Showing 15001 words to 18000 words out of 100561 words

Chapter 6 - BAKAR TUKUNYA hausa novel

07 Feb 2026

454

0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*

HUMAIRAH BULAMA

Yota

*07*

Follow our channel zaka samu daga farko.
https://whatsapp.com/channel/0029Va5fqs7E50UpMpXolU1T


Da kyar ta iya ce musu
“Anne ce ta fad’i kamar ba ta numfashi ma” sai kuma ta saki kuka, dukda kuwa abubuwan da Annen ta yiyyi mata tabbas ta ji babu dad’i sosai..Uwa uwace….

Ya Amir shima a take ya rikice hatta Amal itama k’ok’arin tashi ta shiga yi ta zauna yayinda Adda ta shiga k’ok’arin ganin ta k’arasa inda su ke ta na mai tambayarsu “mai ya faru?”

A take tsoro ya game su gaba d’aya a lokacin da Aliya ta shiga cewa
“Abu ne ya cijeta,
kowa ya kula”
Kuma k’asa-k’asa su na ji kamar hissing d’in maciji.

Fashewa da kuka Adda ta yi haka wasu a cikin mazan da su ke a tsaye
dan kasancewarsu maza bai sanya su ka ji rashin tsoron mutuwar da su ke ganin ta tunkarosu muraran a halin yanzun ba.

Dudduba Anne Aliya ta shiga yi sosai ta na so ta ji wajen da macijin ya cijeta ko ta samu ta d’aure mata amma ba ta gane komai ba, dukda ba ta ma da tabbacin Annen ta na raye.

Mazan ne su ka cewa su Aliyan su nutsu sosai su shafa ta a dubata da kyau
ko za a ji alamun wani
Abun a san mai ya sameta…in macijin ne kuma a samu a d’aure mata…


Chan k’asa wajen guiwowinta duk biyun su ka ji alamun jini ya na fita.
Ba su san tak’ameme menene ba Yadikko ta bada d’an kwalinta, sannan aka ciri na Annen aka had’a da shi mazan su kuma su ka daidaici wajen da aka nuna musu da ake jin jinin ya na fita su ka shiga fafutukar ganin sun d’aure mata shi katamau! Suna tab’a y’an kwalayen wani smell ya na fita daga jiki mai wari da k’arni ga kuma danshi saboda daga Yadikkon da take ta kwance har Adda da ma matan wajen duk y’an kwalayen nasu sun shafi amai sosai musamman ma na Annnen lokacin da ta fad’a kan Aliya kanta ya gogi wani ramin da amai ya taru a ciki bai kai ga tsotsewa ba.

A hakan..ba sa gani, su ka saita saman inda su ke jin zubar jinin wajen tsoka duka k’afafunta biyun su ka d’aure mata su one by one katamau!
D’aurin da ba na wasa ba!
Dan in da ace idanunta biyu ba ta kai ga shemewaba tabbas da tuni ta tsala masifaffiyar k’ara.

Kasancewar duk a rikice ga shi ba ma sa ganin komai kawai basira ce ya sanya ba su lura da akan wajen harbin su ka d’aure y’an kwalayen duk biyu ba kamar had’in baki
Sannan ba su lura sun d’aure mata da masifar k’arfi ba….

Mazan ne su ka tabbatar da ‘duk yadda aka yi maciji ne sai dai su gode Allah dan da ga dukkan alamu macijin ba mai dafi bane ba
tunda gashi sarar ta na zubda jini, kuma wani a cikinsu ya tab’a ya tabbatar musu jagular vein d’inta ya na harbawa kawai dai numfashin ne ba a ji..’
Dan haka kowa ya nutsu ya yi shiru watak’ilan ma tsorota macijin ya yi ga kuma hayaniya shiyasa ya fara irin hakan.

Dan haka dukkansu su ka yi shiru kowa ya nutsu ya yi tsit a waje d’aya Ita kam
Amal dama ba ta ma k’arasa sosai garesu ba amma still sai da Ya Abba ya sa hannu ya janyota ya dawo da ita ta ci gaba da zama a inda ya yi
musu kamar katanga daga koma menene, ita da Adda.


Kusan awa d’aya su ka yi a haka sai da su ka
daina jin motsin komai tukunna su ka shiga neman taimako…

Sosai Ya Amir ya ke jijjiga gate d’in ya na hawaye ya na jin Aliya ta na cewa “ta mutu fa!
Ba ta motsi, ko hannunta in na d’aga komawa ya ke yi…
Haba dan Allah,
Y’ar tasu y’ar gwal ce ne?
Saboda an mareta shine za su kashemu gaba d’aya wanne kalar rashin adalci ne wannan? Ya za su saka mu a waje mai had’ari kalar wannan fisabilillahi…”
Ta na maganar ta na sake k’ank’ame Anne da gawar d’anta wadda ta ke ta sake suntuma sosai.


Ihu da kukan duniya babu kalar wanda ba su yi ba, amma aka k’i kulasu..haka nan su ka hak’ura su ka koma kowa ya zauna zuwa wannan lokacin duk sun fita a haiyyacinsu babu k’arfi babu lafiya…sama da 24hours kenan babu abinci…
Haka nan su ka shiga addu’a wasu su na kuka, sannan Ya Amir da Aliya su ka saka Anne a addu’oinsu da fatan ba ta mutu ba, duk wannan bidirin da ake yi Baba bai ce musu ku ci kanku ba, addu’oinsa kawai
ya ke yi ya na istighfari wanda suma d’in suna kammala fafutukar d’aurewa Anne k’afafunta tamau da ife ifen neman agaji su ka jona shi…a haka su ka
dinga addu’a ba tare da idanunsu su na gane musu juna ba sai dai fa duk wani motsi na Amal Ya Abba ya na sane da shi sarai…..
A haka gari ya waye musu wanda su na duba Anne aka tabbatar da maciji ne ya cijeta saboda ga jini nan ya na ta fita, kuma ashe a k’afar hagu har sau biyu ya cijeta wajen cinya inda ya ciji d’ayar da alamun tsakiyar k’afafun nata ya shige ita kuma ta ji tsoro ta matseshi shiyasa ya yi mata a duka k’afafun a saiti d’aya, da kuma sangalalin k’afarta ta hagu nan ma maybe da ya zo fita ne, dan haka Adda ta sake bada d’ankwalinta aka d’aure dukda su na da tabbacin in ma dafin ne ya gama zuwa har zuciyarta sannan ba lalle mai dafi bane ba, amma gara su yi mata iyakar taimakon da su ke ganin za su iya.
sai dai sauk’in abun sun fahimci kamar ba mai dafi bane ba dan gashi ta na a raye har zuwa lokacin pulse d’inta Sun shaida hakan, kawai dae suman ne ba su san na menene ba hala tsorata ta yi ko kuma dae wani abun da ba su san da shi ba, shiyasa ba su yi gigin kunce d’aurin da su ka yi mata ba dan basu tab’a jin irin hakan ba gashi sun ga k’afar tata daga inda ya cijetan su ka d’aure zuwa k’asa har ma
Da sama-sama koina ya chanja colour sosai. Yayinda ake da tabbacin itama Yadikko wani kunamar ne ya sake cizonta dan gari yana wayewa su ka ganta a sheme, babu alamun cizon maciji a tattare da ita amma ta sheme itama, akwai dai pulse kamar na Anne sai dai kwata-kwata ba sa motsi daga ita har Annen jijjigawar duniya an yi amma sun k’i su farka.



Macijin ya tafi sai dai ramin har yanzu bai gama rufuwa ba dan haka ganin dare ya doso ya sanya su ka bada himma aka toshe shi da kyau su na masu
fawwalawa mai sama komai…
In ka gansu sai ka yi musu kuka kaff cikinsu Ya Abba ne kawai ya ke iya tsayuwar kirki kuma babu alamun wahala a tattare da shi amma gaba d’ayansu wasu ko idanunsu ba sa iya bud’ewa sosai…

Wari! Yunwa!
Uzuri wanda zuwa yanzu kusan kowa ya yi nasa atleast once a wajen, ne. Ga tsoro fargaba da tashin hankali gaba d’aya su suka taru suka sanya kawai wasu a cikinsu su ka fara yiwa kansu fatan mutuwa yayinda su Aliya su ka cire rai da Anne da Yadikko dan sun san ba zai yiu a ce maciji ya cijeka ka yi awanni sama da ashirin da hud’u ba a duba ka ba sannan ka rayu..dukda mazan wajen su na ta basu assurance d’in za fa ta tashi ba ta mutu ba tunda ga shi pulse d’Inta su na harbawa wata kilan doguwar suma ne ta yi, amma su kam gani su ke yi da kamar wuya…ana kaita asibitin ma za ta wuce.


Bayan sun idar da sallar isha, a lokacin da duhu ya wanzu tsoro ya na sake gamesu kawai su ka ji d’aya daga cikin mazan wani tsoho sosai ya yi salati sai kuma k’arar fad’uwa wadda ya yi ta a kansu Aliya, ba su kai ga gama shiga cikin mad’aukakin tashin hankali ba su ka ji wani ya sake sakin ihu sai dai shi bai fad’i ba kuma bakinsa bai mutu ba!!!
Kamar an kunna su haka nan su ka hau kuka su na ihu har Adda Amal kuwa masifar zazzab’i da yunwar cikinta ya sanya ko motsi ma
bata iya yi ba kawai ta shiga nanata kalmar shahada…
Da sauri Ya Amir ya mik’e kamar jiya yau ma ya hau jijjiga gate d’in dan zuwa wannan lokacin salatin mutum na uku kenan suka ji, sannan duk su na cewa “Nima ya cije ni”
A hankali
Ya Abba wanda gaba d’aya jikinsa ya yi sanyi duniyar ta ke juyawa ma ya mik’e ya k’arasa inda ya ke jiyo muryar Ya Amir su ka kama bockler d’in a tare su na jijjigata this time around da niyyar su fasheta kawai..su na a haka su ka ji wani mutumi a cikin mazan shima ya saki salati sai kuma ya soma furta kalmar shahada a hankali….
Da sauri Ya Abba ya juya ya na kiran sunan Amal!! Amal!!!
Wadda ta yi mutuwar tsaye…
Shi da Adda kusan a tare su ka damk’o hannunta jin ta amsa da “na’am”
Cike da fargaba da masifar tsoron rasata ya janyota ya sakata a gabansa jikin k’arfen ya had’ata da k’arfen da jikinsa sosai wanda dukda halin da su ke a ciki na k’ololuwar tashin hankali da matsananciyar fargaba hakan bai hanasa jin wani masifaffen yanayi ya dirar masa mai wuyar misaltuwa ba…
Da kyar jikinsa ya na wani kalar karkarwa ya had’e k’afafunta a cikin nasa ya yi mata ta yadda ko abun ya zo in ma cizon ne sai dai shi ya fara cizonsa sannan da wani kalar masifaffen k’arfi ya ci gaba da bugun k’arfen yana sauraren siririyar muryarta ta na kuka ta na cewa “Ya Abba meye haka? Ka cika ni ba na so….”
In banda ihu da kururuwa ba bu abunda ya ke tashi a wajen
dan zuwa wannan lokacin ko ba a gaya musu ba suna da tabbacin macijin ya ciji kusan duk mutanen wajen, sauk’in abun ma suna jin salati da muryoyin wasu har yanzu, wanda a tunaninsu gubar ba ta kai ga k’arasa game musu jiki ba ne…..

Kamar a mafarki Amal ta ji muryar Ya Asad ya ce “lights pls…”


BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*

HUMAIRAH BULAMA

Yota

*08*

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM....

Tarr!! Haka haske ya wadatu a wajen, wanda hakan ya sanya su ka fahimci ashe akwai bulbs a wajen tsantsar baƙar mugunta ce ta sa aka ƙi kunna musu kenan....

Wata kalar masifaffiyar kunya haɗe da takaici ne su ka hana Amal motsi a wajen kawai ta sunkuyar da kanta ƙasa dan tun da aka kunna wutar Ya Asad ya kafeta da idanuwa ko kyaftawa ya gagara yi...


Ihun jama'ar da su ke a bayansu ne ya katse yanayin dan haka da Abba da Amal su ka juya yayinda Asad ko gezau bai yi ba kallonsu kawai ya ke yi, kuma da wuya ka fahimci yanayinsa.....

Macizai ne har guda uku(garter snakes) su ka yi nashe-nashe a tsakaninsu sai wasu irin baƙaƙen kunami da su ka cika wajen, wanda ganinsu ne ya sanya jama'ar wajen yin ihu...

Zabura itama Amal ta yi wanda hakan ya yi dai-dai da kunnawar wani sauti marar daɗin sauraro very low sannan kamar vibration, cikin rawar jiki ɗaya daga cikin securities ɗin wajen ya ce "wallahi sir it wasnt intentional, mu ma haka nan macizan nan su ka addabemu shiyasa ba ma rabuwa da wannan ƙarar...."
Ya yi maganar ya na mai kunce kwaɗon gate na cel ɗin sai kuma ya zare sakata har guda uku jikinsa ya na rawa ya na satar kallon Asad wanda har yanzu ya kafe Amal da Abba da idanu......
Kamar ba shi ke yi musu tsawa ɗazu ba dan yanzun cikin lallaɓawa ya ce musu "your release has been granted, you can go.."

Tun da aka kunna ƙarar dama macizan su ka gudu waenda duk wanda ya sani da ya kallesu ya san ba masu dafi bane ba.
Kunamin suma guduwa su ka yi zuwa cikin wannan ramin yayinda kowa ya fahimci tsoro ne zallah kawai ya sumar da Anne, Yadukko da waennan tsoffin bayan macizan sun cije su, dan ana kunna wuta ragowar waenda macijin ya sassaresu su ke ta ihu.. rass su ka ware...


Miƙewa Aliya ta yi yayinda Amal ta yi saurin ficewa daga wajen ana buɗe ƙofa wuff! Bata yarda ta kalli inda Asad ke tsaye ba.

Ko kallon Anne Baba bai yi ba su ka kama Yadukko shi da Adda su ka wuce da ita yayinda wasu mutane da su ke kyautata zaton Asad ɗin ne ya zo da su su ka shigo cikin wajen su na tayasu ɗibar marasa lafiya...


A hankali Cikin yanayinsa Ya Asad ya ce “come closer “
Wanda ba dan hankalin Securityman ɗin ya na a kansa ba da ma chan to da ba zai jiyo sa ba.

Matsawa ya yi su ka ɗan yi magana daga haka ya ɗaga masa kai ya ce “yes sir” kafin ya juya ya je ya tsaya a bakin ƙofar fita daga wajen kawai ba tare da ya ce komai ba, yayinda ake ta fafutukar fita daga wajen.

Tunda Ya Abba ya ga hakan dama ya san mai ya faru haka kurum jikinsa ya bashi hakan shiyasa kawai sai ya jaa ya tsaya bai ko motsa ba daga yadda ya ke ba.


Kusan tare za a ce an ga Ya Asad shi da jama'arsa da kuma wasu mutane sun baiyyana a wajen(mace da polisawa biyu), sai dai su ɗin wani uniform ne na manyan polisawa sosai a jikinsu sannan tare su ke ta tsaye a gefe da yayinda matar da su ke tare da ita take ta kuka ta na sharar kwallah..wanda tashin hankalin da kowa ya ke a ciki ne bai sanya sun maida hankali wajen sanin ba'asin abunda ya kawota wajen ba....

Sai da Aliya ta zo fita ta fara ƙoƙarin kinkimar Anne ita da Ya Amir tukunna su ka ji amfanin zuwan mutanen wajen...
Wae..
'Bayan an kawosu nan cel ɗin ashe an bincika gidan ne sosai saboda Sajida ta ce Anne har sata ta yi mata ta kuma duba sarƙarta ba ta samu ba, to garin bincike aka kama Anne da laifin tsafi da ƴaƴan da aka jima ana nemansu bayan an yi garkuwa da su watanni biyu da su ka wuce.
Dan haka za su ci gaba da riƙeta a wajen kafin a wuce da ita inda za a binciketa!!.
Su kansu saboda Ya Asad ne ya sanya aka barsu su ka fita sannan kayan Yaran da shaidu a cikin iyaka ƙasan wajen kayayyakin Anne aka samu inda ta haƙa ta binne da alamun ta ɓoye ne dan kar su kansu su gani..amma da an ce kar a bar kowa na gidan ya fita, Ya Asad ne ya tsaya musu kuma an san ba su da laifi daga bayanan mutanen unguwaa kowa Anne ya ke cewa da kuma wasu shaidu ta su ka sake baiyyanata ita kaɗai shiyasa aka samu aka sake su dan haka an yi releasing ɗinsu su tafi amma banda Anne.....
Suma amma ba a bawa kowa damar barın gari ba har a gama case’.

A fusace bayan ta kammala jin bayanin nasu mai ban tsoro da damuwa, Aliya ta ce
"Amma dae ae atleast kwa kaita asibiti a duba lafiyarta ko?"

"Ƴaƴan da aka kamata da laifin yin garkuwa da su ƴaƴan alhaji sale mai fetur ne!!"
Mutumin ya yi maganar ya na tsatstsareta da idanuwa yayinda itama ta zazzaro idanu waje ta na mammakin yadda Anne ta samu kwarin guiwar iya sace sannan ta aikata aikin tsafi da ƴaƴan babban mutum kamar wannan...
Maganarsa ce ta katse mata tunanin da ta ke yi jin ya ci gaba da cewa “dan haka ko
motsawa daga inda take an ce kar a barta ta yi….ku ma d’in shaidun da ƴan unguwa su ka bayar da sunanta da aka gani a jikin sassan jikin Yaran da kuma ragowar shaidun da su ka tabbatar da ita ɗaya ce mai laifi sai kuma taimakon sir wanda ya tsaya muku ne ya sanya kawai za mu barku ku tafi.
Dan haka ki tashi ki fita ku je ku binne Yaron nan ko kuma in ci gaba da riƙe ku a wajen ke da shi da ita….”
Ya ƙarashe maganar cikin daka mata tsawar da sai da ta sanyata zabura.

Tabbas ita a karon kanta ko me in aka ce Anne ta aikata to fa ba za ta taɓa musawa ba!
To amma yaushe?
Ta yi wa kanta tambayar cikin tsantsar ruɗani da tashin hankali...


Baba dama ko tsayawa bai yi ba, Ya Amir shima hawaye kawai ya share ya fice, a hankali Aliya ta rungume jaririnta wanda uban warin da ya ke yi da suntumar da ya yi bai sanya ta jefar da shi ba, ta fita ta na kuka sosai da tunanin yadda za su yi, dan tabbas ba ta hango musu ko da kyallin mafita a case ɗin Annen nan ba.


Aliya na fita waje matar nan da ta zo da sojojin ta matso, cikin sheshshekar kuka ta ce musu “dan Allah ku bar ni in kalli fuskar matar ko da sau ɗaya ne, Matar da ta yi mini yankan
ƙauna”

A hankali police ɗin ya ɗan sunkuyar da kansa alamun tausayawa da girmamawa a gareta sannan ya ce “to ranki ya daɗe”

Daman wajen ya rage Ya Abba da Anne ne kawai, sai
Polisawan da au ka shiga mutum biyu dan haka su ka sake kafa ido sosai domin su bata kariya ta gama ganin fuskar Annen dan tunda suka ga fuskar ƴaƴan matar da hannayensu da ƙafafuwansu a tukunyar ƙasa daban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login