Showing 78001 words to 81000 words out of 100561 words

Chapter 27 - BAKAR TUKUNYA hausa novel

07 Feb 2026

467

ya shirya hutawa yau, ko kallon Inda Ummee ta ke tsaye bai sake yarda ya yi ba tunda ta juyo, gashi ya haɗe rai tamau! Kamar bai taɓa dariya ba, hatta ragowar Maids ɗin da su ke ta gaida shi hannu kawai yake ɗaga musu.

Har ga Allah Ummee is the last person that he want to see a wannan hali da situation ɗin da ya ke a ciki, dan bayaga selfish reason ɗinta da ya ke da tabbacin shi ya kawota garesa ya san tabbas kafin su rabu sai ta ɓata maasa rai maƙura.....


Gadan-gadan, haka Asad ya nufi bedroom dan Allah Allah kawai ya ke yi ya shige ciki ya rufo ƙofar, sai dai kasancewar ta fi shi kusa da ɗakin ya sanya ta yi nasarar shiga gabansa ta inda ta yi wani abu mai kaama da gudu da sauri sannan ta riƙe masa hannu ƙam! Tana mai mayar da numfashi

Tabbas da ace ba ta riƙe masa hannun ba zagayeta zai yi ya wuce ciki abinsa.....ba ya son ganinta ne sannan ba ya ƙaunar tsayuwa kusa da ita sam-sam, dan ganinta ya na tuno masa da abubuwan da ya yi going through duk saboda selfishness ɗinta sannan tsayuwarsa a gabanta haɗari ne a garesa dan tsaf zai iya aikata mata abunda ya san bai kamata ba na rashin kirki a matsayinta na Mahaifiya a garesa.

"Excuse us"
Ya ce ba tare da Ya juya ya kalli kowa ba, a take Jessica da ragowar Mutanen da su ke kai kawo duk suka bar parlourn.

A hankali Umme ta ce "Ikon Allah, son ba ka ganni ba ne?"

Sai da ya ɗauki lokaci tukunna ya ce "I'm very tired, bacci na ke so in yi, what do you need?”

Murmushi ta yi sannan ta sake ruƙo hannunsa kafin ta ce"akwai wani abu da zan buƙata other than to see my son?
Na yi missing naka ne sosai shine na taso in zo in ganka"

Yadda ya ƙura mata ido ne ya sa ta yi shiru sannan ta gagara sake cewa komai a hankali ta kawar da kanta gefe.

Kamar ɗazu yanzu ma sai da ya jima tukunna kamar an yi masa dole ya ce "tunda ni ki ka zo gani, ki zauna mana ko a shirya miki ɗaki ma sai ki huta, kafin nan nima na huta sai mu gaisa da kyau ki ganni....."
Ya ƙarashe maganar cikin gajiyawa
dan har ga Allah gani ya ke ta saka shi surutu da yaawa, yawan magana ba ya daga cikin ɗabi'arsa.

A ɗan diririce ta ce"Nooo, ae drivern da zai maida ni airport ya na waje ban barshi ya tafi ba, ka zo dai ka ɗan zauna mu gaisa sai in wuce.

Lumshe idanunsa Asad ya yi a hankaliii...
Kafin chaan ya buɗe sannan ya ce "Kin ganni ba sai mun zauna ba,good bye.
In kuma hirar ki ke so to ki jira in tashi a barci. Kaina ciwo."
Daga haka ya zame hannunsa da dabara da hanzari tukunna ya zagayeta ya shige ɗakin nasa ya na shiga ya saka lock a hankali ya jingina a jikin ƙofar...
For once yau dai ya yi kwaɗayin inama ace da gaske zuwa ɗin ta yi domin ta ganshi ta ga lafiyarsa sannan ta ji ya yake! Dan tabbas yana buƙatar hakan...
shekaru biyar kenan yau ya na aiki tuƙuru da dukiyarsa da kwakwalwarsa akan wani gagarumin company da su ka yi nasarar buɗewa, amma kawai jiya aka sanar masa ba shi za a bawa matsayin ceo ba wae age nashi sun yi kaɗan as ceo na babban company kamar wannan!.

Mutane da yawa sun fusata saboda kowa ya san shi ya fi chanchanta a bawa duba da yadda ya tsaya tsayin daka wajen ganin abun ya kafu, shi da kansa ya dinga rarrashinsun dan dayawan ƴan board ɗin cewa su ka yi za su cire shares ɗinsu amma ya tsaya tsayin daka nan ma bai yi ƙasa a guiwa ba sai da ya rarrashi kowa ya tabbatar komai ya daidaitu....
Shi har ga Allah bai ji haushin kowa kuma bai riƙe kowa a rai ba dukda kuwa an yi dissappointing nashi ne amma ya mantar ya yi fatan Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi….kawai shi main abunda ya ke damunsa a halin yanzu shine yadda ransa ya ke ɓaci ya harzuƙa sosai fiye da yadda ya kamata, wanda sam ba yin kansa baneba! He even hate the feeling wallahi dan ji yake yi kamar ana kunnoshi akan abunda Ya riga ya fawwalawa Ubangiji komai, ya karɓa Hannu bibbiyu…
Dauriya ce kawai ya ke yi amma tabbas a yau ɗin he needs someone na jikinsa sosai da zai bashi Baki, he need a shoulder to lean on…yau kam...dan ya gagara gane kansa, gaba ɗaya a burkice ya ke, sam ba ya son abun nan da ya ke ji, its not him gaskiya.

Da ƙarfi ya jaa numfashi ya sauƙe sannan a fili ya ce "Love and care is fake, ba ya existing a duniyarnan, mutane ne kawai su ke faking nashi."
Daga haka ya nufi bed ɗin ɗakin ya zauna bayan ya sakawa kanshi zai yi handling ya yi surviving test ɗin (ɓacin ran da burkicewar) kamar yadda ya saba dealing da dukkan trials ɗinsa na rayuwa....all alone!!!!.


Ya jima
a zaune kafin ya janyo computersa ya kunna cctv ya na ta kallonta, har addu'a ya tsinci kansa da yi Allah ya sa da gasken ta ke zuwa ta yi takanas domin ta gansa dukda kuwa ya san zai yi wuya...

Yanayinsa ne ya ji yana sauyawa yayinda wani kalar maɗaukakin ɓacin rai wanda shi a karan kansa ya san its not normal ya soma mamayeshi ya na cin ƙarfinsa, sai kuma kamar wanda ya bugu ya yi maƙil! Wani kalar nannauyan barci ya yi awon gaba da shi.

Wani irin mugun mafarki ya soma yi….ta inda ya ganshi daga shi sai mutumin da aka bawa ceo a tsakiyar wani ƙungurmin daji, mutumin a kwance rashe-rashe ko motsi ba ya iya yi, sakamokon ɓarnar da Asad ɗin ya yi masa a ciki kuma ya ke kan yi….sam yanayin da ya gansu a ciki ba mai kyau bane kuma shi a karon kansa ya san its impossible dan ko a gigin hauka ya ke to fa ya san ba zai taɓa cin wata halitta daga jikin mutum ba a dafe ma ballanta ɗanya….
Dan haka hankalinsa ya kai ƙololuwa wajen tashi! Gashi ji yake yi kamar gaske!
Wani irin abu dai kamar a farke kamar a mafarki kuma duk yadda hankalinsa ya yi maɗaukakin tashi sam ya gagara hana kansa......
Sun jima a haka kafin dabara ta faɗo masa ai kuwa a gigice ya shiga ambaton sunayen Allah da duk wata addua da ta zo kanshi a wannan lokacin,cikin hukuncin Ubangiji ya farka bakinsa ɗauke da salati sai dai da ikon Allah a baƙin ƙofa ya tsinci kanshi computersa kuma ta tarwatse….gaba ɗaya sai ya sake gigicewa sannan ya tsorace gashi sai ji ya ke kamar ya amayo da dukkan abubuwan da jikinsa ya ƙunsa saboda he is very disgusted by the dream! Ga kuma ƙarni da ya ke ji bayan ya farka ko dan ya saka abun a kansa ne oho dan kaɗan-kaɗan ya ji ƙarnin ya na ta guduwa.

Tsoro da tsantsar tashin hankali ne su ke sake mamayeshi, yayinda wata zuciyar ta shiga ingizashi da ya duba cctv na ɗakin ko zai iya ganin mai ya faru…dan ya ma kasa nutsuwa ya yi lissafin komai
da kyau, kwakwalwarsa duk ta cunkushe tsabar tsoro al’ajabi da kuma mamaki, dan haka ya miƙe daga nan bakin ƙofar inda ya ke ya ƙarasa wajen wata cp ta daban ya shiga dubawa….

Ko da ya duba bai ga lokacin da ya ke a bakin ƙofar ba computer kuma shine ya turota ƙasa garin barci daga kan gado, farkawa kuma a kan gado dai ya yi a gigice kafin ya miƙe ya ƙarasa ya buɗe wannan cp ɗin da ya ke ta faman dube-dube a cikinta yanzun…..saɓanin shi da ya ke da tabbacin a bakin ƙofa ya farka tukunna ya miƙe ya ƙarasa ya je ya kunna cp ɗin.


Da masifar ƙarfi ya dafe kansa jin yana shirin tarwatsewa kafin ya shiga jero addu’o’i….
ƙirjinsa ya na dukan tara-tara gaba ɗaya ya hargitse….
Tsoron ɗakin ma ya soma ji dan haka yana jiri sosai ya buɗe ƙofar ya fito gaba ɗayansa a ɗimauce sannan a firgice ga wani kalar maɗaukakin tsoro da ya ke sake mamaye shi jikinsa har karkarwa ya ke yi.


Kasancewar gaba ɗaya hankalinta ya na a kan wayar da take yi ya sanya sam-sam ba ta ji fitowarsa ba…
Ko a hargitse Asad ya ke Allah ya na bashi ikon riƙe kansa dan he's very gentle and calm all the time...
Shiyasa yanzun ma tsoro da hargitsin da ya ke a ciki ba su saka ya yi motsin da har za su sanya ta fahimci ya fito ba.....

"Kar ki wani damu fa, ya na fitowa zai yi mana signing ɗin sai in taho in kawo, ki ce su ƙara mana lokacin dan Allah, ba na so in yi gaggawa ne zai gane ba wajenshi na zo takanas ba."
Muryar Ummee ta sauƙa cikin dodon kunnuwansa.

Ajiyar zuciya ɗayar Matar da su ke wayar da ita ta sauƙe sannan ta ce"Ummee ki bar batun wani bounding, ba yanzu ba, focus pls. Wannan contract ɗin in mu ka samu mun haye its a life changin chance muna buƙatar influencial people kamar shi ya yi mana signing…
Daddy ya yi har na basu amma sun ce in ba a kawo second one ɗin ba within 10hours wallahi za su bawa wani”

Salati Ummee ta yi kafin ta ce “kinga Asad zai janyo mana asara ko? Akan wani care da na ke so in nuna masa na banza da wofi!! Shikenan ba komai na san mai zan yi! Bara ya fito zan san yadda zan yi ya bamu letter sannan ya yi signing in sha Allahu ba za mu taɓa rasa contract ɗin ba…”

“Ina papers ɗin su ke?”
Ta ji voice nashi a dake a bayanta.

Da mugun sauri ta waiga aikuwa karaff su ka haɗa idanu da shi, idanunsa jazirr gashi duk da build in ac’s ɗin da su ka yiwa parlourn ƙawanya wani kalar gumi ta ga ya na yi na ban mamaki!!

A ɗan tsorace ta miƙe dan yanayinsa ya bata tsoro kwarai ta ƙarasa garesa ta ce “mai ya faru da kai? Are you okay?”

Sai da ya haɗiye wani ƙululun abu da ya tokare masa maƙoshi tukunna ya ce “Ummee ina abunda ya kawoki ƙasar nan ya ke…”

Cikin tarar numfashinsa ta ce “son kai ne ka kawo ni mana, i want to see you”
Da ya ke ita ɗin gwanace a tsaurin ido sai ta ci gaba da cewa “wanchan maganan kawai wani abu ne da za mu yi in ka samu lokaci amma na zo ne asali domin in ganka…”

Sai da ya lumshe idanunsa ya buɗe ya ɗan furzar da iska sannan ya ce “Ummee, for the last time ki kawo abinda ya kawoki in yi miki yanzu ki wuce, in ba haka ba kuma ko kin bani daga baya ba zan yi ba sai dai mu zauna ni da ke ki yi ta kallon nawa…..”
Ya faɗi hakan ransa na suya sosai, duk inda ya kai ka son kaucewa baƙanta mata a matsayinta na Mahaifiyarsa ita kuma ala dole sai ta yi pushing nashi, bai san dalilinta na yi masa hakan ba.


Ta san halin Asad sarai kaifi ɗaya ne ba ya magana biyu, ita kuma har ga Allah in ta rasa contract ɗinnan tabbas daga ita har ƙawartata sai an yi admitting nasu a asibiti, dan haka ba kunya ba tsoron Allah ta je ta buɗe suitcase ta zaro takardun da ta zo da su, da wani blank paper ƴan rubutu a sama da ƙasa kaɗan ta bashi…

Dukda halin da ya ke a ciki sai da ya duba, da ya ga no need of ya yi prolonging kawai ya yi mata komai a take! Ta inda ya rubuta
Letter a blank paper ya yi musu guarantor ya yi
Signing, ragowar takardun kuma duk ya yi mata signing nan ma ya cike komai da take buƙata daga haka ya miƙe ko kallonta bai yi ba ya ce mata “good bye”
Sannan ya wuce sama.


In ta ce za ta tsaya rarrashin Asad tabbas zai janyo mata asara ne dan sai ya cinye lokacin da aka basu tass! Kuma ba lalle ya huce ba.
Dan haka ta ɗauki jakarta da suitcase ɗin da ta zuba takardun ta fito zuciyarta fess ta nufi airport dan farin cikin samun contract ɗin tashi ɗaya ya mantar da ita ƙuncin da ta gani ɓaro-ɓaro baiyyane a kan fuskar gudan jinin nata.


…..ko da ya isa ɗaki sai da ya yi da gaske tukunnna ya iya controlling ɗin kansa.

A hankali ya ke karantun Alqurani yayinda ya runtse idanunsa da masifar ƙarfi…..
Kaɗan-kaɗan ya soma jin sauƙi.

Babu wani abu da Ummee ta nema ta rasa a jin daɗin rayuwar duniya dai ba ta rasa komai ba amma a ko da yaushe burinta shine ta tara dukiya bai san ina za ta kai ba…….
Ba wanda ba za ta iya baƙantawa ba a kan hanyarta ta neman kuɗi, sam ba ta kara.


Knocking ɗin da aka yi masa ne ya katse masa lissafin da ya ke yi ba tare da ya ɗago ba a hankali ya ce “come in”
Kawai…..


Cikin ladabi Jessica ta gaida shi bayan ta shigo sannan ta miƙa masa wayarta ta na mai sanar masa cewa
“Daga board ɗinsu ne tun ɗazu su ke ta nemansa sun ce wayoyinsa a kashe ne, ana son magana da shi…”

A hankali ya saka hannu ya karɓa, sannan ya kara a kunnensa har kawo yanzu bai kai ga buɗe idanunsa ba! Ya ce “talk to me..”

“Hello Sir!!”
Ya ji muryar secretary ɗin ɗaya daga cikin su…

Da mugun kyar ya iya ce masa “i’m listening…..”

“Cikin harshen turanci mutumin ya gaida shi sannan ya shiga sanar masa cewa
“Allah ya yiwa mutumin da aka naɗa ceo rasuwa yanzunnan!
Haka kawai aka ga ya na kashi wani kala kuma ya gagara tsaida shi ga amai shima ya na yi ta Baki kalar kashin!.
Sai da aka kai shi asibiti tukunna Likitoci su ka tabbatar da gaba ɗaya kayan cikinsa sun lalace, ta yiu poision ya sha!
Dan kashin da aka ga ya na yi ashe hantarsa ce da ta zagwanye ta ke fitowa ta ƙasan nasa da Bakinsa.
Ragowar kayan cikin nasa suma komai ya lalace…..”

Asad bai iya jin ƙarshen zancen ba ya kashe wayar da wani kalar masifar sauri jikinsa ya na maɗaukakin karkarwa kafin ya iya buɗe idanunsa da kyar ya na ganin dishi-dishi.
•••••••••••••••
Ana shiga masallaci (sallar asuba) Anne ta fita dan jiya da daddare malaminta ya yi mata kwatancen wata shuka da za ta cira ta kai
masa kuma kafin alfijir ya keto ake so a ciri shukar da asuba.
Ya yi mata alƙawarin indai aka yi wannan aikin to Afra za ta sake burkicewa ne hankalinta ba zai kwanta ba har sai ta bar Isma’il.
…..
Duk yadda Isma’il ya so kasa daurewa ya yi dan haka gari ya na kammala yin haske ya isa ƙofar gidansu Afra ya kirata a waya, ransa na sosuwa amma wani abu mai kama da kishi da ɓacin rai yana daɗa ingizashi da tabbatar masa cewa hakan da ya tsara zai yi shine dai-dai……

Zai dai faiyyace mata ba zarginta ya ke yi ba kawai dai ya tambaya ne kuma ya na so ya ji abunda ya tabbatar (ba ta je ɗin ba) daga Bakinta.


Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING*
Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING*
Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139*

Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudinku tested and trusted.

Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu....
location:Kano
Delivery:NationWide.
kar ku bari a baku labari, sai kun zo🙏
SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA

BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:25 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*

HUMAIRAH BULAMA

Yota011

*31*

Tana zaune, ta na lazimi a lokacin da ya yi kiran nata wanda abun ya bata mamaki sosai dan time ɗin ya yi safiya da yawa.

Sai da ta idar ta yi addu’o’inta tukunna ta miƙe ta fito ta je ta sanarwa Adda ‘Ya Isma’il ya na nemanta a waje’ tukunna ta fita ta bar Addan ta na addu’ar ‘Allah ya sa lafiya’, dan haka kurum ta ji hankalinta bai kwanta ba sannan har yanzu ba su kai ga gaya mata me ke wakana ba….me aka tattauna jiyan da ba ta je ba! Dan haka zulluminta sai ya hauhawa.


A tsaye ta sameshi ya jingina da jikin bangon ƙofar gidan da ɓangarensa na dama ya na kallon ƙasa….
Ka na ganinsa ka san cewa tunani ne ya ke yi.
Har ta ƙaraso garesa ta tsaya bai sani ba, sai da ta ce “Ina kwana Ya Isma’il.”
Tukunna a hankali ya ɗago kyakkyawar fuskarsa ya zuba mata kyawawan idanunsa waenda ka na kallonsa za ka fahimci akwai damuwa ƙunshe a ƙasan ransa…


Ƙuraa mata idanuwa ya yi har sai da ta ɗan tsargu sannan ta sunkuyar da kanta ƙasa sosai.
Tukunna ya ce “Lafiya ƙalau Alhamdulillah, da fatan kin tashi lafiya.”

A voice na shi ma kai tsaye ta jiyo damuwa dan haka duk takaicin da ta ƙunsa jiya a ta dalilin cin fuskar da shi da Mahaifinsa su ke so su yi mata sai ta ji ya na ta sauƙa…zuciya da abunda ta ke so!
A take ta ji kwaɗayin son jin me ke damunsa domin ta samu ta share masa hawayensa…..

A hankali ta ce “Alhamdulillah.”
Sai kuma ta ɗaura da cewa “Na ji muryanka wani iri, Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login