Showing 57001 words to 60000 words out of 103469 words

Chapter 20 - GALADIMA FAMILY Complete Hausa novel

07 Sep 2024

6904

tanuna ta"zuhra!maganar mahaifin ki kike nema ki butulce?yabar wasiyya kice ba haka ba?mekika sani ke?harkin san wani so ne ke?wallahi nasake jin kalmar nan abakinki saina miki bugun tsiya,mtsewww useless"tana kare fadan hakan tafice daga parlour,bakajin komai sai shasshekan kukan ta,shikan shi Sauban din sai yaji wani tausayin ta ya kamashi gabadaya.

Cikin fusata Mom tamike tana duban kowa tace"tsakani da Allah ana rashin adalci a cikin family dinnan,ni nazata Aseef ne za'a bawa zuhra? maganar gaskiya nida 'yayana ba'a Mana adalci,domin kuwa ai wannan tsantsar rashin adalci ne,sai kace duk family din Sauban ne kadai da'? Anbashi Akeela ga kuma zuhra gaskiya....cikin bacin rai baban Hasheem yace"Rabi!! Kishiga hankalinki dani,waye sa'anki anan?itama Mom cikin bacin rai tace"ni iya gaskiya ta nake fada wallahi"tana gama fadan hakan tafice daga parlour tana 'yan kananun surutai.
Daddy yace"koma mene duk abinda zakuyi kuyi babu me kwancen auren nan sai Allah,kutashi ku wuce"yayi maganar yana duban Sauban,cikin sauri zuhra tamike tariga fita,duk da kallon tausayawa suka bita,tafe take kawai tana hada hanya,jitayi tayi tuntu6e da wani interlock na gefen hanyar,gaba tayi zata tuntsira, Sauban dage bayanta cikin sauri yakarisa ya tarota tafada jikinsa, dai-dai kunnenta yace"Kidai kula Saboda wata can banziyar soyayyan ki kina neman kashe kanki a banza,to nina dakika ganni ba sonki nake ba domin kuwa amaryan matata tafimin ke"yana kare fadan hakan yasake ta tare da wucewa yabarta nan tsaye,wani kuka ne taji ya kufce mata tare da sake jin wani haushinsa da tsanar Akeela a ranta.
Da kyar ta lallaba takai kanta sashen Ummie.


Zuhra kuwa banda kuka babu abinda takeyi tarasa gabadaya meke mata dadi a rayuwar ta.

Xahratty CE🥰
Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️
[6/24, 17:32] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳

Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now

*_GALADIMA FAMILY_*

Page:- 57/58

_Bismillahir-rahmanir-raheem._

______A gajiye ti6is ya isa yau ya isa sashen sa,koda yaje ya taradda kulolin abincin akan dinning dama da wata irin yunwa yashigo gidan kaitsaye dinning din yanufa,abinci yasaka jallop din spaghetti yaji busasshen kifi sai tashin kanshi da yakeyi,hadiye miyau yau duk da yasan Ammin shi ce tayi girkin,cikin nishadi yakecin abincin hakanan yakejin farin ciki da walwala,yana gaf da kammala cin abincin yaji sallamar ta,a makoshi ya amsa batare da ya dago ba,kariso wa tayi kaitsaye hannunta ta sakalo wuyansa tare da bashi Peck a kanshi cikin muryan jan hankali tace"welcome honey!hannu gawai ya daga mata Saboda kora lemon Fairless da yakeyi,wani killer smile tasaki,bada wani yawa yaci abincin ba Saboda shi dama ba ma'abocin cin abinci bane,ganin irin shigan da tayi bakaramin tashi hankalin sa yayi ba,ga kamshin body spray din da takeyi lokaci daya yanemi susu cewa, ganin hakan yasa Akeela tashiga yawo da hannunta zuwa ko ina na jikinsa tare da tsananin jin son kasancewa dashi,one time Sauban ya susuce,da kyar ya iya yakice kansa yadube ta"Tashi muje muyi sallah kikoma sashin ki kisanyo gown,cikin muryan shagwaba tace"Nifa honey nayi sallah kabari kawai"takarisa maganar tana dan langabar da kanta,tsinin bakinta na turowa,sai yaga tayi wani muni,kauda kansa side yayi muryan sa babu alamun wasa yace"wannan daban wancan daban,don haka ina sauraren ki,yana kare fadar haka ya mike ya haye stairs.
Cikin tsananin farin ciki Akeela ta nufi apartment dinta,jitake dama kamar ta dannesa,wanka ta kumayi ta shirya sannan ta dauko wani dan turare a kwalba ta kalla tayi wani shu'umun murmushi,a fili tace"Guggo yau ga aikin turaren boka nan za'ayi,tayi maganar tana tuno abinda Guggo Laure tace mata _Kinga wannan turaren yana shafawa zaki mallakesa zeji babu abinda yakeso kamar sama da kasancewa tare dake,don haka kiyi shi kamar yannda boka yace!_ wani murmushi Akeela tayi sannan tasamu cottonwood ta dangwalo turaren sannan ta shafa a kasanta,tayi duk yanda Guggo tace mata,har zata fita sai taji wani irin firsari ya matseta,toilet din ta shiga tayi abinda zatayi tafito katsaye tanufi sashen nasa tare da long hijjab,koda ta isa tasame shi shirye tsaf?sanye yake da coffe din jallabiya yayi kyau ainun,ganinta yasa ya tada sallah,da sauri tabishi itama,koda suka idar kama kanta yayi yamusu addu'o'i da ganin yashiga yi mata tambayoyi akan ibadun ta da sauransu,kwarai ya shiga mamaki ganin baisamu amsar ko daya ba inbanda kame² da take masa,ganin da tayi yana mata wani irin kallo yasa ta latso wahayen karya,tare karyar da murya tace"Bazan iya baka amsa ba honey cuz na fahimci wannan ranar shine zai kasance first night dinmu,kuma ni tsoro nakeji"takarisa maganar cikin muryan kukan munafurci,sosai ya yarda da batun ta Saboda yanda lokaci daya ta koma.
Jawota yayi yashiga lallashinta tare da shafa mata baya hakan yasa tayi luf a jikinsa,tun ana lallashi abin har ya zarce aka cire hijjab din.Ganin haka yasa Xahratty tattare alqalamin ta da littafinta waje daya tamike tafice tare da rufo musu bedroom din,sai da safe Sauban da Akeela.

********

Zuhra kuwa yanda taga Rana haka taga dare tana ganin miscalls din Shuraim but takasa picking Saboda kukan da takeyi,shikuwa ganin hakan da yayi sosai hankalin sa ya tashi don bai natsu da abinda yafaru dazu ba,yanaji a jikinsa tabbas da akwai matsala, sosai yanemi bacci yarasa,hakan yasa yajawo wayarsa yafara typing,text ya tura mata kan gobe yananan zuwa, Allah yasa lafiya,tana kwance tana ayyana irin mijin da aka aura mata,tabbas tasan ya Sauban ya hada duk abinda dole mace ta soshi but ita a nata bangaren su sonsa tarasa dalili,cikin kuka tace"nasan shima baya sona cuz yanada wacce yakeso shiyasa always he's happy"takarisa maganar cikin kuka,jitayi wayan ta tayi kara alamun notification a hankali takai hannu tajawo wayar ta bude da sauri Saboda sunan wanda tagani,ganin message dinsa da abinda yace yasa cikin muryan kuka tafara yimasa voice note"please kada kazo ya Shuraim ina cikin matsala, kawai addu'an ka ita nake bukata"tayi maganar tana me kecewa da kuka tare da kashe wayan gabadaya tana dunkule jikinta waje daya.

A sanda yaji voice note dinta bakaramin gigicewa yayi ba,cikin saura yayi dialling number ta,sai dai jitayi ance switch off,nan ya cigaba da trying but kalma daya ake fada masa wato akashe,kama kansa yayi shima hawaye na silalo masa,cikin raunin murya yace"my zuhra wat's wrong with you?wat happing to you?yayi maganar yana sakin kuka ya cigaba da cewa"duk abinda yafara I know ninaja miki da nazo ,sosai yanemi natsuwa ya rasa tare da kosawa safiya tayi hankalinsa a tashe yake.

_______

Adda Zainab hankalinta yayi kololuwar tashi jinda tayi wai kawar ta hajiya Aliya Alhaji zai aura,acan parlour sa tasame sa a gigice ba cikin natsuwar Saba,tasame sa yana waya da babban abokin sa,ganin yanayin ta yasa ya masa sallama da sauri yakashe wayar,idanuwan ta taf da hawaye ta karisu tana jefa idanuwan ta cikin nasa,cikin daga murya tafara magana"Alhaji da gaske ne abinda naji?da gaske ne hajiya Aliya aminiyata zaka aura?don Allah kayi magana,nace da gaske ne?tasake maganar cikin daga murya,hannu Alhaji iliyas ya nade a kirjinsa tare da kura mata idanuwa cikin natsuwa yafara magana"Kinga hajiya Zainab ki nutsu ki zauna muyi magana nidake na fahimta,ba tahaka ba"yayi maganar yana kamo ta,fusge jikinta tayi muryan ta na rawa tace"kasanar dani zargin da nakeyi gaskiya ne ko kuwa? Alhaji iliyasu yace"please mana hajiya have a sit! Cikin masifa Adda Zainab tace"ba zan zauna ba,saika answering question dina,if not.....tayi magana tana nuna masa yatsar ta tare da tsaida idanuwan sa akanta.
"Hmmm! Hajiya magana ta gaskiya tabbas hakane hajiya Aliya zan aura! Menene don na aure ta?so nake zumuncin ku yakara karfi sannan ai ba haramun bane,ganin da nayi yanda kuke kaunar junan ku yasa na yanke wannan hukuncin,sannan dana auro miki bare ai gwara na gida"tunda yafara magana ta nemin jinta da ganin ta tarasa na wucij gadi, jitayi wani kululin abu yazo mata makoshi ya tokare,batasan sanda ta yanka ihu ba tazube anan parlour,a gigice Alhaji iliyasu yanufe ta.

Hajiya Aliya kuwa a bangaren ta suna can sun sako Alhaji iliyasu gaba ita da boka hatsabibi kan duk abinda zaifaru bazai janye kudurinsa kan auren ba,don tana lure yau saura kwana uku daurin auren, katsaye tanufi gombe wajen yayar ta,kan bazata dawo ba sai lokacin tarewar ta tayi.
Bangaren Adda Zainab kuwa sosai tashiga tashin hankali tayi kuka sosai ta tsinewa hajiya Aliya babu adadi,duk yaranta ukun na zaune suna sauraron ta babban danta namiji mesuna Ammar yace"don Allah mom kidena saka ma ranki damuwa, Daddy fa da alama auren nan yinsa babu fashi ko dazu yafada yace sai dai kisama ranki salama,karamar sa'an zuhra tace"ai wallahi momy Aliya taci amana kuma bamu yafe mata ba tarasa wanda zata aura sai Daddyn mu shine zata aura,ta biyun kuwa banda sauke ajiyan zuciya babu abinda takeyi tana rungume da bbyn ta,cikin muryan kuka Adda Zainab tace"nasani wallahi nasan Aliya ba hakanan tabar Alhaji ba,nasan halinta nasan abinda zata aikata,shedaniya ce.
"Mom kenan sai yau ne kikasan da Aunty Aliya shedaniya ce?tun yaushe nake fada miki kinki yarda,aikinsan mugayen halayen ta tun ada,batare kuke aikata komai ba?sai yanzu data miki shine zaki dawo kifada haka akanta?takarisa maganar tana duban Adda Zainab,itadai shiru tayi ta cigaba dajan hawayen ta, Ammar ne yace"menene kike fada haka islaha?da wanne kiieso Mom taji?Yaya duk abinda nake fada nasani,itama Mom tasani kuma ita tagane karatun da nake nufi,wallahi akan Aunty Aliya har zaneni Mom ta ta6ayi daga nace ni zuciyata be kwanta da ita ba amma tarufe ido tamun duka tana cewa bazan raba zumuncin shekara da shekaru ba"ta ta6e baki sannan ta cigaba"kaga duk wani yake da faran² dinda nake ma Aunty Aliya?inayi ne don kawai Mom kartayi fushi dani don akanta zata iya komai.
Kuka Adda Zainab tafashe dashi tace"please islaha kiyi shiru haka,banson jin ko sunanta wallahi sai nadau mummunan mataki akan cin amanar da tayi min"islaha tace"hmmm Mom kenan kidai bi komai a hankali,cikin 6acin rai Adda Zainab tace"naki nabi komai a hankalin don abu kaza naki,wai dame kikeso naji ne islaha? Ammar yace"gaskiyan ta ne Mom babu wanda beson yanda kuke tare ba,wallahi yanda kike son ta ko Aunty bilkisou bakiso haka,duk fa munsan komai Mom,kin fifita ta akan duk wani dan uwanki,kawai Allah ya kyauta aikin gama ya gama don gobe ne daurin auren"yana gama fadar haka yabar bedroom din.
Kuka sosai Adda Zainab keyi,su dai su islaha suna zaune jugum² tare da tausayin uwar tasu.

*** *GALADIMA FAMILY* ***

Sauban dai yadanji sanyi a ransa jinda yama Akeela a matsayin budurwa sai dai ko kadan bayajin burbushin son,don ko irin tattalin nan da ake na mutum beyi ba da,sosai Akeela tasake jin wani irin son guy din ya ninku mata,sannan sosai ta yarda da cewa lallai tayi sa'a, lafiyayyen namijie ne wanda ko wace lafiyayyar mace take burin samu,lallai yasan sirrin sarrafa mace,sosai takejin ta cikin nishadi,bata farka ba sai wajen 11:16 bata sameshi a bedroom din ba,shikuwa yana mamakin yanda Akeela tazage tana masa abubuwa wadanda sam babu kunya a cikin su.
Yana zaune tafito sanye da night gown,ganin sa yana daddana laptop yasa takariso a hankali tazauna kan rabin cinyar sa shafo gefen face dinsa tayi cikin muryan jan hankali tace"honey wallahi jiyan nan ka gajiyar nan dani don kawlai ni jaruma ce sam banda raki,da dai kamar bazaiyi magana ba sai zuwa can batare da yadubeta yace"sorry! Sosai Akeela taji dadi mikewa tayi da niyyar barin parlour,muryan shi tajiwo babu alamun wasa yace"A haka zaki fita saboda baki da hankali?juyowa tayi tapdubesa kamar bashi yayi maganar ba,cikin sanyin jiki tanufi bedroom dinsa,hijjab dinta ta dauka ta sanya sannan tafito tare da fita tabar apartment din,Suby ce takirata kan tanason zuwa,a take anan Akeela ta dakatar da ita kan cewa batanan yanzu zasu fita ita dashi,sallama sukayi dai-dai nan taja tsaki tace"yau nasamu babban nadau hutu ni kuma da komawa wannan harkan sai an kwana biyu.
Acan gidan Galadima kuwa banda zazzaga ruwan rashin kunya babu abinda Mom keyi harta kaiga Baba Hasheem ya mareta tare da sanar da ita taje gida zai nemeta,sosai Mom ta gigita da wannan furucin nasa,sashin Galadima ta nufa cikin tashin hankali da kukan ta da komai.
Duk hankalin mutanen gidan a ranar yatashi saboda yanda Baba hasheem ya rufe ido kan sai Mom ta tafi gida,sannan ya rantse da muddin bata tafi gida ba to saki ne zai biyo baya idan ta sake ko minti 20 ne,shi kanshi Daddy duk kokarin shi naganin ya shawo kan kanin nasa lamarin ya faskara,waya ya dauka yakira Abba tare da sanar dashi abinda ake ciki,inda yace yananan shigowa gobe da safe.
Da kuka da komai Mom take sanar ma da hajiya Biba abinda yafaru,dogon tsaki hajiya Biba taja cikin fusata tace"wato ke ala dole ga 'yar bala'i ko?to wai ma rabi ina ruwanki da sha'anin gidan da har kika tsoma baki?koko ke kadaice mata a gidan? Mom tace"wallahi hajiya kaddara,ninaso ace Aseef ne ya aure Zuhra ba Sauban ba, saboda...sai kuma tasake karisawa,hajiya Biba tace"saboda ubanta nada kudi?wallahi Saboda haka ne yasa kikeson hada auren,rabi nasanki fa nasan halinki,nice nan na haifeki ba wani ba nasanki da bala'in son kudi to bari kiji koni da kika biyo akan wannan mummunan dabi'ar adace don kuwa yanzu nadaina na shiryu,Kinga Rammat? tayi magana tana nuna Rammat taccigaba"ina mata addu'ah kan Allah ya hadata da miji na gari me dan dai rufin asiri ko yaya ne wanda zai rikemin amanar ta domin Kinga nacire buri dason iyawa.Don haka shawarar da zanbaki kicanza hali rabi tun wuri in bahaka ba kinaji kina gani keda gidan GALADIMA family sai gani sai hange sannan kifadawa gidan wahala,a wannan marran,babu wanda bazaiso jininshi ya shiga gidan nan ba,duk akan maganar Aseef kika nemi kashe ma kanki aure,alhalin kinsan sa kinsan halayen sa wallahi Aseef ba kowa zaiso yabashi mata ba,a haka kamar mutumin arziki,kije ki bincika abinda yake aikatawa,kuma wallahi nida kaina zan sanar ma Taleeb komai kiji ma kisani,tana kare fadar hakn tajuya tashige bedroom dinta, Mom kuwa cike da nadama da danasani tafara laluban number Baba Hashim,sai dai ko dagawa ba yayi.

Bayan sallar isha'i sai ga Ya Asher da Shuraim,kaitsaye sashen Daddy suka nufa don Daddy yasan da zuwar su a can suka cidda Sauban zaune,cikin girmamawa suka Isa parlour Daddy suna mika gaisuwa,duban Sauban ya Asher yayi yana me mika masa hannu yace"babban Yaya barka da dare,Ashe kana nanne?Sauban cikin kamewar sa yace"wallahi kuwa kwana biyu ya gida ya family? Asher yace"Alhamdulillah ya amarya?Sauban yace"amarya tana lafiya.
Nan Shuraim shima yagaisa da Sauban,amsa masa Sauban yayi kamar wani abu baita6a faruwa ba.
Kawo musu kayayyakin motsa baki akayi,duk da anyi-anyi suci amma sunki ci akan daga kan abincin ma suka fito, Daddy yace"Malam Asher abinda yasa na nemeka magana ce akan dan uwanka Malam Shuraim gashi!tare da mamana na wajen marigayi sadeeq,kasan alakar dake tsakanin su?Asher yace"Ea to Daddy kwanakin safeena ke fadamin,sannan take nuna min ai suna son junan su,sai nace to me ake jira basai magabata su shiga ba?sai take cemin ai sai ta gama degree dinta,sai nace to aje ko izinine a nema masa yasan anbashi saboda yanayin Shuraim ya nuna serious yake son ta,to nidai tundaga ranar bamu sake magana ba sai kuma dazu Shuraim yazo harda kukan shi.
Bayan yakare magana Daddy yace"Malam Shuraim ya mana babban lefi a cikin family dinnan,wanda tunda muke ba'a ta6a mana makamancin sa ba,nafara kula yarinya kafin a nemi izini, ba don komai ba sai saboda gudun matsala"hakuri Asher da Shuraim suka shiga bawa Daddy.
Daddy yace"No no no no aini everything will be gone cuz shine zamu bawa hakuri domin mamana akwai aure akanta.....ai wani irin zabura Shuraim yayi yamike tsaye,mouth dinsa yafara rawa,ko kafin yayi magana ruwan hawaye ya riga sirnano masa,kamar ba namiji ba.

Xahratty CE🥰
Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️
[6/30, 07:41] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳

Page:- 59/60

______Dukawa yayi da rarrafe yakariso wajen Daddy tare da kama kafansa cikin muryan kuka yace"please please Daddy help me I love her so much,I can't live without her don Allah kada ku rabani da Zuhra rasata babban asara ne a rayuwa ta da nakasu,tana da wasu qualities wanda ba kowa ya sani ba sai wanda yake zaune da ita,naroke ka kamin duk hukuncin da zaka yimin amma banda na rabani da ita"yakarisa maganar yana wani irin kuka mai tsanani,sosai yabawa duk wanda ke parlour tausayi banda Sauban don wani mugun jin haushin yaron yake jiyake kamar yatashi ya rufeshi da duka sai dai face dinsa yagaza nuna hakan,baka isa ka fahimci mode nasa ba.
Daddy yace"kayahakuri Malam Shuraim nace maka da auren wani akanta, Daddy kamin alfarma kahadani da wanda ya auretan na rokesa.Kamashi Daddy yayi ya zaunar dashi domin kuwa yayi bala'in basa tausayi matuka"Kunga irin shi ko,kunga dalilin da yasa muke fighting akan kafin afara neman yara a nemi izini, Zuhra tana aure da yayan ta Sauban"da sauri Shuraim ya maida duban sa ga Sauban wanda shima shi yake kallo,haka ya rarrafa wajen shi yana me kama hannayen sa cikin kuka yace"please Yaya don Allah kabarmin zuhra,domin don ni akayi t.....baikarisa ba sukaji Sauban yace"you re very stupid?re you mad?matar auren kake cewa don kai akayi ta?nima inason ta!yes I love her!bude baki yayi zai sake magana amma sai yakasa kawai sai ya girgiza kanshi yafita daga parlour.
Dafa kafadansa Daddy yayi yace"kayahakuri kaji ba'a aure akan aure,sai dai temako daya zan maka kaje kasamu natsuwa idan komai yawuce sai kazo ina son ganinka,kamashi Asher yayi yace"babu komai Daddy Allah yasa hakan shine mafi alkhairi,a'iya sanin da nayiwa su Daddy Shuraim da babu aure akanta Allah sai sun baka ita,gabadaya ko matsawa Shuraim yakasa a ransa kuwa fadi yake _Yanzu shikenan dama bashi ne yake da rabon mallakar zuhra ba?_ ganin da Daddy p yayi kamar ma yaron baya a hayyacinsa yasa ya kamasa ya mikar dashi da kanshi yarikeshi suka fito har parlour, Sauban na zaune a gefen Ammi,suma fitowa sukayi dai-dai lokacin ZUHRA sun shigo dasu Laila,idanuwan su ne suka shiga na juna,atake anan zuhra jikinta yadauki rawa,shikuwa Shuraim hawaye kawai yakeyi,cikin tsananin sauri hade da gudu zuhra ta juya tabar apartment

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login