Showing 12001 words to 15000 words out of 100561 words

Chapter 5 - BAKAR TUKUNYA hausa novel

07 Feb 2026

449

“na haihu d’anka ya rasu, muna cell da gawar har ta fara kumbura, ka zo in ni ba za ka fitar da ni ba shi ka karb’esa a yi masa sutura a binne sa dan Allah kar ya rub’e…”
Ta k’arashe maganar ta na fashewa da kuka”

Cikin tsantsar rashin imani ya ce “dan uban ki a kan gawa ki ka kirani?”

Zabura ta yi jikinta ya hau karkarwa dan duk rashin imaninsa ba ta tab’a tunanin zai yi hakan ba, haka suma mutanen wajen dan haka kowa sai ya yi tsit! Ya sha jinin jikinsa suna masu ci gaba da sauraronsa ya na cewa “Allah ya ji k’ansa ya sa mai ceto ne, duk sanda Allah ya sa ki ka fito ki binne abinki, ba zai yiu ki je ki tafka laifi ki saka ni yawon cell a banza da mutuncina ba…..wallahi wallahi in ki
ka k’ara kirana sai na tarwatsa ahalinki!
Da ace ma Yaron ya na raye ne to da sai ki kira ki fad’a in so ki ke a karb’a in karb’i abina amma kar ki sake d’agamin hankali a kan abunda ya riga ya shud’e na san kin san ba na son waiwaye…”
Daga haka ya kashe wayar ko sake sauraronta ta na cewa “yanzu ya rub’e kenan?”
Bai yi ba.


Shiruuu haka kowa ya kasance, tausayin ta ya cike zuciyar kowa a wajen sannan a take duk d’insu su ka fidda ran samun taimako daga garesa.

Anne kuwa gazawar Aliyar ta gani da Mijinta bai iya cetonsu ba gashi d’ansa ya na shirin fara azabtar da su da wari…ba bu wanda ya iya cewa komai kamar an yi ruwa an d’auke haka cell d’in ya kasance sai sheshshek’ar kukan Aliya da ya ke tashi….duk kalar zazzafan rashin adalci da muguwar muguntar da ta tafkawa Amal d’in da kuma mugun aikin da su ka tafka wanda zai zama silar yankewar duk wani sauran farin cikin su…
A take sai ta ji tausayinta ya lullub’eta, abunka da zuciya mai kyau.
Da sauri kuma sai ta kawar da kanta ta shiga k’ok’arin korar tausayin Aliyar da ya ke shirin dirar mata….

Cikin inda-inda da kyar Anne wadda itama duk jikinta ya yi sanyi ta ce “duk laifin shegiyar nan Sajida ne…za ta ci ubanta kuwa za ta san ta yi da ni! Wallahi sai ta yi yawon bara, hmmm, ba ta san wacece Anne ba!
Duk ita ce ta janyo miki halin nan da ki ke ciki har ma da mu kanmu…”

Cikin tarar numfashinta Aliya ta d’ago jajayen idanuwanta ta kalli
Annen sosai sannan ta ce
“Itace ta tilasta mini auren Mai Nasara shima?”

Inda-inda Anne ta fara, ba ta samu amsar da za ta bawa Aliyar ba ta d’aura da cewa “Anne kin cuceni, sarai da ni da ke duk mun san waye mutumin nan amma haka nan ki
ka bad’awa idanunki toka ki
ka jefani cikin bala’i….”

Mugun kukan da ya ci k’arfinta ne ya sanya ta kasa ci gaba da magana yayinda takardar scholarship d’inta da ta samu a uk ta shiga yi mata gizo, da tuni yanzu haka ta na chan….da tuni ba ta tarwatsa rayuwarta ba…

Cikin b’acin ran da har ya kai ga baiyyana a kan fuskarta
Annen ta ce “na cuceki ko dae Mai Nasara ya cuceki?

A mugun fusace Aliya ta ce “ae da ban auresa ba da ba zai iya cutar da ni ba!
Kin lalata mini dream d’ina Anne kin tarwatsa mini rayuwata gaba d’aya duk wani Abu na jin dad’i Anne kin janyo mini na yi hannun riga da shi….
Ki daina cewa Sajida ko Mai Nasara, dan wallahi duk wani halin da mu ke ciki a da da yanzu da har abada wallahi ko wanne duk ke ce sila.
Mai ya sa ki ke da son kanki ne?
Mai ya sa ki ke so ki lank’ayawa mutum sannan ki tabbatar da mugun halin a idanun kowa muddin ki ka ji ba kya son shi ko bai yi miki yadda ki ke so ba?
In kud’i ne ae Afra ya kamata ki fara tunkara ba Sajida ba,
Mai ya sa ki ke da son kai ne kuma ba kya son gaskiya? Mai ya sa duk b’arnar da ki
ka tafka in ta dawo miki sai ki ce wani ne sila? Shin sai yaushe za ki gane gaskiya ne Anne? Halinda nake ciki bai isheki ishara ba?
Tunda nake a rayuwata ban tab’a ganin mutum irinki ba!
Duk son zuciyar ko wacce kalar uwa muddin ta ga abu zai tab’a sannan ya gurb’ata rayuwar y’ay’anta ta kan sarara amma banda ke Anne!
Ba ki damu mu yi kuka ke ki yi dariya ba! Duk wani kalar Hali marar kyau akwai shi gareki Anne babu wanda ba ki kware a kansa ba!”

Cikin tarar numfashinta Yadikko wadda tunda Anne ta bi ta kanta duk wani gigin Maye da zafin cizon kunama suka barta, ta ce “Aliya….”

Cikin kuka ta ce “barni in fad’a mata na ga kamar har yanzun ba ta san wacece ita ba wata k’ila in na fad’a mata ta sani ta shiryu….
Kalli yadda ki ka lalata komai ki ka tarwatsa kowa duk cikinmu babu wanda ya ke farin ciki..
Hatta ita kanta Afran ae kin san ba wanda ya ke sonta ta aura ba dan haka dole akwai k’alubale a gabanta na sani..”

Cikin tsawa Aanne ta ce “in ji uban waye ne ba ya sonta?”
Ta yi maganar ta na mai satar kallon Amal, wadda ita kam ta zazzab’in da ya tusota a gaba ma ta ke..

Ya Amir shima ko
kallonsu bai yi ba dan ba ya son jin muryar Aliya, yayinda Baba Adda da Ya Abba kowa ya yi
d’iff dan su kam ba su da ta cewa…..



BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*

HUMAIRAH BULAMA

Yota

*06*
Masu buƙata daga farko su shiga channel ɗinmu.
https://whatsapp.com/channel/0029Va5fqs7E50UpMpXolU1T

Wani mutum ne a cikin mazan wajen ya ce “dan Allah dan Annabi ku barmu mu ji da abunda ya ke damun mu!
Haba mana dan Allah.
Wallahi-wallahi duk wadda ta k’ara yi mana hayaniya a cikinku sai ta daku!
Ku nutsu ku daina ife-ife ko ma samu su ji k’anmu su bud’e mu kar ku yi abunda za a barmu a nan da wannan Gawar wari ya kashemu…”
Ya k’arashe maganar ya na huci, yana mai jin haushin Anne sosai da tsanarta, gaskiya y’arta ta fad’a dan ko y’an Unguwa dama tuntuni Anne ta addabesu, kwata-kwata matar ba ta da Hali mai kyau ko guda d’aya.


Ta yunk’uro kenan za ta yi magana kowa ya yi d’iff sakamokon engine mai shayi da su ka ji an kashe wanda ya yi dai-dai da d’aukewar hasken wajen, d’iff!! Haka nan ko Ina ya kasance babu alamun Haske ko k’ak’a.
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”Anne ta furta a hankali jikinta ya na wani kalar karkarwa dan ta san wahala kam da azabtuwa sai ta sha ta a wannan k’arnin that’s if an zo an fiddasu basu kai ga mutuwa ba kenan!.



Sai yanzu da Aliya ta ambato Afra tukunna ta tuna Afran fa za ta iya kawo musu d’ouki tabbas..to amma kuma ta san dole Afran ta sako Asad wanda ta samu ta kad’a su shi da Afran da kyar su ka yi nisa…
Ba ta son ya had’u da Amal ko kad’an dan haka ta kawar da lissafin sako Afra a cikin jerin waenda za su taimaketa ta fad’a duniyar neman taimakon wasu…
Ta na cikin nazarin ta ji Ya Amir ya ce “ba ni wayar in gwada kiran Afra”
“Ungo” d’in da Aliya ta ce ta na mai mik’a masa wayar da kunna hasken fuskar wayar ne ya sanya Anne ta zabura..har an mik’a masa ya mik’o hannu ta saka nata hannun ta buge nasa sannan ta warce wayar daga hannun Aliya ta na mai zabga masa wata uwar harara, wadda hasken wayar da aka kunna ya taimaka masa wajen ganinta…
Da sauri kusan mutum uku su ka ce “fara bar mana haske tukunna.”
dan haka ta kunna flash d’in wayar har yanzun idanunta su na a kan Amir wanda ya d’auke kai daga dubanta.
‘In ta ga ba sarki sai Allah za ta kirata kam dan duk yadda ta kai ga son Afran ta yi farin ciki bai kai nata farin cikin da ranta ba, but for now ba za ta yi garajen bawa Amal abunda ta san ta fi buk’ata ba wallahi…’
Anne ta aiyyana hakan a cikin ranta ta na mai sake yiwa Ya Amir sign d’in ‘kar ka kuskura’
da ido.

Wannan mutumin dae da ya ke ta jin haushinta ne ya ce mata “ki bashi ya kirata mana!” Sai kuma ta ga duk sun tsura mata idanu.
Dan haka cikin kame-kame ta ce “bara in gwada kiran da kai na..”
Daga haka ta hau daddanna wasu nambobi da ta san ba za su yi ba, sannan ta danna call.
Jin ta yi wani irin sound ya sanya ta yi sauri ta sauk’e ta kashe ta ce “a kashe ne duk yadda a ka yi, ba zai je ba…”daga haka ta ajjiye wayar su ka ci gaba da zama…..
Har sun d’an samu sauk’in hasken da su ka samu kawai sai ga matar ta dawo ta ce su bata in sun gama…ba ta iya tsayawa ta ji feedback d’in yadda su ka yi da mutanen da su ka kikkira ba ta yi gaba dan a tsorace ma su ka ganta kamar an kama ta ne.


Tsayuwa gajiya da kuma wahala ne su ka sanya wasu maza a cikinsu su biyu su ka shiga shek’a uban amai mai masifar k’arni ga yawa wanda hakan ya sake tada hankalin Anne da kowa ma na wajen kwarai da gaske dan babu yadda su ka iya haka nan su ka ci gaba da zama da tsayuwa a cikin aman nan wanda tun a yi na farko ya cika d’akin ya wanzu a koina saboda ba wani girma ne da d’akin ba…sai kuma chaan su ka ji ya d’an fara raguwa ya na tsotsewa alamun ya na gangarawa ne cikin wannan rami inda kunamaa ta fito d’azu….
A take tashin hankalinsu ya sake hauhauwa dan basu san me ke tafe ba, gashi sun dad’e da daina ganin hatta tafukan hannayensu, d’id’iff su ke gani kawai tsabar uban duhun wajen…
Kayayyakin jikinsu mazan su ka yanke shawarar kwakkwab’ewa…dan haka su ka cire rigunansu su ka danna a ramin aka samu ya rufu tsaf!
Tsoro ya na sake game su sakamokon wani kalar sound da su ke ji ya na fitowa ta ramin kamar motsin kwari
kamar kuma hissing na maciji.


Kowa ba energy, barcin ma ya k’aura..Yadikko
sai wannan tsohuwa da Amal wadda ta ke yin nata kamar suma ne kawai su ke d’an gwadawa..dan haka wajen ya kasance shiruuu kowa ya na nasa lissafin…ta inda matan su ka kasance a zaune yayinda mazan su ke a tsaye.
A hakan su ka yanke shawarar kowa ya yi taimama a jikin bango ko inda sumintin ya farfashe k’asa
mai yawa ta baiyyana a samu a yiyyi sallah…
Hakan kuwa aka yi, har Amal wadda jikinta ya tsananta karkarwa…su ka yi su na masu jero istighfari da addu’ar su samu su fita su rama sallolin dan su kansu basu gama yarda da sallar ba…Yadikko ta shek’a fitsari a nan inda ta ke ya fi sau biyar dan tun d’azu in ta yi barcinta ta gama fitsarin ne ya ke tada ita
Sanin babu halin fita ya sanya ta ke fakar ido ta sake shi a wajen kawai…Wanda abunda ba ta sani ba shine rabin mutanen wajen sun fahimceta musamman ma Anne wadda itama ta yi guda d’aya a zaune lokacin da duhu ya wanzu, ga uban zarnin da ya had’e musu da wari….
Kasancewar yanzu duk wani abun maye ya saki Yadikko ya sanya ta na gama wartsakewa garau ta ji wata mahaukaciyar yunwa ta na kwak’ular kayan hanjinta dan haka ta saka kuka marar sauti domin kuwa ta san tabbas wannan yunwar, dafin kunama da warin amai had’e da zarnin fitsari da duhu sai sun yi ajalinta kafin abunda duk a ke tattaunawa ana jin tsoron fitowarsa daga cikin ramin da ya fi komai d’agawa duk wani na cikin d’akin hankali ya fito, dan dukda sun toshe hakan bai hanasu jin wani motsi-motsi a hankali ba wanda sautinsa ya na fitowa daga cikin ramin ne…
Wani kalar wahalallen barci ne ya fara fisgar wasu daga cikinsu dan zuwa wannan lokacin dare ya tsala sosai, masu yi a tsaye su na yi a matuk’ar wahale haka suma na zaune yayinda wasu da ga cikinsu babu alamun ma barci a idanunsu sam saboda tsabar bak’in ciki takaici tashin hankali da kuntatacciyar damuwa..


Anne itama kuka ta fashe musu da shi wae ta gaji
dan ta na fara gyangyad’i ta ke k’umewa ga wari ya hanata yin barcin…
Sai da mutumin d’azu waenda su su ke a tsaye shi da su Ya Amir ya bud’e mata wuta tukunna ta yi musu shiru…
Ya Abba kuwa mik’ewa ya yi Amal ta kwanta a kan cinyar Adda ta mik’ar da k’afafunta a wajensa da nata dan tun d’azu dama ya fahimci zazzab’i ya rufeta yanzun kuwa ya ji numfashi ma da kyar ta ke iya jaa….


Iya wahala sun wahala
In banda kukan zuci babu abunda Aliya ta ke yi ji ta ke kamar ta had’iye zuciyarta kawai ta Mutu ko ta samu ta huta…


A tsaye mazan su ka kwana a kan k’afafunsu matan kuma a zaune kafin Safiya gaba d’aya jikin kowa ya yi tsami masu ciwon sugar kuwa duk jikinsu ya soma suntuma gawa kuwa ta na ta sake kumbura itama.

Bayan awanni biyar…
A tare dukkanin su su ka furta kalmar “Alhamdulillah”sakamokon hasken da ya fara ratsowa na gabannin safiyar ranar…
Ba su ji ko alamun kiran sallah ba sai haske kawai su ka gani
Dan haka wasu a cikinsu suka kare wasu su ka yi tsarki su ka yi taimama sannan aka shiga gabatar da sallar asuba
dan zuwa wannan lokacin duk sun farka

Anne kuwa ta fuske ba ta yi sallah ba, bayan ta gama sanar musu ba fa za a karb’a ba duk sun yi mata baanza….dama d’azu (jiya) ma
ba ta yi ba
A nata mentality d’in a yadda ta ke a fusacen nan ko
nutsuwar yin sallar ba ta da ita sannan ita har ga Allah ta ce ba a sallah in ba tsarki, dan ita dai ba ta tab’a jin in da aka yi tsarki da dutse ba….


Sai Aliya itama wadda ta ke jinin bik’ii ga shi pad d’inta gaba d’aya ta jik’e d’inkinta ya na yi mata wata kalar azabar zugi da jan ruwa da alamun tsami ya yi…

Zuwa wannan lokacin ta ma kasa kuka tsabar bak’in ciki yunwa wahala da azaba sun kai k’ololuwa wajen azabtar da ita…


Kunya ce ta fara kama mazan da su ke a wajen domin kuwa daga su sai wandunansu sakamokon kayayyakinsu da su ka sassaka su ka toshe wannan ramin..da sauri sannan kusan a tare duk su ka juya a ka hau zak’ulo
kaya ana sassakawa……
Wani Abu mai kama da yanayin sab’ar maciji su ka gani a gaban rigar d’aya daga cikinsu wanda hakan ya sanya hankalin kowa ya tashi chaaa! Su ka tsaya turuss idanunsu a kan ramin.

Kallon-kallo aka shiga yi a wajen jikin kowa ya na sake yin sanyi sai kuma su ka saki salati a tare yayinda wasu a
su ka rushe da kuka…
Tana kuka sosai Anne ta ce
“Ku je ku lek’a cikin ramin mana ku duba mana abunda ya ke a ciki dan Allah
In na cutarwa ne ku kashe shi…”
Cikin daka mata tsawa wannan mutumin dai ya ce “ke dalla Malama rufa mana baki! Mai zai hana ke ki zo ki duba? In muka lek’a kuma da me za mu kashesa? Ko kin ga makamai a hannunmu ne?”

Banza ta yi da shi kawai amma ta saka a ranta wallahi in ya sake yi mata ihu sai sun kwashi y’an kallo tabbas..
Tun d’azu ihu ya ke ta yi mata yana jin haushinta ba gaira ba dalili ko uwar me ta yi masa oho….

Dole wasu a cikinsu su ka yi sacrifice su ka sake kwab’e rigunan nasu a ka rufe ramin laba’asa, wanda
zuwa yanzu kowa ya tabbatar da maciji ne a cikinsa.

Bayan awanni sha biyu…
zuwa wannan lokacin duk sun k’arasa fita a haiyyacinsu, Ya Abba shi kam ranar da aka kawosu ma azumi ya yi shiyasa tsabar wahala da yunwa har dishi-dishi ya ke gani, sauk’inta d’aya dai shi fitsari bai kamasa ba kamar yadda ya gigita ragowar har ta kai su ga ware wajen fitsari a cikin gurin.
Jikin kowa ya yi la’asar ko maganar kirki ma
ba sa iyayi….
Fitsari kuwa za a iya cewa daga Aliya sai Ya Abba da Amal wadda duk wani ruwan jikinta ya fice da hanyar gumi da azabar zazzab’i ne kawai ba su matsa d’aya daga cikin inda sumintin wajen ya fashe wajen ya kasance zallar k’asa sun yi ba.
Ganin duhu ya soma yi sosai ya sanya su ka gabatar da sallar magrib sannan aka shiga tunanin yadda za a yi da wannan ramin dan yanzu da su ka fahimci menene a ciki dole hankulansu su ka kai k’ololuwa wajen tashi kuma sun san rigunan su ba lalle su iya hanashi fitowa ba….mazan jikinsu saura wanduna matan kuma iyaka riga ne da zani d’an babu hijabai duk an kwace kafin su shigo ciki.
A haka har duhu ya yi musu ba su tab’uka uwar komai ba Anne da wannan mutumin suna ta fad’a kamar za su had’iye juna…

Baba ne ya daka musu tsawa duk su biyun d’an haka aka yi tsit su na mayar da numfashi….

Wani kalar nishi suka ji ana yi wanda ya ke baiyyana tsantsar firgici da tsoro, basu kai ga yin wani abun ba
su ka ji Aliya ta saki salati sakamokon fad’owar da ta ji Anne ta yi a kan jikinta….
Cikin tsantsar kid’ima mazan da ke a tsaye su ka shiga tambayarta “ lafiya? Mai ya faru?”

BULAMA ✍️
0806 402 1951

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login