Showing 15001 words to 18000 words out of 103469 words
wasu daga gidajensu wasu kuma suna tsare adaidaita sahu,da yawansu zuwa daukansu akeyi.
Samun gefen gate din tayi tatsaya.
Duk wanda yazo wucewa sai yadubeta fuskar nan a hade wayanta taciro da niyyar kiran Ammi sai taji magana daga gefenta,cikin natsuwa ta dago don ganin me maganar.
Wani saurayi tagani a tsaye yadubeta tare da nuna mata bakin titi yace"Wai kije inji brother naki,a hankali zuhra ta sauke wani gwauron ajiyar zuciya cikin nutsuwa tanufi motar.
Sukuwa gabadaya student dinnan hankalinsu yakoma kan motar da ya Sauban ke ciki,'yan mata kuwa da dama ganinsa yasa sun susuce.
Sallama tayi iya labba har tanufi gidan baya da niyyar shiga sai tatuno da maganar Aunty Mashahuda don haka sai tabude front seat tazauna,tare da gaidashi.
Da kamar bazai amsa ba sai kuma zuwa can ya amsa.
Sunyi tafiya babu wanda yayi koda tari sai zuwa can Sauban yadan dubeta, gyaran murya yayi tare da sake dan tsuke face yace"wannan Jamb din da kikayi tamkar aikin banza ne don basan karatun kike ba.
Cike da rashin fahimta Zuhra ke dubansa,ta wutsiyar ido yake dubanta,gane bata fahimci abinda yake nufi ba yasashi cewa.
"Zansamu Abbie nafada masa cewa keba karatu ne a gabanki ba aure kikeso tunda nakama ki sau biyu kenan.
Da sauri tadago tana dubanshi tare da tsantsar mamaki da razana da kalamanshi mouth dinta har rawa yake tace"a'ah wallahi Yaya burina nayi karatu nazaba journalist don Allah kada kafada mai niba aure nakeso ba,kuma ma wazan aura?cike da yarinta tare da tsantsar shagwaba take maganar.
Shi Aseef din dana ganku tare ba soyayya kukeyi ba?sannan yaron da yakawo ku gida keda Mashahuda ba soyayya kuke ba?cikin sauri tafara girgiza kai tace"wallahi duka babu Wanda nake soyayya dashi kuma nibansan wani abu soyayya ba niko friend namiji bantaba yiba Allah.
Ta sake magana cikin tsantsar yarinta,shiko Sauban dage kafada yayi irin ko a jikinshin nan ya cigaba da driving dinsa cikin kwanciyar hankali.
Itakuwa zuhra gabadaya neman natsuwa tayi tarasa burinta yace bazai fada ba.A haka dai suka karisa gida.
Da sauri ta balle murfin motar tafito kaitsaye apartment din Ammi tanufa,shikuwa Sauban koda ya ajeta juya kan motan yayi yasake fita.
Da sallama tashiga parlon babu kowa sai Aunty Mashahuda,ganin ta yasa tasaki murmushi tana cewa.
"Yawwa Zuhra naje nemanki ai dazu shine bodejo tace kinje rubuta Jamb kinsan menene?
Girgiza kai Zuhra tayi.
Mashahuda tasaki murmushi tace"guy din jiyane da muka hadu a supermarket yakira wai Shuraim koh?shine fa yace nahadashi dake nace baki kusa kinje zana Jamb.
Waro idanuwa Zuhra tayi tare da dafe kirji tace"please Aunty Mashahuda kirufamin asiri wallahi adena maganar sa kinsan idan Daddy ko Abbie sukaji zanshiga uku,sannan za'ace guda nawa nake.
Mashahuda takama baki tace"toh yanzu zuhra cemasa za'ayi baki sonsa? gaskiya nibazan iya fada masa haka ba sai dai ke kice masa.
Zuhra tace"ni bazan iya waya dashi ba Aunty wallahi inajin tsoro kawai abar maganar kirabu dashi Allah,takarisa maganar tana mike tare da fita daga parlon.
Murmushi kawai Mashahuda tayi sannan tamike tanufi stairs din Daddy.
_____+++_____
A bangaren su Guggo Laure kuwa sai shirye-shirye suke saboda Galadima yakirata cewa su Abba zasu zo daga kaduna a tsayar da magana asa ranar biki.
Cike da farin ciki Guggo Laure da Akeela suke,don itama Akeela tsaban murna ma har walima tace zata hada,daga mamanta har Alhaji Mansir sunsamu Ido duk da abin alfaharinsa ne ace 'yarsa tashiga ahalin Galadima amma aida kunya amma wani alqawarin za'a bashi ita akuma zo a fasa.
Akeela ce da qawayen ta a dakinta sunata tayata murna daya daga ciki maisuna Suby tace"nikoh akeey baki nuna mana hoton wannan mai sa'ar ba,dayan mesuna zuleey tace"ai da alama shidin ke tsadane fah,dayar maisuna siyama tace"komin tsadarshi ai mu dole tanuna mana shi don ko ba komai anatare duk wanda yaji cewa ma mu nakusa da ita bamusanshi ba ai wallahi dariya za'a mana.
Suby tace"gaskiya ne siyama maganar ki
Murmushi Akeela tayi wanda dama tun sanda suka fara maganar tashiga gallery dinta inda tayi saving din photos dinshi a IG account dinshi da yake sawa.
"Hmmm bbys kenan ku kwantar da hankulan ku gashi tayi maganar tana mikamusu phone dinta.
"Wow,suby tafada tana bude mouth, zuleey tace"handsome, siyama tace classic guy.
Itakuwa Akeela banda mnurmushi babu abinda takeyi don tasan muddin Allah ya mallaka mata Sauban amatsayin miji to lallai tana daya daga cikin mata masu sa'a.
"Kai bby akeey wannan Rich Man din?wanda ko wace mace ke burin aura kika samu?kinsan ko yanda mata ke hauka cewa akansa?to koni ina daya daga cikin fan dinsa.
Dan tabe mouth Akeela tayi tace"aiko ko wacce mace kwalelenta don inada tabbacin ahalin da ake ciki babu macen da takaini daraja a wajensa.
Suby tace"Lallai ne akeey dole ne team dinmu yasake haskawa dole muba haters wuta.
"Yanda kikajin nan Suby,hmm lallai kinyi babban kamu kekam.
Akeela tasake sakin murmushi akaro na babu adadi tace"ko babu auratayya tsakanina dashi shidin brother nane da hajiya Laure da Alhaji Muhammad Taufeeq Muhammad (GALADIMA) uwa daya uba daya.
Duk zaro idanuwa sukayi waje cike da mamaki.
Suby tace"lallai kam muntayaki murna,nanfa suka fara shirye-shiryen yanda party din sa ranar zai kasance don dole duniya Susan wannan abin ko ba komai zamu sake zama celebrates a duniyar tiktok musamman ma ke akeey,cewa zuleey nanfa suka hau ihu bakajin komai sai hayaniyar su da hirarrakin su.
Acan fam din Galadima kuwa Daddy ne yakira Sauban bayan sallar isha'i yake tambayar sa wata nawa yake ganin za'a sa ranar.
Wani gwauron ajiyar zuciya Sauban ya sauke cikin kamewar sa da nutsuwa yafara magana.
"Daddy inda so samu ne asa nanda 1 year saboda inaso naje naga yacce aikin zai kama sannan nayi duk tsare-tsaren da zanyi kafin lokacin insha Allahu everything will be fine.
Kura masa ido Daddy yayi tare da dan murmushi yace"gaskiya baza'a sa 10year ba to bari kaji koda mukayi shawara da Alhaji Mansir dasu Abbie dinku da za'a sa 4month ne shine Abbie naku yace a tuntube ka aji tabakinka,Amma wani irin 1 year Sauban babu dadin ji.
Sake tsuke face yayi tare da sake rissinar dakai yace"please Daddy a duba a gani.
Daddy yadaga masa hannu tare da dubansa face nashi babu alamun wasa ko kadan yace"Za'a tsaida ranar auren ku nanda 8month shikenan.
Sosai ransa baiso ba kuma ko kadan baya farin ciki bare mara ba da auren,sai dai duk kwakwanka bazaka gane hakan akan fuskar sa ba.
Dan rausayar dakai yayi gefe yace"Shikenan Daddy Allah yasa hakan shine yafi alkhairi.
Da Ameen Daddy ya amsa,tare da sa masa albarka don har ransa yake farin ciki da irin danda Allah yabashi,duk da kasan zuciyansa cike yake da tausayin Sauban din.
Mikewa yayi tare da masa sai da safe.
BAYAN KWANA BIYU
Zuhra tunda taji Abbie dinta zaizo takasa sukuni tsananin farin ciki ya dabaibayeta,kudi ta amsa wajen bodejo tabawa security mai bawa fulawa ruwa tace yasiyo mata kaji na turawa guda uku da wasu dai siyayyan,zama tayi ta hada ma mahaifinta lafiyayyen dambun kaza dasu cake da dubulan,da temakon Hannemai aikin bodejo tahada masa komai,ana gobe zasu taho shida Abba tahada komai ta adana,daren ranar cikin tsananin farin ciki tayi bacci.
Washegari su Daddy suka shigo maidugri kuma kaitsaye gidan Guggo Laure suka sauka a hanya suka hadu da Baba Hasheem da komai na al'adar saka rana,nan aka musu tarba ta girma wajejen la'asar aka sanya ranar wata takwas.
Itadai Guggo Laure ba haka taso ba amma tunda ansa babu yacce zatayi.
Haka suka dawo gida, Baba Hasheem apartment dinsa yashiga, Mom yacidda tana hada abinci a dinning,koda yayi sallama da mamaki tajuyo tana dubansa.
Murmushi yayi tare da cire hulan kansa ya zauna akan kujerar,sannu da zuwa tamasa sannan tace"wallahi nadamu Abban Aseef tundazu hankalina yaki kwanciya ganin baka dawo daga office ba gashi inata kirar wayar ka taki shiga.
Cike da farin ciki Baba Hasheem yace"ya hakuri Rabi wallahi abubuwa ne suka shamin kai munacan wajen sa ranar auren Sauban ne da jikan Guggo Laure!!
Wani gingirin gin Mom taji kanta ya mata cikin tsananin rudewa ta dubi Baba Hasheem.
Xahratty CE🥰
Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️
[3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽🦳
Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*
Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now
*_GALADIMA FAMILY_*
Page:- 11/12
_Bismillahir-rahmanir-raheem._
*_Ba zaku gane maza security bane ga mata sai mijinki ya rasu ko kun rabu ..._*
*_Duk ranar da akace baki da Aure toh fa sai ahankali kin zama hanya mai insecurity, keda hanyar Zamfara ko Rijana na Kaduna kusan daya 😃😃😃_*
*_Yo harda wanda bai isa ya maki magana ba zaiyi.._*
*_Amma in kina da Aure Koda mijinki baya tabuka maki komai ke kike ciyar dashi mutane ba zasu taba miki kallon banza ba ..._*
*_Don Allah Yan uwa mata mune zamu gayawa juna gaskiya idan matsalar da kike fuskanta ba matsala ta transformer bace da baya kawo wuta , ba Kuma dukanki yake ba kiyiwa Allah kiyi hakuri ki zauna.._*
*_Babu auren da ba a fuskantar matsala sai dai muce na wani yafi na wani..._*
*_Babban matsalar Bai wuce talauci ba , kuyi hakuri lokaci ne , wannan keburan na taba kowa Dan dai mutane Basu fito sun Fadi matsalarsu bane ..._*
*_Ina bawa duk wata matar Aure hakuri, a Kara hakuri, Allah yaci gaba da baku hakuri ya biya maku bukatunku na Alkhairi._*
____Au yau akasaka ranar?tayi tambayar fuskarta dauke da murmushi iya labba.
Baba Hasheem yace"Eah yau akasa wata takwas muka sanya saboda yanzu za'a fara aikin so sai yaga kamun ludayin aikin,idanma komai yayi normal before lokacin so za'a iya dawo da ranar baya insha Allah.
"Kai! Mom tafada wanda sam batayi zaton bakinta ya furta hakan ba,dubanta Baba Hasheem yayi yace"Kai mene kuma Rabi?
Da sauri ta wayance ta hanyar sakin wani kayataccen murmushi yace"Hmmm kasan kuwa irin tsananin farin cikin da nayi?wallahi na taya maimuna murna da samun siriki irin Sauban.
Wani murmushin jin dadi Baba Hasheem yayi"Tabbas kuwa don Sauban yaro ne wanda kuwa zaiyi sha'awar sa.
Mom tasaki murmushi tace"Aikuwa!
Zuhra tarasa inda zata saka ranta tsananin murnan ganin Abbie din nata bodejo ta tabe baki tace"Gaskiya Sadeeq duk kabi ka shagwaba yarinyar nan tare da sangarta ta.
Dariya Abbie yayi"Bodejo to yaza'ayi?
"Abbie kataso kaci abinci tundazu nahada maka lunch saboda nasanka da son cake da meat pie shiyasa namaka sannan na dama maka kunun gyada,takarisa maganar tana kama hannun Abbie din.
Murmushi yayi tare da mikewa kai tsaye suka nufi dinning room.
Tabe baki bodejo tayi"uhm uhummm tafurta.
Dan dariya Galadima yayi yace"hajiya bodejo duk kishin ne haka?
Bodejo tace"wane kishi zanyi kawai sai nahau yin kishi saboda wancan kwailar?takarisa maganar tana nuna zuhra.
Itadai Zuhra akaikaice tasakin ma bodejo gwalo.
*KADUNA JABI ROAD*
"Lallai Bilkisou sai yau nasake tabbatar da baki da hankali gabadaya kin wofantar da diyarki ta karfi da yaji kinmaida ita abokiyar gabanki?yarinyar ki nutsattsiya karfi da yaji kinmaida ta marainiya?meye lefinta?itace tace a sanya mata sunan surukarki?ke kanki ba sunan mahaifiyar ubanki kikaci ba?
To bari kiji wallahi wallahi ina sake jaddada miki muddin baki shiga hankalinki ba Bilkisou bazan taba yafemiki ba,yarinyar nan ko wajenmu baki kawota sam Fateema batasan niba yanzu ke kin kyauta?ke ba abin kunyarki bace ace 'yarki batasan gidanku ba?sai dai tadinga ganina a photo?tsaban hankali irin na yarinyar nan har kirana take a waya.
Narantse da Allah Bilkisou fateeman ma tafiki hankali,har mahaifinki ya rasu da bakin cikin abin nan yatafi.
Duk da kinkasance mai biyayya amma akan wannan abin kinkasa wa mahaifinki biyayyaaaaa......
Takarisa fashewa da kuka cikin takaici.
"Mtsewwww ai wallahi Amma kinma mata da sauki da yacce tayi watsi da diyarta,kekuma kiyafeta a cikin 'yayanki....
Da sauri Ummie tadago tana duban yayanta Aunty Zainab tace"Haba Aunty mezesa kicewa Amma haka?kunsan kuwa irin zafin da nakeji a cikin zuciya ta?wallahi inajin sonta da kaunar sai dai tsanar da nake mata ya danne sonta da nake mata.
"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un Bilkisou dinyar taki kike cewa kike tsana?lallai.
Zainab tashi muje wallahi wallahi Bilkisou muddin baki kaunace diyarki ba All....da sauri Ummie ta rufe bakin Amma tana girgiza kai hawaye na tsiyayo mata.
Fincike bakinta Amma tayi sannan tamike tadubi Aunty Zainab tace"Zainab tashi muje.
Gyara mayafin gyalenta tayi tadauki jakanta sannan suka fita,Ummie tabiyo bayansu da sauri tana kiran sunan Amma dana Aunty Zainab Amma ko waige.
Daidai nan Taufeeq yashigo a gigice yasamu daya daga cikin sofa din yazauna tare da duban Ummie yace.
"Ummie meke faruwa ne?Kinga yadda Amma tafita tana kuka nagaishesu amma bata amsa ba infact ma ko tsayawa batayi ba Adda Zainab ce tatsaya muka gaisa.
"Ummie nasan dama bazaki bani answer ba amma nasan akan maganar Zuhra ne hakan ke faruwa,wallahi Allah yasani koni banjin dadin abinda kike mata haba Ummie kamar bakece kika haife zuhra b.....
"Tasssss!karar mari yafito.
Ummie ce ta zabgama Taufeeq marin tana huci tare da nunasa da yatsa alamun gargadi tace"Tashi kafita.
Sakin baki Taufeeq yayi yana duban Ummie cike da mamaki don tunda yake a rayuwa ko dunguri Ummie bata taba yimishi ba.
"Kana mamaki ne?tashi kafita nace kafin nakuma yarfa maka wani marin.
Mikewa yayi tare da duban ta yace"Allah yahuci zuciyar ki Ummie.
Wani banzan kallo ta watsa masa.
Sum sum Yaya Taufeeq yafice daga parlon.
*BAYAN KWANA BIYAR*
Ayau ne Sauban jirginsa yadaga sai kasar maleyshia.
Bayan tafiyarshi da kwana biyu aka bashi aiki matsayin M.D na company,wadanda hada takalma sukeyi,sannan aka bashi gida hadadde Wanda ya kawatu matuka babu abinda babu a gidan,sannan anbashi mota kirar Benz G-Wagon tabbas duk wani masoyin Sauban yaji labarin nan dole yatayasa murna.
Ranar monday shine ranar da yafara fita daga office babu abinda kakeji sai sautin tas tas tas tas sautin karar covershoe dinsa ne.Sosai ayau din kensa yasake fitowa na jinin shuwaarab da kuma buzaye,pink lips dinsa gunin sha'awa,sajen nan nasa yakwanta sai sheqi yake kamar balarabe gashin kansa baki sidik gunin ban sha'awa duk da cewa Ya Sauban ba fari bane amma yana da wata irin kyakkyawan fata irin na Zuhra wato half-caste haka colour nasu yake.
Sanye yake da designer suit kirar company Gucci black colour,agogon dake daure a hannunsa Kuma Cartier.
Hannayensa riqe da wayoyinsa guda biyu iPhone 11pro da iPhone 13 pro max.
Kaitsaye inda motarsa take kirar Benz G-Wagon yanufa da sauri driver din yafito tare da bude masa bangaren back seat,dan rissinawa driver yayi tare da cewa.
"Good morning sir!
"Morning David hope everythig is Ok?
"Yes Sir,David ya amsa dashi yana me yaba kyan da ogan nasa yayi a ransa.
Bangaren driver David yashiga tare da tada motar,gate Man ne ya wangale musu gate din kaitsaye David yacilla motar kan kwaltan dake area din.
**********
"Ranka yadade dangudelle haba taya zan raina aikinka nida nasanka kasanni shekaru 28 kenan munatare tabbas nasan aikinka yana kyau shiyasa ma koda yaushe nakeda yaqini agareka sam bana wasiwasi akan aikinka.
"Hahahahahahahaha! Aka saki dariyar cikin wani murya marar dadi wanda gabadaya sai da sautin dariyar ya amsa dajin,itakuwa Mom banda rawa babu abinda jikinta keyi saboda tayi tasananin tsorata.
"Biba kenan nasan abinda yakawoki nakuma san abinda yake tafe dake,yayi maganar cikin wata irin murya marar dadi.
"Hahahahaha wannan yaron dakikeson hada 'yarki dashi tabbas hatsabibi ne don kuwa sam baya wasa da azkar,sannan ita yarinyar da akeson yanzu a hadashi aure da ita ba sonta yakeyi ba sai dai tabbas daga baya zaisota ta hanyar asirii....hahahahaha"
Yakarisa maganar yana sakin wannan dariyar nasa da muryansa marar dadin ji.
"Hmmm dangudelle nasani nasan komai so nake kamun aiki akansa ya birkice akan maganar aurensa da wancan kodaddiyar yarinyar,ajuyar da akalar maganar kan Rammat,don idan har Rammat bazata sameshi ba to itama Akeela bana fatan tasameshi.
Wani irin kallo dangudelle yayiwa Biba tare da sakin wani dariya,zuwa can yatsuke fuska yace"tirkashi aiko bazai yuwuba sai dai suyi zaman kishi tare saboda wannan tsohuwar tsaye take akansa don so take da bala'i su mallake yaron.
Share gumi Biba tayi tace"nikam yaza'ayi kenan?tabbas Biba itama saita shiga gidan idan yaso daga baya takoreta.
Wani dariyan boka dangudelle yasanya yace"lallai yaron dangata ne don a kaddararsa yanuna daga baya da mace daya zaiyi rayuwa tare da yimata wani irin mahaukacin so,don ko ayanzu yana sonta.
Dafe kirji Biba tayi cikin tsananin rudewa tace"wacece wannan yarinyar?
"Bansanta ba!duk iya kokarina naganin gano yarinyar nakasa amma tabbas itace matarsa uwar 'yayansa,boka dangudelle yakarasa maganar yana diddilo da idanuwa waje.
Itadai Mom banda rawa babu abinda jikinta keyi dukda kuwa yanda takejin daci aranta saboda ta tsani Sauban tun randa ta haifi ɗa namiji, saboda yanda Sauban keda kwarjini da farin jinin jama'a sam danta baidashi wannan dalilin ne yasa daga ita har Aseef din suka tsane Sauban.
Biba tace"dangudelle so nake duk halin da ake ciki Sauban yafada tarkon son Rammat.
"Hahahaha....Ke shedaniya! tabbas kinsan zan iya zanyi abinda yafi haka,yayi maganar yana jawo wani kwarya wanda babu komai sai toka yafara cakuda garin tokan da hannu,cike da al'ajabi hoton Sauban ya bayyana yana zaune a office dinsa.
"Hahahaha.. dangudelle yasake sakin wata dariyar yace"Zoki ganshi tabbas yaron yasamu daula.
Jikin hajiya Biba dana Mom har rawa yakeyi."Aiko tabbas Sauban ne hajiya,hajiya kinga wani irin office dayake zaune a cikinsa?
Kafin hajiya Biba tayi magana dangudelle yadaga hannu tare da shafe tokar,nan take hoton ya bace.
"Kutashi kuje tabbas zakuji sakamako mai dadi don yanzu haka na wada da dantsaka da lituwa suna hanyar dawowa daga masar kawon saqo kuje na sallameku".
Hajiya Biba na shirin magana kenan dangudelle yabace bat,dole suka mike badon sunso ba kowacce da abinda take saqawa a ranta don Mom ita inda dayanda za'ayi kashe mata Sauban kawai za'ayi.
_________**________
Yauma kamar kullum tashinta kenan dai² karfe hudu a dalilin wani mummunan mafarki da tayi wai anyi rasuwa ga mutane nan cike a Galadima fam sai dai bataga gawar ba sosai hankalinta yayi kololuwan tashi,koda tamike bathroom tashige tadauro alwala tafito tare da shimfida praymat tatada sallah.
Koda ta idar lokacin anfara kiraye-kirayen sallar farko,sosai tayi addu'ah.
Tadauki tsawon mintuna tana lazimi zuwa can aka tayar da sallar asuba don haka sai itama tamike tatada sallar.
Acan gidan Guggo Laure