Showing 12001 words to 15000 words out of 103469 words

Chapter 5 - GALADIMA FAMILY Complete Hausa novel

07 Sep 2024

6875

tashige,koda tashigo bodejo bataji shigowanta ba tana kitchen itada nana mai aikinta itama dattijuwa ce suna abincinsu ita da Galadima don suna da diabetes.
Shiyasa bataji shigowar zuhran ba,can bedroom dinta tashige tare da sanya key tafada kan bed tana dafe kirji,gabanta banda dukan uku uku babu abinda yakeyi,tadade anan kwance zuwa can tamike tashiga toilet don dauro alwala.
Bata jimaba tafito koda tafito kunna dum light tayi ta shimfida praymat ta tada sallah.
Koda ta idar zama tayi har akakira sallahn isha'i tayi sanna tabude bedside drower dinta tafito da cake da doughnut wanda mommy tamata kafin su koma,cake uku ta dauka doughnut biyo,tabude dan fridge dinda ke cikin dakin ta dauko lemon mountain dew.
Kan bed din takoma tahau tare da dauko phone dinta tashiga tiktok,da videon wannan yarinyar da ta shahara a duniyar tiktok tafara cin karo,wato Aakeelah Mancy don tashi take amfani,bude videon zuhra tayi nan taciddata taci kitson attached,tana sanye da riga da wando murna takeyi tayi tanama fans dinta albishir din cewa ankusa samata rana,sai ihu da tsalle take .
Dan siririn tsaki zuhra taja kasa kasa a ranta tace"Kai wannan yarinyar ta cika rawar kan tsiya.

Bodejo kuwa sai da sunacin abinci hankalinta yadawo jikinta cewa su Zuhra fa basu dawo ba tun wajen biyar da suka fita,dai dai Sauban yayi sallama.
Galadima da bodejo suka amsa masa idanuwansu na kansa cike da tsantsar soyayyan sa a zuciyoyinsu, cike da zolaya yace"Don Allah tsofaffin nan kada kucinye ni batare da nima naga 'yayana da jikoki na ba,ku gwara daku don da alama har tattaba kune zaku gani.
Dariya suka sanya bodejo tace"Ungo nan,tayi maganar tana aika masa da daquwa,murmushi yayi tare da jan kujerar Galadima ya zauna,bude warmer din yayi yazuba lafiyayyen dambun accan Wanda yaji kayan ciki tare da vegetables.
Duban shi Galadima yayi yace"ai shiyasa kaji muka damu dakayi auren kaima shiyasa muka zaba maka mata.
Dan hade face yayi yana Kai lomar dambun bakinsa.

Murmushi kawai Galadima yayi yana girgiza kansa don tabbas yasan cewa Sauban biyayya kawai yake kokarin yimusu amma batare da yanason yarinyar ba.

Galadima yace"munyi magana da mahaifinka kan zasuje gidan Laure wajen Sani a tsaida ranar aurenku....cikin sauri Sauban yadago tare da sauke ajiyar zuciya.

Dan yatsine face yayi cike da aji da natsuwa don kowata macen albarka yadubi Galadima yace"please Galadima kada asa ranar nan kusa nida so samune ma asa nan da two year's.

Wani kallo Galadima yayi masa irin na yhu re not serious dinnnan,budejo kuwa dariya tayi.
Sauban yace"bakace komai ba Galadima.

Galadima yace"kabari anjima sai kaje wajen mahaifinka ka tuntubeshi abinda yace shikenan.
Wani wawan ajiyar zuciya Sauban ya sauke yace"ai idan nayi magana kamar nayi rashin kunya ne inhar nayari Daddy da zancen.

Murmushi Galadima yakuma saukewa a karo nabiyu yasake cewa"Kaje kasamu Hasheem kayi maganar dashi.

"Huhhhhhh wannan tsohon sam bazai ganeba, Sauban yafada a ransa yana share gumin dake keto masa duk da kuwa AC dake a wajen.

Koda suka kammala cin abincin mikewa Sauban yayi yamusu sai da safe, bodejo tace"kabiya sashin Aisha katuromin Zuhra.
"Hmmmm kawai Sauban yace yafita kai tsaye apartment din Ammi yanufa,da 'yar siririyar muryansa yashiga parlon da sallama,babu kowa sai Mashahuda tana waya,ganin shi yasa takatse wayar tafara tsilla-tsilla da idanuwa,sake hade face yayi don yana sane dasu.
"Ke ina yarinyar nan?sosai Mashahuda cikin rudewa tace"Tatafi apartment din bodejo,don tagani wanda yake nufi.
Harara ya zabga mata tare dayin kwafa yace"zanyi maganin ki soon,yana gama fadar haka yanufi corrridor dinda zai sadashi da parlon Daddy don yasan Ammi nacan.

*******^^^^^^^******

Cikin muryan kuka take magana"wallahi hajiya ina sonshi nidai gaskiya ayi duk yanda za'ayi aga wannan auren baiyuwu ba tsakanin shi da wannan yarinyar,don ni natsaneta kodan fans dinda takedashi a tiktok.
Wacce aka kira da hajiya na duba sai karkade kafa takeyi,face dinta murmushi kwance daga ganinta kasan idanuwan ta kyar suke.

"Haba Rammat to meye kuma abin kuka?nimafa inaso ki aure Sauban don yanzu shine tauraron sa ke haskawa, Mom tayi maganar tana dafa kafadar Rammat.

"Hajiya gaskiya duk yanda za'ayi ayi don ganin Rammat tashigo cikin GALADIMA FAMILY,yanda kika shiga kika fita harnima nashiga to itama tashiga,kinsan kuwa nan da 1week Sauban zai koma Malaysia akan sun daukeshi aiki,Mom tayi maganar.
Ai dasauri wacce suka Kira da hajiya tadubi Mom tace"Wai Rabi dagaske kikeyi?kinfasan burina baiwuce Koda yaushe ku aure manyan mutane ba kushiga dangina dana ubanku ana girmamaku,tuntuni nayiwa Rammat sha'awar auren yaron nan,Ashe makirar Laure tarigani hada nata tuggun?hmmm nasan Laure farin sani sai dai ita batasanni ba batasan koni wacece ba,amma muje zuwa a sannu zanyi maganinta.
Ki kwantar da hankalinki Rammat,insha Allahu sai kin aure yaron nan Koda kuwa zakiyi kishi da wancan kodaddiyar yarinyar ne,tuni zamuyi waje da ita bayan auren.

Rammat tace"A'ah hajiya ni gaskiya bazan iya zama da wannan munanan yarinyar ba,natsaneta.
Mom tace"muma bamu fata insha Allahu bazakiyi zaman kishi da ita ba aikinfi karfinta wallahi.

Hajiya tace"hmmm ku yarane bazaku gane me nake nufi ba amma a hankali zanyi muku bayani, Rammat ki kwantar da hankalinki indai Sauban ne kisa aranki kinsame ahi kingama.
Dariya Rammat da Mom suka sanya cike da farin ciki.

_TAB CAKWALKWALIN CAKWAKIYA KENAN SAUBAN KAIKAM KAGA TAKANKA_🥴 _YANZU FA WASAN ZAIFARA KUDAI KUCIGABA DABIN ALQALAMIN OUM ÃJMÃL._

Xahratty CE🥰
Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️

22/2/23.
[3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳

Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now

*_GALADIMA FAMILY_*

Page 08

_Bismillahir-rahmanir-raheem._


____Sai bayan sallar la'asar Taufeeq da Kareem sukaje daukoshi a airport yadawo gida cike da nasara inda gabadaya farfajiyan gidan GALADIMA FAMILY cike yake da yara da jikoki don taryan Sauban.
A hankali motan tashigo cikin farfajiyan gidan bata tsaya ko inaba sai parcking space,su duka ukun suka fito daga motan kowanne dariya ne kwance akan fuskar sa.
Yaran gidan ne suka fara tsalle da muryan dawowan sa inda suketa tururuwan yimasa barka da zuwa.
Yassir babba ne yajawo trolly bag din.

Uban gayyar kuwa direct wajen Ammi yanufa kaitsaye murmushi kwance akan fuskar sa ya furta "Oyoyo sweetheart yayi,yayi maganar tare dayin hugging nata.
Murmushi kwance akan fuskanta tadan bubbuga bayansa tace"Oyoyo son hope kadawo lafiya?
"Alhamdulillah sweetheart ! Ya ambata.

Nufar bodejo yayi da niyyar yin hugging dinta itama,da sauri taja baya tare da mere baki tace"Allah yatsareni da wannan dabi'ar yahudawan inazan iya wannan shedancin saudan?boko yagama lalataka gabadaya😏

Murmushi su Ammi suka sanya.
Nufar Ummie yayi fuskar sa cike da fari'ah ya miqamata hannu don musabaha,itama miqamasa tayi don gaisuwan su kenan muddin zasu hadu.

"Ummie na yaushe kuka shigo Mai din?ainazata sai gab azumi zaku iso? dariya Ummie tayi tace"aikuwa wannan zuwan munzo da wuri amma jibi zamu koma saboda school dinsu Laila da Nihal.
Gyadakai yayi tare da murmushi yanufi Mom tare da rissinawa ya gaisheta itama ciki da fari'ah ta amsa yanufi mommy,hannu ta miqa masa suka tafa duk dashi a kunyace yake.
Bodejo tace"Uhm uhumm lalacewa yakai lalacewa yanzu ke hauwa ko kunya bakiji ba?kika miqama kusan danki hannu kuka kashe?

Gabadaya wajen dariya aka sanya,a zahiri kuwa Aunty hauwa bata wuce shekaru uku zatabawa ya Sauban ba,Yan matan gidannan suka fara gaida cike da girmamawa.
Zuhra kuwa tana gamai gaisheshi ta sunkuyar dakai tamkar wata munafuka,akanta ya tsaida idanuwan sa sai dai kallo daya yamata yakauda kai.

Dunguma sukayi suka shiga cikin parlon Galadima don da alama yau anan za'ayi dinner akuma taba hira.
"Sweetheart Inasu Daddy da Galadima?

Ammi tace"Basunan sunje masallaci kuma daga can zasu wuce jana'izar ladan don Allah yamasa rasuwa dazu wajen 3:30.

"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un yarasu? Ah muma zama baikama muba yakamata ayi jana'izar damu ko friend?
Kareem da Taufeeq suka mike, Ummie tace.

"Haka zaka kuma fita babu abinda zakasa abakin ka?

Bodejo ya alhamis ina azumi ko kin manta ina azumin litinin da alhamis?yaqarisa maganar yana fita.
A kaikace bodejo ta makama bayansa harara tace"Oho maka nina manta ma kanayin wani azumi.

Bayan sallar isha'i gabadaya ahalin sun hallara a hall din cin abincin wanda yatsaru iya tsaruwa fada kuwa bata bakine sai dai kai maikaratu ka kiyasta irin tsaruwar Galadima family.
Bayan Sauban yagama gaida iyayen nasa maza sun taba 'yar barkwanci da hausa shida Galadima anan akafara cin abinci harda matayen.

Babu wanda yasake magana sai zuwa can ne mommy talura babu zuhra awajen cin abincin,gyaran murya tayi tare da duban nihal tace"Nihal ina zuhra ne?gashi anacin abinci batanan,tashi kije ki kirata.

Miqewa tayi zata tafi Mashahuda tace"Bari nakirata a waya muji mommy,Kiran wayar zuhran tayi ba'a dau wani lokaci ba akayi picking.

Da yake a handsfree wayar take cikin sanyin muryan ta maicike da natsuwa tare da shagwaba tace"Hello Aunty Mashahuda inayini?

Mashahuda ta amsa tana me cewa"kizo dinning cin abinci anata jiranki fah,cikin shagwababbiyar muryan ta tace"Aunty Mashahuda na qoshi nikam shiyasa ma banzo cin abinci ba.

Har Mashahuda zatayi magana Ammi ta amsa wayar,cikin muryan rashin wasa tace"Me kikaci?kiyi maza kizo kici abinci ina jiranki ne.

Tana gama fadar hakan ta datse wayar.

Mommy tayi murmushi tace"Zuhra hmmm batason cin abinci kwana biyu ina lura da ita.

Cin abincin suka cigaba dayi.

Ko 5minute ba'ayi ba tashigo tare da sallama cikin sanyinta,duk dagowa sukayi suna dubanta, Sauban kallo daya yamata sai dai kayan jikinta sun mata kyau,sanye take da riga da skirt English wears,long skirt mai budewa tundaga kugu sai rigar iya kugu mai gajerar hannu kalar ruwan hoda,hula ne akanta black sai black din flat shoe wanda suka hade da fatarta kalar half-caste sukayi mata kyau sosai hannunta riqe da wayarta iPhone 8+ da ita da Nihal da Laila wayarsu iri daya.

Amsa sallamar sukayi,nan tafara gaida kowa tare da jan kujera tazauna.
Bodejo tace"kawai saboda bakin hali saikishige kurya kiqi fitowa?akan wane dalili?
Turo mouth gaba tayi tace"Kai bodejo uhumm,awara ta zuba da egg source tare da tsiyayan kunun gida tafara sha.
A lokacin su Daddy suka kammala harma da Galadima suka miqe.

Suma su Sauban basu wani jimaba suka tashi, dama a takure take saboda irin kallon da Kareem ke mata a sace.
A hankali kowa yadinga tashi duk aka watse yarage daga Zuhra,Laila,Nihal da maimoon.

Wajejen 9:30 kowa yana apartment dinsa inda su Zuhra ke apartment din Ammi dakin Laila.
Sauban ne ya shigo bedroom din Ammi,cike da girmamawa yace"Sweetheart kenan haryanxu baki baccin wurin ko?duk da kallo daya zakama fuskansa zaka fahimci yana cikin damuwa.
Kura mishi idon Ammi tayi tare da aje hisnul muslim din hannunta akan side drower tace"Son lafiya?naga kacanza ne bakamar sanda kadawo cike da farin ciki ba?
"Sweetheart Daddy p suka sameni akan wani magana wanda Allah yasani tun farko nace banason yarinyar amma sunce umarni suke bani kan na amince inhar sun isa dani,bama kaman Daddy sweetheart bakiga yanda yakeyi ba.
Shikuma Galadima harda rokona wai yana gudun lalacewar zumuncin su day rigimammiyar tsohuwan nan hajiya Laure.
"Wallahi muddin akamin haka ba'a kyauta min ba sweetheart don sam yarinyar batamin ba,yaqarasa maganar tare da murza forehead dinsa da babban yatsan hannunsa.

Ajiyan zuciya Ammi tasauke tace"Amma basun fadamaka dalilinsu na umurtanka da auren ba?
Sauban yace"A'ah sweetheart kawai sunce sunyimin mata sannan umarni suke bani wai inhar sun isa, Galadima hardamin kuka gabadaya sun daddaure ni,mema sanyi a ciki shine Abbie, yanzu yazanyi da rayuwata?wallahi sweetheart banason yarinyar nan please kisa Baki.Yayi maganar idanuwansa nasake jajazur.

Ajiyan zuciya Ammi tasauke tare dayin murmushin da baiwuce iya labba ba don Allah yasani har zuciyarta bata aminta da aurensa da Akeela da akeso a hada ba amma bazata hanashi yima iyayensa biyayya ba,kuma bazatayi sanadin abinda zai bata zumunci ba.
"Kaine kajawa kanka Sauban tun tuni ake maka maganar kafito da matan aure amma kaqi to ya kakeso ayima nibazan goyi bayan kaqi yima iyayenka biyayya ba kacigaba da addu'ah Allah yasa hakan shi yafi alkhairi.
Shiru ya ratsa na wani lokaci,mikewa yayi yace"shikenan sweetheart nizan tafi na kwanta ina furar da kika mun magana?
"Yananan a cikin karamin fridge dincan.

Nufar fridge din yayi yabude yadauki furar sannan yamata sai da safe tare da jan kofar yabar bedroom din,girgiza kai kawai Ammi tayi tacigaba da duba hisnul muslim dinta.

Washegari zuhra zaune take a qasa kusa da Abbie tana saurarensa,gefensa Ummie ce fuskanta kadaran kadahan sai ya Taufeeq da yake zaune kusa da Ummie.
"Kinji mamana anan zaki cigaba da zama saboda munyanke hukunci dasu Daddyn ku kan zaki shiga University of maidugri ne tunda kindage bakison zarian koh?baki kewar mune?
Dago dararan idanuwan ta tayi tadubeshi cikin cool voice nata tace"ina kewanku mana Abbie musamman ma kai dasu maimoon da mommy,amma nafison nandin,takarisa maganar muryanta na rawa.

Sosai Abbie yaji wani irin tausayinta saboda yasan badason ranta zata zauna anan ba amma saboda mahaifiyar ta tazabi nisantar su.
Cike da barkwanci ya Taufeeq yace"Ai Abbie tagaji da ganinmu ne musamman ma ni.
Turo mouth tayi tace"Kai ya Taufeeq wallahi niba haka nake nufi ba kawai dai....tayi shiru batare da takarisa ba,kasa² take duban Ummie wacce take lallatsa wayarta tamkar bata a wajen,ajiyar zuciya mai karfi ta sauke tare da rintse idanuwan ta.
Dafa kanta Abbie yayi yace"shikenan Allah yayi miki albarka kinji Allah yabada sa'a akan KARATUN da zakiyi 'yar jarida,nan yashiga yimata nasiha masu shiga jiki,wanda har sai da zuhra jikinta yayi tsananin sanyi,duban Ummie yayi yace.
"Ummien yara to kema kiyi naki nasihar mana.
Barin lallatsa phone din tayi tace"Allah yabada sa'a ubangiji kuma yamiki albarka.Tana gama fadar haka tamike.
Duk cikansu da kallo suka bita,sosai zuhra jikinta yayi sanyi.

Shima ya Taufeeq 'yar nasihar yayi mata tare da dan zolayarta kamar yanda yasaba.

Bayan kwana daya Abbie,Abba,Ummie,mommy,ya Taufeeq, Laila, Nihal suna shiga motoci inda Ummie, mommy,Abbie, Abba suka shiga mota guda Abba ne kejan motar sai dayar ya Taufeeq, Laila, Nihal dasu maimoon inda ya Taufeeq kejan motar sosai zuhra ke kuka na kewarsu don tunda take ko hutu bata taba zuwa ita kadai ba,inda Abbie yaturama da ya Sauban kudin shopping dinda za'a ma zuhra don before azumi zasu fara attending lectures,shiko ya Sauban yamaida masa yace ai za'ayi mata duk siyayyan daya kamata.

Kowa haka ya watse cike da kewar mutanen kadunan.

*_IDAN NAGA RUWAN COMMENTS ANJIMA NASAKI DAYAN PAGE DIN😃._*

Xahratty CE🥰

Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️.

19/2/23.
[3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽‍🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽‍🦳

Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now

*_GALADIMA FAMILY_*

Page 10

_Bismillahir-rahmanir-raheem_

_____Ayau Saturday ne kuma su zuhra zasuyi jamb dinsu,tun wajen 7:30 tatashi tayi duk abinda yakamata.
Don Daddy yace 8:00 zai dauketa su tafi wajen bodejo taje don mata sallama ita da galadima a parlon taciddasu su duka sanye da medical glass suna kallon tashan aljazeera.
Amsa sallamar da tayi sukayi suna maida hankali akanta,duban tsanaki bodejo kemata sosai take mamakin girman zuhra don zakayi tunanin takai shekara 18 koma 20 saboda yanda Allah ya halicceta da diri sosai ko ina tubarkallah Masha Allah.
Sanye take da Dubai gown Army Green sai white flatshoe duk da cewa face nata babu makeup sai dai tayi kyau sosai.
Gaishesu tayi cike da kulawa suka amsa mata,bodejo tace"Har anfito za'a tafi?
Daga kai zuhra tayi tace"Eah bodejo zanje wajen Daddy ne mutafi.

Galadima yace"toh Allah yabada sa'a ubangiji yasa kifito da 300 score.
Dariya suka sanya gabadaya zuhra tace"Ameen my Galadima na tafi.

Fatan dawowa lafiya suka mata sannan suka fita, apartment Baba Hasheem tafara shiga, Mom tasamu a kitchen don haka tafara gaisheta tana tambayar Baba,cike da fari'a Mom ta amsa anan take sanar da ita baima tashi daga bacci ba.
Sanar mata tayi da yanzu zata tafi wajen exam din jamb idan ya tashi ta gaisheshi.
Fatan alheri Mom tamata.

Koda tashiga apartment din Ammi a dinning ta taddasu itada Daddy,cikin shauki takarisa garesu face nata dauke da yalwataccen fari'a.
"Good morning Ammi, good morning Daddy.
Cikin fari'ah suke dubanta, Ammi tace"Morning my zuhra antashi lafiya?
Daddy yadubeta yace"ah lallai mamana har anfito ne?
Murmushi tayi tace"Ea.
"To kizauna kiyi breakfast tare da Daddyn naku kafin shima Sauban yafito.
Sosai kirjin zuhra yabuga saboda batason haduwa da Sauban din.
Cikin sauri ta girgiza kai tace"A'ah Mom nayi breakfast Alhamdulillah bari naje dakin Aunty Mashahuda nayi mata bangajiyan jiya.

Ammi tayi murmushi tace"ai bata tashi daga bacci takoma gashi ansamu hutun hadda.
Cikin sanyin jiki zuhra tajuya don komawa parlon ta zauna, clashing sukayi da Sauban wanda fitowanshi kenan,suit ne a jikinsa blue black da covershoe black agogo kirara Gucci yake daura bakajin kamshin komai sai na perfume din da yasanya.
Hada ido sukayi da zuhra wani harara ya gallamata,itakuwa cikin sauri ta dukar dakai tana murguda baki a hankali tace"Ina kwana.
Ko amsawa beyi ba yasamu waje ya zauna,tare da gaisar da iyayen nasa.
Cike da kulawa suka amsa,Ammi tace"Son kanwarka na gaisheka.

Dan yamutsa face yayi sannan yace"Sweetheart banji bane hankali na na wani wajen,daganan sai ya cigaba dacin abincin sa.
Daddy da Ammi kuwa murmushi kawai sukayi,a gurguje suka gama cin abincin,mikewa Daddy yayi Sauban ma yamike. kaitsaye parking space suka isa inda Daddy yashiga gidan baya zuhra kuwa gaba tashiga.

Sauban ne yaja motan tare da sanya karatun alqur'ani na Abdullah Abba Zaria,zuhra kuwa a ranta tace"wannan mutumin mayen karatun Abdullahi Abba ne idan anbibiya ma baisan shi ba.
"Idan ni bansanshi ba aike kinsanshi koh?taji muryan Sauban yajefeta da wannan tambayar a rikice zuhra tadago tana dubansa.
Don sam batayi zaton karatun zucin da takeyi yafito fili ba,idanuwanta gabadaya ta diddilo waje tana duban Sauban.
Shikuwa ko kallon inda take beyi ba yacigaba da driving dinsa.
Koda suka kariso center da zatayi Jamba din Daddy dakanshi yashiga yakaita don har anfaffara shiga hall din.

Nan Daddy yace tanatau tamaida hankali tayi exam din cikin nutsuwa,cike da girmamawa ta amsa masa da toh.

Sai wajen karfe 11:30 su Zuhra suka fito daga wajen rubuta Jamb din,cike wajen yake da maza da mata,wasu sa'o'inta wasu sungirme mata wasu kuma ta girmesu sai hayaniya yake tashi a wajen cikin sanyin ta itakuwa take tafiya a kofan gate din center tatsaya tana tunanin ta inda zata koma gida gashi ita bawani sanin maidugri tayi ba.
Hankalinta gabadaya yakoma gida saboda yanda taga anata zuwa daukan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login