Showing 21001 words to 24000 words out of 100561 words
to sai dai su tashi dan ba zai yiu ya tsaya Anne ta maida masa unguwa wajen zuwan sojoji da ƴan sanda kullum ana hayya-hayya ba gashi dae shirun da ya yi ya sanya ta je ta taɓo mutumin da wataƙila har su ta gogawa kashin kaji... abun nata ya yi yawa, a barshi ya ji da case ɗin su Yagwalgwal ma kaɗai da su ka addabi kowa..
Sosai mutumin ya bawa Ya Amir mamaki dan kamar bai sanshi ba haka nan ya yi masa..
Kamar ba Abokin Baba ba shima amma da ya yi la'akari da yadda Baban kanshi ya yi wa Annen da kuma halinda ya ke a ciiki yanzu duk saboda ita sai ya yiwa mutumin uzuri su ka tafi neman wata mafitar...
Kafin awanni biyu kacal labarin abunda ya samu Anne ya zagaye koina na Unguwar har wajenta yayinda mutane da yawa su ke ta binta da fatan 'Allah ya ƙara!' Dan kaff a areansu kai tsaye za a iya cewa babu wanda ya tausaya mata kowa ya san halinta ne ya ke binta.....
Bayan kwana biyu...
Wannan mutumin da tshoho har sun dawo gida, yayinda Adda itama ta dawo bayan mutanen nan maaikatan lafiya sun je sun rarrasota da kyar tare da Baba. Ya Abba dai ba su ma san ina ya ke ba.
Kamar yadda su Ya Amir su ka zata Anne a ajjiye kawai ta ke har yanzu ba a fara bi ta kan lafiyarta ba, yayinda kowa ya ke jajanta yadda ta kasance a raye har zuwa wannan lokacin domin an tabbatar musu da ta na raye kawai dai ba a barsu sun ganta ba....wae pain reliever kawai ake bata, a taƙaice dai su na jinyar tata sai dai ba ta kai ta kawo ba shiyasa su Ya Amir su ka saka abun a mazaunin ba a kula ma da ita kwata-kwata....dan ko farfaɗowa ma ba ta yi ba har kawo yanzun an dai jona mata ruwa sannan ana mata pain releiver ta, an fi maida hankali akan tsareta da binciken su tomb print nata akan lafiyarta. Likitocin fata dae sun zo sun dubata ana jiran na ƙafar da aka tarar a ɗaure su ƙaraso har yanzu...yayında aljuhu Kaka Nura ya ke ta ihu har sata sai da ya yi jiya tukunna aka samu a ka yi mata allurarta.
A kwana na uku aka samu ta farfaɗo sai dai ko da ta farfaɗo ɗinma kamar sumammiya haka nan ta ke a jangaɓe! Dan ta na azabtuwa ne gwargwadon iko....
Kawai dai ta kan shaƙi numfashi ta ambaci sunan mahaifiyarta daga nan ta koma ta ci gaba da abunda za a fi kiransa da suma dan azabar wahala take sha ba ta wasa ba…sam! Pain releiver ba ta yi mata aiki yadda ya kamata kuma ashe da wuri ta ke sakinta da zarar sun yi.
Da yake an tula maaikatan tsaro a ɗakin sai wajen ya zama kamar wani police station, likita ɗaya ne kawai kuma fanninshi bai shafi abubuwan da su ke damunta ba an ce ya tsaya kwararru su zo...
Kaka ne kaɗai a wajenta dan an ce in banda iyaye ba za a bar kowa ya ganta ba.
Kaff ƴan arean nasu babu wanda ya yarda ya taimakawa su Ya Amir dan case ne babba Anne ta jangola babban ɗan kasuwa ne a Nigeria, ko ma ace Africa gaba ɗayanta mutumin da ta yi garkuwa da ƴaƴannasa dan haka dole su ka haƙura su ka dawo zuciyoyinsu duk a dagule.
Anata shiga gidajen maƙofta a na yi musu jaje yayinda su kuwa babu wanda ya leƙo su dan ƴan Unguwa zuwa wannan lokacin kowa tsoron shiga harka su ya ke yi duba da yadda mutanen layin da su ka yi musu kara lokacin rasuwar ɗan gidan Aliya duk su ka ƙare a cel saboda bala'in su Annen.....shiyasa hatta Abokin Ya Amir ɗin da su ke ta faɗi tashi ya kasance ba ɗan layin bane ba, jita-jitar da ya ke ji a bakin mutanen da su ka ƙi taimaka musu game da Annen ya sanya ya sare shima ya zame ya barsa shi kaɗai.
Bayan kwana biyu.
Sosai lamarin nata ya sake firgita su dan zuwa wannan lokacin manyan Likitoci sun ƙaraso kuma sun dubata sosai..
Sai dai kuma sun makaro domin su na duba ƙafafun nata da ba a kai ga kuncewa ba an duba tun a karon farko su ka fahimci tabbaas ƙafafun Anne duk biyun sun ruɓe dan haka sai dai a yanke ƙafafuwan nata duk biyu sakamakon infection ɗin da ya shiga sannan masu matsewa su kuma sun matse ƙafar katamau wanda hakan shima ya taka rawar gani kwarai wajen sake ruɓar da ƙafafun nata...
Dan haka ba su yarda sun sake ɓata wani lokaci ba a take aka wuce da ita asibitin Murtala inda za a yi mata aikin....
Ga Adda itama wadda su ka gagara zama ita da Baban still akan lamarin Ya Abba wanda ba ma su san inda ya ke ba, sun kira Afra da niyyar ta yi wa Mijinta magana ya saki Abban amma ta ma ƙi ta tanka musu akan batun, da farko ma su na ɓoye mata halin da Anne ta ke ciki wae dan kar hankalinta ya tashi har su ka gaya mata wanda ga mamakinsu sai su ka ga kamar ba ta wani damu ba dan baya ga “Allah ya bata lafiya” ɗin da ta ce bata sake cewa komai ba game da Anne..
Ta ce musu in Ya Asad ɗin ya shigo za ta yi masa magana ta ji tun daga nan har yau kusan kwana uku kenan ba ta sake kiransu ba…
Wanda abunda ba su sani ba tsantsar damuwa ce ta ke shirin haukata Afra....
Sosai kan Amal ya ƙulle...ta rasa dalilin Ya Asad na ƙin sakin Ya Abba da kuma jinya da uban kuɗaɗen da ya ke ta kashewa har kawo yanzu da ta warke duk dan saboda ita kaɗai, dan bayan an gama dubasu a asibiti har yau nurse ba ta tafi ba sannan an ɗaurata akan magunguna masu tsada kuma hatta ruwan da su ke sha a gidan duk shi ya kawo komai da sunanta...
Tabbas ta san ya manta da ita, to meye ribarsa? Ta san dai kasancewarta ƙanwa ga matarsa bai kai a ce ya yi mata hakan ba......
Gaba ɗaya hankalinta a tashe yake
Ga abunda ya ke damunta wanda ya ke sake yin gaba kullum...
Ga kuma tashin hankalin da ta ke a ciki a ta sanadiyyar ɗaure Ya Abba da aka yi dan tuni ta daina fushin da take yi da shi, dan haka gaba ɗaya duk sai ta firgice ta sake gigicewa duk ta fita a haiyyacinta.
BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*
HUMAIRAH BULAMA
Yota
*10*
Hatta Baba sai da ya ji babu daɗi a lokacin da Ya Amir ya kira Kaka Nuran ya ke sanar musu
‘ƙafafun Anne duk biyun sun ruɓe za a cire sannan ƙirjinta shima akwai wajen da ya yi ɗiwa bayan an watsa mata acid dan haka ana kan bincike aga mai acid ɗin ya yi triggering har ya kai ga yin ɗiwar..muddin aka gano abunda ake zargine wato jeji to nan ɗin ma sai dai a yanke tun kafin ya bazu…
Ranar gidan duk wuni su ka yi sukuku, ga Aliya wadda su ka kasa gane kanta
dan sau biyu su na hanata kashe kanta a cikin gidan, duk yadda Amal ta kai ƙololuwa wajen fushi da Aliyar zuwa yanzun kam ta fara bata tausayi matuƙa dan tabbas dukda ta na ta ƙoƙarin ganin ta ɓoye da kyau zuwa yanzu kowa ya fahimci akwai abunda ya ke damunta bayan takaici Anne da Mai Nasara…
Sosai lamarin Anne ya gigita Kaka Nura duk masifa da bala’in tsohon zuwa yanzu ya yi sanyi..
suna ɗaya Anne ta ke ta kira wato sunan mahaifiyarta tunda ta farfaɗo wannan dalilin ya sanya kawai bayan an shiga da ita theater room Kaka Nura ya wanke ƙafa ya nufi inda Uwani take, zuciya cike da ƙunci....
Ya na tafe ya na hawaye ya na nazarin...
Duk bala’insu shi da ita (Anne) wajen ganin sun tara abun duniya ba ya taɓa taruwa! Kamar waenda aka tsinewa..Ko da ya ke ya san ko sun tara ɗin daga a damfaresu sai ko kuɗaɗen su ƙare a wajen malamai da bokaye, ko kuma su tafi a banza, dan gashi a yanzu haka daga shi har ita ba su da uwar komai wanda a yadda shi da ita su ka dinga neman kuɗi na haram da na Allah ya isa har ma da na sata a gaskiya ya kamata a ce sun sayi estate a cikin garin Kano...sai dai kash! Dan a halin da ake ciki dai yanzun da ta ke a kwancen nan in ba satar zai ci gaba da yi ba tabbas ba ya jin za a iya sake yi mata wata allurar ma saboda tsabar fatara da babu! Gaba ɗaya ya rasa mai yasa su ke ta sake tsiyacewa haka daga shi har jikokinsa... Amir ma da mugun kyar ya iya tura masa dubu biyar tunda ta kwanta dan ya ce wallahi ko bashi an ƙi a bashi saboda an san ba shi da yadda zai yi ya iya biya.
Ciwon Nuratu (Anne) ya lashe asusunsu gaba ɗaya..in ba dan ƙalubalen da su ka fuskanta ba na damfara da shi da Anne da Aliya wallahi ya ci ace sun yi maganin abunda ya ke damunsu sam ciwon bai isa ya tsotseshi haka ba, tsaf za su yi magani sannan su ji daɗin rayuwa sai dai da ikon Allah a halin yanzu daga shi har ita (Anne) bayan ta warke da Amir da ita kanta Aliyar in har Ubangiji bai rufa musu asiri ba to tabbas sai dai su yi bara da roƙo..dan shi dai Asad an san zai kula da Afra amma batun su tsafe shi su kwaci kuɗi daga hannunsa ya san ƙaryansu sai dai shi da kansa in ya yi niyya ya basu.....
Ya na wannan lissafin ya karasa garin da Uwani ta ke wadda daga shi sai Annen ne kaɗai su ka san ta na a raye!
Dan tun shekaru ashirin da biyu Baya lokacin da su ka cinnawa gidan Baba Yusufa wuta kowa ya yi tunanin Uwani ta rasu ne a ciki.
Chan wani Ƙauye a tofawa ya gangara, kwata-kwata gidaje ba su fi bakwai ba a a kaff ilahirin wajen dan in ka ga ɗaya to sai ka yi tafiyar da ya ɓacewa ganinka tukunna
za ka sake ganin wani….
Bukkoki ne gaba ɗayansu yanayin kalar fentin da ake yi a jikinsu ne kawai ya ke bambanta su dan duk giramnsu ɗaya sannan wani a zagaye ya ke wani kuwa ko kara guda ɗaya bai samu arziƙin samu ba ballantana ya baiyyana keɓantuwa..
Tunda ya nufo bukkar gabansa ya ke ta faman faɗuwa zuciyarsa ta ke zillo..a kaff tarihin tsari na rayuwarsa bai taɓa tunanin akwai ranar da za ta zo ya yi shakka ko shayi ko tsoron wani Abu ba sai yau....
Tabbas a halinda ƴartasa Aba mafi soyuwa a garesa ta ke a ciki yafiyar mahaifiyarta kawai ta ke da buƙata sai dai kuma baya jin Uwani za ta taɓa yafe masa shi da Anne, shi kuma a halin yanzu ya fahimci wannan taimakon da zai yi mata shine duk wani ƙarshen gata, besides shi fa tunda ya ganta a haka gaba ɗaya ya gigice ya firgice ya nemi duk wani kuzarinsa ya rasa gaba ɗaya its like he's trying to loose himself....dan haka babban gatan da zai yi mata ya san shine ya taimaka ya kai mata Uwani ta ganta ko a samu ta yafe mata dan ya san abunda ta ke da buƙata kenan. Bai san mai ya sa ba haka nan ya cire rai gani ya ke kamar Nuratu tata kawai ta ke jira..bai taɓa tunanin zai yi mata wannan fatan ba ko a tsaka mai wuya kamar wannan amma tabbas akan ta gama shan wahalar nan kuma a fille mata kai kamar yadda ya ji polisawan su na faɗa gara ma ta mutu tun yanzu!.
Kuka ne sosai ya kufce masa...ya na
wannan lissafin ya ƙarasa bakin bukkar da ya ke da tabbacin nan ɗin ce ta Uwani ya tsaya dan ya gagara tattaro courage ɗin da zai fusakanceta...
Tsoro ya ke yi kar ta ƙi amincewa da buƙatarsa, tsoro sam ba ɗabi'ar Kaka Nura bace ba amma tabbas yau kam ya na jinsa a kan halittar da a shekarun baya ya raina fiye da yadda ya raina kashin gindinsa.
Da ƙarfi ya fesar da wani kalar huci sannan ya daddage ya ɗaga hannunsa ya na shirin taɓa ƙofar ya ji tsohuwar muryarta a bayansa ta ce "Ya Nura"
A hankali kamar mai mamaki da tantamar ko shi ɗinne…
A hankali ya juyo ya na kallonta...
itan ce kuwa! ya aiyyana hakan a ransa.
Itama ta na tsaye kawai ta kafesa da idanuwanta…
Da alama ruwa ta je ta debo daga rafi ko kuma har da wanka ne duk ta haɗo ta yo dan ga alamu nan sun baiyyana...
Ta ƙara tsufa sosai tabbas dan gaskiya ta fi shi nuna tsufa itakam dan ta yi tukuff-tukuff da ita babu wata ragowar mamora a tattare da ita…
Ganin an tsaya ana ta faman kallon-kallo ne ya sanya ta zo ta fara ƙoƙarin shigesa dan ɗan ruwan da ta ɗebo a cikin kaplas har ya fara sagar mata da tsohon hannunta…
Da sauri ya matsa ta shige ciki sannan ya bita a baya…
Rabonsa da ita tun shekaru ashirin da biyu baya da su ka wuce lokacin da ya kawota nan ɗin ya ce ta zauna kafin a san abun yi!
Wanda har ga Allah maitar son Yadikko ce ta sake tunzurashi wajen yin hakan dan ita a lokacin ya san ba za ta taɓa yarda ta auresa ba..
Sai kuma rufin asirin ƴarsa da shi kansa, dan haka ya zaɓi ya ɓoyeta sannan ya ɗaura laifin kacokam akanta...ya jefi tsuntsu biyu abunsa da dutse ɗaya buƙatunsa duk su ka biya ita kuma su ka kawota cikin wannan wahalalliyar rayuwar…
A zuwan hideout.
Tunda ya tafi babu ko waya ko wani abun, bayan da ce mata ya yi za su dinga zuwa duk sati…
A hakan fa wae da sunan aurensa a kanta ne har kawo yanzun dan kowa ya na tunanin ta Mutu ne yayinda ita kuwa tun lokacin da addini ya ɗiba mata ya cike bai zo gareta ba ta yi idda ta saka kanta a sahun zawarawa….
Da ita da shi duk lissafi ɗaya su ke yi dan haka ta ajjiye ruwan ta nemi waje ta zauna sannan ta ɗago ta kallesa ta ce masa “wani abun ka ke da buƙata ko?”
Dibi-dibi ya fara abunda sam ba ɗabi'arsa ba dan shi kansa ya san ko an tona a zamani da tarihi tofa ba lalle a samu halitta mai kalar tsaurin idonsa ba, kamar wanda ya girma a gaban karuwa haka nan ya ke bai san ya ake kawaici ko kaucewa ba ballanta ya yi dibi-dibin..amma yau gashi da ikon Allah ya kasa magana..
Itance dai ta sake magantuwa dan ya gagara cewa komai “zan sake fita, mai ka ke da buƙata?”
A hankali ya sauƙe ajiyar zuciya...
Ba batun gaisuwa ko rarrashi saboda dama chan shi bai iya ba a kan ƴarsa ne kawai ya iya rarrashi, sannan a halin yanzu ya san in ya fara ma tsaf za su iya shafe shekaru ba su gama debate ɗin ba kuma a ƙarshe shine zai zama marar gaskiya, ko da kuwa ya yi borin da ya kan yi a duk lokacin da ya fahimci ba shi da gaskiya an bashi gaskiyar amma wannan karon kam ya san ko point ɗaya Uwani ta kawo ta gama da shi.
Dan haka ya sauƙe ajiyar zuciya a karo na ba adadi ya ce mata "ƴarki ce ta ke da buƙatarki" sannan ya shiga zaiyyano mata halinda Annen ta ke a ciki a wannan lokacin....
Ajiyar zuciya ta sauƙe ya na kai aya sannan ta ce "Allah ya bata lafiya, in kuma mutuwa ce to Allah ya ji ƙanta."
Daga haka ta fara ƙoƙarin ficewa ta ga Kaka ya durƙusa a gabanta ya riƙe ƙafafunta, sai kuma ya fara hawaye, ya na cewa "kar ki yi taurin kai dan Allah, yau kwana huɗu kenan ke kawai ta ke ta ambato, ki taimaka dan Allah ki zo mu je ki ga halin da ta ke a ciki na san za ki tausaya mata ki taimaka ki yafe mata…."
Har ga Allah ko
Muryarsa ba ta ƙaunar ji, Allah Allah kawai ta ke yi ta fita..banda tsabar tsaurin ido ita da bata da maraba da gawa a wajensu mai za ta yi musu yanzun? In da ace sun yi nasarar kasheta a wanchan lokacin da ya za a yi ta yafe mata? A Ina zai ganta ballanta su nemi yafiyar?.....
Ta na wannan lissafin ta ji ya ce "ki rufa mini asiri ƴata ta Mutu ba da hakƙin kowa a kanta ba dan Allah…"
Murmushin takaici Uwani ta yi sannan ta kallesa da kyar, tukunna ta ce “Ashe kun san akwai hakki Ya Nura…”
Sannan ta ɗaura da cewa “A ganina na yi muku ƙarshen kara! A kalar abubuwan da ku ka yi mini har na iya yi mata fatan ta cika lafiya da fatan waraka ae na yi muku ƙarshen kara.
Sannan fa bara ka ji...Ina yi maka albishir ɗin cewa ko da ace na yafewa Nuratu! To tabbas akwai tarin hakkoki na jam’a bilaadadin a kanta..dan haka kar ka soma yaudarar kanka ka san ta zalinci da yawa….dukda kun kawo ni nan hakan bai Hana ni bibiyar al’amuranku ba ae..sarai na sani kuma na ji yadda ta tarwatsa rayuwar mijinta shima da ƴaƴan da ta Haifa a cikin cikinta!
Bayaga su ma ae kai kanka ka san Nuratu ta zalinci da yawa wanda in ka ce burinka shine ka nema mata yafiyar duk wani mai hakƙi a kanta ne tabbas ko da ace za a ƙara maka shekarunka a kan shekarunka