Showing 57001 words to 60000 words out of 100561 words

Chapter 20 - BAKAR TUKUNYA hausa novel

07 Feb 2026

469

jininta bai ɗauki Yaron ba ko kallonsa ba ta son yi kamar ma tsoro ya ke bata dan duk in dai su ka haɗa ido sai ta ji gabanta ya yanke ya faɗi.
Dan haka ta tisa Adda a gaba ta na ta bala'in 'su kansu da za a samu mai ciyar da su ae so su ke yi amma shine tsabar kankamba ta ɗauko musu tsintacciyar mage ta bata abincinsu...'

Waya aka yi mata ta fita dan haka Adda ba ta kori Abba ba saboda dama ba ta son ya tafi ya barta cikin kaɗaici...dan Amal in sun tafi islamiyya tun safe sai yamma har asabar da lahafi, Amir Aliya har ma da Afra da su ke haɗawa da zuwa makarantar boko kuwa sun fita zama scarce dan ita bata kai ga shiga ba lokacin shekarunta biyu da rabi Afra huɗu Aliya shida Amir takwas…

Dukda tashi ɗaya Adda ta gane Yaron miskiline na gaske amma ta fahimci ya na sonta itama kamar yadda ta ke sonshi itama.
Duk kalar tarin tambayoyin da ta yiyyi masa ce mata ya yi kawai “Matar da ta riƙesa ce ta fahimci wanene Mahaifinsa shine ta kore shi ta ce ya je wajensa ae ya na da gata to shi kuma Mahaifin nasa ya je wajen nasa amma shima ya koreshi..”
Daga haka bai sake bata amsar komai ba ya ja bakinsa ya yi shiru.

Su na zauna a haka har su Afra su ka dawo daga islamiyya Wanda shigowar Yaran ta yi sanadiyyar zaman Abba a gidan na har abada dan tun da ya gansu ya kasa ƙauracewa gidan!
Kullum sai ya zo, ya na ganin Anne sai ya fake da aiki, ya gyara nan ya gyara chan ya na yi ta na hantararsa ta na zaginsa....
Tun Anne ta na zaginsa har ta haƙura ta daina daga ƙarshe sai ta fara tula masa uban aiki kamar hauka, duk wankin gidan in ya zo shine zai yi, sannan duk wani aikin gidan shi ya ke yi dan ta lura Yaron ya iya aiki kuma ya na da tsafta sosai sam ba ya so ya ga waje da datti shiyasa wani abun ma tun kafin ace ya yi ya ke yi.
Ita dai Adda burinta a bar mata shi shiyasa ta haƙura ta kauda kai daga wahalar da Anne ta ke bashi, ta zuba musu ido kawai bayan ta gayawa Baba ta na so ta yi adopting Yaron ne.

Har gidan Matar su ka je inda ta sanar musu wata Yarinya ce ta kawo sa a tsumma ta na kuka. ita kuma ta karɓa da tausayin shi ɗin maraya ne ashe da Ubansa dan haka ta na ganewa ta sallameshi tunda ya na da gata sannan ba ta san asalin dalilin da ya sanya Uban nasa ya ke gudunsa ba.

Sosai Matar ta basu takaici dan a ganinsu hakan bai kai dalilin da zai sanya ta guje shi ba da ta haƙura ta ƙarasa ladanta!
Dan haka su ka ce sun ji sun gani aka yi masa ƴan gwaje-gwaje Baba ya bashi sunan Mahaifinsu (Yusufa) suka mayar da shi ɗan gida.

Sun san sunan Mahaifin nasa dan Babban mutum ne sosai a ƙaasar har ma da duniya baki ɗayanta wanda da kyar Adda ta gasgata hakan...
Saboda ba dan komai ba yadda zai yiwa gudan jininsa haka, amma sai kawai ta share tunanin ta rungumeshi a matsayin ɗanta ta ƙoƙarta ta saka shi har a makarantar gomnati inda Amir ya ke zuwa, islamiyya kam dama chan ya yi sauƙa ma a tsangayar Mijin matar da ta riƙesa.

Kamar yadda Mahaifin Abba ba ya ƙaunarsa haka nan shima Abban, dan ko sunansa in aka kira sai an sha fama da shi a ranar sai ya kwana ya wuni bai ci abinci ba.

Anne kuwa kasancewarsa ɗan mai kuɗi ya sanya ta amince da farko har da zalamar a karɓesa sai da ta ga zallar ƙiyayyar da ke a tsakaninsu ta fahimci ba fa za ta samu komai daga jikinsa ba sai wahala da nauyin da ya ƙaru musu a gidan sai ta ce bata yarda ba a lokacin kuma har an riga an karɓesa Baba ya na ta fafutukar gina masa ɗakinsa a soro dan haka da ikon Allah duk fafutuka da borin da ta yi bai yi aiki ba sam! Da ya ke Ubangiji ya riga ya tsara akwai shan ruwansa a gidan.
Haka nan ta yi ta gaji ta haƙura duk ƙarfin ikonta a wannan lokacin bai yi tasiri ba dan haka sai ta tsiri huce takaicinta a kansa.
Azaba kala-kala babu kalar wadda ba ta gana masa wai duk dan ya gudu amma a banza gashi Yaron kwata-kwata ba ya biye mata kuma abinda ya ke sake ƙular da ita da shi shine 'ba za ka taɓa gane halinda ya ke ciki ba' shiyasa ko ta yi masa abu ba ta ganin alamun fushi ko wahala a kan fuskarsa sam.
Ga wani kalar farin jini da Yaron ya ke da shi dan ya na zuwa aka sanshi ake kuma yabonsi a Unguwar Adda da Baba kuwa kamar su cinyeshi saboda so! Dan shima Uwa da Uba ya ɗaukesu ya na musu biyayya fiye da misali kuma ya na sonsu dan haka ya sake shiga ransu shima su ke ji da shi.

Shiyasa sosai Adda ta ke jin zafin abubuwan da Anne ta ke yi masa dan a duniyar nan in har ka na so ka ƙuntatawa Adda to ka taɓa Abba ko Amal....
Ba yadda ba ta yi da Anne ba amma ta ƙi ji ta ƙi gani ta uzzurawa Yaron wani zubin har Addan ta ke haɗawa in ta yi magana, sai da ya kawo ƙarfi tukunna da kansa ya kwaci kansa a hannunta dan Abba wani kalar mutum ne mai masifaffiyar zuciya da zafin rai gashi miskili na bugawa a jarida.

Gov school ya yi da kyar ya ƙarasa waec tun daga nan karatunsa ya tsaya dan daga shi har Adda da Baba babu yadda su ka iya, Amir dai Anne ta yi masa cuku-cukun poly ya na kai Abba kuwa
sai yanzu (2025) ne ya ke ta tataɓurza da kuɗin sana'ar da ya ke ɗan kakkamawa ko wacce ta na lalacewa a hakan da kyar ya ke ta ƙoƙarin ganin ya haɗa degree ɗinsa.



Sai da ya ɗan kwana biyu a gidan shekaru su ka ja tukunna Anne ta fahimci manufar Abba! Ashe son Afra ya ke yi shiyasa ya nacewa gidan tun a karon farko.

Tatas!!! su ka yi masa ita da Kaka Nura a wanchan lokacin wanda shima ya tsani Abban su ka tabbatar masa ‘ba talaka wulaƙantacce su ka haifawa Afra ba’! Ranar gori kala-kala babu wanda bai ji ba! Har sai da su ka saka Adda kuka sosai. Shi kam Abba kukan nata ne ma ya taɓa shi sosai sai ko yadda su ka nuna masa ba za su bashi Yarinyar da ya ke matuƙar so kamar ransa ba, ammaa ranar kam da ikon Allah gorikansu ba su wani fusatashi sosai ba, Dan tunda rannan ya yo kan Anne a haukace kamar zai daketa ta tsorata sosai da shi ya firgitata…shiyasa da su ka zo yi masa wanna tujarar daga ita har Kaka Nuran ba wanda ya kira sunan mutumin da su ka san ya tsani a ambato, sun dai yi gori amma shakkarsa a wannan lokacin ba ta barsu sun yi abinda su ka san ya fi tsana ba.


Da Yarinyar(Afra) ta fara tasawa kuwa
Da gangan su ka dinga maƙala mata Isma’il tun ba ta Isa zance ba saboda su ƙuntatatawa Abba!
Isma’il ɗin makwafcinsu ne...
Tun Afra ta na da shekaru uku shima ya na Yaro lokacin ya ke nacin zuwa gidan saboda ita (wanda kishin Isma’il ɗin ne ma da Abba ya ke yi bayan sun fara girma ya fara tona masa asiri aka ɓaro jirginsa)…
To dae kaff layin iyayen Isma’il sun fi hannu da shuni shiyasa Mahaifiyarta ta yarje masa ba wai dan ta ji ta gani Afra ta auresa ba, A’a!! Sai dan abubuwan da ya ke kawowa Yarinyar su chocolate da kayan alkhairi dan ko Abu aka bashi a gida to sai ya kawo mata nata itama tukunna zai ci.
Komai Afra itama uwar Yaron tun su na ƙanana ta ke cewa Afra surukar ta saboda in aka cire Anne a rayuwar Afra tabbas Yarinyar wife material ce gata da hankali da kunya
Uwa uba duk layin sun shaida Kaka Nura da Anne ne su Afrra su ka yi rashin sa’ar su amma uba kam sun mori uba shiyasa ta yarjewa ɗan nata ta amince masa auren Afra musamman ma da suka lura uwar ta na so
Dan haka su ka zage su ka dinga yiwa Yarinyar bauta kamar Allah ya aiko su
Har private school su ka haɗa ita da Aliya suka saka ta, Amal ce dai da ya Amir su ka yi makarantun gomnati.



Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING*
Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING*
Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139*

Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudin ku tested and trusted.

Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu....
location:Kano
Delivery:NationWide.
kar ku bari a baku labari, sai kunzo🙏
SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA

BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*

HUMAIRAH BULAMA

Yota

*24*

Follow our channel
https://whatsapp.com/channel/0029Va5fqs7E50UpMpXolU1T

Kowa ya san su tare, dan in ka na so ka farantawa Isma’il to ka ambato sunan Afra….
Bayaga soyayyarta halaiyyarta tana daga cikin abubuwan da su ka sake dilmiyashi cikin kogon so, ƙauna da begenta. Tun kafin Afra ta rufe shekaru goma sha biyar ta sauƙe AlQur’ani Mai girma yanzu kam ta zama Malama a islamiyyar tasu inda take koyarwa safe da yamma, da daddare ne kawai ta ke zuwa ajin hadda ta na ɗauka da kuma karatun wasu littafan, kuma nan ɗin ma har sun kusan idarwa.

Ya Amir shima Babban Malamine a Islamiyyar dan Babban aji ma ya ke koyarwa kuma shine Amir na makarantar, duk wata gasa da makarantar za ta shiga muddin Amir ya bada gudummawa to in sha Allahu sai sun yi ƙololuwar nasara.
Aliya ce ma wadda ta ke zaman hostel yanzu haka inda ta ke diploma za a ce zurfin iliminta na addini bai kai nasu ba, ta dai yi sauƙa itama Alhamdulillah ta na da nata ilimin dai-dai gwargwado, Amal kuwa yanzun (2025) ne ta kammala secondary ta na ajin sauƙa.


Kamala ilimi da riƙon amana ya sanya Baba ya shiga sahun dattawan Unguwa, sai dai kuma dukda haka sai da ya ɗan fuskanci ƙalubale tukunna aka amince aka bashi limamin layin saboda Kaka Nura, Anne har ma da Yadikko ɓaragurbi ne a Unguwar, ko Islamiyyar da ta ke zuwa daga baya dainawa kawai ta yi saboda ba sa maraba da ita kuma wani zubin ma a buge ta ke zuwar musu ta yi ta abubuwan ban mamaki da takaici har sai an kira Baba ya wuce da ita gida, ga faɗa da ƴan makarantar kamar wata Yarinya shiyasa kawai kowa ya bi bayan ta haƙura ta zauna a gida in Baba ya dawo salla aka idar a masallaci sai ya shiga ya yi mata nata dan ba ta ko da ƙaunar ganin Adda ne ballantana ace ita ta yi mata. To dai duk in ya dawa (aka idar da sallar) ma sai dai ya yi karatunsa shi kaɗai saboda baya so ya koma shago a gane ba ya yi mata karatun dan already mai wajen da maaikatan duk sun san uzurinsa dan haka ake bashi awa ɗaɗɗaya a duk bayan ko wacce sallah sai dai kullum in ya zo
a buge take wani zubin ma ta na barci har ya koma ba ma ta san ya shigo ya tafi ba!
Shi da Adda har ma da jikokinta da su ka fara wayo…sun yi kuka sun yi yaƙin amma abun ya ci tura dan in sun kwace na wajen ta akwai a wajen Anne wadda sai daga baya ne su ka gane ashe itace ta ke bata, zuwa wannan lokacin duk wani ƙarfin asiri da surƙullen Anne akan ‘Baba ya so ta’ baya tasiri dan ƙarfin zafin zugin ɓarnar da ta yi wa rayuwarsa kuma ta ke kan yi ya danne duk wani asirinta, ba dai ya iya yin musu da ita ba kasafai ba gaskiya kuma ya kasa rabuwa da ita a cewarsa ko dan ƴaƴansa da Yadikko wadda take auren Ubanta ya san kuma ko an rabu ba a rabu bane, amma fa duk duniya babu wadda ya tsani ya ji ko da sunanta ne kamar Nuratu, dan masifa wani zubin in ya na saduwa da ita kuka ya ke yi tsabar ba ya sonta, shi kansa ya na so ya rage tsanar saboda ya san ba kyau ka tsani ɗan uwanka musulmi har
haka amma ya gagara.


Garin tsabar shaye-shayen Yadikko ne ta je ta shawo kwayar da ta fi ƙarfin kwakwalwarta tun daga nan ta ɗauke wuta ta koma kamar robot. Watanninta takwas a asibiti ta na jinya inda ta tatike aljihun Baba ƙaƙaf!! Kafin aka samu ta fara motsi ta dawo da magana sai dai babu ido sam bata gani da duka biyun har gobe.

Aikin gida da girki dama Adda ce, Anne za dai ta kawo sometimes Baba shima ya kan kawo wani zubin har Ya Abba shima ya na taimakawa da kayan abinci Adda ita kuma ta girka Kaka Nura kuwa ko ya samu sai dai ya bi mata da kuɗin…sam! Ba a cin kuɗinsa Amal kawai ya ke ɗan kashewa kuɗi wadda itanma a ganinsa adashe ne ya ke yi dan ya na da yaƙinin samarinta da Mijinta za su biyashi a gaba.


*2025*
Mariri, 1:40pm

Karo na uku kenan daga faɗa mata saƙon zuwa yanzu da ta ɗago labulen ɗakin nasu ta kalleta, sai da ta gama ƙarewa doguwar rigar material ɗin da ta sanyawa jikinta ɗinkin A shape kallo tukunna ta ce mata “ki yi sauri!”
Daga haka ta fara ƙoƙarin sauƙe labulen za ta koma tsakar gida ta ci gaba da wanke-wanken da ta tashi Yarinyar a kai ita ta amsa ta ke yi yanzun, ta ji an ce “yanzu Nuratu gidan Matar nan za ki yi aikenta? Saboda kawai ta karɓo miki kayan da na tabbata duk tsadar su ba za su wuce dubu hamsin ba!”

Kamar ba za ta kula shi ba sai kuma ta watsa masa manyan idanuwanta cikin yaɓa magana ta ce da shi “kawo naira dubu hamsin ɗin sai ta zauna a haƙura da karɓo kayan”.

Shiruuu, kawai ya yi ya na kallonta kafin ya girgiza kai ya mayar kan Alqur’anin da ke riƙe a hannunsa ya na karantawa kawai ba tare da ya ce mata ƙala ba.
Tsaki ta ja sannan cike da raini ta ce “dan haka sai ka ja bakinka ka yi shiru, dan banga dalilin da zai sanya ka hanata karɓo kaya ba bayan kai ɗin ka kasa siya mata ko da na dubu biyar ne.”
Tana gama faɗin haka ta sauƙe labulen ta yi gaba ta na mai sake nanatawa Yarinyar da “ki yi sauri”.

A hankali Yarinyar ƴar shekaru goma sha shidda ta sauƙe ajiyar zuciya, kwata-kwata ba ta jin daɗin yadda Mahaifiyar tasu take yiwa Mahaifin nasu, amma ta san ba ta Isa ta faɗa ko ta nuna ba dan haka ta yi hanzari ta ɗauko hijab ba wani mai girma ba ta zura a kan rigar material ɗin da ke a jikinta sannan ta kalli Mahaifin nata ta ce “Baba na tafi”
A hankali ya ɗago kai ya kalleta sannan ya jinjina kai ya ce “sai kin dawo, ki yi addu’a kafin ki fita.”
“Tam Baba” ta ce da shi daga haka ta saka kai ta fice.

Fitarta ke da wuya! Anne ta miƙe daga wajen wanke-wanken ta hau rafka salati ta na tafe hannu.
Turuss!! Haka Yarinyar ta ja ta tsaya kafin ta waiga da mugun sauri ta na mai jin wani tsoro ya na shigarta dan tabbas duk wanda ya ji kuma ya ga salati da yadda Annen ta yi tsaff zai ɗauka wani abun tashin hankali da al’ajabi ta gani, sai dai kuma ita bata ga komai ba a wajen bayan ita kwallin kwal dan ko Baba bai fito ba.
A fusace Annen ta ƙaraso ta wuceta ta shige ɗakin, jimm kaɗan sai gata ta fito ɗauke da mayafi ɗan ƙarami baƙi riƙe a hannnunta.

Cikin turo baki kaɗan gudun kar Annen ta gani ta rufar mata
AMAL ta ce “Anne ana sanyi dan haka ni dai gaskiya baa zan iya saka ƙaramin mayafi ba, kuma ma babu man shafawa (ban shafa ba) hannuwana duk sun yi furu-furu, dan haka hijabin shine rufin asiri na..”
Ta ƙarashe maganar cikin kawar da kai gefe ta na guna-guni.

Kamar mai shirin rufeta da duka amma ƙasa-ƙasa Annen ta ce “duk ba talauchi da ƙunshe-ƙunshen naki bane ba ya sanya kika rasa man shafawar?
Mai yasa kike da taurin kai ne Amal? Mai yasa ba za ki nutsu ki yi abunda ake gaya miki ba.”

Sosai ran Amal ya soma ɓaci dan haka ta kawar da kai gefe sannan ta haɗe rai tamau kafin ta ce “babu fa mayafin da zan rufa, na gama magana”
Cikin ɓacin rai Anne ta ce “ni kuma na ce da mayafi za ki fita daga gidan nan yau ba hijab ba dan uwar ubanki…”

Cikin tsananin ɓacin rai Adda wadda take ta saurarensu tun ɗazun ta miƙe daga durƙuson da ta yi a gaban murfi ta ajjiye wuƙar hannunta sannan ta fito daga cikin kitchen ɗin ta ƙaraso inda su ke, ba da hayaniya ba amma dai kana gani ka san

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login