Showing 51001 words to 54000 words out of 100561 words

Chapter 18 - BAKAR TUKUNYA hausa novel

07 Feb 2026

463

ɗaya tak! Ne ya tara al’ummar gidan karankatakaf ɗinsù a ƙofar ɗakin Habu har da Ya Mustapha wanda ya ke kwance a ɗakin Yadikko ana ƙara masa ruwa, dan wata matashiyar budurwa ta na shiga cikin parlourn ta ce "ga Nuratu chan ta shiga ɗakin Ya Habu, kuma basu fito ba…"
Ta yi maganar kamar mai
Yekuwa.
Dan haka aka fito rututu da masu barcin da masu ido biyu har wasu na bige wasu, dan yadda su ka shiga parlour da durufta tun a karon farko ya janyo kusan kowa ya farka dama.


Sama-sama su ka fara jin kuka mai haɗe da shauƙi, kafin kunnuwansu su fara jiye musu abubuwan da ya sanya dole aka tattara Yara aka yi ciki da su.
Yadikko bata Kai ga ƙarasawa inda Mustapha ya ke tsaye ba kawai ta ga ya daki ƙofar da masifar ƙarfi ta tafi ta buɗu ya afka ciki...
Tsit! Haka kowa ya yi wanda hakan ya yi dai-dai da tsayuwar bugun zuciyar Mustaphan a lokacin da ya gansu turmi da taɓarya kuma yanayin su duk biyun ya tabbatar masa babu guda da aka yi wa dole.

Faɗowar da ya yi waje ta baya ne ya sanya Yadikko ta daskare a wajen ta gagara motsi tsoro da karkarwar jiki su ka sanyata ta sume a wajen.

Asibiti aka kwashesu aka wuce da su ita da Mustapha wanda tun a gwajin farko aka tabbatar da ya rasu...zuciyarsa ce ta buga.
------------
Sosai mutane su ka tausayawa al’amarin yayinda Kaka Nura ko isashshiyar gaisuwa bai yi musu ba ya maka Habu a kotu wae ya yiwa ƴarsa fyaɗe.


Tun ranar da abun ya faru gaba ɗaya Habu ya gigice ya fita a haiyyacinsa sai dai kuma sai ya zamana kamar tsoron Nuratu(Annen) ya ke yi dan ko tsine mata in Yadikko ta na yi ji yake ba ya so…gaba ɗaya ba ya son abunda ta ke yi wanda hakan ya ɗaure masa kai tamau!! Dan shi dae ya san ya tsani Anne (baƙar tsana ma kuwa) tun usul gashi ita ta yi silar mutuwar ɗan uwansa kuma sun san ita ke korewa Adda samari dan suma waennan tunda aka ganta (Anne) da shi(Habun) Unguwa ta ɗauka shikenan su ka ce 'a ɗaga tukunna komai ya lafa' har yau ba su nemesu ba...da haka kamata ya yi ace ya sake tsanarta fiye da farko amma wani nauyi da tausayinta ya ke ji wanda sam bai san dalili ba…tun da ya haɗa jikinsa da nata gaba ɗaya nauyi da tausayinta ya danne tsanarta wadda ke danƙare a cikin zuciyarsa wanda kasancewar bai taɓa kasancewa da ko wacce ɗiya mace ba ya sanya ya ke tunanin to ko dai duk matar da ka kwanta da ita sai ka ji hakan a kanfa dukda kuwa ya san kamar da wuya dan in dai haka ne babu matar da za ta saka kara Mijinta ya tsallaka besides to ya mazinata ma su ke yi?.....
Waennan tunane-tunanen ne su ka sake hargitsa Habu yayinda takaicin yadda ya yi zina kuma ya kasa katsewa ko bayan da aka gansu har sai da ya je in da ya ke so.....su ka taru su ka maida shi duk wani firgichachche ga takaicin rashin ɗanuwansun wanda ya san shi da Anne ne sila.


A ɓangaren Uwani kuwa...
Gaba ɗaya itama ba ta san Ina kanta ya ke ba, zuwa wannan lokacin ta koma kamar wata mutum mutumi kuma hakanan ta ke jin duk duniya babu wanda ta tsana kamar Baba Yusufa!
Wannan dalilin ya sanya ranar sadakar ukun Mustapha da ya ce 'su fito su bar masa gidansa' ta yi tsalle ta dire ta ce 'babu inda za su je ae da kuɗin gadonsu shi da ita ya siya gidan...
Amma ya bata wani fanni a ciki ɗan ƙarami…'
Wanda hakan ya janyo kokwanta bayan duk an juya ana kallonsa da son jin ta bakinsa aka ga ya yi shiruu ya gagara cewa komai wanda shi a nashi ɓangaren al'ajabi ne ya hanashi magana dan sosai kanshi ya ɗaure zuciyarsa ta ƙuntata yayinda ya ji duk ya muzanta!
Duba da yadda ko satin baya da aka gama tsarawa akan an basu sati ɗaya su tashi!
Ita Uwanin ta yarda ta amince, itance ma ta dinga tausar sa akan 'ba komai ae ya ma yi ƙoƙarin zama da Nuratu da Ubanta!
In sha Allahu za su nemi wani wajen kar ya damu da ita she can take care of her self. Dan ko saboda Nuratu ba za ta bar Nura da ita(Nuratun) kawai ba gara in ta na tare da su ta na yi musu addu’a'.
Shiyasa yanzu da ta tara masa mutane tana ife-ife kamar ba Uwani ba gaba ɗaya kansa ya ɗaure ya ma kasa cewa komai.
Rashin sanin abun yi ne ya sanya ya ce mata 'ba komai' kawai ya sallami kowa ya shige parlour ya barta ita da Yadikko a waje su na ta hayya-hayya kamar za su cinye junansu abunda sam ba halin Uwani ba….

Nuratu kuwa ta na Ɗaki daɗi har kwanyarta! Domin kuwa aikinta ya na tafiya yadda ta ke so......
Ta inda ta ke da tabbacin a yanzu haka Uwani ko mutuwarta da kafirai bata tsanesu kamar yadda ta tsani Baba Yusufa ba!
Faɗa kuwa yanzu aka fara dan in har ta gansa su ka yi ido biyu to sai sun yi!
Maitar da ke tsakanin mayunwacin Zaki da ɗanyen nama aka yi amfani da wajen dasa ƙiyayya a tsakaninsu…
To shi Baba Yusufa da alama hakan bai kamashi sosai yadda ta ke so ba saboda Uwani ta fishi hauka, tunda a tsaye ya ke da addu’o’i Uwani kuwa wadda da dabara ta dan janyeta daga kan Azkar ta hanyar ɗauke littafan nata ta ɓoye sannan ta ci sa'a Uwanin ta soma al'ada a tsakankaanin kwanki ukun dan haka ta yi mata aikin a dai-dai lokacin da take al’adar, tabbas da alamun sun kamata da kyau!!!!..
In sha Allahu nan ba da jimawa ba ita da shi sai sun zama yadda wani abun ya na samun Baba Yusufa kowa zai shaida itace ta kashesa...
Shikenan ta jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya!
Ta san dai a prison Uwani sai dai ta yi ta kanta ba dai ta ce za ta yi mata maganin kafiya ko ta yi mata auren dole ba.…
Ta na wannan lissafin ta na cin biscuit ta na karkaɗa ƙafa ta na sauraron yadda Uwani da Yadikko su ke tashin hankali a waje muryoyinsu sun cike Unguwar.


A tsakanin sati uku kacal Nuratu da Ubanta wanda ya ke ji kamar ya haɗiye ɗiyar tashi saboda tsabar so da ƙauna da proud ɗin abunda ta ke yi dan zuwa wannan lokacin ya fahimci mai ta ke yi, su ka kusan tashin gidan nan...amma ba wae su-i-su ba! Uwani ne da Baba Yusufa kullum in sun haɗu sai dai faɗa, gashi har sun fara iƙirarin kashe juna tsabar baƙar tsana!
In su ka yi suka gama sai Uwani ta koma Ɗaki ta zauna ta rasgi kuka kamar ranta zai fita saboda ita dai ta san ta tsaneshi kuma su Nuratu da ita kanta ta san basu da gaskiya, a halin da ake ciki kuma ba ta so a tagaiyyara su a koresu a gidan dan sai dai su yi yawa a titi duba da yadda itama ta yi ƙaƙaff!!.
Idan ta na rigimar da shi sanyi ta ke ji a ranta amma da zarar an rabasu ta dawo Ɗaki sai ta fara ganin rashin kyautawarta, ko ba komai Baba Yusufa haifarta ne kawai bai yi ba.
Gashi gaba ɗaya ita kanta zuwa wannan lokacin ta san ta koma kamar wata doluwa kwata-kwata ko Abu ta ajjiye bata iya tunawa.....
Sometimes mantawa ma ta ke yi shin ta ci abinci ko ba ta ci ba!
Hatta sunanta wani zubin haka Kaka Nura zai yi ta kwala mata uban kira amma wallahi ta manta nata ne ballantana ma ta amsa..
Kuma duk ba komai ya janyo hakan ba sai tsabar ƙarfin asirin da Nuratu ta yi mata wanda ya fi ƙarfin kuruwarta. Gaba-ɗaya asirin da kuma ƙarfinsa ne su ka taru suka mayar da ita hakan.


Tsakaninta da Kaka Nura kam sai dai kallo dama babu duka ba hantara duk ya daina amma amfaninta a wajensa bai fi ya sakata ta yi masa abu in buƙatar hakan ta taso ba ko kuma girki dan gaba ɗaya hankalinsa ya sake komawa kan Yadikko wadda Nuratu ta rantse masa akan ta kusan zama Matarsa, shiyasa ya nutsu ya kwantar da hankalinsa ya rage hayagagar da ya ke yi da jin haushin kowa.


Tun satin rasuwar Mustapha lokacin da Habu ya ga ba zai
Iya jurar zage-zagen da Yadikko ta ke yiwa Anne ba ya tartare kayansa ya bar gidan a cewarsa ba ya son zaman ɗakinsa dan haka ya koma gidan maƙotansu da zama sai in ana rikici ne ya ke shigowa gidan, inda ya share sati uku da kwanaki uku a chan..
A ranar da ya tattaro kayansa ya dawo cikin gidan aranar ne Anne ta sanarwa kowa ta na ɗauke da cikinsa dan haka ko ya aureta ko ta tona musu asiri ta yi yekuwa a Unguwa.



Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING*
Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING*
Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139*

Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudin ku tested and trusted.

Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu....
location:Kano
Delivery:NationWide.
kar ku bari a baku labari, sai kunzo🙏
SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA

BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*

HUMAIRAH BULAMA

Yota

*22*

Sosai aka sha ɗan ƙaramin yaƙi a gidan dan Uwani cewa ta yi "sai an biwa ƴarta hakƙinta yayinda ƙiri-ƙiri Baba Yusufa ya ce mata "ba fa zai yiu ba wallahi muddin da ransa ko sama da ƙasa za ta haɗe ba zai haɗa jini da su ba.
Ae ba fyaɗe aka yiwa ƴaartata ba ita ta kai kanta"
Yadikko kuwa rufe Nuratu ta yi da duka ta na kuka ta na bugun cikin Nuratun, a cewarta 'duk ranar da aka haifi cikin nan ta san sai ta haɗiyi zuciya tsaf ta Mutu har lahira…tsabar baƙin ciki'
To dae wannan karon duk irin ƙaunar da Kaka Nura ya ke yiwa Yadikko ya gagara haƙura dan har marinta sai da ya yi saboda ta taɓa masa ƴa wanda hakan ya sake fusata Baba Yusufa aka kusan kwana ana rigima a gidan!
Har sai da shi da Uwani su ka yiwa juna alƙawarin ‘sai na ga bayanka/ki’.

Ba abunda ya ke sake baƙanta ran hatta ƴan Unguwa waenda su ke rabiya kamar yadda Uwani ta ke biyewa su Nuratu kwana biyun nan dan ƙiri-ƙiri kowa ya san a side ɗinsù ta ke shiyasa kusan duk aka ƙullaceta ake jin haushinta…
Sai kuma Habu wanda zuwa yanzu mazan layin su ke ce masa 'shanyayye' dama tunda aka kamasa da Nuratun ake ta zaginsa kowa ya na cewa shine ya kashe ɗan Uwansa, dan a ganinsu ƙaryar kaidin mace ko ya yake kuwa! Ta chanja masa akala haka lokaci guda, kawai komai da ya yi to ya yishi ne da saninsa dan biyewa son zuciyarsa…
To yanzu kuma haka nan Nuratu za ta zage ta zaage Uwarsa tsaf a gaban idanunsa amma ba zai taɓa cewa uffan ba, shiyasa kowa ya ke a wuya da shi...



Nuratu ta riga ta samu abunda ta ke so dan jama’a kowa ya gani ya shaida lokacin da Uwani ta cewa ɗan Uwanta “sai na ga bayanka, kuma gida ba za mu fita ba sai dai kai ka fita ka bar mana wallahi, a raye ko a mace…”
Gashi zuwa wannan lokacin wasu ma sun soma cewa Uwani taɓin hankali gareta duba da abubuwan da ta ke yi da yadda ta canja akala lokaci guda da kuma yadda ta ke a firgice ko da yaushe!
Wanda hakan ba ƙaramin daɗi ya sake yiwa Nuratun ba...
Dan haka a washegarin Daren ranar ta bi ta bayan windown ɗakinsa sai da ta leƙa ta tabbatar shi kaɗai ne babu Yadikko a ciki tukunna ta jefa masa ruwan maganin a ledar da ta zuba ba tare da ta ƙulleta ba a kan jikinsa sannan ta watsa fetir ta cinnawa ɗakin wuta!
Bayan ta yi amfani da abun shaye-shayenta marar ɗanɗano over dose tun magrib
ta zuba a cikin ruwan gidan kowa ya sha ya bugu maƙil shiyasa har sai da wutar ta cinye Baba Yusufa a cikin ɗakinsa ta fara kama wasu wajajen a cikin gidan tukunna da mugun kyar Habu ya fito ya na layi ya shiga ihun a kawo musu ɗouki dan ko gani sosai ba ya yi…sakamokon buguwar da su ka yi gaba ɗayansu ban da ita da Ubanta wanda ta cewa kar ya sha ruwan gidan dan har a na ɓangarensu ta zuba saboda kar Uwani ta fita da kwarinta ta kawo jama’a a kashe wutar ba ta riga ta kashe wanda ta bayar a sacrifice ba.


Garr! Su ke ita da Kaka Nura amma suka ƙi
motsi suma..
Sam babu wanda ya ji ife-ifen Habu dan a hankali ya ke yi sosai, har ya zube a wajen...ya na ganin wuta amma ya kasa taɓuka uwar komai...
Ga wuta nan ya na gani ta winduna ta na cin ɗakin Baba Yusufa kamar hauka sannan ta na cin ɗakin Yadikko da parlour, ya na jin wasu kalar koke-koke mai alamun salati ne ake yi, da su ke tabbatar da masu yi su na cikin azaba ne amma ya gagara motsi, takaici da baƙin cikin hakan ya sanya ya sume a wajen kawai.


Su Nuratu, sai da su ka tabbatar wutar ta je inda su ke so..su ka kintaci lokacin da ya ci a ce ta yi yadda su ke so tukunna ta ɗauka
waya ta kira wani a layin muryar a hankali sannan da kyar ta shiga cewa "wuta ta kama, su taimaka musu, ita dai duk cikinsu kowa ya kasa motsi bata san mai ya faru ba da kyar su ke iya fitowa tsakar gida ma…"
Dama hayaƙi da ƙauri ya tashi wasu a cikin maƙwafta... a haka ma wutar ba ta yi hayaƙi sosai ba saboda babu kayan katako sosai da abubuwan da za su taimaka mata ta bada hakan(hayaƙin) a cikin gidan amma dukda haka ƙauri da hayaƙi sai da ya tado wasu daga cikin maƙwafta ya kawo su ƙofar gidan ana ƙoƙarin ɓalle ƙofar ne ma Nuratu ta yi kiran wayar.
…………
A hankali Nuratu ta miƙe ta na kallon Uwani wadda itanma ta ke kallonta ta na hawaye itakam ko ƙoƙarin da Habu ya yi ma ta kasa dan ba ta jin alamun ƙafafunta ma kwata-kwata a jikinta!....
Juyawa kawai Nuratun yi ta fita ba tare da ta yi mata komai ba...lokacin wutar har ta yi ƙarfi! Hayaƙi ya game koina a gidan har ba a gani sosai…
Yanzu in ta fiddata ta san za ta iya cewa ba ita bace ta kunna wutar, kuma a yadda ta san Uwani ta tsaneta tsaff za ta iya tona mata asiri dan in bata ji wasu ba to tabbas ta san ta ji wasu daga cikin maganganunsu ita(Nuratun) da Kaka Nura, dan haka gara ta ƙone ta na cikin jinya a yanke mata hukunci ko kuma ta wuce kawai saboda har ga Allah ita dai kullum dubawa ta ke yi ta na sake dubawa amma bata ga amfanin Uwani a rayuwarta ba!
Gara Kaka Nura sun fi fahimtar juna, ya na sonta sannan kuma ba ya daƙile ta ba ya ƙoƙarin hanata yin abunda ta ke so sai dai ma ya goya mata baya...
Uwani kuwa liability ce kawai.
Shikenan yanzu za a yi case da victim da suspect duk sun mutu dan haka bata da damuwar komai sannan bata da jigilar zaryar zuwa prison.


Da wannan tunanin ta fita zuciyarta fes dan ta san a yadda ta bi duk sharuɗan boka tabbas duniya a tafin hannnunta ta ke, dukkan burikanta ta san za su cika in sha Allahu.

Ta na fita ta ji ana gab da ɓalle ƙofar ma dan haka ta yi sauri ta nemi waje kusa da Habu ta wani kwanta fuskokinsu su na kallon juna.
.........
Har ya miƙe zai fita sai kuma ya kalli window ya ga zai iya fitar da Uwani dan katangar babu tsayi kuma baya dogon lungu ne, dan haka ya koma ya ƙarasa ɓalle net ɗin windown ya kinkimeta ƙarshe ma ya yi kamar ya goyata tukunna ya fice da ita daga windown ya taka abu ya fitar da ita daga cikin gidan.

Sai da ya fitar da ita daga layin ya ajjiyeta a wani kongo Allah ya so shi ba a ganshi ba dan lungun babu fuskar gida ko ɗaya, ya dawo, ya na shiga cikin ɗakin ya kwanta dai-dai mutane su na shigowa dan zuwa wannan lokacin an gama fidda kowa shi da Uwani ne kawai ba a gani ba.

Ana ƙoƙarin ɗaukarsa ya na ce musu "su fara fita su kamo Uwani ta yi hanyar banɗaki yanzunnan ita ce ta kunna wutar....."
Ba su wani biye masa ba su ka ɗaukeshi aka saka shi a mota duk aka yi asibiti da su.
Inda ya samu ya zille bayan wasu ƴan awanni ya koma ya je ya ɗauki Uwani gabannin asuba ya wuce ƙauyen Tofawa da ita.

BAYAN KWANA BIYU….
Baba Yusufa ya cika da imani dan da kalmar shahada ya rasu a bakinsa bayan an fidda shi a ƙone daga cikin ɗakin nasa...ana shirin saka shi a cikin mota a kaishi asibiti ya ce ga garinku nan…

Unguwar gaba ɗayanta a hargitse ta ke a wannan lokacin sannan cikin jimami dan sai da wutar nan ta kai asuba ta na ci da mugun kyar aka kasheta kasancewar a makwaftansu...Yaron gidan ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login