Showing 63001 words to 66000 words out of 100561 words
baku labari, sai kunzo🙏
SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA
BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*
HUMAIRAH BULAMA
Yota
*26*
Ya kafeta da shanyayyun idanunsa bai ce komai ba kawai ya na kallonta wanda hakan ya sake kiɗimata cikin rawar murya ta ce “ddd-da-maAnn…”
“Ina Islamiyyar?”
Dakakkiyar muryarsa ta katse tata siririyar Muryar.
Zuwa yanzu gaba ɗaya ta kiɗime, ba za ta iya cewa ga lokacin da Ya Abba ya daketa ba dan babu amma wallahi in yana waje ba ta samun nutsuwa har sai ya bar wajen…
“Na zama sa’an wasanki kenan”
Ya faɗa hakan cikin muryar da ke baiyyana ransa ya soma ɓaci dan ya tsani kyaliya.
Ɗaya daga cikin ɗabi’un Amal shine saurin kuka, dan haka a take idanunta su ka cika tap da hawaye kafin kuma ta ɗago a hankali ta na kallonsa sai kuma ta yi saurin kawar da kanta gefe ta fara magana “ba zan je ba yau, Anne ce ta aikeni gidan Hajiya Altine in karɓo kaya.”
Kusan mintuna biyu da gama maganar jin bai ce mata komai ba ya sanya ta waigo ae kuwa karaff su ka haɗa idanu….
Da ace ya san gidan tabbas Amal ba za ta je ba zai je ne kawai ya karɓo kayan da kansa ya dawo.
Dan in har ya yi guessing dai dai to Hajiya Altine itace ya ji Baba da Amir su na zancen cewa Yaronta ya na son Amal ɗin, sannan matar gaba ɗayanta sai a hankali, yo to dama duk ƙawayen Anne da ta samu ta ke hulɗa da su a wajen Unguwar ae duk sai addu’a kawai kusan halaiyyarsu duk ɗaya….Matar bata taɓa haihuwa ba amma ta raini Yara maza guda biyar waenda su ke sheƙe ayarsu a gabanta da ɗaurin gindinta…
A karo na uku Amal ta ɗan sake satar kallonsa ganin ya kafeta ne kawai da shanyayyun idanuwansa ya sanya ta sake sunkuyar da kanta ƙasa ƙirjinta ya na mai ci gaba da bugawa….
“Jira a nan”
Kawai ya ce mata, daga haka ya wuce ya bar wajen ransa a ɓace, sai dai ba ka isa ka ga hakan kwance a kan fuskarsa ba.
Ya na wucewa Amal ta sauƙe wata bahaguwar ajiyar zuciya ta na mai sakin numfashinta yadda ta ke so saɓanin ɗazu da ta ke yin komai a ɗarare.
Dukda ta san bai san gidan ba sai ta tsinci kanta da addu’ar ‘Allah ya sa kar ya shiga sabgar Anne ta inda zai iya cewa ta zauna shi ya je’
Dan ta san Ya Abba da Anne kamar wuta da auduga su ke a kan hakan tsaf sai a iya shafe sati ɗaya ana case…….
Ta na wannan lissafin ta na ta faman waige-waige gaba ɗaya tsoro da fargabar da ya dasa har yanzu ba su barta ba ga kuma banɗokin mai ya ke da shirin yi sai kuma tsoron kar ta je Anne ta ga mayafi ta biyota a baya har ta kai ga cin mata ya Abba bai ƙarasoba…..
Ƙarar machine ta ji dan haka ta waiga ai kuwa shi ɗin ne kamar yadda ta zata, kafin ƙiftawar ido ya ƙaraso inda ta ke tsaye ya ce “hau”
Kawai ba tare da ya kalleta ba.
“Tsaka mai wuya kenan”
Ta aiyyana hakan a ranta ta na mai jin kamar ta zunduma Uban ihu.
Agogon hannunsa kawai ya ɗaga ya kalla ba tare da ya ce mata uffam ba! Ta fahimci Yaren nasa dan haka ta lallaɓa ta haye a hankali kamar wadda kwai ya fashe mata a ciki sannan ta matsa baya sosai.
Cikin nutsuwarsa ya kunna machine ɗin da sannu su ka kama hanya, su na tafe ta na yi masa kwatance a hakan har su ka ƙarasa…
Su na isa ta sauƙa ta tsaya shi kuma ya ɗan gyarawa machine ɗin zama sannan ya ce”jira a nan”
Bai bi ta kanta ba ya wuce zuwa gidan da ta yi masa nuni da shi ya barta a nan wajen tsuru-tsuru kamar an ritsa ɓera a buta gaba ɗaya tsoro yagame ta dan ta san dole Matar za ta sanarwa Anne ba Amal ɗin ce ta karɓa ba kuma ta na yi mata kwatance za ta gane Ya Abba ne.
Tsoro ya sanya zuciyarta over racing dan haka ta ɗan nemi guri ta zauna ta na jin kamar ta nutse kawai dan ta san dole akwai ƙalubale a gabanta yau…
Ta na zaune ta na ta saƙe-saƙen yadda za ta kaya yau ɗin ta ganshi ya dawo ga dai kayan nan ya karɓo bai bar musu ba amma kuma fuskarsa a murtuke fiye da ko yaushe dan haka a take ta sake rikicewa, kafin ta miƙe tsaye da kyar ƙafafunta su na karkarwa.
Ya na ƙarasawa gareta ya tsaya a gabanta gab dan har sai da ta ɗan ja baya tana mai ɗagowa ta ɗan saci kallonsa ba ta kai ga mayar da kanta ƙasa ba ya ce “wato zance za ki zo ki yi da! Ko?”
A rikice ta ɗago ta na kallonshi kafin ta hau girgiza masa kanta ta na gab da sakin hawaye ya ce “in ki ka bari su ka zubo sai na baki mamaki a wajen nan, zancen ne za ki zo yi mana tunda gashi matar ta na mini maganar ina ki ke wani ‘Mustapha’ ya na ta jiranki!”
Ya ƙarashe maganar tone nashi ya na baiyyana tsantsar ɓacin ran da ya ke a ciki.
Tsoro ya soma bata dan har kalar kwayar idanunsa sun soma chanja kala. Dan haka ta shiga ja da baya sosai cikin tsantsar fargabar kar ya yi mata shegen duka a wajen.
Kallonta ya ke yi sosai yana karantar yanayinta, kafin kuma kawai ya juya ya haye kan machine ɗin ya kunna batare da ya ce mata komai ba.
Ta san Mustaphan sarai dan tun ranar da ta rako Anne yanuna intrest ta shaidashi kuma ita har ga Allah tsoro ma ya ke bata bakinsa baƙiƙirin, a gabansu ya dinga shan taba ranar, shiyasa ta zaɓi ta bi Ya Abba ko da kuwa zai niƙata ne a hanyarsu ta komawa gida akan dai ta tsaya Mustapha ya ganta ya ce su yi zance.
Ta na gama zama ya juya akalar machine ɗin ya bar layin kamar mai fushi da titin.
Ita dai Amal ƙarshe runtse idanunta ta yi da masifar ƙarfi har aka ƙarasa gida ba ta yarda ta buɗe su ba dan ta gama sadaƙarwa…
………
Su na barin Unguwar Matar ta kira Anne, rai a ɗan ɓace ta sanar mata ‘Amal ta zo amma ita da saurayinta, dan bai ma barta ta shigo gidan ba itama ta window ta hangota, ya hanata shiga shi ya karɓi saƙon….
tun safe kuma Mustapha ita ya ke jira ko kasuwa bai fita ba, kuma ya fahimci da saurayin nata ta zo sannan ba ta ko shigo cikin gidan ba, ga shi nan sai faɗa ya ke yi wai an ci masa fuska an wulaƙanta shi.”
Ana cewa Amal ta zo ta saurayinta dama Anne ta fahimci Abba ne, dan duk duniya shi kaɗai zai iya yi mata wanna tsaurin idon. Kuma ta san Amal ba dai ta ko iya jerawa da wani namijin dan ita tsoron mazan ma ta ke ji, dan haka ta ci buri kuma ta ɗau aniyar tadama Abba hankali da shi da Adda wadda ta san ita ce ta bashi full goyon baya.
Dama tana gama waya ta je ta shiga zage Adda tass!!
Sai da ta ji tsayuwar machine tukunna ta fita ƙofar gida daga ita sai doguwar riga da hula.
……….
Ta na ji ya tsaya ta fara kiciniyar sauƙa jin hakan ya sa ya juyo zai yi mata magana ita kuma tsoron rashin sanin mai zai yi matan ya sanya ta sauƙa da sauri, garin saurin kuwa ta goga sangalalin ƙafarta a jikin salansar machine ɗin dan haka ta ƙona ta.
Ba ta san lokacin da ta saki wata ƙara ba ta fara ja da baya ba, ta na shirin afkawa kan itacen da maƙofcinsu ya tara zai yi faskarensu Ya Abba ya yi saurin ruƙota ta hanyar kamo hijab ɗinta sannan ya ce “ki nutsu mana! Me ye haka, mai ya faru?”
Sai kuma ya kalli ƙafar tata sannan ya ɗan durƙusa zai gani su ka ji Anne ta saki salati sannan cikin ɓacin rai ta ce “Fyaɗe za ka yi mata a ƙofar gida saboda tsabar rashin mutunci?.”
Sai kuma ta ƙarasa garesu ta kalli Amal ta ce mata “wuce cikin gida dan ******ubanki.”
Hawayen da ta ke ta ƙoƙarin riƙewa ne su ka shiga ziraro mata, kafin kuma ta juya da sauri ta wuce ciki jin Anne ta sake danƙara mata wani ashar ɗin a jere da maganar da ta yi mata ta farko ba tazara.
Amal ta na gama wucewa Ya Abba shima bai tsaya bi ta kan Anne ba ya fara yunƙurin wucewa amma sai ta saka hannu ta wani fizgoshi har sai da ta kai ga yaga masa rigar shaddar da ke a jikinsa dan Anne ba dai ƙarfi ba!
Da sauri mai kantin da ke a kusa da gidan ya fito ya na salati yayinda wasu a cikin waenda su ka gani su ka wurwuce kawai abinsu dan sun gaji da dramar su Anne.
Ya na ƙarasowa ya ce “haba mana dan Allah!
Cika shi ko meye ne kwa ƙarasa a cikin gida!”
Dai-dai nan Baba da Ya Amir su ka ƙaraso wajen.
Dan har an zagaya dama an sanar masa Anne da Adda su na faɗa tun ɗazu, luckly kuma su na tare da Ya Amir a lokacin.
Wani ƙululun takaici ne ya mamaye Ya Amir ganin yadda ta ke tsaye a waje ko mayafi babu, dan haka kamar mai shirin fashewa da kuka ya ce “Anne babu ko
Mayafi fa a jikinki. Babu kyau ki koma ciki dan Allah.”
“Ae duk laifina ban kaishi ba! Kun san kuwa mai ya yi? A ƙofar gida saboda tsabar mugunta ya ke ƙoƙarin kwaɓe mata kaya!”
Sai kuma ta juya ga Ya Abba wanda ya runtse idanunsa kawai ya na salati a cikin ransa sannan ta ce “mun yi maka sutura amma shine tsabar butulci mu za ka wulaƙantamu ko? In da kara ae Amal dai na ga ƙanwarka ce bai kamata ka ji ko da ƙanƙanuwar sha’awarta ba ballanta har ka so baje bajintar kwartancinka a kanta”
Zuwa wannan lokacin duk an fara taruwa a wajen dan wasu sun gagara kauda kai.
Da ƙarfi Baba ya runtse idanunsa, sai kuma kawai ya juya ya bar wajen, dama ya yi tunanin ita da Adda ne shiyasa ya zo ya rarrashi ƙanwar tasa kuma ya yi tunanin a cikin gidane, amma tunda hau ɗin nata a waje ne kuma da namiji ba zai biyeta ta bashi kunya ba dan ya san ba iya comtrolling Anne zai yi ba, Abba kuma ya san muddin ya na tsaye a wajen ko marinsa za ta yi ba zai ce mata komai ba dan haka ya ga gara ya basu guri......
Ya Amir ne ya sake matsowa kusa da ita da ƙoƙarin ganin ya kareta dan an cika a wajen wasu sai ƙus ƙus su ke yi su na mata dariya a ganinsu mace kamar Anne dai bai kamata ace ta damu da wani abu wai shi mutunci ba tunda kowa ya shaida ba ta da shi….
Ƙasa-ƙasa ya ce “Anne har da Amal fa ki ke tozartawa..”
Wata ƴar taya ɓera ɓari ce ta matso itama sannan ta ce “kai kuwa Abba mai ya kaika, kar ka ciji hannun da ya baka abinci mana..”
Da sauri Ya Amir ya juya gareta bai san lokacin daya ce mata “ba haka bane ba fa!”
Tunkuɗeshi Anne ta yi sannan ta saka hannayenta duk biyun ta cukumo wuyar rigar Abba da kyau tukunna ta ce “ka juya min kwakwalwar Yaro kalli yadda ya ke ƙaryatani ba tare da ya bi baasi ba sannan yanzu ka biyo Yarinyata za ka….”
Ɗiff!!! Haka ta ɗauke wuta sakamokon ware mata shanyayyun idanunsa da ya yi waenda su ka
soma ƙanƙancewa sannan su ka yi wani kalar jaaaa na ban mamaki.
Ita dai ta sani kuma ta shaida ba ta da tsoro amma ba ta san dalilin da ya sanya ta ke shakkar Abba ba!
Muddin su ka haɗa ido da shi to sai gabanta ya yanke ya faɗi ta ji kamar zuciyarta ta tsage ne kuma duk wata kalar masifa da tsiwarta ƙaryanta ta ce za ta yi masa.
Yanzun ma kasa magana ta yi sai kuma ta sauƙe hannu ɗaya ta kama ƙugunta da shi sannan ta kawar da kanta gefe ta na girgiza.
Muryarsa a matuƙar shaƙe ya ce mata “cika ni!”
Da mugun kyar ya na mai dannar kanshi da addu’ar Ubangiji ya bashi damar riƙe kan nasa saboda ya san in ya ce zai finceke to tabbas sai ya iya karyata a wajen ma shi kuma kunyar Amir ya ke ji a halindaake ciki Yaron ya na bashi girma tamkar ciki ɗaya su ka fito.
Tabbas in ba ƙarya ƙwaƙwalwarta ta ke yi mata ba kamar alamun matsanancin tsoro ne ta ke ji ya na rufeta dan gashi hatta hannun nata da ta riƙesa da shi karkarwa ya soma yi…
Haka kurum ba ta san dalili ba ta cika shi a lokacin da ya sake ce mata “cika ni”
A karo na biyu.
Wuff kamar mai shirin tashi sama ya wuce ya shige ciki
Direct ya afka ɗakinsa ya banko ƙofar ya saka sakata dan ya san Amir zai biyo sa tabbas.
Shiruuu wajen ya kasance bayan wucewar Ya Abba kafin aka soma watsewa a hankali a hankali.
Dukda ta so ta yi masa cin mutuncin da ya fi wannan ne sannan ta so ta kawo silar da za a ce ya bar gidan ne amma ta ɗan samu relief!
Ita ba Yarinya ba ce ba dan haka sarai ta fahimci tsare gida da takurawar da Abba ya ke yiwa Amal akwai wata a ƙasa tunda da gani Yaron maye ne ya nace sai ya auri jininta!
Ta samu ta rabashi da Afra shine saboda rashin zuciya ya ke wani shishshigewa Amal to ko ma ba so bane ba ita kam ba ta so!
Sam-sam! Ba ta ƙaunar alaƙarsu ko wacce kala ce shiyasa ta yi wannan borin saboda yanzu ta san shi kansa zai ja jiki ya kuma ji kunyar sake shiga sabgar Amal ɗin, sai kuma baƙin cikin hana Amal kula Mustapha da ya yi (ya yi mata kutse)
Hakan ma ya taka rawa wajen ingizata ta tozartashi, dan ya jawo mata asara yau ɗinnan ta ci burin abunda ta yi tunanin Amal za ta dawo da shi saboda Mustaphan ba dai kyauta ba gashi yanzu Abba ya janyo har ya yi fushi amma ba komai za ta shawo kansa ne….
Ta na wannan lissafin ta wuce ciki bayan ta ɗauki ledar kuncen kayan da su ka dawo da shi, ba kunya ba tsoron Allah.
Direct ciki da parlourn Adda ta nufa dan ta san Amal ta na ciki.
Ta na shiga kuwa ta gansu a parlour Amal kwance a kan cinyar Adda, Addan ta na yi mata firfita ta na share mata hawaye.
A fusace Adda ta ɗago ta kalli Anne sannan ta ce mata “ki fita ki kyale Yarinyar nan! Ki yi mini komai zan ɗauka amma wllh in kin taɓa Amal za ki ga ɓacin raina!!”
Kafin Adda ta rufe Bakinta Anne tuni ta ƙaraso inda su ke ta kamo Amal ɗin ta miƙar da ita tsaye kamar wata Yarinya ƙarama haka ta kamo kunnuwanta duk biyun ta murɗe su da masifar ƙarfi!
Matsowa Adda ta yi za ta taɓa su amma sai Anne ta daka mata wata uwar tsawa ta na cewa” wallahi ki ka taɓani sai mun kwashi ƴan kallo ni da ke! Na san kin san zan aikata!
Ki daina yi mini shishshigi akan ƴaƴana na gaya miki ko?
Ke ce ki ka haifa mini su ne wai?!”
Ta ƙarashe maganar ta na daka mata tsawa ta na huci sannan ta ɗaura “idan fitsari banza ne kaza ma ta yi mana!”
Adda ba ta san lokacin ma da hawaye su ka zubo mata ba ta na jin wani radaɗi da azaba na yadda Annen ta murɗe kunnuwan Amal numfashin Yarinyar ya ke sama da ƙasa kamar zai ɗauke tsabar azaba!
Ta san in ta ci gaba da tsayuwa a wajen wahala kawai za ta bawa Amal ɗin shiyasa ta wuce cikin ɗakinta kawai ranta ya na suya ta rufo ƙofar….a samu ta gama da wuri ta fita ta kyale Yarinyar.
Kwafa Anne ta yi ta na mai hararar ƙofar kafin ta dawo da dubanta ga Amal wadda ta haɗa Uban gumi azaba ta na ratsata sannan ta fara magana cikin sake murɗe kunnen kamar so ta ke ta cire mata su ne”kalle ni nan!!”
Sai da Amal ɗin ta kalleta sosai tukunna ta ɗaura da cewa “tunda na ga kunnen ƙashi ne da ke bara in yi miki wanda za ki gane, sannan ban ga alamun kin girma ba dan haka bara a yi miki yadda ake yiwa Yara”
Ta sake murɗe kunnen da har sai da Amal ta saki salati da ƙarfi sosai sannan Anne ta ce “daga yau har gaban abada in na sake ji ko ganinki tare da Abba na lahira sai ya fi ki jin daɗi!
Sannan in na sake cewa ki saka mayafi ki ka yi mini gardama tabbas sai na illataki!
Kuma Mustaphan da ki ka yiwa taurin kai zai zo ko kuma ma ke ki je ki bashi haƙuri sannan ki saurareshi in ba haka ba sai na tsine miki!!!”
Ta ƙarashe maganar cikin wurgar da ita ta na mai cewa “shegiyar Yarinya mai shegen taurin kai! Ana nuna mata Annabi ta na runtse ido, muguwa kawai! Da tuni yanzu kuɗaɗe ne riƙe a hannuna dumuss!! Ba raɗaɗin murɗe miki
kunne da na yi ba……”
Daga haka ta juya ta fita rai a ɓace dan ganin Amal ɗin da ta yi ya sake tuna mata asarar da ta janyo mata na kuɗaɗen da ta ke da tabbacin Mustaphan zai bayar in da ace ta tsaya ta saurareshi, sannan dan iskanci wai ta saka wani hijabi………..
Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin