nazo saboda nace da zafi zafi ake bugun karfe shiyasa,tadubi Galadima tace"kada dai agaji dani akan kokari na nason aikata alkhairi.
"Maganace dai akan yaran nan Akeela da Sauban shiyasa ma nace Akeelar tashirya tazo muje ayi komai a gabanta.
"Shima kuma Sauban din ayi komai a gabansa.
Cike da mamaki duk suke duban ta.
Galadima kuwa abin duniya ne ma ya isheshi yayi dan murmushi irin nasu na manya yace"Laure kenan kekam akwaiki da wutan ciki, gashi yaran ba dukansu ne suke nan ba don shi sadeeq yau ya koma kaduna,shikuma Hasheem yaje ta'aziyyar amininshi da yarasu.
Guggo Laure tace"toh nidai Yaya hakanan za'ayi hakuri ayi maganar nan yau a wuce wajen.
"Yarinyar nan tana tsananin son Sauban,duk cikin jikoki na babu mafi soyuwa agareni kamar Akeela.
Galadima yace"toh shikenan bari nakira taleeb din,hannunsa yakai gefen lumtsememen leaderseat dinda yake zauna yadakko wayarsa kirar sumsung yafara nemo number,baiwani dau lokaci ba yakira har takatse ba'a daga ba,ko kafin yasake danna kiran,Kira yashigo wayan nasa.
Dauka yayi tare da sallama,daga can bangaren Daddy yagaishe shi,amsawa yayi kaitsaye yace"inason ganinku kai da Aliyu idan anyi sallar azahar,daga can bangaren aka amsa da toh insha Allah,sannan Galadima yakatse wayan.
Guggo Laure kuwa murna takeyi kamar yakasheta,dakin da take sauka wanda aka mata nan tanufa harzata shiga sai Kuma tajuyo tace"ke Akeela zo muje mugaisa da matan gidan tukuna koh?
Akeela kuwa farin ciki takeyi kamar anmata kyautan hajji,aranta kuwa fadi take itace zata mallaki Sauban jinin GALADIMA FAMILY?tabbas tayi sa'a,don Sauban namiji ne wanda da dama mata ke bibiyan sa,don ko a yanar gizo maganar sa mata keyi namiji ne mai tsadan gaske.
Kai tsaye apartment and Ammi Guggo Laure tashiga,sallama tayi itama Akeela tayi cike da kissa.
Su mashahuda ne a farlon,hada idon da muneefa zatayi aiko tamike da gudu tanufi Akeela tace"Kai lallai ma Akeela yau kece a gidannan haka? Akeela ta watsa idanuwa tace"aiko gani ai muneefa bakida kirki ko Guggo bakizuwa gaishewa.
Mashahuda ta dubi Guggo cike da mutumtawa ta gaisheta,inda kallo daya tama Akeela ta watsar don sam ita Akeela bata burgers barin yanda take ganin tanasa pic dinta a Instagram na shirme.

Muneefa tace"Tabb yaushe zaki ganmu so kike ya Sauban ya babballamu?dariya sukayi.
Kujera Guggo Laure tazauna, Akeela da muneefa kuwa daki suka shige inda mashahuda tashiga kitchen don kiran Ammi,Ammi bata zama duk da masu aiki suke aiki Amma girkin mijinta ita takeyi tunda yanada suger,masu aiki kuma suyi na gida gabadaya ko da ita bata dauki wata mai aiki tayiwa mijinta girki ba.
Mashahuda bajima ba tafito kitchen hannunta dauke da tray inda ruwa kekai da lemo.
Ammi ce tafito fuskanta dauke da murmushi tace"Guggo ce a gidan? Guggo ta amsa fuskar ta dai kadaran kadahan tace"yauwa sannu Aisha nice.
Ammi tace"inayini Guggo,kunzo lafiya?
Guggo Laure tace"lafiya lou,munsameku lafiya?
Ammi tace"lafiya ALHAMDULILLAH ya karfin jiki?jiya zamuzo da Rabi sai mazan sukaci mubari suje mu mazo yau Ashe jikin ma yayi sauqi?
Guggo tace"jiki Alhamdulillah sai dai tasowar na dole nayi saboda mahimmiyar maganar dake tafe dani.
Ammi tace"Allah sarki sannu da zuwa.
"Yawwa Aisha,inasu Yaya na muhammadu?
Murmushi Ammi tayi tace"Sauban yana dakinsa anata shirye²n tafiya Malaysia.

Guggo cike dason jin Karin bayani tace"mekuma zaije yi can?
Mumushi ammi tayi tace"zaije interview ne idan da rabon yasamu aiki a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login