Showing 9001 words to 12000 words out of 100561 words
mutanen da su ka kama dan kamar yadda mutumin ya fad’a basu d’agawa kowa k’afa ba gaba d’aya suka kame kowa aka had’a da su a motar aka yi gaba da su.
Y’an Unguwa ana ta kallonsu wasu su na yi musu dariya yayinda hankalin iyalan mazan da aka kama ya tashi chaa suna ta kuka da wannan cin mutunci da aka yi musu, su Anne kuwa Allah shi k’ara kowa ya ke ta cewa.
A haka aka nufi chan wani waje mai kama da barikin Sojoji da su….
Anne ta had’e rai ta na lissafin yadda za ta yagalgala rayuwar Sajida dan wallahi in za ta k’arar da duk abunda ta tara sai ta tarwatsa rayuwar Sajida da Ubanta…
Baba kuwa hawaye ya ke yi a b’oye ya na sharewa a hankali a hankali, yayinda Ya Abba ya kafe Amal wadda ta sunkuyar da kanta k’asa kawai da idanu zuciyarsa ta na wani kalar k’una….
A haka su ka k’arasa wajen kowa da abunda ya ke tattaunawa da zuciyarsa…
Cike da wulak’anci a ke firfito da su daga cikin motar
sannan aka shige da su ciki….
Da Mazan da Matan da tsoffin duka aka gwamutsa su a waje d’aya su goma sha biyar har da gawar jaririn Aliya sha shidda saboda suna shiga matar ta bawa Aliya gawar jaririn dan ce mata su ka yi ‘ta bata abarta ta rik’e za su san abun yi….’
Dole maza bakwai d’in da su ke zaman makoki waenda hau ya fad’a musu su bakwai aka taho da su…su ka tsaya a tsaye dan babu wajen zama enough su da Ya Amir Baba da Ya Abba….
Yayinda Amal, Yadikko, Anne, Adda, Aliya da wannan tsohuwa su ke a zaune a marmaste sosai dan kwata-kwata wajen bai fi wajen tsayuwar mutum sha biyar d’in ba….
Suna gama zama wani
Barci ya sake yin awon gaba da Yadikko, yayinda wannan tsohuwa ta yi shiruuu ta na addu’a a cikin ranta.
A hankali Amal ta mayar da kanta k’asa ta fashe da wani kalar kuka siriri mai cin rai….
Tunda Ya Abba ya ke bai tab’a jin kansa helpless kamar na yau ba..tabbas he is useless ba shi da power d’in komai sannan ba zai iya protecting nata ba no matter what….
Zuciyarsa na k’una ya sunkuyar da kansa k’asa ya sake damk’ar k’arfen k’ofar cell d’in da ya rik’e da masifar k’arfi zuciyarsa ta na yi kamar za ta fito daga cikin k’irjinsa….
‘K’i-k’-k’i-k’iiii’ d’in da su ka ji k’arfen ya soma yi ne ya sanya duk aka mayar da duba garesa.
Da sauri d’aya daga cikinsu ya d’an tsattsallake su ya matsa kusa da Ya Abban ya d’an dafa shi dai-dai da mik’ewar Adda itama ta dafa shi a hankali ta na cewa “Abba…”
Kamar wadda ta ke jin tsoro…
Ko kad’an bai ji su ba sai da ta sake cewa “Abbaaa”
A hankali kusan a tare ita da mutumin tukunna ya ji sai kuma ya tsaya chak da abunda ya ke yi dan shima sai a lokacin ya ji yadda tafin hannunsa ya d’auki zafi matuk’a a ta sanadiyyar k’ok’arin fasa k’arfen wajen da ya yi…
Sai da aka d’auki kusan mintuna uku tukunna ya iya bud’e idanuwansa da mugun kyar waenda su ka yi wani
kalar jaaa na ban mamaki…
A hankali
Adda ta sunkuyar da kanta k’asa yayinda mutumin ya d’an yi tapping shoulder d’insa ya ce masa “sai hak’uri” daga haka ya juya ya bar wajen ya tsallaka ya koma inda ya ke dan bai san me zai ce masa ba kuma sannan har ga Allah yanayinsa ya bashi tsoro matuk’a dan kamar ba shi ba haka ya koma.
So ya ke ya je ya zauna amma ya gagara yin hakan, sai bayan kusan mintuna ashirin tukunna ya ji ya iya motsa k’afafunsa dan haka ya nufi inda Amal ta ke zaune kai tsaye ya zauna a kusa da ita shima ya kifa kansa k’asa a kan guiwwowinsa kamar yadda ta yi…chaan ya
d’ago kansa a hankali ya na kallonta ganin kamar ma ba ta lura da shi, ya ce “Amal”.
Har yanzu kuka ta ke yi ga muryoyin Ya Asad da ta ke ji su na yi mata yawo a ka, in ya yi maganar gaba d’aya sai ta ji kamar ta bar wannan duniyar ta koma wata daban ita kad’ai
It’s like soul d’inta ya ke d’aukewa daga wajen gaba d’aya…..
Yanzun ma haka ce ta sake faruwa ta inda ta ji ya na cewa “ki ba da had’in kai, duniyar nan babu komai a cikinta sai tarin bak’in ciki…let me
End your suffering…”
Ya yi maganar a jikinta ta na ji kamar ya na mik’o
mata hannu..
Har ta fara k’ok’arin mik’a masa nata hannun a chan inda ta ke jinta ta ji Ya Abba ya ce “Amal….”
Da sauri sannan firgigit lissafinta ya dawo inda su ke sannan ta shak’i numfashi da nauyi kafin ta shiga sauk’e ajiyar zuciya a hankali a hankali ta na mayar da numfashi sannan ta shiga k’ok’arin d’agowa a hankali…
Da Aliya su ka fara had’a idanu ta kafeta da ido kawai wanda abunda Amal d’in ba ta sani ba shine kwata-kwata hankalin Aliyah ba ya ma kanta, gaba d’aya hankalinta ya tafi wani wajen shiyasanya
ba ma ta gane a ya
Amal d’in ta ke ba…
Chan ta ke lissafi da tunanin
Mai Nasara da Anne wanda takaicinsu ya taru ya sake haifar mata da wani sabon tarin bak’in ciki…
A hankali Amal ta d’an matsa jikin Adda sosai jin Abban a kusa da ita…one by one ta ke bin kowa da kallo ba tare da ta waiga ga Ya Abban ba wanda ta ke ji a jikinta ita ya kafe da idanu…
Idanunta su na sauk’a a kan Baba wanda ya yi
shiruuuu ya sunkuyar da kansa k’asa kawai sai ta sake fashewa da kuka, cikin kukan sosai k’asa-k’asa ta ce “Ya Abba dan Allah ka ce musu su sauya mini waje ko Ina ne su kaini…
Ba na son kallon fuskar Aliya zuciyata za ta buga!”
A hankali ya sauk’e numfashi cikin tsantsar karyewar zuciya ya ce “I’m soo sorry Amal.
Ki yi hak’uri dan Allah, ba ni da taimakon da zan iya yi miki, kwata-kwata ba ni da wannan power…”
Ya yi maganar a hankali sannan kamar mai shirin fashewa da kuka.
Shiruu itama kawai ta yi ta na mai jin babu dad’i..
Ta d’ago kenan za ta yi masa magana ta ji Aliya ta ce “Amal ki yiwa Yagwalgwal magana mana, tunda ita d’in shahararriyar karuwa ce na san za ta iya yin magana a fitar damu daga nan tunda ta san maza bilaadadin…”
D’ifff! Haka wajen ya kasance kowa ya yi shiruu babu mai cewa komai…
Anne so ta ke yi ta yiwa Abba magana shima ta ce ya kira musu ‘Mai Dala’! Amma haka nan yau sai ta gagara yi masa magana wani kalar tsoro da shakkar Yaron duk su ka bi suka rufeta tun d’azun…dan haka ta ja bakinta ta yi gum! Hau d’in nata bai fad’a a kansa ba yau…zuciyarta ta na k’una ta rasa inda za ta sami salama, ta ji Amal ta ce “tabbas Aliya dukkanin abunda ya faru da ke halinki ne ke bin ki…”
Da sauri kamar mai jira Aliya ta ce “kazalika ke ma, halinki ya sanya Asad ya guje ki kuma halinki ne ya janyo ki ke cikin halinda ki ke a halin yanzu sannan mind you
This is just the begining of your sufferings
In shaa Allahu…..”
Da k’arfi Ya Abba ya ce “Aliya!!!!”
Yana mai zuba mata jajayen idanuwansa…
Dole ta rufe bakinta gam! Dan a take ya razana ta matuk’a ba ma ita kad’ai ba duk wani wanda ya ke a cikin cell d’in sai da y’ay’an hanjinsa su ka kad’a har da Baba wanda ya ji dad’in yadda Abban ya shigarwa Amal dan sarai ya lura da yanda Anne ta soma jin dad’in cin zarafin da aka fara yiwa Yarinyar ya san tsulum yanzun za ta shige su tarar mata su yi
mata tatas!.
A hankali Adda ta kamo hannun Amal wadda ta san ko me ye ta cewa Aliya to fa bango ne aka kaita shiyasanya dan sam ita magana ma ba d’abi’arta bace ba….
Cikin sanyin murya Adda ta ce mata “na san kina hak’uri amma zan rokek’i ki k’ara, ko me za a yi miki ki daina tankawa dan Allah…”
Jiki a mace sosai ta na ji kamar ta kurma uban ihu ta ke kallon Adda wasu zafafan hawaye su na zubo mata, kamar za ta yi magana sai kuma ta yi shiru kawai ta mayar da kanta k’asa…
Farkawar Yadikko wadda ta yo ta cikin kuka a ta sanadiyyar kunamar da ta d’alle ta ne ta katsewa kowa hanzari, da sauri duk aka maida kallo a kanta saboda ba damar matsawa dan duk a dunk’ule su ke a waje d’aya….
Ya Amir ne ya hangi kunamar sakamokon juyowar da Yadikkon ta yi ta hau kan wannan tsohuwar dan haka ya yi saurin taketa da k’afarsa cikin ikon Allah ta mutu bata d’alle sa ba saboda babu takalmi a k’afartasa saboda duk saida aka sanya su ka cire takalmansu tukunna aka sakasu a cikin cell d’in bayan an amshe wayoyinsu….
Da sauri ita kuma Aliya ta ware d’ankwalinta ta d’aure k’afar Yadikkon dukda kunamar mitsitsiyace amma ta yi mata hakan saboda kar dafin kunamar ya game mata jiki sannann ta shiga cewa “ku zo ku taimaka mata “
Da k’arfi! Ita da Anne
suka fad’i hakan har sau biyu amma babu wanda ya nuna alamun ma ya jiyosu ballantana a zo a kulasu, sai Ya Amir ne ya gyara tsayuwarsa sannan ya kalli Anne ba tare da ya yarda ya kalli fuskar Aliya ba ya ce “Anne a k’a’idar wajen nan fa sai mun yi kwana biyu a haka tukunna za a fara bamu ruwan sha ma…”
Cikin hayagaga ta ce “ko kuma a zo a fidda gawarwakin mu ba….
Fisabillahi in dare ya tsala wanda na ke da tabbacin ana kashe wutar mai shayin chan za mu daina ganin komai, ya za mu yi?
Babu fa fitila a nan sannan kalli ramin chan na tabbata ta nan kunamar ta fito shin me kake zaton zai sake fito mana nan gaba?”
A hankali ya ce “to Anne yanzun hayaniyar nan da ki ke yi ita ce za ta fitar da mu?
Meye amfaninta?
Mu zauna kawai mu yi salati…gara ma ku a zaune ku ke….”
Ya k’arashe maganar cikin sanyin murya zuciyarsa na zafi…
Cikin b’acin rai ta ce “ae dole ka ce haka dama!
Tunda y’ar gwal d’inka da ba ka so a fad’i laifinta ce ta janyo komai.
Ita ta janyo muka rasa jaririn nan saboda mugunta da bak’in halinta sannan dan na yi magana aka kawoni nan!
Wanne kalar rashin imanine wannan fisabillahi ko da ya ke talauchi da rashin gata su suka janyo mini komai..”
A hankali tsohuwar nan ta ce “ki daina danganta kaddararki da talauchi ko rashin gata.
An riga an rubuta za ki yi zaman nan wajen tun kafin ma ki zo duniya…dan haka babu ruwan talauchi..”
Cikin rashin mutunci ta cewa tsohuwar
“Ki rufe mini baki tunda na ga alamun ba ki gama sanin ciwon kanki ba…”
“Hmm” kawai matar ta ce ta kawar da kai
Yayinda Anne ta fara k’ular da mazan da su ke tare da su a wajen, kunyar Baba ce kawai ta sanya su ke d’aga mata k’afa dan ta addabi kowa ta k’i bari kunnuwansu ma su huta..
Cike da takaici Anne ta juya kan Aliya ta ce “ki kirawo Mai Nasara..
Ko ya yanke huld’a da ke da jaririn dae ae zai so a yiwa d’ansa sutura cikin mutunci….”
Haushin Anne sosai Aliya ta ke ji shiyasa kawai ta yi mata banza bata ko kulata ba!
Dan haka Annen ta mik’e ta k’arasa jikin k’arfen ta hau jijjigawa ta na cewa “akwai wani a kusa?!“
Da masifar k’arfi…saboda Allah Allah ta ke a zo a fidda ita a nan kafin dare ya yi mai shayi ya tashi ya kashe wutarsa wadda haskenta da ke ratsowa ta window ne ya ke taimaka musu su ke iya ganin komai.
Kar ta je maciji ya b’ullo musu ta wannan bak’in ramin da ta gani, gashi ta lura ta fahimci alamun d’an gidan Aliya har ya soma kumbura saboda kwata-kwata wajen babu iska sai uban zafi da hucin d’umi duk sun jik’e saboda gumi…kar ta je gawar ta fashe musu ya yi tsutsa wari ya kashesu…
BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*
HUMAIRAH BULAMA
Yota
*05*
Da gudu ta ji an taho
kamar za su tsaga k’asa dan haka ta yi saurin jaa da baya ta shige cikin mutanen, har ta na tumurnushe y’ar tshohuwar nan, Yadikko, Aliya da jaririnta.
Baba ne ya kamo kafad’unta duka biyu ta bayanta sannan ya yi k’asa da ita da k’arfi dan gab take da fad’awa jikin Limamin layin nasu..
Cikin tsiwa ta juyo za ta yi masa ihu wata dakakkiyar murya ta katseta ta inda ake cewa
“Waye ya ke magana?”
Aka yi maganar cikin daka musu tsawa.
Mintsinin Aliya Anne ta yi alamun ta yi magana…
Da kyar Aliya muryarta ta na rawa dan mutanen kansu ababen tsoro ne ta ce “ddama Mahaifin jaririn nan zan kira, na yi muku alk’awarin in ya zo shi da kansa zai yi muku kyauta mai tsoka! Kar ku bari d’ansa ya rub’e ku taimaka a sanar masa, ko gawar ce a samu ya zo ya karb’a ni ku ci gaba da rik’eni.”
Ta k’arashe maganar ta na hawaye.
Cikin kwakkwaran kashedi mutumin ya nuna ta ya ce “daga yanzu har a zo gareku kar in sake jin bakin wata a cikinku, ku yi saving energy d’inku har zuwa nan da 48 hours!”
Sannan ya d’auke dubansa daga kanta ya fara kallonsu one by one yana nuna su tukunna ya d’aura da cewa
“Duk wanda na sake jin bakinsa kuma wallahi sai an kai shi wajen horo, ya yi 48hours d’in a chan.
Babu waya ko taimako a cikin punishiment d’inku dan haka kar ku b’ata mini rai…”
Daga haka ya juya ya wuce ya bar wajen.
Matar d’azu da ta ke ta jin tausayin Aliyar ce yanzu ma su ka zo tare da mutumin, dan haka kafin ta wuce a hankali ta d’an durk’usa kamar za ta gyara takalminta cikin dabara ta garo mata wayarta cikin gurin…
Sai da su ka bari sun yi nisa tukunna su ka taso kamar mayunwatan zakuna sun ga nama..haka su ka rarumi wayar!
Anne har da y’ar dariyarta…
Sai da su ka danna kiransa wajen sau biyar tukunna Saminu ya d’auka a na k’arshen ta na gab da tsinkewa…
Kasancewar wayar matar ba a ji sai a speaker ya sanya tunda su ka fahimci hakan su ka barta a speaker.
“Assalam alaikom”
Muryar Saminu (Yaron Mai Nasara) ta katse musu addu’o’in da su ke ta jerowa akan Allah ya bashi ikon d’auka a samu ya kawo musu d’ouki…
Aliya kuwa addu’a ta ke yi Allah ya sa ya d’auka d’in in sha Allahu ita kuma ko an zo fita ba za ta tab’a bari a fita da Amal ba ce masa za ta yi ya barta a cell d’in ita kad’ai duk a watse a barta…Allah ma ya sa abun cikin ramin chan ya kasance mai matuk’ar muni apart from kunamomin da ta ke da tabbacin akwaisu duhu kawai su ke jira su fito… ta yadda zai fito ya kasheta har lahira kowa ma ya huta…
A hankali ta cewa Saminu “Saminu ni ce, Alhaji ya na kusa?”
Cikin d’an fad’a-fad’a Saminun ya ce “ke ce wa?”
Da sauri ta ce “Aliya, na haihu ne..to jaririn ya koma..”
Jin ya yi shiruu ya sanya ta ce “Aliya mana Saminu…matar Mai Nasara..Ina so in yi magana da shi, ta gaggawa”
“Aliya Aliya Aliyaaa”
Saminun ya ambata kamar mai son tuno wani abun…
A hankali
ta ce “Aliya ta Mariri”
Cikin fahimta ya ce “Owkay mai cikin nan ko?“
Cikin sauk’e Ajiyar zuciya Aliya ta ce “eh, ni” da sauri, sai kuma ta d’aura da cewa “Ina so zan yi magana da shi dan Allah…”
Ashe ma su na tare dan k’asa-k’asa sosai ta ji ya ce “ranka ya dad’e Aliya za ta yi magana da kai, tshohuwar matarka…”
Kamar yadda Saminun ya yi da farko haka shima Mai Nasara ya yi sai dai shi d’in da ikon Allah ya gagara tunowa da ita sam, sabida cikin ikon Allah matan da ya aura masu suna Aliya su na da yawa gashi dai sunan unique ne amma shi Allah ya had’ashi da su sau dayawa.
Ganin Saminun ya na shirin saka masa ciwon kai ne ya sanya duk su na ji kawai ya rufesa da fad’a!
Ko bari Saminun ya yi masa cikakken bayanin da zai gane ta bai yi ba hakanan ya rufesa ruff da fad’a kamar mai shirin dukansa, dan shi a k’a’idarsa in ya bar mace to ya barta kenan har gaban abada, kuma Saminun ya sani amma ji bi dan iya shege ya na yi masa maganar wata wai ita Aliya.
Cikin tsantsar ladabi bayan Mai Nasara ya dire aya yana haki su ka ji Saminu ya ce “ranka ya dad’e ji na yi ta ce ta haihu ne kuma ta na buk’atar taimakon ka cikin gaggawa…”
A hankali Aliya wadda jikinta ya yi mugun sanyi ta tari nunfashin Saminun ta hanyar cewa “Yaron ya koma kuma an k’i bari mu binne shi Ina cell yanzu haka har ya fara kumbura…
Sakamokon wajen akwai masifar zafi mu kanmu da kyar mu ke iya zuk’ar iska, ga numfashi ya yi yawa a d’an k’aramin d’akin da su ka gwamutsa mu…”
“Subahanallah” Saminu ya ce sannan ya shiga sanarwa Mai Nasara abunda Aliyar ta gama zaiyyane masa yanzun…..
Amma ga mamakinsu sai su ka ji a fusace Mai Nasara ya ce “ka ci kutumar ubanka Saminu!”
Sai kuma ya warce wayar daga hannunsa sannan ya ce “Ke! Naira miliyan nawa aka baki bayan na sake ki? Meye naki na bibiyar rayuwata ko wani sabon raini ne ya b’ullo muku?
Kin kashe kud’ad’en shine za ki sake dawo min sabida ga ATM machine nan kin samu ko?”
Cikin sharar hawaye zuciyarta ta na wani kalar k’una ta ce