Showing 102001 words to 103469 words out of 103469 words
na ganta?cikin sanyin jiki Dr jamila tace"dama tace"akira mata kai, Ammi tace"muma zamu iya shiga? Dr Jamila tace"Ea ai angyara ta".
Koda suka shiga a kwance suka taradda ita inda sai murmushi takeyi,hannu ta miƙa ma Sauban tace"Yaya kaga Babyn mu ko?nasan ni ba wani kula dasu zanyi ba Please ga amanar su nan a hannun ka,ka tarbiyyar tattadasu,ina son ka mijina, ina so ko a aljanna nayi rayuwa dakai"taƙarisa maganar sai hawaye, Sauban cikin sauri ya kamo hannun ta ya matse"wani irin magana ne kike yi haka?wani waje na miki ciwo ne?girgiza masa kai tayi tana kwance hawaye na mata wani irin zarya,duban su Ammi tayi tace"Mom, Ammi Ina son ku kuce ma Ummie na ina son ta koda na mutu kada tamin kuka zanje inda Abbie yaje ne"wani kuka Mom ta fashe dashi Ammi kuwa jikinta har tsuma yakeyi tace"Zuhra wani irin magana kikeyi haka?meya kawo zancen mutuwa?girgiza kai Zuhra tayi tace"Ni kaɗai nasan azabar da nakeji wallahi,kuna jin wani ƙara kamar abu na turowa a gabana?ga cikinana wani irin karta?duk shock suka shiga Sauban jikinsa na rawa ya fita saboda ya fara tsora babu jimawa suka dawo da Dr Ahmad da Dr jamila, ɗan ɗaga doguwar rigar asibitin Dr jamila tayi,wani jini ne ke gudu yana wani zubowa a gaban Zuhra tare da wasu dunƙule²,cikin tashin hankali tace"Ya Salam Dr da matsala jini fa ya kece mata".
Gabaɗaya tashi hankulan su yayi,nan ya danna wani ƙarar rawa kafin kace me Dr uku sun shigo tare da roƙan su Ammi su fita, Sauban kuwa dagewa yayi kan bazai fita ba,daƙyar aka samu ya fita,don a lokacin Zuhra har ta suma, nan yaran dake hannun su Mom suka shiga tsala wani irin kuka.
Duk iya ƙoƙarin su don dakatar da jinin yaƙi tsayuwa,don wani numfashi Zuhra ta saki tare da fara kalmar shahada a take anan rai yayi halinsa.
********
After 5 minutes doctor's ɗin suka fito ko wanne na share zufa, Dr Ahmad ne a ƙarshe,da sauri suka nufe shi,girgiza kai ya shiga yi yana dafa kafaɗar Sauban,ko kafin yace wani abu Sauban ya yanke jiki ya faɗi, dai-dai lokacin su Daddy sun iso don Ammi ta Kira shi.
Da gudu su Mom suka nufi ɗakin da Zuhra take,ga shi nan an rufe face ɗin ta da farin ƙyalle sai sheƙi yakeyi murmushi kamar yin sa takeyi ta sake wani irin kyau.
Ammi jikinta rawa ya kama suna sakin wani irin kuka inda suma su Daddy suka nufo ɗakin suna salati.
[7/30, 15:31] 𝐎̃𝐔̂𝐌 𝐀̃𝐉𝐌𝐄̨𝐑𝐋💜🤍: Muryoyin Mom da Ammi kakeji cikin kuka suna salati saboda kwata² babu rai a tattare da Zuhra ko kaɗan,ga Sauban likito ci na kansa don ceto rayuwar sa.
Ƙarfe biyar na a asuba su Daddy suka taho da gawar Zuhra,inda a hospital kuma Kareem ne ke zaune da Sauban, gabaɗaya idan kaga ahalin nan a wujijjige suke,wani irin kuka Boɗejo keyi,haka su Rammat ma su Guggo Laure kafin takwas gida ya cika tanƙam,mutuwa kenan me tambari.
****
A Kaduna kuwa koda Baba Hasheem ya Kira Abba ya sanar dashi shima tashin hankalin yakeyi, Mommy da taji wanda ya rasu kuka sosai takeyi wani irin zazzaɓi lokaci guda na rufe ta,ita ta shiga wajen Ummie ta sanar da ita sai dai ta nuna mata Galadima ne sannan gashi yanzu zasu tafi,ƙarfe huɗu na asuba suka fito duk cikan su ahalin har da Nihal da Laila motoci uku sukayi tunda shima Shuraim na garin lokacin,duk kazan sunji wanda ya rasu,a mata kuwa Mommy ce kawai, itama Ummie gaban ta faɗuwa yake hakan ya saukar mata da ruɗu da tsoro ta saki kuka,basu isa Maiduguri ba sai azahar a lokacin su kawai ake jira,tun daga farkon layin har ƙarshe jama'a ne,tunda suka shigo gidan kallo ya dawo kan Ummie da Taufeeq,abin mamaki gawan a sashin Ammi ne hakan yasa suka nufi can,dafo kafaɗun Ummie Ammi tayi lokacin Sauban na duƙe gaban gawar yana wani irin kuka duk da babu sauti ga baby ɗaya a bayan Muneefa ɗaya bayan Rammat sai kuka sukeyi,domin kukan su shine yake sake tayar ma da mutane hankali.
Nan fa jikin Ummie ya kama rawa a sanda aka buɗe fuskan Zuhra.
A take anan Laila da Nihal suka zube sumamnu,ita kanta Mashahuda sai da aka riƙe ta.
"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, hasbunallahu wa ni'imal wakeel!!!shine kawai kalmar da Ummie furta idanuwan ta kan Zuhra jikinta na kyarma.
Nan tashiga faɗin"Allah ya jiƙan ki Fatima,Ubangiji Allah yayi miki rahama,ashe kece me bin mahaifin ki?kin mutu kinbar ni kin bar ƴan uwa? innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, addu'o'i ta shiga zubo mata wanda yasa a take anan ta burge mutane da dama, majority kuka kawai suke,mutuwar Zuhra mutuwa ce me tsayawa a rai,mutuwar ƙuruciya Wanda mantawa ba nan kusa ba,nufar yaran Ummie tayi sai a lokacin tafara zubda hawaye,shi kan shi Taufeeq kukan yake yana jijjiga, addu'o'i shima ya shiga kwaranyo wa,atake anan aka kira duk wani makusan cin ta ya fara mata addu'a saboda za'a kaita gidan ta na gaskiya.
******
Laila kam jiki yaƙi har jini tafara zubarwa aka nufi asibiti da ita,lokacin da za'a wuce da ita kuwa haka wasu suka sake shinsshin fiɗewa a ƙasa sumammu,ita kanta Boɗejo tana can ana mata ƙarin ruwa.
*******"
Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un mutuwa mutuwa mutuwa babu daɗi,daka kalle Sauban kasan a gigice yake,ko abinci be iya ci, gabaɗaya ya rame ya sake wani haske,haka ake zuwa mishi gaisuwa tun daga uwa duniya,idan kuwa yaran suka fara kuka kamar zai shiɗe shima tsaban kuka,yana tuno soyayyar su bai taɓa kawowa ɗayan cikin su mutuwa nan kusa ba, Zuhra ta daban ce a cikin mata baijin sai samu me maye gurbin ta har randa shima nashi mutuwar zaizo.
Wasa wasa har anyi bakwai masu tafiya sun tafi su Aunty Maryam nanan sam ahalin gidan mutuwar ya kasa goge musu, Sauban ya kasa dawowa dai-dai,haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda Mashahuda ita ta cigaba da shayar da yaran Sauban,bayan sati biyu suka tafi dasu Kaduna.
*******
Boɗe idanuwan shi yayi waɗan da sukayi jajawur,yana ɗaukan hanky ya share tears ɗin da suka zubo mishi,wata yarinya ce da bazata gaza 3 yrs ba ta taho da gudu ya faɗa jikinsa"Daddy kaga Ajmerl ko?tayi maganar yana faɗawa jikinsa,wanda aka kira da Ajmal ne ya ya ƙariso zabori a hannun shi,duk da ba manya bane amma idan ka gansu zakayi tunanin ƴan 5yrs ne saboda girman jiki da shegen wayo, yaran kyawawa sosai kamar ka sace.
Shafa kan macen Sauban yayi yace"Idan yaya Ajmerl ya daki mun little Zuhra sai na zane shi"ƙarasowa Ammi tayi duk da bata wani canza ba Amma ta girma,duban Sauban tayi tace"Yau ma kayi tunanin naka ko? Sauban duk cikan mu haƙiri zamuyi kafin lokacin mu yayi tabbas mutuwar Zuhra manta shi ba nan kusa ba,amma banjin daɗin rashin walwalarka mundena ganin fara'an ka, kayahakuri ka sake kamar da ka bita da addu'a" tayi maganar tana share hawayen da ya gangaro mata,"insha Allah zaka samu wata ta gari itama"
Duban Ummie Sauban yayi tare da yin yaƙe yace"har abada Ammi bazan samu makwafin Zuhra ba,na rasa ta ban kallon sauran mata a mata yanzu don haka banjin zan ƙara aure nan kusa".
Da mamaki Ammi ta kalle shi tace"Galadima tun kafin ya rasu yake maka nasiha da lallashi,haka ma Boɗejo duk da tsakanin su shekara guda ne,tabbas munga tashin hankali ya Allah kajikan bayin ka"da Ameen Sauban ya amsa.
Rayuwa kenan duk abinnan Sauban ne yake tunanin rayuwar shi da Zuhra da ahalin Galadima family,ga Galadima ya rasu,haka Boɗejo rasu, duk bayan rasuwar Zuhra,inda Mashahuda yaran ta uku, Laila da Nihal bibbiyu, Muneefa ɗaya, Rammat biyu,sauran jikokin gidan duk sun girma, Ummie ma tana can a Kaduna don tace ita bata sake Aure duk da su Sauban suna ƙoƙarin Daddy ya aure ta.
ALHAMDULILLAH DUKDUKA ANAN NA KAWO ƘARSHEN LITTAFIN GALADIMA FAMILY,KURAKUREN DAKE CIKI ALLAH YA YAFE MIN,BADA CIN ZARAFI NAYI BA SANNAN ƘIRƘIRARREN LABARI NE,INA GODIYA MASOYA TABBAS NAGA SOYAYYA INA KAN GANI DUK DA WANNAN BASHI NE BOOK ƊINA NA FARKO BA AMMA NAGA KULAWA ALLAH YASAKA DA MAFIFICIN ALHERI.
JINJINA.
Muhammad Kareem kaima kayi iya ƙoƙarin ka Nagode Allah ya saka da alkhairi Allah yabar zumunci.
Ban manta da GALADIMA FAMILY group ba ina miƙo gaisuwa a gare ku Allah yasa ka da alkahiri,haka mutanen facebook musamman HAFSAT HAUSA NOVE H² Allah ya saka muku da alheri.
Gargaɗi
Kada a canza min komai na book yin hakan babban kuskure ne akiyaye😡
Sai kun sake jina a zazzafan next book ɗina Wanda zaizo bada jimawa ba,kudai ku kasan ce da alƙalamin XAHRATTY ✍🏽