Showing 75001 words to 78000 words out of 100561 words

Chapter 26 - BAKAR TUKUNYA hausa novel

07 Feb 2026

479

su tashi zama ba dan kaɗan daga aikin Anne ta bisu har majalisar ko shagon da Baban ya ke a yi ta ka-ce-na-ce da ita.

Ife-ife ta ke yi sosai kamar za ta haɗiye harshenta.

Ganin sun fita sun barta su na shirin saka mata hawan jini ya sanya ta miƙe tsaye za ta bi su kamar yadda su ka zata.
Da sauri Afra ma ta miƙe dama a bakin ƙofa ta ke dan haka sai ya zamana kamar ta tare mata hanya ne.

Sai da hasken kendir ɗin ya haske fuskar Yarinyar tukunna Anne ta fahimci kuka ne ta ke yi sosai dan idanunta har sun sauya, cikin kukan Afra ta shiga cewa “Anne ya kamar ki na baƙin ciki da farin ciki na ne, Anne da gaske tarwatsa aurena da Ya Isma’il ki ke son yi?…”
Shiruu Anne ta yi kafin ta runtse idanunta da masifar ƙarfi a ranta ta na tsinewa Baba tun daga kan kakannin kakanninsa har shi!
Domin kuwa shi ne ya tunzurata ya sa ta yi behaving hakan a gaban Afra, bata so Yarinyar ta tsaneta fiye da yadda ta san ta tsaneta dan in hakan ta faru ba lalle ta ji ƙanta ta kula da ita ba wanda jin ƙan nata shine main goal ɗin komai da ta ke yi yanzun, duk wani plan nata akan Yaran su auri mai kuɗi da faɗi tashin da ta ke yi duk sabili da su ji ƙanta ne….

Dai-dai nan Kaka Nura ya ɗaga labulen ya shigo!
Jin Afra na kuka ya sa ya ƙarasa shigowa ciki da sauri kamar ba ɗakin surikinsa ba ya ɗan waigo da ita ya na kallonta sosai kafin ya kalli Anne ya ce “Mai ki ka yi mata? Shigowata kenan tun daga waje na ke jin hayaniya sannan na ga su Habu sun fita da wuri”
Sai kuma ya yi shiruu ya na kallon fuskar Annen itama sosai kafin ya ce “me su ka yi muku dan ubansu?”

Share hawayen takaicin da su ka zubo mata babu shiri! Anne ta yi, sannan ta shiga zaiyyano masa komai, tun daga saka ranar Afra da aka yi a ɓoye(wanda already ta gaya masa bayan ta sani shima a ɓoye) har kawo yanzu da Baba ya dage sai an yi auren ta na kaiwa nan ta fashe da kuka sannan ta durƙushe a wajen kawai duk dan Afra ta tausaya mata….ta na cewa “saboda ban isa ba saboda ban kai ba in haifi Yarinyar amma a nuna mini isa da mallaka….”
Numfashi Kaka Nura ya jaa ya sauƙe sannan ya kamo kafaɗun Afra ya juyo da ita saitin shi tukunna ya soma magana
“Kinga in har ki na da hankali tou kalmar ba a chanjawa tuwo suna da suka yi amfani da ita su da su ke manya ya kamata ace kema ƙarama kin ɗauka kin yi amfani da ita, kin ga wannan..”
Ya yi maganar ya na nuna mata Anne sannan ya ɗaura da cewa “ba ki ta tamkarta ko da a bola ta ke yawo ita ɗin ce dai ta haifeki ba za ki taɓa sauya ta ba, in har ki ka yarda ki ka bari su ka raina miki ita to wallahi kin shiga ukunki, dan ba ki isa ki chanjawa tuwo suna ba haka maganar ta ke, sannan kalli ki ga tun yanzu sun fara yi miki gori tou na tabbata in ki ka bari aka kai ki gidansa babu kayan ɗaki a yadda su ka iya gorin nan su na gani kamar sun yi miki alfarma tabbas nan ma wahala za ki sha a hannunsu, kuma above all ma ta ya za ku yi amfani da kayan matar da ba ta raye, ke ba ki da tsoro ne? Ki bari in shi Habu ya ce ba zai yi miki ba, da ni da Annenki mun yi miki alƙawarin za mu yi miki kinji ko?
Ki tashi ki tsayawa kanki tun yanzu ki san darajarki ki nuna musu ki na da daraja, kar ki yarda wani wai dan a na tausaya miki a yi rushing aurenki in ki ka bari aka tafi a haka har abada gani za su yi kamar alfarma su ka yi miki, ki kwantar da hankalinki in kinga ba ki auri Isma’il ba to ba Mijinki bane ba, ina guje miki shiga gidan miji babu daraja Afra sam kar ki yarda da hakan kin ji ko? Kar ki yarda a ci miki fuska!
Ba wai auren ne ba ma so ba a’a rainin wayon da su ka zo da shi ne ba ma so sam-sam dan Allah kema kar ki yarda da shi, a bi komai a hankali a kwatar miki hakƙinki da darajarki in Mijinki ne za ki aureshi amma in ba Mijinki bane ba yadda su ka soma wulaƙancin nan za su iya ƙasƙantar da ke kuma still su hana auren tunda har su na gani kamar alfarma za su yi miki, sannan Annenki mace ce fa kawai da ta ke frank haka Allah ya yi ta ba wai muguwar banzar shaidar da su ke shirin ƙaƙaba mata ku ku ke son karɓa hannu bibbiyu ba, akwai Matan da su ka fi ta fitina ma kuma an auri ƴaƴansu wasu ma karuwai ne amma surukansu su na darajasu da girmamasu dan haka kar ki yarda a ɓata miki sunan Mahaifiya a ɓata miki tarihinki sannan a raina miki ita, shawara ce kyauta na baki ki yi tunani a kai….ki taimaka ki takawa isma’il burki tun yanzu dan in an tafi a haka ba za ki ji daɗi ba gashi daɗin daɗawa shine komai naki tun ki na Yarinya dan haka in ya fara goranta miki za ki sha wahala, shi aure daga ɗokin amarci ya fita halin kowa ya ke fitowa…
Kayan ɗaki na yi alƙawari zan yi, ni da Annenki kin san dai in na ce zan yi abu to zan yi ko? Dan haka ki nutsu kuma ki yi tunani na san ki na da hankali da zurfin tunani, sai ki yi abunda ya dace…..”
Ga mamakin Anne sai ta ga Afra ta hau ɗagawa Kaka Nura kai a hankali kafin ta ce “tam”
Murmushi ya yi ya shafa kanta tukunna ya ce shikenan ki je abinki sai da safe ko? Allah ya yi miki albarka….
Jikinta a matuƙar sanyaye dan ba ma ta san ta ina za ta yi tunani ba sun soma birkitata, haka nan ta juya ta fita kamar wadda kwai ya fashemawa a ciki….

Sai da Anne ta tabbata Afra ta shige ciki tukunna ta ce “ka na ganin maganganun nan sun yi aiki?”
Murmushi Kaka Nura ya saki kafin ya ce “ae shi Yaro duk wayonsa in ka ɗauresa ta koina dole za su bi ta inda ka ke so ne, ki jira ki ga ikon Allah ko duk ba su shiga kanta ba dole wani ya shiga.
Ki kwantar da hankalinki na san wacece Afra ba ta so a taɓa mata darajarta da na ahalinta, ae Habu da shi kanshi Usman ɗin sun yi laifi dan kamar sun bada ƙofa ne…

Yanzun nan fa da Samuel mu ka rabu, jari ya ke shirin bata miliyoyin kuɗaɗe! A haka su ke so su aurar da ita a Isma’il dan hauka da rashin sanin ciwon kai, hmm Ana nuna musu Annabi su na runtse ido, Allah wadaran naka ya lalace…”
Cikin sauƙe wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya Anne ta ce “Ameen”
Sannan ta ce “amma ka na ga ko ita Afra ta birkice za su yarda a ɗaga bikin nan kuwa anya..”
Dariya Kaka Nura ya yi sannan ya ce “Bari ta birkicema Isma’il ɗin ki ga ikon Allah, ae su kansu akwai shakku a kansu dama trigger kawai yakamata mu nema kuma gashi mun samu damar dasa ta cikin sauƙi, ke kuma daga nan sai ki san abun yi kafin wani ikon Allahn ya sa a daidaita tsakani.”
••••••••••
Vietnam, Asia.
Ho Chi Minh(Saigon)
5:30am

Babban gym ne wanda ya ƙunshi komai da za a buƙata a duk wani gym har ma da extra!

Girmansa har abun ban mamaki yayinda kayayyakin da su ke a ciki kai kana gani ba sai an gaya maka ba ka san each and everyone ƙarshe ne a fannin tsada quality da kuma kyau!
Sai wanda aka gayawa ne zai san cewa personal gym ne ba public ba saboda tsabar yadda ya ke da girma, kyau da kuma yadda aka narka uwar dukiya a cikinsa kamar ba gobe.

Bayaga kayan ciki sai wasu maka makan speaku da su ke a cikin wajen suma har abun tsoro dan tsawonsu da faɗinsu ma kaɗai abun kallo da mamaki ne , ɗaya ta ɓangaren dama ɗayan kuma ta ɓangaren hagu, su na fidda wani sauti na asalin duma mai tsananin ƙara da ratsa kwakwalwa.


Gudu ya ke yi sosai akan treadmill machine ɗin dan ya kaishi kusan ƙarshe, ga uban kiɗa ya ƙure, ya na fidda zufa ta ko wacce ɓular gashi da ke a jikinsa…kallo ɗaya tak za ka yi masa ka fahimci ranshi a masifar ɓace ya ke dan yadda ya ke gudun ya na huci kaɗai ya isa ya faiyyace maka hakan…
Dogo ne sannan ƙaƙƙarfa wanda motsa jikin da ya maida ɗabi’arsa ta yau da kullum ya taimaka sosai wajen sake maida shi murɗaɗɗe sai dai ba chan sosai kamar na ƴan wrestling ba kawai dai ka na ganinsa ka san ya ji exercise yadda ya kamata…
Ba za a kirashi fari ba sannan ba Baƙi bane ba wanda hutu da asalin jin daɗi su ka taimaka kwarai da gaske wajen sake tsara fatar tashi da colour ɗinta ta zamto abar sha’awa, kallo har ma da ban mamaki….


Ya jima ya na gudun ya na furzar da numfashi ganin ɓacin ran ya ƙi raguwa sam-sam ya sanya kawai ya danna abun ya fara slowing down a hankali a hankali kafin ya chan kuma ya tsaya chak!
Gege da gefen handle ɗin ya kama duk biyun ya tsaya ya ɗan rankwafa yayinda fuskarshi ta ke kallon ƙasa ya yi shiruuu kawai trying to calm himself down amma sam ya gagara! Zuciyarsa sake hawa kawai ta ke yi, bai san lokacin da ya ɗago ya yi fatali da bottle water ɗin da ya ɗaura a kan machine ɗin ba sai kuma ya yi shiruuu kawai ya ƙurawa bottle water ɗin idanu…

Kafin chaan ya ɗauka remote ya kashe kiɗan sannan ya lumshe idanunsa sosai ya na mayar da numfashi…
Ba wai abunda ya faru bane ya ke sake ɓata masa rai ba, yadda abun ya ɓata masa rai ne main damuwarsa saboda a kaff yanayi da tsarin rayuwarsa bai kamata ya zama envious akan kowa ba…ba ya yi kuma ba ya so ya fara, duk da dai shi ya kamata a bawa, kowa ya shaida hakan kawai kwatsam ya ga an bawa wani but still kamata ya yi yai masa murna dan its obvious to him ba wai betrayinng nasa da aka yi bane ya fi fusata shi ba yadda aka ɗauki matsayin da ya yi working very hard for it aka bawa waninsa ne ya fi ɓata masa rai…
Wanda shi kuma he hate the feeling sosai he’s not suppose to be this envious no matter what….

Ƙarar wayarsa ce ta katse masa lissafin da ya ke yi, a hankali ya buɗe idanunsa waenda su ka kaɗa su ka yi jazuur! Har abun tsoro….
Bai ko motsa daga inda ya ke a tsaye ba ballanta a saka ran zai amsa, a haka har aka jera masa 5 misscalls, tun ɗazu ake ta kiransa yana ganin wayar ta na ta yin haske daga nan inda ta ke a kan kujera wanda yadda aka kirashi a yanzun a jejjere kaɗai ya isa ya fahimtar da shi wacece dan duk duniya ita ɗaya ce kwallin kwal ta isa ta yi
mishi kalar wannan kiran ta dameshi har haka…
Tunowa da ya yi da ita da kuma yadda ta samu audacity na takura masa ya sanya ransa ya harzuƙa ya sake ɓaci!

A hankali ya ɗaga kanshi sama ya runtse idanunsa kafin ya furta “Ya Subahanallah…..”
Ya jima a haka bai ko motsa ba kafin ya sauƙe kan nasa ya na mai jan numfashi tukunna ya juya kawai ya nufi bathroom ɗin da ke a cikin wajen ya na shiga ya sakarwa kansa ruwan sanyi, sai da ya ɗan soma dawowa dai-dai tukunna ya shiga zamiye kayan jikinsa a hankali cikin nutsuwa ya yi wanka mai ma’ana da tsafta.


A nan cikin bathroom ɗin ya shirya tsaf ta inda ya shafa mai ya fesa turare sannan ya sanya wata hoodie mai asalin kyau da tsada milk colour brand na Nike wadda ta taimaka wajen sake fito da shi ras!
Tukunna ya fito daga cikin bathroom ɗin ya na zuba ƙamshi da asalin kyau! Domin kuwa in dai maganaar kyau ne ake yi tabbas ya ci a bawa ASAD award, namba ɗaya!.


Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING*
Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING*
Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139*

Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudin ku tested and trusted.

Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu....
location:Kano
Delivery:NationWide.
kar ku bari a baku labari, sai kun zo🙏
SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA

BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252[10/22, 8:25 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*

HUMAIRAH BULAMA

Yota011

*30*

Ya na fitowa ƙarar wayarsa ce ta yi masa sallama, kamar ba shi ake kira ba haka ya yi dan sai da ya tsiyayi coffee ya ɗan yi sipping har kusan sau uku ma tukunna a nutse ya ƙarasa inda wayoyin nasa su ke zube nan kan kujera.

Kamar yadda ya zata ɗin kuwa ya na kai idanunsa kan screen ɗin wayar da ta ƙi daina ƙara ya ga sunanta ɓaro-ɓaro akan screen ya na yawo “Ummee”
Tsaki ya yi kawai ya zubawa wayar idanu ransa na kammala ɓaci, kafin kuma ya ɗauka ta na gab da katsewa ya yi rejecting!

Shiruuuu, ya yi kamar ba zai yi wani abun ba sai kuma kawai ya kashe wayar sannan ya kashe ragowar saboda ya na so ta san ba katsewa kiran ya yi ba shine ya kashe sannan ya kashe wayar ma gaba ɗaya as a result of annoying calls nata da ta ke ta damunsa da su kamar ba ta san safiya ce a nan ba! Besides ta ya ma za ta kirashi yanzun da ya ke da tabbacin sha biyu ta wuce ma a Nigeria……

A aljihu ya zuba wayoyin nasa, ya ajjiye cup ɗin a wajen sannan ya wuce zuwa wajen elevator wanda zuwan nashi da kunnawar da ya yi ya shigeta ne zai sanya a fahimci ashe gym ɗin underground ne a cikin haɗaɗɗiyar villar tasa da ke a cikin birnin Saigon ɗin.
……
Tsaye take ta na ta faman kai kawo a tsakiyar tafkeken parlourn nashi da ke a ground flour!

Ganin hakan ba zai fishsheta ba ya sa ta ɗago wayarta ta sake gwada kiran layin nashi.
Jin ba ta shiga ba a kashe, ya sanya ta sake tabbatar da tabbas rejecting ya yi ɗazun kenan kuma ya kashe wayar ma gaba ɗaya duk dan saboda ita….
Kamar ta haɗiye zuciyarta haka ta ji, gashi wae da ikon Allah an hana ta hawa sama a iyaka wannan parlourn masu yiwa gidan hidima su ka barta a gantale kamar basu san matsayinta a wajen Mai Gidan ba!
“Ko da ya ke ba laifinsu bane ba ae, shi ya bada fuska dan ina da tabbacin ma hakan dokarsa ce…”
Ta furta hakan a hankali kwallah ta na taruwar mata a idanunta.

Dai-dai nan ƙarar tsayuwar lift ta iske kunnuwanta, sai dai sam ba ta yi tunanin shi ɗin ne ba dan haka ko yunƙurin juyawa ma ba ta yi ba.
Tana ta ƙoƙarin ganin ta hana kanta zubda hawaye yayinda shi kuma tunda lift ɗin ta buɗu ya ƙurawa bayan nata idanu sosai ya na mamaki

A ranshi ya ce “zuwa ta yi kenan.....”

Gold ne ƴan Ubansu a hannayenta da ya ke iya hanga sannan lace ɗin da ke a jikintaa kallo ɗaya za ka yi masa ka san cewa mai asalin tsada ne na fitar hankali, suitcase da handbag nata duk suma na bugawa a jarida ne haka vail ɗinta shim, a taƙaice dai ka na ganinta ka ga kuɗi!
A hakan ma ba ta kai ga juyowa gaba ɗayanta ba.

A hankali Asad ya sauƙe ajiyar zuciya, dama yadda ta ke ta kiransa tun jiya yau kuma a jejjere ko shakka babu ya san wani abun ta ke da buƙata a wajensa! Yanzu kuwa da ya ganta a nan ɗin ya tabbatar tunda daga gani ba tambaya kasa haƙura ta yi ta taho da kanta.

"Good morning sir"
Muryar Jessica(a maid) Ta katsewa duk su biyun lissafin da su ke yi.

Da mugun sauri Ummeen ta juyo har kamar za ta kifa dan sau bakwai elevatorn na yin ƙara in ta juya sai ta ga ba shi bane ba masu yiwa gidan Hidima ne su ke ta kai kawo, shiyasa yanzun ma sam ba ta kawo shi ɗin bane ba.


Fara ce sosai tass!! Dan har ɗaukar idanu ta ke yi, ba ta cika tsayi ba sannan ta na da ɗan jiki, a fuska kuwa in ka kalleta kai tsaye za ka fahimci ta na matuƙar kama da Asad wanda hakan zai sanya a gane ita ɗin Mahaifiya ce a garesa.
Kamar yadda gold su ka yi mata ƙawanya a hannu haka nan wuyanta da kunnuwanta har ma da ƴan yatsunta abun har kamar hauka tsabar yawa da girmansu......

"morning"
Kawai Asad ya ce da Jessica daga nan ya nufi masters bedroom ɗinsa wanda ya ke a nan ground floor ɗin dan a cikinsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login