Showing 42001 words to 45000 words out of 100561 words

Chapter 15 - BAKAR TUKUNYA hausa novel

07 Feb 2026

475

ban mamaki, shiyasa kawai Uwani ta nemi sallama su ka dawo gida ba tare da ta shirya ba, bayan ta tabbatar Amarya ta wuce Gidansu.


An samu hutu daga Kaka Nura sakamakon rashin lafiyar da ya kwanta mai tsanani tunda ya dawo daga hannun ƴan sanda, yayinda wasu su ka ce Baki ne ya kamashi dan zuwa wannan lokacin Kaka Nura ya yi popular a Unguwar sosai saboda bala'i da halayensa ko ina zancensa ake yi, in dai ana so a bada misalin mugu, butulu, ɗan iska, marar mutunci d.d.s to da Kaka Nura ake gwadawa.

Ya yi jinya sosai kamar ba zai tashi ba, yayinda Uwani ta zage dantse wajen kula da lafiyarsa da jikinta da kuma aljihunta, dan bayan sana'ar gwanjo har da wasu sana'o'in ta kakkama...
Tausayinta ya sanya Baba Yusufa bai ƙara zancen su tashi ba dan in aka tashesu a haka bai san ya ƙanwartasa za ta yi ba bai kuma san da wanne za ta ji ba, shiyasa ya toshe kunnuwansa daga bala'in Yadikko wadda tunda ta fahimci Mustapha son Nuratu ya ke yi ta ɗaga hankalinta kamar wadda aka yowa wahayin tashin hankali.
Hankalinta bai kwanta ba har bayan ta tabbatar ta nesantashi da Annen, ta inda ta turashi karatu chan da nisa (gidan Baba Ali)
gaba ɗaya ta ɗaga hankalinta ta birkice har kauce hanya sai da ta yi wae dukdan ta rabasu kuma Nuratun(Anne) ta sani amma kawai sai ta rabu da ita dan itanma ta na buƙatar iska daga Mustaphan, saboda duk a takure ta ke jinta (ta ɗaurawa kanta kissa da shiryuwar dole shiyasa ba damar ta yi duk wani abu ba dai-dai ba a gabansa) gashi ya na da sakin hannu da kyauta kuma ta hanyarsa ta na ƙunsawa Yadikko ta yi ta haɗasu faɗa shiyasa ta gagara ce masa ba ta sonshi kuma ta ƙi daina yin duk wata kissa da ta ke yi a gabansa....shiyasa ta ji sauƙi da ya bar gidan.
Yayinda ta ke yiwa Yadikko kallon mahaukaciya saboda ita a ganinta in da ace ta na sonshi(Mustaphan) to fa ƙaryanta ta gwada mata bin malamai har ta rabasu. Kuma ko a yanzu ba wae ta rabasun bane ba dan ya na nan manne da ita kullum maganarsa ɗaya ba sauyi 'da zarar ya gama karatu ya na dawowa za su yi aure' ita kuwa ta raina arziƙinsa sam kuɗinsa bai yi mata ba shiyasa ta daɗe da tsarawa kanta ba za ta taɓa aurensa ba.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Sai da Kaka Nura ya yi shekara Uku ya na rashin lafiya tukunna aka samu ya warke da izinin Allah, wanda tunda Allah ya sa ya warke ya fara ta kan Uwani dan wani hali ya tsiro da shi sabo ya ɗaura a kan tulin mugayen halayensa..abunda da bai saba yi mata shi ba wato 'duka'.
°°°°°°°°°°°
Shekaru sun ja...
yayinda Adda ta kammala secondary daga nan ba ta samu ta ci gaba ba, Arabi kuma sauƙarta biyu Anne kuwa ko jenior ba ta samu ta iya kammalawa ba saboda tsabar baƙin daƙiƙancinta da bala'insu ita da ubanta dan ƙarshe haƙura su ka yi da karatun gaba ɗaya ta ce ta gaji, shi kuma ya ce shikenan dan haka ta ke zaune ba bokon Arabin ma babu saboda haka nan Anne ta ke kamar wata mai Aljanu ko wajen da ake karatun AlQur'ani ba ta iya zama kwata-kwata, kamar yadda Ubanta ya alƙawaranta dai ya na koya mata yadda ake sallah, duk ta san karatun sannan ta haddace wanda za ta iya dan kasancewar kwakwalwar ba ta ja ne ma ya sanya a yayin tsayuwa Nasi ta ke karantowa kullum bayan fatiha dan su ta iya ta haddace... karatun tahiya shima ta kasa riƙewa yadda ya kamata, wanda za a iya cewa Sallar tata 'da babu gara ba daɗi' dan sam ba ta yinta a nutse sannan sai in ranta ya na a ɓace ne tukunna ta ke tunowa da Ubangijinta ta bauta masa.

Yawo kuwa a cikin Anne kamar ta ci ƙafar kare....
Gashi Uwani ba ta isa ta yi magana ko ta hana ta fita ba tuni Kaka Nura zai gwada mata abinda ya fi kwarewa a kai wato tijara, ita Uwani babban damuwarta ma inda Annen ta ke samo kuɗi saboda komai na Anne mai tsada ne, waya dai ta san Mustapha ne ya siyo mata amma kayan sakawa da cimar da ta ke shigowa da su cikin gidan ta san ba daga shi bane ba kuma ta san babu wani saurayi apart from Mustaphan da zai yarda ya kashe mata kuɗi a banza....
Tabbas Uwani ta na ƙoƙari, dan tsoronsu wanda ta rasa ta yaya ya dasu a zuciyarta ba ya hanata ta ƙi yi musu wa'zi da kuma addua daga Annen har Kaka Nuran wanda a kullum ya ke sake godewa Ubangiji da ya bashi ƴa mace dan tunda ta fara riƙe shi ta na tufatar da shi da ciyar da shi shikenan kakarsa ta yanke saƙa ya ke jin kanshi a sama dai-dai da uban kowa.
Shiyasa sam bai wani damu da rashin auren naya ba tunda dai ba su da matsalar kuɗi gashi ana kashe mata kamar hauka kuma shi dama ko menene Anne ta zaɓa ta nuna zai goya mata baya ɗari-bisa-ɗari.
Shiyasa Uwani kawai ta dage da Addua dan ita kaɗai ce mafita har da Adda itama ta na taya ta da adduar wadda sam ba ta gajiya da yi mata wa'azi itama dan ko Anne ta ɓoye wasu mugayen halayenta bin maza abu ne wanda ba zai ɓoyu a halaiyyarta ba kowa ya shaideta da wannan.

A lokacin da Anne ta rufe shekaru sha takwas Adda kuma ashirin dai-dai, duk wata sa'arsu a Unguwar ta yi aure amma banda su....
Ita dai Anne za a iya cewa ba ta samu Mijin aure ba ne, kasancewar ta lalace kuma ta fanɗare tun kafin ta balaga ma, wanda hakan ya taka gudummawa kwarai wajen hanata samun mijin aure bayaga rashin farin jinin da ita kanta ta shaida ta na da shi, sai kuma mai kankat wato 'lokaci'....duk ƴan iska ne samarin nata babu mai nemanta da aure sai dai lalata, kuma haka nan ta ke ba ta da wani farin jini dama tun chan...dan a yadda ta ke da kyawu har ƴan Unguwar su ke yi mata laƙabi da 'wanke hannu ka taɓa' tabbas adadin farin jinin da take da shi ya yi rauni matuƙa a mace kamarta dan hatta samarin nata ƴan iskan ma kusan duk ita ce ta ce ta na sonsu, wasu kuma ta ƙarfin tsiya ta ke jawosu tunda Allah ya sa idanunta su ka buɗe da bin malamai.....shiyasa su na gama abunda ya kawo su su ke ɓacewa ko damar damƙarsu da maganar aure ba sa bata ballantana ta yi.
Adda kuwa ta taso da farin jini matuƙa ta inda kowa in ya zo gareta da maganar aure ya ke zuwa, sai dai kuma in aka yi bincike aka tabbatar da ƙawar Anne ce kuma ƴar Uwa a gareta sai iyayen manemin nata su janye jiki da dabara, an yi haka har kusan sau uku wanda zuwa wannan lokacin Yadikko ta yi Yaji ya fi sau biyar ana maidota duk akan sai an kori su Anne daga gidan amma Baba Yusufa ya ƙi kulata saboda shi ya san Ubangiji ne mai lokaci, dan haka Yadikko ta dasa Allah ya isa kawai ta ci gaba da yiwa Addan tata Addu'a, ta na mai ji kamar ta bi dare ta cinnawa Nura da ƴarsa wuta har ma da Uwanin duk su mutu kowa ya huta.


Da taimakon ƴan Unguwa aka samu aka wanke Adda bayan sun yi mata kyakkyawar shaida saboda da farko-farko in an zo ba a bincike a kanta kwakkwara daga anga gidansu ɗaya da Anne sai a yi musu kuɗin goro....
Dan haka wannan karan iyayen manemin nata(waenda su ka kasance ƴan uwa ga makwabtansu) su ka tsaurara bincike luckly su ka karɓeta hannu bibbiyu bayan sun ji kyawawan shaidu akanta daga wajen ƴan uwansu da su ka kasance neighbours da ita Addan da kuma ƴan Unguwa.
Murna a wajen Yadikko ba a magana dan mutumin yanzu duk ya fi na baya, mai hankali, dattako da rufin asiri sai dai tunda Allah ya sa Anne ta ga Adda ta yi sabon saurayi gaba ɗaya duk sai ta gagara sukuni, dama chan duk ranar da Addan ta yi saurayi ba ta iya barci dukda kuwa itama ta na da nata samarin amma ta san ba aurenta za su yi ba kuma haka nan ta ke ji ba daɗi da baƙinciki in aka ce a na son Addan, shiyasa ta ke ɗaga hankalinta sannan ta dage da sallah ta na gayawa Allah kar ya bari Adda ta rigata yin aure, har sai ta ga abin ya lalace tukunna hankalinta ya ke kwanciya.
To dai wannan karan ba ta ga alamun saurayin Addan ya na da shirin fecewa ba dan haka tashin hankalinta sai ya fi na kullum, daɗin daɗawa tunda Allah ya sa su ka gaisa ta yi eyes to eyes da Yaron shikenan ta ji duk duniya babu wanda ta ke so sai shi.


Ta so ta kawar da tunanin a kanta ta so ta manta da komai duba da yadda su ke ita da Addan amma duk sai ta gagara, ba ta iya yin barci gashi duk ta rame ta fige ta gigice gaba ɗaya ko abinci ba ta iya ci sosai....
A ganinta ta yaya Adda za ta fita farin jini bayan ta fi ta komai-da-komai.
Gashi ita a lokacin ko maskini mai niyyar aure ba ya kulata, A Unguwar kuwa hatta ƴan iskan ma duk sun yi sun gama da ita sun kama gabansu gashi kowa ya san halinta ana ta munafurcinta, dan haka duk yadda ta so sai kishi ya ƙi ya barta ta yi farin ciki ta bar Adda ta yi auren...


Ta fi so sai ta yi tukunna itama Addan ta yi, gashi sam ba ta ga alamun aurenta nan kusa ba dan hatta Mustaphan da ta rainawa hankali (Mutum ɗaya a duniya da ya taɓa yi mata maganar aure) kuɗinsa bai yi mata ba, kuma Baba Yusufa shima ba ya so, shi(Mustaphan) kaɗai ya ke ta haukarsa amma iyayensa sun tsaneta dan haka yadda ta ga iyayen manemin Adda su na yi mata kamar za su cinyeta saboda so abun sai ya ƙarawa kishin nata ƙaimi.

Dan haka ta tsara akan dole sai Adda ta jira kalar Mijin da ta ke so ya ƙaraso ta (Annen) yi aure tukunna in Yadikko ta nutsu wataƙila ta barta ta yi auren.
Shiyasa ta tashi ta tsaya da duk ƙarfinta da son ganin ta hana Adda yin aure...
Gashi a lokacin Yadikko ta ɗaga mata hankali da gori na yau daban na gobe daban musamman in ta lura Kaka Nura ba ya cikin gidan, wani zubin Yarinyar ta kulata wani zubin kuma kawai sai ta rabu da ita domin kuwa a wannan Lokacin babban burinta shine ta raba Adda da wannan aure ba wai Yadikko
ce a gabanta ba!
Matar da ta ci burin tarwatsawa rayuwa har gaban abada.

Akwai wani a cikin samarinta Mahaifiyarsa kwara ce yayinda Mahaifinsa ya kasance ɗan bori, ba ta ɓoye masa ba ta ce masa ƴar uwarta ce za ta yi aure ita kuma bata so ta rigata yin auren, dan gashi har an fara yi mata gori, Abu ɗaya ta ɓoye ba ta gaya masa cewar ta na son shi Yaron bane ba , saboda dama ita wannan mutumin ba da shirin aurensa ta ke ba, shima kuma haka dan shi a lokacin ma matansa biyu kuma bashi da niyyar ƙara wani auren dan har ya gaya mata ma ba zai iya aurenta ba.
Watsewa ta kawosa wajenta ita kuma kwaɗayi da son abun duniya ya sanya ta ke kulashi.


Dan haka su ka yi agreement ta inda za ta debe masa kewa na tsahon mako biyu in sha Allahu shi kuma zai tsaya mata har sai ta tarwatsa auren Adda.
A wannan lokacin ko maganar hidimar biki in Adda ta yi da saurayinta sai ta gayawa Anne dan komai da ita ake shiryawa kusan ita za a cewa ƙirjin biki…
Gashi ita ce babbar ƙawarta sannan itace sister ɗinta.
Ƙiri-ƙiri gashi dai Yadikko
ba ta so amma Mahaifin Addan ya tashi ya tsaya ya ce wallahi ba ta Isa raba musu zumunci ba
In batun ɓata tarbiyya ne shi ya san Nuratu ba ta Isa ta ɓata Adda ba kuma Addan ma gidan Mijinta za ta tafi dan haka ta barsu na ɗan lokaci ne kawai…komai ya kusan wucewa.
Gaba ɗaya kamar an toshe masa kwakwalwa haka nan ya bi bayan a bar Adda da Nuratu saboda ya na ganin ae aure ne ma ƴartata za ta yi.
Ba dan Yadikko ta so ba ta koma gefe ta zuba musu ido kawai tsanar Anne ta na daɗa ninƙaya a cikin zuciyarta....
Ta samu ta tura Mustapha inda ɗan Uwansa yake amma dukda haka hankalinta ba a kwance yake ba, gashi Mustaphan shima ba ta barshi ba dan sarai ta san su na waya sai dai kasancewar zuwa wannan lokacin ita kanta ta san Nuratun ba wani son Mustaphan ta ke yi da gaske ba ya sanya ta ɗan kwantar da hankalinta sai dai takaicin ganin da Mustapha da Adda har zuwa wannan lokacin ba su fahimci Anne ba son ɗan nata ta ke yi tsakani da Allah ba ya hana ta sakawa zuciyarta salama.
Wanda abinda Yadikko ba ta sani ba shine ita kaɗai Allah ya bawa wannan baiwar, ta iya gane Nuratu, dan kamar hawainiya haka ta ke, shiyasa itama Adda ta sake mata sam ba ta gane ta na mata baƙin ciki ba wanda hakan ya bawa Anne dama ta samu ta shiga jikinta kwarai da gaske ta dinga asirceta ba dare ba rana....
Har ta kai ga yi mata illoli mabambanta..dan ta sha bata magani ta ce mata maganin mata ne ko na gyara ita kuma ta karɓa ta yi ta afawa wani abun kuma a ruwan wanka ta ke zuba mata wani ta saka mata a kaya wani a abinci a man shafawa d.d.s.......
Cikin ƙanƙanin lokacin ta
saka mata warin jaaɓa a wajen saurayin, ta tura mata aljanin da ke sauya mata kamanni in ta fita zance wajen duk wani Namiji sannan ta cireta gaba ɗayanta a cikin zuciyar saurayin da danginsa har ma da Abokansa
sannan ta rufewa Yadikko baki ruff akan ta gagara yin magana kuma ta ɗaure mata hannu tamau saboda kar ta yi komai, gudun kar tausayin ƴar tata ya ci ƙarfin aikin da ta yi har ta kai ga a ji yunƙurin yin wani abun ya sanya ta shiga ta fita ta cire Addan a cikin zuciyar Yadikkon itama gaba ɗaya…
Wanda aka yi asiri a jikin wata gawa aka yi rashin sa’a gawar ta yi kwanan Keso cikin dare gobara ta tashi komai ya k’one kurmus shiyasaaa har gobe tsanar Adda ta ke sake yin tasiri a cikin zuciyar Yadikko….


Rana tsaka uwar saurayin Adda ta zo ta ce "an fasa"
Juyin duniya kuma ta ƙi faɗin abunda aka yi musu ta ce ba komai ƙarshe ma ta ce 'an bar musu kayan toshi da aka kawo, sun bar musu komai, kawai Allah ya haɗa kowa da rabonsa'.
Ta na gama faɗiin haka ta juya ta fice ranta ya na a ɓace har a lokacin...
Jiya ɗanta kwana ya yi ya na mata kuka akan baya son auren to kuwa a kan me za ta yi masa dole saboda farin cikin wasu?
Ta na wannan lissafin ta wuce zuwa gida abunta
Yayinda Nuratu ta ji wani masifaffen daɗi kamar an yi mata bushara da gidan aljannah...
Ba abunda ya ke sake ƙona mata rai irin yadda ta lura Addan kamar ma wani sabon kinibibi ta ke yi mata tunda auren ya matso...magana kaɗan komai sai ta ce wani 'her soon to be husby'
Ae yanzu sai ta ga ƙaryar Iskanci.


Tabbas Adda ta girgiza matuƙa, dan sai da Yadikko ta kusan yi mata shegen duka saboda takaici tukunna ta tattara ta koma wajen Anne su ka taru su ka dinga kukan tare....
Dan ƙarshe ma sai da ya zamana Addan ita ta ke rarrashin Anne saboda uban takaicin fasa auren da aka yi da ta nuna ta na yi….
A washegarin ranar Anne ta tari Yaron har wajen aikinsa da zancenta bayan ta tsafe jikinta tsaf sai dai cikin hukuncin Ubangiji abun nata bai kamasa ba dan fata-fata ya yi mata sosai kuma ƙiri-ƙiri ya ce mata "ba zai auri karuwa ba"

Bayan kwana biyu, bayan ta je ta sake haɗo uban kayayyakin asirinta za ta yi masa kawai ta ji labarin ya yi aure ya bar garin(sun tafi honeymoon)
Duk Inda ta je sake tabbatar mata ake yi akan ba Mijinta bane ba amma za’a iya gwada sa’a shiyasa kawai ta haƙura ta bar mata (matarsa) shi.


Ko wata ɗaya kwakkara ba a yi ba wani saurayin ya sake fitowa Adda.


BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*

HUMAIRAH BULAMA

Yota

*19*

Ko wata ɗaya kwakkara ba a yi ba wani saurayin ya sake fitowa Adda.

Shi kuma ɗan gidan Malamai ne sosai shiyasa ko ya zo baya ganin duk waennan abubuwan.

Tunda Allah ya sa Nuratu(Anne) ta ji ta gani wannan karon ma sai ta gagara kau da kai, a ranta har ta na mamakin shin wae ta yaya Adda ta ke samo kyawawan maza masu kwarjini da ɗaukar hankali......
Tashi ɗaya ta burkice.
A lokacin sun rabu da ɗan ɗan bori saboda lokacin da su ka ɗauka ya cika amma fa garin raba auren Adda na baya ya harhaɗata da Malamai da bokaye mabanbanta...
Dan haka ta tashi ta tsaya wannan karon ma.
Wani zubin ma in ta je wajen Malaman bata da kuɗi cewa su ke yi sai dai su yi amfani da ita a bakacin ladan aikinsu a hakan kuwa ta ke amincewa kuma da yake Yarinyace ko batun kariya bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login