Showing 18001 words to 21000 words out of 103469 words
kuwa Akeela ce ta tasata agaba wai ranar da akasanya yayi tsayi da yawa ai 'yan kauye ne kecika ranar aure ita gaskiya a rage.
Guggo Laure kuwa sai lallashinta takeyi takuma tabbatar mata da cewa suna zaune ma Sauban din da kanshi zaizo yana neman alfarmar a rage.
Dan yatsine face Akeela tayi cike da rashin jin dadi a ranta tace"Ni Guggo ina tsananin kishin sa ne wani irin zazzafan so nake masa,wallahi nida da yanda zanyi kan kada yaso ko wacce mace zanyi saboda ina tsananin kishin sa.
Dariya Guggo Laure tayi"mekike ci nabaka nazuba 'yannan?kisa a ranki zai soki kedai kidage da kissa da kisisina sannan ki tabbatar da kin jawosa a jiki ya zamana babu macen da yake gani a matsayin mace saike.
Dariya Akeela tayi tace"yanda kikajin nan Guggo kuwa sai dai nayi tsananin yarda dasu Suby su kansu zasu tayani shawo kansa.
Mere baki Guggo Laure tayi"Hmmm kesam bakisan sharrin kawaye ba koh?ina gargadinki Akeela amma sam bakiji.
"Wallahi Guggo basu da matsala don kawai bakisan su bane domin duk suna tsananin sona wallahi.
Murmushi Guggo Laure tayi tace"Yaro yaro ne to shikenan Allah ya kyauta.
Xahratty CE🥰
Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️
25/2/23.
[3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽🦳
Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*
Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now
*_GALADIMA FAMILY_*
Page 13/14
_Bismillahir-rahmanir-raheem._
______Ummie abin duniya duk yataru ya mata yawa taje wajan Amma don bata hakuri amma gabadaya taki saurarenta tasake jaddada mata cewa muddin bataja'yarta a jiki ba to tamance itama tana da uwa a raye.
Kiran number Aunty Zainab tafada mata duk yacce sukai da Amma,itama fir tarufe Ido tama Ummie sol.
Tsakanin Ummie da hajiya Zainab tazarar shekara daya da rabi ne.
Haka dai Ummie tadawo gida jikinta sam babu kwari tarasa wanda zataje wajensa suyi magana taji dadi ita ba kawaye ba,a yanzu duk wanda zataje wajensa neman shawara kara mata takaici zasuyi,banda huci babu abinda takeyi a fili tafurta"Natsaneki Zuhra tabbas bacin nice dakaina na haifeki zan iya tsine miki saboda kina daf da rabani daduk wasu masoya na,na haifawa kaina masifa na haifawa kaina jaraba?
Sosai hankalin ya Taufeeq yatashi don yana gaf da shigowa parlon yaji zan tuttukan da Ummie keyi, idanuwansa sun kada sunyi jajazur juyawa yayi yafasa shigowa parlon,kaitsaye bq dinsa yanufa a daddafe, Aseef sai masa magana yake amma Ina baiji ba.
Da harara Aseef yabishi a fili yafurta"Idiot"cikin murya kasa kasa.
******
Zuhra ce cikin shagwaba da sangarta take latso wasu hawaye mere dan mitsitsin mouth lip dinta tayi tana muttsike Ido cikin muryan son kuka tace"Toh yanzu Abbie idan kuntafi yaushe zaka dawo?ni wallahi bangaji da ganinka ba fah.
Dan dariya Abbie yayi tare da shafa kanta yace"zamu dawo azumi mana kinmanta azumin saura 1month?so insha Allah I think sai lokacin zamu sake zuwa.
Daddy ne suka kariso shida Abba da Baba Hasheem, Daddy ya dubi zuhra yace"A'ah mamana kema yau zaki koma ne bamu da labari?
Dan sinnar da kai zuhra tayi cikin girmamawa tana wasa da yatsunta tace"A'ah Daddy narako su Abba ne da zasu tafi.
Dan murmushi sukayi gabadaya Abba yace"hmmm kya fadi gaskiya,Yaya kuka take nema tamaka koh?yakarasa zancen cikin zolaya.
Dan rissinawa tayi tadauki ledan dake gefenta tamika ma Abbie tace"Abbie gashi abaiwa Ummie na da mommy,akwai sweet da chocolate na maimoon da Ateek.
Abbie ya amsa yace"toh shikenan Allah yamiki albarka.
Da Ameen ta amsa tare da matsawa saboda gabadaya sun nufi mota daya motar Daddy kenan da ita zasu fita, Baba Hasheem ne ke driving gefensa kuma Abba ne,sai baya Daddy da Abbie cike daso da kaunar junansu suka fita,zuhra natsaye har Baba mudi yabude musu gate suka fice,hawaye ne ya zubu mata da sauri tasa hannu ta goge,saboda shigowar Aunty muneefa datagani da wasu 'yanmata biyu.
Abangaren Abbie shima runtse idanuwa yayi yabude tare da sauke ajiyar zuciya yana mejin tsananin tausayin diyarsa duk Daddy na lure dashi shima girgiza kai kawai yayi,kaitsaye motar airport tanufa.
Zuhra murmushi a face dinta tatare Aunty muneefa.
"Aunty muneefa barka dama kece?muneefa na murmushi tace"Eah zuhra kwana biyu bananan ina school shiyasa.
Haka kawai Zuhra taji sam wacce suke tare da muneefa batayi mata ba don haka ko kallonta batayi ba,a gefen ma haka ne don lokaci daya taji tsanar zuhra ta dirar mata,sake shaqa tayi a dalilin ko inkular da zuhran tanuna mata,yarinya qarama da sanabe,tafadi hakan a ranta.
"Dawowata kenan yanzu nabiya gidan Guggo Laure shiyasa ko hutawa banyi ba,murmushi zuhra tayi.
"Eyya Aunty nima apartment dinku zanshiga don ko jiya danazo gaida Mom batanan.
Muneefa tace"ok muje koh?
Dayar ce tayatsine face"Muneefa bari naje nafara miqa gaisuwa ta ga Ammi kafin nadawo.
"Kai Allah don Allah kizo muje mu warware gajiya dududu yaushe muka shigo?dayarl budurwar tafAdal
Zuhra kuwa ko sauraren su batayi ba tanufi sashen Mom,a kaikace budurwar ta dalla mata harara.
Muneefa tace"Don Allah rabu da ita Suby kinsan Akeela da rawar kai.
Zuhra kuwa koda tashiga sashen Mom tagaisheta sosai Mom din taji dadi don Allah yadora mata son zuhra tun sanda Ummie ta haifeta sannan takema Aseef sha'awar auren ta.
Tana gafda shiga apartment din Ammi Akeela tafito, Zuhra dauke kai tayi kamar bata ganta ba itako Akeela wani banzan kallo ta watsa mata.
Koda zuhra tashiga kai tsaye ta nufi kitchen don tasan Ammi tana can,ilaikuwa sunata aiki itada Aunty Mashahuda da maid dinta Amina.
Murmushi kwance a face din Ammi ta tarbe Zuhra,dan rissinawa tayi ta gaishe da Ammi.
Dan turo mouth tayi alamun shagwaba tare da karyar da wuya tace"kai Aunty shine ko ki aiko nazo nataya aikin?nasan Daddy akema abin shan ruwa.
Hararar wasa tawatsa mata sannan tace"Aiba sai nace kizo ayiba keda kanki zakizo"takarisa maganar tana dan murmushi.
"Ammi wallahi namanta Daddy yana azumi saboda naje raka Abbie ne shiyasa duk na shagala.
Kallon ta Ammi tayi fari'a kwance a saman fuskarta tace"Don Allah kirabu da wannan Auntyn taki,aikinma da sauki don mesa ana masa girke girken bashi nan.
Dan dariya kadan zuhra tayi batare da tayi magana ba tafara yanka cabej din dake kan mable din.
Mashahuda tace"Hmm ai Yaya akwai shi da iyasa aiki ni wallahi tausayi matar sa kebani.
Sallaman su muneefa ne yasasu juyawa gabadaya,kallo daya zuhra tamusu tadauke kai saboda ganin yarinyar nan tadazu.
Da murmushi Akeela tamatso kusa da Mashahuda tace"sis kawo in tayaki goge carrot din,dan yatsine face kadan Mashahuda tayi tare da dan sakin yaqe tace"No kada kidamu munkusa gamawa ma ai tunda ga zuhra na gyara cabej.
Akeela badon taso ba haka tahakura,ita kuwa Suby gabadaya hankalin ta yakoma kan zuhra faffadan kugunta kawai take kallo( _acewarta_).
Muneefa tace"Sis muje kada kuyi magrib, Ammi tasaki murmushi tare da duban Akeela"Akeela ya hajiya maimunan take?
Cike dajin dadi tace"wallahi tananan lafiya mommah.
Murmushi Ammi tasake saki akaro na biyu tace"to don Allah kigaisheta mungude sosai.
"Ai babu damuwa mommah nima fa 'yar gida ce.
Ammi murmushi kawai tayi bata sake magana ba,muneefa tace"yee gaskiya ne Auntymmu, Allah dai yabar kauna keda ya SAUBAN!
A gigice zuhra tadago tana duban muneefa sai dai kowa hankalinsa baya kanta,wani mummunan faduwar gaba ta tsinci kanta a cikin jin an ambaci sunan Wanda batayi zato ba,a kaikai ce tasake duban Akeela da wasu second's zuwa can ta sauke ajiyar zuciya,aranta tace toni meye damuwa na?
Nanfa muneefa tafara magana"Ai wallahi bikin nan haba za'ayi abinda ba'a taba yiba sai ansan anyi biki na jinin Galadima auren ya Sauban ai dole muci uwar sabada.
Akeela tace"ai gaskiya za'ayi biki nagani nafada hmmm kudai Allah yakaimu lokacin, mommah muntafi tayi maganar tana ma Ammi bye bye.
Daga Zuhra har Mashahuda kallon mamaki sukabi Akeela dashi, Mashahuda tadubi Ammi tace.
"Cabdi wallahi Ammi kinsan da matsala Yaya Maison mace mai kunya amma jibi wacce aka bashi matsayin mata?hmm wallahi nidai bana son Yaya ya aureta sam,tayi maganar tana daga hannu tare da nuna iyakacin gaskiyar ta, sauke ajiyan zuciya Ammi tayi tace"please Mashahuda ni bana son kananun zantuka haba abar maganar.
"Hmm Ammi kema fa kinsan Yaya be dace da wannan yarinyar b....
"Allah Mashahuda zan saba miki,tayi maganar cikin muryan bacin rai.
Itadai Zuhra ko tankawa batayi ba tanata yanka cabej dinta,sai dai hakanan tatsinci zuciyar ta cikin bacin rai lokaci guda.
Hakanan taji tayi mugun tsanar Sauban din dashi da Akeela.
*******^^^******
Sosai yaqara gogewa da kyau yazama wani classic guy wanda ko a malysia ma 'yan mata rububinsa sukeyi.
Yarasa dalilin da yasa yake sake tsanar auren da ake nema a qaqaba mishi itakanta yarinyar bayajin zai iya aurenta duk da kuwa besanta ba.
Messenger sane yashigo office din yace"Sir kayi baki.
Duban CCTV camera dinda ke office din yayi yana duban mutanen dake Zaune a wajan office din nasa,maido da duban sa yayi ga massenger yace"Miracle who re those people?
"I don't know Sir,yayi maganar cike da girmamawa.
Dan girgiza kai Sauban yayi tare da cewa"Ok jeka shigo dasu.
"Ok Sir,yayi maganar yana fita babu jimawa yashigo da baqin.
********
"Boka so nake a sauko da auren lokacin da aka sanya na bikin nan wallahi yayi tsayi ita kanta yarinyar takosa ace tayi aure tahuta,bari kaji nifa so nake a mallake mana yaron ya zama na bayajin maganar kowa sai nawa,kai yazama mai taurin kan tsiya.
"Hahahaha,aka kyalkyale da dariya,wani dan wadan aljani ne wanda sam bayada kyan gani ko kadan kuma daga ganinsa baya da imani yace"
_BANADA LAFIYA FANS DON ALLAH INA BARAR ADDU'AN KU👏🏽_
Xahratty CE🥰
Lallai Alqalami 🖊️ yafi takobi🗡️
[3/21, 22:27] Xahratty (OUM AJMAL): 👨🏽🦳 *_GALADIMA FAMILY_*👨🏽🦳
Story&Written
By
*FATEEMA ZAHRA LAWAL*
Marubuciyar⤵️
A DALILIN'YAR TSINTUWA.
MIJIN ZAHRA.
DIAMOND LADIES ( Daukar fansa)paid book.
RUHIN AMRITA (FATALWA CE).
Now
*_GALADIMA FAMILY_*
Page 15/16
_Bismillahir-rahmanir-raheem._
PLS KUTAYANI DA ADDU'AH MASOYA ALLAH YAKARAMIN LAFIYA DON CIWO YASANI GABA SHIYASA KUKA JINI SHIRU KWANA BIYU BANJIN DADI, NAGODE SOSAI DA SAKONNIN GAISUWAR KU MUSSAMMAN MA KE *MAMAN HEELAL* KEDIN TA DABANCE.
_____Zuhra ce zaune a parlon Bodejo tana yimata massage,sallamar Baba mudi gateman sukaji a bakin kofan parlon,amsawa sukayi inda Bodejo tabashi izinin shigowa.
Cike da girmamawa ya rissina yace"Barka da warhaka Bodejo,inayini ina gajiya? fuskar ta kadaran kadahan tace"yauwa mudi lafiya Alhamdulillah ya kuma aiki? Baba mudi yace.
"Alhamdulillah! Dama wani yaro ne a waje yazo yake cemin don Allah nakira masa Fateema.
Cikin natsuwa Zuhra tadago tadubi Bodejo itama ita take kallo,maida dubansa tayi ga Baba mudi tace"Fateema kuma mudi?wa Fateema tasani a garin nan har zai aiko akira masa ita? Tayi tambayar cike da mamaki.
"Wallahi kuwa Bodejo bansan shi ba nidai yanata roqona kan nakira masa ita.
"Ikon Allah ko wanene haka oho?tashi kije kiji ko wanene.
Dan tsamm Zuhra tayi tare da dan bata face tace"nikam bazani ba Bodejo wallahi bansan shiba kawai ina zaman zamana ya wani kirani? Takarisa maganar tana kokarin shiga hanyan corridor din Bodejo,sakin baki Bodejo tayi tana duban Zuhra,kallon Baba mudi tayi tace"shikenan mudi kace tana zuwa.
Mikewa yayi tare da fita,murmushi kawai Bodejo tayi tana kokarin mikewa ne sai ga Mashahuda tashigo,dan gaida Bodejo tayi sannan tace.
"Bodejo ina Zuhra ne tundazu Shuraim yazo nemanta Baba mudi yace yazo ya kirata amma taqi fitowa.
Dan tabe mouth Bodejo tayi"Toh ni ina nasanin mata,bansan me take nufi ba,wanine shuraish?dan gwalo idanuwa Mashahuda tayi"kaji Bodejo kuma da bata suna bafa shuraish ba Shuraim ake cewa.
"Uhum kudai kuka sani da wani iyayi da sanabe abinda dai nafada shikika maimaita.
Rausayar dakai tayi kaitsaye ta nufi bedroom din Bodejo.
Koda tashiga kwance taga Zuhra sai daddanna phone nata take hankali kwance,ganin Mashahuda yasa tamike cike da fara'a a fuskarta tace"Aunty Mashahuda kece?
Hararar wasa ta zabga mata tace"kyace mana nice tun dazu mutumi yazo nemanki kina wulaqanta sa haba Zuhra menene haka?
"Aunty nifa bansan shiba bansan koshi wanene ba akan me zan fitan masa?shiyasa ma ban fitaba,takarisa maganar tana dan babbata fuska.
Itama Mashahudan bata fuska tayi tace"Lallai ma yarinyar nan kinci uwar rainin wayo to Shuraim ne yazo kitashi kuje ku gaisa mana.
"Shuraim! Zuhra ta maimaita sunan alamun bata ganesa ba tace"Aunty ni bansanshi ba.
Mikewa Mashahuda tayi tare da fita tace"idan kinje wajen ai zaki gane wanda nake nufi,takarisa mgnr tana barin dakin.
Tsuru tayi tana bin kofan da kallo tadau kusan 6 minute's a zaune kamar wacce aka dasa,zuwa can tasauke ajiyar zuciya tare da mikewa,closet din ta tabude taciro wata Dubai gown mai taushi wanda yaji wasu irin flower's maroon colour,sannan tasaka viel din tayane kanta dashi,flat shoe baqi tasaka batare da tamurza ma kyakkyawan face dinta komai ba tafito parlon, Bodejo ta taras a zaune tana kallon Africa TV 3 dan sunkuyar dakai tayi like munafuka sum sum tafice.
Cikin sanyin jiki take tafiya kamar mejin tausayin kasa acan gefen apartment din Ammi ta hango Mashahuda da wani don bata ganesa ba saboda ya juya mata baya,a hankali take tafiyar har ta isa inda suke zaune,sallama tayi cikin zazzaqar muryanta mai sanyi da dadi,da sauri yadago don jin muryanta.
Da mamaki Zuhra take dubansa a hankali tace"Yaya dama kaine? murmushi kwance akan fuskar Shuraim yace"Ea nine Zuhra.
Dan tsamm tayi tare da duban Mashahuda,mikewa Mashahuda tayi tare da duban Shuraim tace"bari nashiga na fito kafin ku gama gaisawa,sake fadada fara'a Shuraim yayi tare da cewa"Allah yafito dake lafiya Auntymmu,zuhr kuwa sakato tayi tana duban Mashahuda har tashiga parlon su,ajiyan zuciya ta sauke saboda muryan Shuraim da taji yana cemata ta zauna.
Karasawa tayi kujeran da Mashahuda ta tashi ta zauna,dukar da kanta tayi kasa tafara wasa da yatsun hannunta.
"Babu gaisawa ne Zuhra?Shuraim yace.
Cike dajin nauyi da kunya cikin sanyin muryanta tace"eyya ba haka bane wallahi yaya don Allah kayahakuri, inayini?
"Sai dana roka?yayi maganar still murmushi kwance saman fuskansa.
"Kayahakuri,tasake maimaitawa cikin sanyin muryanta.
"Lafiya lau Alhamdulillah ya kwana biyu?
"Lafiya lau wallahi.
"Ashe anata shirye-shiryen school ne?to Allah yabada sa'a Aunty Mashahuda take fadamun.
Zuhra tace"Ea anata shiri munkusa fara zuwa school tafada cike da murna da zumudi murmushi kwance saman fuskanta,daidai nan Baba mudi yafara wangale gate,hancin mota ne ta shigo kirar Corolla ( _da take bansan kan motoci ba amma motar daga gani medan tsada ce._ ) duk cikansu maida dubansu sukayi kan motar,shikuwa tun sanda yashigo gidan idanuwan sa ke kafe a inda suke zaune,sosai yaji zafin ganinta da wani,balle murfin motar yayi ya fito,dole idan zai shiga apartment din Ammi ta gabansu zai wuce,koda yakariso fuskar sa a sake yake dubansu,mikawa Shuraim hannu yayi sukayi musabaha tare da cewa"Barka da warhaka.Duk da cewa ya girmi Shuraim din sosai ma don Shuraim ai sa'an kaninsa ne na biyu kuma akwai tazarar shekaru tsakanin su.
Duban Zuhra yayi face dinnan cike da fara'a yace"kanwar mu bako akayi ne haka?dan rissinar da kai tayi tace"sannu da zuwa ya Kareem,cikin fara'a yace"yawwa mun sameku lafiya?ya shirye-shiryen school Kuma?
Zuhra tace"Alhamdulillah.
"To Allah yabada sa'a! A takaice ya fada.
Da Ameen duk suka amsa.
Wucewa yayi.
Duban Zuhra Shuraim yayi yace"Ina me neman gafarar ki akan maganar da nazo miki dashi bansani ba dai ko zaki iya amincewa dashi? Zuhra tace"me kenan ya Shuraim?
"Idan babu komai inaso kibani wani matsayi da wajen zama a jerin masu kula dake,cikin rashin fahimta take dubansa.
Gane bata fahimci abinda yake nufi ba yasa yace"kibani matsayi na yayanki muzama Yaya da qanwa nidake don Allah.
Murmushi tayi tace"Kai Ya Shuraim nina dauka wata magana ce,haba ai babu komai nabaka wannan matsayin Yaya.
"Masha Allah kanwata godiya nake Allah yasaka da alkhairi.
"Ai babu komai Yaya ta fada cikin sanyin murya,nan suka cigaba da hirarsu don Zuhra sosai ta sake da Shuraim.
** *MALAYSIA* **
Yauma kamar kullum shirinsa yayi yafito cikin suit blue black,takalminsa kamfanin Gucci ne dai cover shoe black colour sai agogon hannunsa Rolex,Kai tsaye driver yaje yabude masa back seat yashige shikuma yaja motar, gaisheshi gateman yayi sannan suka fice, laptop dinsa yafara daddanawa yana duba saqonni ta email daga wasu kasashe da dama nason takalman company nasu, wayar sace tafara neman agaji.
Sai da yadau lokaci yana ringing kafin yakai hanny yadau wayar,sunan Kareem ne ya bayyana akan screen din,cikin kamewa ya dauki wayan batare da yayi magana ba,sallama Kareem yayi.
Amsawa Sauban yayi nan suka fara gaisawa inda Kareem keta masa shikiyanci zuwa can yace"yawwa dama kira nayi na sanar dakai wani abu don kaine babban Yaya, kuma babban wa uba.
"Malam katafi maganar ka kaitsaye, yafada cikin kamewa.
"Dama akan kanwar ka nakira muyi magana don naga iri ina nema don alamu sun nuna idan banyi da gaske ba za'a mun shigo² ba zurfi,kai nifa idan na so samune ma a hada bikin mu tare.
"Akan wa kake magana kenan? Sauban yayi maganar wanda ko driver din ba lallai yaji abinda yake cewa ba.
Kareem yace"Akan zuhra mana nake magana gaskiya ni nagani inaso asan yanda za'ayi dani dazu na ganta da wani karamin yaro sa'an kabeer dinmu ne ma dagani wannan yaron wai yazo zance,so please ga dan gida nan.
Lumshe idanuwana Sauban yayi tare da kwantar dakai dakai a jikin seat din motar wanda duk kwakwanka bazaka gane yanayin da yake ciki ba yace"menene haka Kareem?so kake ka zubar mana da mutumci yarinya karama tanemi ta raina mu?look gaskiya kada ma kafara wannan tunanin,guda nawa take wannan yarinyar neman zubda mana da mutumci gaskiya ban goyon bayanka",yayi maganar cikin kwanciyar hankali. Daga can bangaren Kareem kuwa baki da hanci yasaki yana sauraran Sauban sai da yabari yakai aya sannan yace"Nikam Sauban gaskiya bazan iya da wadannan halayyan naka ba menene aciki?
"Komaima! Sauban yafada a takaice,a zafafe ya kuma cewa"inbanda jawo raini ina kai ina kula wannan kwailar yarinyar?yana gama fadar haka ya yanke kirar.
Cigaba da danne dannensa yake a laptop din wanda sam baka isa ka karanci yanayinsa ba.
Ta bangaren Kareem kuwa mamaki sosai ya gama rufeshi da halayyan aminin nasa shisam yafiye son girma da rashin son raini.
( _A daiji maganar babban Yaya Kareem don shine madaurin auren zuhra._ )😜
A haka suka isa babban company wanda gabadaya ma aikatan wajen sai girma suke bashi.
**** *KADUNA JABI ROAD*
Ummie ce zaune akan lumtsememen leaderseat din dake parlon