Showing 60001 words to 63000 words out of 100561 words
ranta a ɓace ya ke ta ce “Ni kam Anne wae mai yasa hankalinki ba ya taɓa kwanciya ne sai kin taɓo mahaifiyarmu kin zaga? Mai yasa ba ki da kirki kuma ba ki da kara ne?
Sannan fisabilillahi wae sai yaushe za ki yarda amana ce ta Yarannan Allah ya baki? Ya tana ta ce miki ba ta son yawo a tsirara amma kina ƙoƙarin tilasta mata bayan na san duk jahilcinki kin san hakan haramun ne….”
Ƙuraa mata idanu kawai ta ga Anne ta yi, kafin daga bisani kuma ta ce “chaab!!”
Ta na jera mata kallon mamaki sai kuma kamar an tsinkareta ta rushe da wani kalar rikitaccen kuka mai tsananin sauti, kukan da dole ya razana duk wani mai raunanniyar zuciya.
Shiruu kawai Adda ta yi tana kallonta da takaici da mamaki ta na jin kamar ta rufeta da duka…ta na wannan lissafin ta ji motsin ƙaure, aikuwa ta na juyawa ta ga Yadikko ta fito ta na lalube da hannun damanta ɗayan hannun nata kuma sandarta ce itanma dai ta ke laluben da ita.
Wani kalar kallon takaici Adda ta watsawa Anne kafin ta nufi wajen Yadikko wadda ta ke lalube ta na cewa
“Waye ne ya ke kuka haka? Mai ya faru?”
Da sauri Adda ta tareta ta na cewa
“Ba kowa fa, ki koma ciki kawai “
“Ƙaniyarki! Ya Ina jin kuka amma ki na ce mini babu kowa,
Mai ya faru?”
Cikin kuka sosai Anne ta ce
“Yadikko daga magana tsakanina da Amal a kan ta sauya hijab ta saka mayafi shikenan Adda ta fito ta fara min abunda ta saba wae zan ɗaurata a kan hanyar haramun…sannan haka nan ta fito tana ta cewa wae na zageki…”
Da mamaki Adda ta ke kallon Anne, ɓacin rai bai iya hanata cewa “da kika ce uwar ubanta me kike….”
Sandar da Yadikkon ta ɗaga da niyyar makawa Addan ce ta sanya ta yi shiru da sauri sannan ta yi saurin kaucewa, cikin fushi sosai Yadikko ta hau cewa “tsinuwar nan ita kike biɗa ko? Ban Isa in hana Abu a hanu ba Ashe? Ni dae ban ji nata zagin ba amma na ji naki kin yi mini…
Wae shin sai yaushe za ki daina sakani kuka ne Adda, sai yaushe za ki daina cizon hannun da ya ke baki abinci?…Duk kalar ɗawainiyar matar nan a kanku amma a ce ba kya gani?….
Ko dan darajar Ubanta a cikin gidan nan ae kya sarara mata ko?
Mai yasa ba za ki daina kishinta a zauna lafiya da ke bane?
Mai yasa kullum ke burinki ki saka ni magana ki nuna min ban isa da ke ba ne?”
Ta ƙarashe maganar cikin rushewa da kuka.
Sosai jikin Adda ya yi sanyi ƙalau! Dan sam sam ba ta ƙaunar ta ga Anne ta saka hawayen uwarsu ya zuba a ta sanadiyyarta!
A hankaki ta fara ƙoƙarin kama Yadikkon ta na son ta mayar da ita ɗakinta ta na mai bata haƙuri amma sai ta hau tuttureta cikin kuka ta na cewa kar ki kuskura ki taɓa ni, matsa Muguwa wadda ta ke son ganin bayana matsa daga jikina, baƙin halinki ne ya janyo Miki za ki ƙare babu Mijin aure!
Ni inama ace mutanen da su ka yi garkuwa da ke ba su dawo mana da ke ba, inama sun riƙe ki har abada wallahi da na hutama raina….”
Cikin kukan munafurci Anne ta matso ta kama Yadikko sannan ta hankaɗe Adda wadda zuwa yanzun hawaye sun cika mata gajiyayyun idanunta tap!
Suna haɗa idanu da ita ta kashe mata ido ɗaya sannan ta yi mata gwalo daga haka ta jaa Yadikko ta na mai cewa “Yadikko ni ce ba Adda ba mu je in mayar da ke ɗakinki…..”
Sannan ta kalli Adda ta ce “in kin saita kan girkin ga wanke-wanke nan ki ƙarasa.”
Ko da wasa Baba bai yi yunƙurin fitowa daga ɗakin da ya ke ciki har yanzun ba, dan ya san muddin ya fito to a kansa komai zai ƙare, amma fa ya shaƙa! Yayinda tsanar Anne ta sake samun matsugunni a cikin zuciyarsa.
Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING*
Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING*
Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139*
Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudin ku tested and trusted.
Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu....
location:Kano
Delivery:NationWide.
kar ku bari a baku labari, sai kunzo🙏
SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA
BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*
HUMAIRAH BULAMA
Yota
*25*
https://whatsapp.com/channel/0029Va5fqs7E50UpMpXolU1T
Mariri, Kano State.
Babban gida ne sosai a cikin Unguwar Mariri, dake a ƙarƙashin hukumar Kumbotso LG, Kano, Nigeria.
Irin gidajen nan ne masu soro mai ɗauke da ɗakuna sannan in ka shanye soron za ka tarar da ƴar ƙofa wadda in ka shigeta za ka yi arba da tamfatsetsen tsakar gida mai ɗakuna barkatai! Da kuma ƙafafuwan bene wajen guda huɗu, sama shima ba a barshi a baya ba wajen tarin ɗakuna kala-kala wani room and parlour wani kuma single room ne kawai…
A ƙalla dai ɗakunan gidan sun kai hamsin dan gida ne babba kwarai da gaske…
Ahalin gidan kuwa mafiya akasarinsu ƴan mata ne masu jini a jika sai ko waenda suka ɗan sha miya waenda kana kallonsu ka san sun ga jiya sun ga yau a fannin harkar komai….
Banɗaki kwalli ɗaya ne a gidan kitchen shima guda ɗaya ne tak! Waenda kofofunsu su ke kallon juna sun saka ciki da parlourn magajiya (Uwa) a tsakiya, kasancewar ita ɗin a ƙasa ta ke sakamokon ciwon ƙafar da ya sakota gaba aka hanata hawan bene sam-sam…
Kamar kullum yau ma haka nan ta ke zaune a wajen ta dasa kujerarta a bakin ƙofar ɗakinta wanda fitsari ne kaɗai ke tada ita daga wannan zaman sai ko ba haya dan hatta abinci a wajen aka kawo mata ta ci a ɗauke, batun sallah kuwa dama sai dare ya yi in ta shiga ɗakinta tukunna ta ke jero iyaka waenda suka sauwwaƙa gobe kuwa sai dai a ɗaura daga inda aka tsaya dan babu batun carryover…
Ta na zaune cikin ƴar rumfa ta na kallo da amsa gaisuwar Matan gidan da su ke ta faman kai kawo wanda babu mai ƙasa da shekaru sha biyar a kaff cikinsu…
Dan tun kwanaki da Mai Unguwa ya yi galaba a kansu shikenan dole
ta sanyata aka tattare Yara daga sha biyar zuwa ƙasa aka yi waje da su….ba dan ranta na so ba sai dan babu yadda za ta yi(an fi ƙarfinta) dan ita rabin customominta sun fi son Yara ƙananu dalili kuwa shine a tasu yanayin fuskar fahimtar sa’a tana cikin saduwa da ƴan Yaran da basu kammala nuna ba….
Takaicin tunowa da ta yi da hakan ne ya sanya ta sake zuƙar sigarinta ta fesar da masifar ƙarfi zuciyarta ta na wani kalar tafarfasa!
Tabbas tsakaninta da Mallan, Baba (liman) da Mai Unguwa sai dai ta ce musu Allah ya Isa!
Sana’arta ta ke yi, ba ta shiga hurumin kowa a Unguwar amma an kafa mata ƙahon zuƙa! Sai da ta kai ta kawo ta kafa sharaɗin kwata-kwata ba ta yarda a kawo mata maza fa cikin gida ba amma dukda hakan bai ishesuba an saka mata ido an uzzura mata!
Ita kuwa ba zata ƙaura ba dan wannan itace Unguwa ta uku da aka koreta ta dawo daga karɓar karagar mulkar kungiyar da ta yi daga hannun Ladiyo kawo yanzu…
Ta lura in ta biyewa mutane ƴar kwallo za su yi ta yi da ita….
Zuwa yanzu gaba ɗaya komai sai faman suɓurɓuce mata ya ke yi, kwata-kwata ta gagara lalumo bakin linzamin ballanta ta ja su su tafi…
Dama ana ta cewa ba lalle ta iya ba duba da ba gadar abun ta yi ba mulkinma da kuɗinta ta siya ta kwace ta ƙarfin tsiya, to gashi kuwa abun ya na neman gagarar ta!
Tabbas da gaskiyar Innayo da ta ce mata ‘harkar dole sai an haɗa da tsaurin ido da ƙin bin duk wata doka da tsantsar rashin kunya dan su mutanen Unguwa babu ruwansu da son wani zaman lafiya a tsakani muddin mace ta amsa sunan karuwa! To fa ƙahon zuƙa su ke kafa mata har sai sun ga bayanta…
Dan haka gara ta fito musu da ƙarfinta kar ta yi wani shayi ko ɓoye-ɓoye hakan ne kawai zai sanya a ji shakkarta a sakar mata mara….’
“Ina kwana Uwa”
Muryar wata mata wadda ta zo wucewa ta katsewa Yagwalgwal ɗiin tunanin da ta ke yi!
Dan a ƙa’idar gidan muddin ka fito to dole sai ka gaida ita ko da kuwa kun gaisa tun farko.
Ta na shirin amsa gaisuwar wata mata wadda ta fito yanzun ta ce “lafiya ƙalau yar albarka, ya jikin naki? “
Kasa amsawa Yarinyar ta yi ta hau kame-kame sannan ta rissinar da kanta ƙasa jikinta ya na wani kalar karkarwa….
“Wuce ki bar nan Aimana.”
Yagwalgwal wadda ta miƙe tsaye ta na ɗan riƙe ƙafarta mai ciwo ta ce da Yarinyar, a take kuwa kamar ta na jira ta yi wuff ta bar wajen…
Juyawa ta yi ta mayar da dubanta zuwa ga matar wadda ta fito wasu Mata guda biyu na biye da ita su na take mata baya!
Baƙa ce sosai kuma doguwa sannan ƙaƙƙarfa…irin murɗaɗɗun Matan nan…
A hankali Matan da su ke biye a bayan nata suka ɗan rissinar da kawunansu ƙasa sannan suka ja baya kaɗan saɓanin Ladiyo wadda ta kafe Yagwalgwal da idanu kyarrr ta na kallonta…
Sai da Yagwalgwal ɗin ta yi wani murmushin takaici sannan ta ce “Uwa ɗaya ce tak! A gidan nan. Ki kwantar da kanki ki zauna lafiya ko kuma ki bar tawagar nan a yi tafiyar babu ke dan ba a sarki biyu a gari ɗaya…”
Murmushi itama Ladiyon ta yi sannan ta ce “eh kam ba a yi, amma kin san ana juyin mulkiiii…”
Ta ƙarashe maganar cikin isa tana mai jaan ƙarshen maganar sannan ta matso kusa da ita daff!! Kafin ta ɗaura da cewa “sannan, yeah! Na san ana iya yin gari biyu amma tabbas za a ci ragon Sarki da yaƙi a kwashe jama’arsaaaa, kamar dai yadda ki ka yi a baya lokacin da ki ke da abunda na tabbata ba ki da su a yanzuuuuu(kuɗi)”
Ta sake jaan maganar ƙarshe cikin isa ta na huci ta na ji kamar ta murƙushe Yagwalgwal saboda tsabar tsanarta da ta addabi zuciyarta amma da ta tuna cewar a yanzu haka ta kusan haɗe kan fin rabin jama’ar gidan a ɓoye da wayo, sai kawai ta kyaleta ta na mata wani kalar murmushin da Yagwalgwal ɗin ta gagara fahimtar na menene…
“Allah ya kaimu ranar juyin mulki…”
Ladiyo ta aiyyana hakan a ranta daga haka ta juya ta fita Matan nan guda biyu suka mara mata baya.
•••••••••
Su Yadikko su na gama shigewa ciki Adda ta fashe da kuka, sai kuma ta juya da sauri ta bar wajen dan ba ta so Amal wadda ke a tsaye idanunta sun yi rau-rau itama ta saka mata kukan….
A wajen Anne hakan nuna isa ne da gadara da win! Amma ita a wajenta tabbas tarwatsa mata rayuwa ne, ko ba komai bakin uwa masifa ne, wanda ita kuma Anne ba ta da wani buri sama da ta yi ta cusguna mata ta hanyar yin amfani da mugayen alkaba’in Yadikko akanta (Addar).
Ko kammala shiga ɗakin ba ta yi ba Amal ta biyo ta … dan kusan a tare su ka shiga cikin ɗakin, wadda already fuskanta ya jiƙe sharkaff da hawaye.
Kasa kallonta Adda ta yi amma kuma ta kasa tsaida kukan nata wanda hakan ya sanya kawai ta sake shi bagatatan.
Da sauri Amal ta ƙarasa gareta ta rungumeta cikin kuka sosai ta ke cewa “Adda ki yi haƙuri dan Allah, Allah zai saka miki”
Tabbas ta san bai kamata ba amma wani kalar takaicin Anne ta ke ji ya na taso mata marar misaltuwa.
Ta tsani ta ga Addan nata a cikin damuwa sam-sam ba ta so.
….
Sai da ta tabbata ta ajjiye Yadikkon a kan gadonta tukunna ta juya za ta fita, da sauri Yadikkon ta riƙo hannunta jikin tshohuwar har karkarwa ya ke yi ta ce “ya batun wanchan abun da ki ka ce za ki bani ? Tun ɗazu da safe fa ke na ke jira, ki sallame ni yanzu kafin ki fice.”
Taɓe Baki Anne ta yi sannan ta ce “in sallameki a sake gaya mini wani sunan na daban ko? Dama ni su ke zargi dan haka na daina biye miki haka kurum kura da shan duka gardi da kwace kuɗi.
Shekaran jiya sarai na gaya miki binciken da su Amir su ka yiwa kayana amma ban ga kin yi
komai ba.”
Da sauri Yadikko wadda gaba ɗaya yanayinta ya ke baiyyana asalin rashin nutsuwa ta ce "ki barni da su, duk zan yi miki maganinsu. Ba ki ganin yadda na ke takawa Adda burki ne a kanki? Suma su Amir ɗin duk za su zo su sameni ne.
Yanzu ki taimaka ki sallameni."
Ta ƙarashe maganar ta na mai jan ajiyar zuciya, ji take kamar ta yi ta zabga ihu.
Shiruu kawai
Anne ta yi ta na kallonta kafin chaan ta ce “shikenan bara a kawo
miki.”
Daga haka ta sa kai ta fice, zuciyarta fes.
…….
Sai da su ka yi mai isarsu tukunna Amal ta iya aro jarumta ta shiga gogewa Adda hawaye ta na mai cewa “Adda dan Allah ki yi
haƙuri”
Cikin sauƙe ajiyar zuciya Addan ta shiga girgiza mata kai kafin ta kamo cute face ɗinta itama ta goge mata nata hawayen sannan ta ce “ki daina kuka ki tashi ki je aikan da aka yi miki, nima gashi kinga na daina”
Ta rufe maganar tata ta na mai ƙaƙalo murmushi ta yafawa fuskarta a ranta tana dannar kanta da ƙoƙarin son aro jarumta dan ba ta so ta dinga zubda hawaye a gaban Yarinyar sam-sam sannan gashi itama ta sakata kuka.
Zama Amal ta gyara daga durƙuson da su ka yi a wajen sannan ta sa hannu tasake goge fuskarta tukunna ta ce ”ba zan je, ba na son zuwa gidan Matar kuma Anne ta sani amma ta ke tilasta min sannan ta ce in saka mayafi, gashi ba na so in yi fashi a makaranta. Ni dai makaranta kawai zan tafi.”
Sai kuma ta rushe da kuka cikin kukan ta ke cewa “Alllah Adda ba na son halin Anne, ba na son…..”
Da sauri Adda ta ɗaura hannunta a kan Bakin Amal sannan ta ce “shhhh..
Mahaifiyarki ce, kar ki zafafa, ki yi haƙuri.
Tashi ki je aiken, ba abunda zai sameki, ki yi addu’a kamar yadda ki ka saba har ki je ki dawo.”
Kwaɓe fuska ta yi da shirin sakin wani kukan amma ganin yadda Adda ta haɗe rai tamau! Ya sanya ta haɗiye kukan.
Cikin rashin jin daɗi Adda ta ce “so ki ke ki sake janyo min wani abun da za a yi ya sanyani kuka ko?”
Da sauri ta shiga girgiza kanta ta na hawaye at the same time tana goge hawayen da ta gagara tsaida su.
Sai da Adda ta ce “to dan Allah ki tashi ki tafi aiken, ki yi addu’a kin ji.”
Tukunna ta jinjina kai kawai ta na matse Baki dan in ta buɗe Bakin kuka ne zai kufce. Ba ta ƙaunar Adda ta yi mata magiya shiyasa yanzun ma kawai ta miƙe a hankali
ta fice.
Amal na fita daga cikin ɗakin Adda ta saki wani sabon kuka mai tsananin cin rai da azabtarwa. Duk yadda ta so ta zame hannunta daga lamarin kamar yadda ta daɗe da yiwa kanta alƙawari, sai ta ji ta gagara, dan haka ta janyo wayarta….
Dama ƙuɗin motarta ya na hannunta dan haka ta yi sauri ta yi addu’a ta fice daga cikin gidan ba tare da ta rabu da Hijabin da Annen ba ta so ba, mayafin da ta ke so ta rufa wanda ta ganshi yashe akan dandamalin ƙofar ɗakin nasu kuwa ko kallonsa ba ta sake yi ba ta yi ficewarta!…
Ai Allah ma ba zai yi farin ciki da ita ba in ta saɓa mishi ta farantawa Anne dan ta na matsayin Mahaifiyarta.
Sai da ta fita daga cikin layin nasu ta soma hango titi tukunna hankalinta ya kwanta dan ta san tsaf in Anne ta fahimci ta fita a hakan za ta iya biyota kuma ba ƙaramin aikinta bane ta kwaɓe mata hijab ɗin a bainar nasi ta musanya mata shi da gyale.
A gani da tunaninta sauri ta yi, sai dai kasancewarta Mace mai sanyin jiki ya sanya in da ace tseren tafiya su ka yi da Yaro tsab zai yi mata nisa ma.
Jin ta na haki ya sanya ta ɗan tsaya chak ta sunkuyar da kanta ƙasa ta na mayar da numfashi….
Ta kai kusan 2 minutes a haka ta ji ƙamshin turaren da ta sanshi dashi tun Yarinta ya gauraye wajen ta na shirin ɗagowa ta ji an ce “ke!”
Da sauri ta ɗago a ɗan tsorace sakamokon jin muryar dodon nata da ta yi, ai kuwa ta na ɗagowar su ka yi ido biyu da Ya Abba, fuskar nan a murtuke kamar kullum.
Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING*
Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING*
Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139*
Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudin ku tested and trusted.
Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu....
location:Kano
Delivery:NationWide.
kar ku bari a