Showing 6001 words to 9000 words out of 103469 words

Chapter 3 - GALADIMA FAMILY Complete Hausa novel

07 Sep 2024

6874

wani company a can ne toh.
Cike da farin ciki har zuciyar Guggo Laure ta yashe baki tace"Alhamdulillah Allah mungode maka,a zuciya Guggo Laure tace"(ya ubangiji Allah yakai damu ga harawa,lallai Akeela duniya sabuwa,duniya nakine.)
Allah yabada sa'a ubangiji yadorashi bisa kawunansu.
Da Ameen Ammi ta amsa.
Nan Guggo tamike tamata sallama kai tsaye sasan Mom tanufa.

Mom taji dadin ganin Guggo don ko babu komai da mijin Guggo da baban Mom uwa daya uban daya,anan suka gaisa Guggo tace"gaskiya Rabi bakida kirki yanzu kiri² dan naman nan ma kindena aikomin dashi sai dai kikaiwa hajiya habi?haka amana yace? Dama ana saka alheri da mugunta?a fakaice mom ta watsama Guggo Laure harara,a zabiri kuwa dan marairaice fuska tayi tace"toh yazanyi Guggo?kiri² baban Aseef ba siyowa yakeyi ba sai lokaci zuwa lokaci,nima kaina baya isata balle nabaiwa wani.
Guggo Laure ta kama baki tace"Oh a haka Hasheem sumumi sumumi Amma duk Wanda yaganku yaganku cikin hutu don ke tunda kika shugo cikin a halinmu zaka sheda.

Mom tayi dariya tace"gaskiya ne Guggo,amma bajiya akace bakijin dadi ba? Guggo Laure tace"hmmm aikedai bari ai tafiyar nan ta dole nakeyinta,nan Guggo Laure tazauna tabawa Mom labarin duk wani qudurinta kaf nason hada auren Sauban da Akeela.
Kirjin Mom ne yayi wani irin mummunan bugawa hankalinta yayi qololuwan tashi,a diririce Mom tace"Guggo wani Sauban din?
Harara Guggo Laure ta maka mata tace"Sauban nawa ne a gidannan?to dan uwanta mana nake nufi.
Guggo tace"Bari naje rabi yanzu zakiji ankira azahar.
Gabadaya har Guggo Laure tagama maganarta tabar farlon Mom bataji ba sai da taji karar rufe kofa tajuyo a hautsine.

Mikewa tayi cikin gigita da rudewa tace"Inah? Sauban da Akeela?wallahi bazai yuwuba bazan taba bari Sauban ya auri Akeela ba.
Duk irin son da Rammat takeyi masa ana nufin zaitashi abanza ne?wallahi bazai yuwu ba,qanwata Ina ganin yanda takeson Sauban kamar zata rasa ransa,Rana tsaka azo da maganar wata shegiya Akeela?wallahi bazai yuwu ba,Ina wayata?

Tayi maganar tare da nufan hanyar wani corridor cikin gigita.

_TIRQASHI ANA WATA GA WATA._
_MEKE SHIRIN FARUWA NE?ME MOM TAKE NUFI?DUK WANNAN ABINDA AKEYI SHI ME GAYYA ME AIKIN MA BESAN ANAYI BA,KUDAI KU KASANCE DA ALQALAMIN ÕÙM ÃJMÃL🖊️_

Xahratty Ce🥰
Lallai Alqalami🖊️ yafi takobi 🗡️

12/2/2023.
[3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳

Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now

*_GALADIMA FAMILY_*

Page 05

_Bismillahir-rahmanir-raheem._

_______A tsananin rikice mom take shiyasa koda tashiga cikin bedroom dinta sam hankalin ta baikai wajen phone nata ba,fita tayi daga bedroom din tanufi wani corridor wanda kaitsaye ya sadata da parlon Abba,neman wayar tashiga yi sai dai duk iya neman da tayi bata gani ba ( _Nikoh nace su hajiya mom manya tsaban rudewa a bedroom dinki kika bar wayan😆_ ).

Dan siririn tsaki taja tare da fita tanufi bedroom dinta dai,gabadaya ta hargitsa dakin bata gani ba,banda numfarfashi babu abinda takeyi cikin sa'a kuwa idanuwanta suka sauka akan bedside drower dinta,sake watso idanuwa tayi cike da tsananin mamaki,mikewa tayi ta dakko wayar tare da komawa tazauna a bakin gadon hannunta har rawa yakeyi wajen dialing number Rammat,ganin andauka ne yasa Mom kara wayar a kunne bakinta na rawa tace"Hello Rammat kina jina ne?kina gida?
Daga can bangaren akace Eah, Mom ta cigaba da cewa"kiyi maza maza kizo inason ganinki yanzu fah,still dai da toh aka amsa mata.

Katse kirar tayi inda tafara safa da marwa a cikin dakin.

A bangaren su Guggo Laure kuwa bayan sallar azahar duk suka hallara a parlon na Galadima, Galadima,bodejo, Daddy,baba hasheem.

Guggo Laure tace"Yaya ayi maganar da za'ayi don Allah saboda nisam bansan sharrin shedanu.
Dan murmushi Galadima yayi yace"Laure kenan bari akira yaran duk aji ta bakunan su.
Duban Daddy yayi yace"taleeb lalubomin Sauban a wayarsa daganan kace masa su taho da mashahuda.Da toh Daddy ya amsa sannan yafara neman Sauban a wayarsa.
Cikin kankanin lokaci kuwa ya dauka inda Daddy yasanar masa da saqon Galadima.

Ba'a dau lokaci ba yayi sallama mashahuda na biye da ita,duqawa sukayi cike da mutumtawa suna sake gaishesu,nan Baba Hasheem yadubi mashahuda yace"takira masa Akeela daganan tawuce,amsawa tayi da toh tare da miqewa.
Basu wani jima ba itama tashigo sai wani sake karairaya take tamkar iccen da yake gaf da karyewa,samun gefen kafar Guggo Laure tayi ta zauna sannan tafara gaida su Daddy.
Gyaran murya Galadima yayi yafara magana.
"Toh Alhamdulillah Muhammad wannan taron da akayi akanku kune kai da kanwar ka Akeela gatanan!yayi maganar yana pointing din Akeela,yaci gaba"Toh 'yar uwata Kuma kanwata kakanka Laure gatanan tanaso musake danqon zumuncin mu ta hanyar hada auratayya tsakaninka da Akeela.
Da sauri Sauban yadago tare da duban Galadima.

"Ita kuma yarinya tana sonka shine nace kaima munason muji ta bakinka kana sonta kokuwa?
Sauban mutum ne wanda sam baida boye² kaitsaye yake magana don watarana su Daddy har takaicin hakan sukeyi,bude baki yayi da sauri yace"wallahi Galadima bana sonta,nisam bata cikin jerin matan danake son na aura don haka ku bata haquri,saboda sam bana fatan abinda zai taba mana zumuncin m......
Ko kafin Sauban ya ida abinda zai fada Guggo Laure tafashe da kuka cikin tsananin fusata ta dubi Sauban tace"Baka Isa ba,baka isa ba muhammadu!ubanka Taleeb ma bai isaba balle kai karan kada miya,nikuke so ku watsama kasa a ido?mene nayi muku?lefi ne don Akeela nason ka? Akeela jininka ce kuma 'yar uwanka.
"Ko babu komai so muke muqara danqon zumuntan mu.
Sauban dafa kai yayi zuciyar sa na tsananin bugawa don har ransa shi baya son hadin zumunta.
Cike da bacin rai bodejo tace"dakata don Allah Laure,wani zumunci kike maganar za'a gyara?a gyara ko a bata?yaro yafito yafada ra'ayinshi kuma a neme a tilasta sa,wallahi bazan lamunci cin kashin kowa ba a yanzu wannan son zuciyar taku tafara isatal!
Tayi maganar tare da watsa ma kowa kallon banza harda Galadima ( _Omg🤔_ )
Mikewa Guggo Laure tayi cike da jin haushin bodejo tace"lallai ma Yaya bodejo sannu me jika kenan Akeela ba jikar ki bace sai Sauban?yanzu niba zan iya neman alfarman wani a gidan nan ayimun abu baaa?takarisa maganar tare da fashewa da kuka mai tsanani tamkar ba tsohuwa ba,gabadaya hankalin su yatashi idan kacire bodejo da Sauban.

Bodejo tace"Laure nice bansan makircin ki ba?kukan d.....
"Ya isa don Allah kubar maganar haka, Galadima ya katse bodejo.

Wani kololuwan takaici bodejo taji a zafafe tanufi hanyar kofar parlon Galadima don fita,daga murya Galadima yayi yakira bodejo.
Sai dai ko waiwaye batayi ba balle asa ran tsayawar ta.

Jinjina kai Galadima yayi saboda hankalinsa yatashi,ransa Kuma yabaci,a zafafe ya daka ma Guggo Laure tsawa akan kukan da takeyi tamkar ba tsohuwa ba( _Koda aidama tsoho akwai rikici,sai dai guggo Laure macece see shu'uma._ )

Daddy ne yayi gyaran murya sannan ya dubi Guggo Laure yace"Am Guggo don Allah kiyahakuri kiyi shiru haka za'a San abinyi yanzu kuji gida insha Allah zakiji alkhairi.
Galadima yace"Laure meyasa kikeso kibata zumunci gabadaya?

Sakin baki Guggo Laure tayi tana duban Galadima,aituni zuciyar ta yayi mata wani fassaran saba.
"Yaya! Saboda inason karfafa zumuncinmu shine zakace inaso na lalata?meyasa bodejo batason jinina? kuyahakuri insha Allah bazan sake maganar Akeela da Sauban ba,sai dai na haqura dakai da ahalin ka Yaya,don bazan zauna da wadanda basason jinina ba.
Gabadaya a firgice suka dago suna duban Guggo Laure,dayake Galadima Sarai yasan halinta.

Mikewa tayi a zafafe tacema Akeela" ki mike mutafi.

Fuuuu kuwa suka kama hanya suka fita.
" _Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un! Allahumma ajirni fi musibati wa'aklifni khairan minha_.
Kalmar da Daddy yafada kenan tare da duban Sauban.

"Yanzu Galadima ya za'ayi a shawo kan wannan matsalar? matsala cefa wacce idan ba'a ma tufkar hanci ba to zai iya taba zumuncinmu da Guggo Laure.
Jinjina kai Galadima yayi"Hasheem narasa ma mezamuyi,daga bodejo har Lauren kaf sun dauki zafi yakamata ace daya a cikinsu ya sauko,duban Sauban Galadima yayi yace"muhammadu Kaine sanadin wannan rikicin don haka kai zaka gyara.

Sauban ya sauke wani nannauyan ajiyar zuciya don shi mutum ne mara son hayaniya yace"Galadima bana son ta Allah ma yasani kuma.
"Keep quite Sauban! Daddy yafada cikin bacin rai.
Bakaga abinda ke faruwa bane?meye yashiga kanka?kasan kuwa wacece Guggo Laure?kakuma son me ake nufi da zumunci?hmmm katashi kabamu waje,don mune muka haifeka bakai ne ka haife muba,kaje duk hukuncin da muka yanke zakaji.

Mikewa Sauban yayi tare da rissinawa yace"Allah yahuci zuciyarku nabarku lafiya,yana gama fadar haka yajuya cike da mazantaka da salon tafiyarsa mai burge duk Wanda ke kallo yafita.
Baba Hasheem yace"gaskiya Yaya kada kashiga haqqin Sauban.

"Don Allah Hasheem kadena wannan maganar bana fatan abinda zai bata sunan GALADIMA FAMILY,kakira su Sadeeq a waya akwai meeting ranar Friday insha Allah,mukuma kafin lokacin mungama magana da bodejo don shawo kanta.

Gabadaya jinjina kai sukayi, Galadima kuwa sosai yaji dadi don matansa da kanwar tasa sun gwara mishi kai.

*KADUNA JABI ROAD*

Gabadayansu zaune suke akan dinning din suna dinner cike da farin ciki zuhra tace"Abbie nayi missing dinka sosai.
Murmushi Abbie yayi yace"nima nayi missing dinki mama na ya gida ya shirye²n jamb kuma?
Zuhra tace"alhamdulillah munanan munayi.
"Toh alhamdulillah agama cin abinci sai muje parlona inji wani jami'a kika cike a slip din jamb din.
Dariya sosai zuhra tayi tace"toh shikenan Abbie.
Ummie kuwa tsaban takaici jitayi tamkar tayi Aman wuta 😡 saboda bacin rai. ( _Ko na menene oho._ )

Basu jimaba suka kammala,duk suka hallara a parlon Abbie, Taufeeq, Laila, Aseef, Nihal, ZUHRA.
"Abbie nafiso nayi Dan fodio don haka shinasa.
Murmushi Abbie yayi irin nasu na manya yace"meyasa bakisa ABU Zaria ba ko Kuma KASU mamana?
Dan Jim zuhra tayi sai Kuma tace"Abbie banason ABU nikam,kuma abinda yasa banason KASU afa kaduna nayi nursery, primary, secondary, shiyasa nakeson nacanza gari Amma nafison Danfodio Abbie.

"Bakiga duka 'yan uwanki ba suna ABU?ga kuma yayanku Aseef,inaganin zakisamu kulawa sosai sannan zakiji dadi.
Dan rau rau zuhra tayi da ido dama ita abin kuka baya mata kadan muryan ta na dan rawa tace"please Abbie nikam banason ABU don Allah.
Laila tace"Abbie wallahi kada abari tayi Danfodio tazo ABU zataji dadi fa,takarisa maganar tana dariya kasa²

Cikin barkwanci ya Taufeeq yace"wallahi Abbie yarinyar nan tana mana bakin cikin dan jellof rice dinda zata dinga mana ne.

Gabadaya dariya aka Sanya,nihal tace"da dan sululu Koh Yaya?aka Kuma sa dariya.
Ya Aseef yace"Abbie aiba sai abinda takeso za'a biba dole umarnin iyaye zatabi ko 'yar jarida.

A kaikace zuhra ta dalla masa harara.

Fira sukayi sosai da Abbie kafin kuma kowa yawatse yaje kwanciya bacci.

*OLD MAIDUGRI*

"Aunty wai don Allah dagaske kikeyi?inafa son sa wallahi bazanyi fatan Sauban ya kubucemun ba,idan nashigo zura'ar GALADIMA FAMILY wallahi cele zan sake zama a wajen kawaye na da abokaina.
Wacce tayi maganar bazata gaza 27 yrs ba.


Mom tace"Rammat kenan nafiki son shigo cikin wannan family din don arziqi yaci uban nada kinsan kuwa waye Sauban?hmmm awajen dangin Aisha kawai idan kikaga gatan da Sauban ke samu sai kin gigice, Rammat da arziqi agidan wasu gwara a gidanku a gidanku ma a dakinku,hmmm wai Akeela.

Wani tsanar Akeela Rammat taji har cikin ranta saboda tsananin son da takewa Sauban.
"Aunty nidai gaskiya asanar ma da Mama halin da ake ciki don ni babu dalilin da zaisa nayi zaman kishi da Akeela ( _Sauban kaga takanka,tun yanzu anfara maganar zaman kishi a dalilinka._ )

Mom tace"Ea zanje bari ko zuwa anjima idan su Yaya (Daddy) sun fita sallar la'asar sai mufita don kinsan dokar gidan nan namu.
"Gaskiya kuwa Aunty don da zafi² ake bugun karfe.

A gidan Guggo Laure kuwa banda kuka babu p abinda Akeela takeyi gabadaya ta tadarma jama'ar gidan da hankali, Guggo Laure kuwa sai girgiza kafa takeyi.

Xahratty CE (ÕÙM ÃJMÃL )🥰

Lallai Alqalami🖊️yafi takobi🗡️

15/2/2023
[3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳

Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now

*_GALADIMA FAMILY_*

Page 06

_Bismillahir-rahmanir-raheem._

*NAGA SAKO NAGODE SOSAI MY SOFY ALLAH YASAKA DA ALKHAIRI UBANGIJI YAKARA RUFA ASIRI DUNIYA DA LAHIRA😊ALLAH YAKARA GIRMA ACEMA OGA SAUBAN MUNA GODIYA TARE DA AJMAL🙏🏽🙏🏽🙏🏽*

https://www.facebook.com/profile.php?id=100074816894956


Guggo Laure tace"Haba Akeela meyasa kikeso tayarmin da hankali ne?nace miki indai ina raye Sauban mijinki insha Allah idan Kinga baki aure Sauban ba ki tabbaci hakikan bana numfashi ne.

"Wai Guggo meke faruwa ne?tundazu kunshigo gabadaya Akeela tahana kowa sukuni a cikin gidannan,har yanzu bazata dena tabara ba kamar wata karamar yarinya?shekara ashirin da biyar Amma ace har yanzu mutum bai girma ba wallahi waje tasamu.
Harara Guggo Laure ta aika mata dashi tare da watsa yatsu tace"Maimuna kinsan Allah kikiyaye ni kifita idona,to ina ruwan wani kokuwa nina nemi wani yazo?inbanda munafunci da tsugudidi meyakawo ku?

Guggo Laure tayi maganar tare da watsama mama hajiya zainab harara matan baba sani,ganin hakan yasa sumi² tajuya tabar wajen.

"Guggo kada fa kimanta tun Akeela na qarama mujaheed kesonta wallahi idan akayi haka ba'a ma Yaya sani da Aunty zainab karaba.
"Maimuna kinsan Allah zan batamiki a gidan nan,ina ruwanki?ko kinfini son Akeela da mujaheed ne?duk son da mujaheed kema Akeela tunda ita batason shi aiduk zance ne.
Banga dalilin da zaisa ayi abinda za'a zo ana danasani ba,kinga kiwuce kiban waje.

Cike da bacin rai mahaifiyar Akeela ta wuce flat dinta tare da matsananciyar bacin rai.
Da daddare kuwa Guggo Laure tasa aka kiramata Alhaji Sani da Alhaji Mansir nan tazauna taratsa su tare da shirya musu karya wai Galadima ya nemeta akan yanaso a hada Akeela da Sauban aure.
Sosai sukayi murna duk da cewa sunsan maganar mujaheed da Akeela, Alhaji Mansir yace"Amma hajiya kinmanta da maganar mujaheed da Akeela ne?
Cikin sauri Alhaji Sani ya katseshi.

"Haba Mansir meyasa kake hakane?neman alfarma fa wan mahaifiyar mu yayi kan yanaso a hada jikinsa da jikanta aure,ba Kuma don komai ba sai don karfafa zumuncinsu to mezesa ayi haka?
Guggo Laure tace"Hmm rabu dashi Sani kaji,nan dai ta sallamesu.

Akwana a tashi babu wuya inda Allah yakawo mu yau Friday,gabadaya family din Galadima suna MAIDUGRI idan kacire matan Adda Labeeba da Adda Maryam.
Abbie yazo tare da kaf iyalensa,haka kuma Mommy ma sunzo dama da Abbie da Abba ne suke zaune a kd.

Zaune suke a parlon Galadima gabadayansu,bodejo, Daddy,Abbie, Abba,Baba Hasheem.
"Alhaji kunason shiga hakkin saudan da yawa,yanzu fa lokaci ne na kowani dan Adam nada 'yancin kansa Amma tunda kun rijayene shikenan Allah yasa hakan shiyafi zama alheri Amma sam ba'a yimana adalci ba,tayi maganar tana sake tsuke fuska.

Duk cikansu sauke nannauyan ajiyar zuciya sukayi,domin da bodejo bata amince ba to tabbas da akwai gagarumar matsala kuwa.

Murmushi ne ko wanne akan fuskansa, Galadima cike da jin dadi yace"Allah yayi miki albarka fadimatu.
Da Ameen su Daddy duk suka amsa.
Bodejo ta qanqantar da idanuwa tace"wallahi an shiga hakkina ba kadan ba saboda ni tuni Sauban na zaba masa matar aure,amma babu komai in matan shi ne nan gaba Allah yabashi.
Su Daddy suka sake amsawa da Ameen,duk da kuwa kowa yaso jin Karin bayani a wajen bodejo Amma gudun maido da hannun agogo baya yasa sai suka haqura.

Anan aka tsaida magana inda Galadima yayanke shawarar da kanshi zaije yawa kanwar sa wannan albishir din.
Tabe baki bodejo tayi tare da mikewa ta gyara zaninta tawuce ko sallama batayi musu ba.

Abba ne yasauke ajiyar zuciya yace"Yaya taya zamu sanar da Sauban wannan batun?kaga yaron nan yanuna bayason wannan abin tunfarko.
Daddy yace"yakuwa zaiyi auren biyayya shine abinda zaiyi ko kuwa Sadeeq?

Abbie Wanda koda yaushe fuskansa baya rabo da murmushi yace"Allah yasa hakan shine abinda yafi alkhairi.
Sunji dadin addu'ansa.

Nan suka kammala tattaunawan su sannan suka miqe.

Zuhra ce kwance akan kujeran Ammi ta lumshe idanuwanta saboda tsananin ciwon da kanta ke mata,sosai jikinta yadauki zafi alamar zazzabi nason saukar mata.
Yaran gidan gabadaya suna wajen Ummie don Ummie macece meson yara sai dai tsakaninta da zuhra sai a hankali.
Ammi ce tafito daga kitchen hannunta rike da wani plate tayo inda zuhra ke kwance,zama tayi a gefenta sannan tadauki kanta tadora akan cinyar zuhra.
"Subhanallah zuhra ai ba ciwon kai kadaine ke damunki ba ga zazzabi nan a jikinki, tashi kisha wannan fruit salad din.

Batare da tayi musu ba tamike,wani irin Sara mata kan yayi da qarfi,hannu takai tare da kama kan,jijiyoyin kan sun firfito.

Sake rikicewa Ammi tayi domin sosai Allah yadora mata son zuhra tun sanda Ummie ta haifeta tare da wani burinta akan zuhran.

Sanyayyan muryanta tabude a hankali,muryan inbanda rawa babu abinda yakeyi tace"Ammi ki Kama mun kaina inajin kamar zai fashe.
Kama mata kan Ammi tayi tafara yimata addu'o'i a hankali wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita.

Ajiyan zuciya Ammi ta sauke tare dajin wani tausayin zuhran a ranta.
Samun gefen ta tayi ta zauna tana duban kofar parlo tare da amsa sallamar da akayi.

Kareem ne yashigo fuskar sa dauke da murmushi dama shi mutum ne wanda baya rabo da murmushi.
"Barka da gida Ammi,yafada tare da rissiniwa.

Cike da fari'ah Ammi tace"A'ah Kareem har kadawo daga airport din?
Kareem yace"Ea Ammi nadawo don sai da natsaya ma har jirginsu yatashi sannan nataho.

"Allah sarki Allah YAKARA muku dankon zumuncin nan naku da kaunar juna Kareem anfa gode,angode sosai.
Dariya Kareem yayi yace"Haba Ammi tsakani na da Sadauki ai babu haka, bari naje gida hajiya tanata kirana.

Ammi tace"tohm Allah yayi albarka ka gaisheta,kace inanan zuwa,anfa gode.

Fita yayi tare da satan kallon inda zuhra ke kwance,duk da yaso yaga fuskanta Amma Allah baibashi sa'a ba.

Da daddare yaran gidan duk suna sashin bodejo harda zuhra.
Bodejo tadubi zuhra tare da kyabe baki tace"waike yarinyar nan lafiyanki?tundazu kiketa yatsina ko bakijij dadi ne?
Shiru zuhra tayi tare da sake lumshe idanuwanta.
"Yarinyar nan haryanzu wannan shegen miskilancin naki yananan,nidai keda saudan bansan wanda yafi wani wajen miskilanci ba.
Gabadaya yaran parlon suka sanya dariya,maimoon tace.
"Bodejo bafa saudan ba, Yaya Sauban.
Bodejo tace"Toh uwar feleke,ni ina ruwa na,haka na iya haka kuma zan fada.
Murmushi Galadima yayi yace"zuhra zo nan kinji.

Mikewa zuhra tayi a hankali kamar wacce kwai ya fashe ma a ciki ta nufi inda Galadima yake ta zauna a gefensa tace"granny mezaka bani na dadi.
Duban Laila Galadima yayi.

"Zonan Laila,jeki kitchen din bodejo saman fridge dinta zakiga bakar leda ki daukomin.
Zuhra batasan sanda wani murmushi ya subuce mata ba jin amfani hakar leda.

Daga murya Galadima yayi yace"ki kuma zo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login