Showing 87001 words to 90000 words out of 100561 words
ni ki fita kar zuciyata ta buga dan Allah, kin tarwatsa dukkan farin cikin rayuwarmu kin kashe Ya Amir da ranshi, kin juyawa Baba lissafinsa kin chanja shi, Anne ba zan iya ci gaba da yafe miki ba ki fita kawai…saboda kawai an dakatar da ke daga aikata tsafi a cikin gidan nan shine ki ka burkice kai tsaye ki ka tarwatse duk wani abun daɗi da ya yi mana saura? Da wanne ido ki ke so Ya Amir ya kalli mutanen da kika gama dasa kokwantonsa a kansu? Wanne kalar ɗanyen aiki ne wannan ki ka aikatama rayuwarsa? Menene wannan baƙin fentin? Daɗi kika ji yanzu da ki ka yi masa haka?
Ke fa uwa ce Anne amma wae yau da bakinki ki ka faɗi hakan a kanshi kin san tasirin da maganar za ta iya yi kuwa?
Innalillahi wa inna ilaihirrajiun.”
Afra ta ambaci hakan cikin dunƙulewa waje ɗaya ta samu da kyar ta zame daga jikin Anne ta durƙushe a wajen ta na kuka sosai…
Muryarta har ta disashe amma hakan ta ci gaaba da cewa “ki fita…ki fita Anne, ki fita ba na ƙaunar ganinki.”
Cikin kwantar da murya Anne ta ce “Afra komai fa na yi na yishi ne domin ke dan Allah ki nutsu ki ji ni…
Mahaifiyar Isma’il….”
Cikin katseta Afra ta ɗago rinannun idanunta ta zuba mata su sosai sannan ta ce “ki ji da kanki! Ki je ki fara neman yafiyar Ubangiji na shirkar da ki ka yi! Sannan ba ni ya kamata ki ji da ba a halin yanzu, kamata ya yi a ce ki na tare da Ya Amir….
Anne ki fita daga ɗakin nan tun ban gudu na bar rayuwarku ba na har gaban Abada…”
Ta faɗi hakan cikin tsantsar ɓacin rai, kwata-kwata ba ta ƙaunar ganinta wallahi.
“To”
Kawai Anne ta ce daga haka ta juya ta fita kanta na soma yin ciwo, ba ta so ta sami matsala da Afra dan Yarinyar ta na da ruƙo, so take ta biyo ta ƙarƙashin ƙasa ta tarwatsa auren…..ba ta so Afra ta fahimci ba ta son ta auri Isma’il dan in Yarinyar ta fahimci hakan tabbas za ta ga kamr bata son farin cikinta ne kuma ba lalle ta kula da ita a gaba ba, ba lalle ta ji ƙanta ba ko da kuwa ta auri mai kuɗin ne a gaba…shiyasa take ta fakewa da a ƙara lokaci da ragowar kame-kamenta ba ta so ta fitowa Yarinyar ras!.
Gashi yanzu aikin da ta shiryo ya warware, ga Baba shima ta na da tabbacin komai na kanshi ya ware, kar fa ta je ya saketa! Sannan ga batun aure yana ta ƙaratowa…
Ta ina ma za ta fara ne oho!!!
Ba ta Ya Amir ta ke ba ita kam yanzu shi ya sani, ya so ta ko kar ya so ta ba damuwarta bane ba, dan bata hango kyallin arziƙi a tattare da shi ba ballanta ta yiwa kanta tanadi da shi, dan haka in ya ga dama ya ƙullaceta, ita su Afra su ne damuwarta! Shiyasa ko kallon hanyar ɗakinsa ba ta yi ba ta nufi nata sai kuma ta juya ta wuce hanyar Banɗaki, tabbas ta na buƙatar kusanci da Ubangijinta dan a yadda abubuwa su ka caɓe mata haka ta na buƙatar ya kawo mata ɗouki….
Ba tare da ta yi addu’ar shiga cikin banɗakin ba ta afka kanta ko hula babu, kanta tsaye ta kwaye ta durƙusa ta shiga sheƙa fitsarin shaa!! Kamar an kunna shower. Sai da ta kammala ta janyo buta tukunna ta ga ashe ruwan ɗan mitsitsi ne sosai…ganda ba ta barta ta fita ta je ta ɗebo wani ba da wannan ɗan mitsitsin da bai fi cikin cokali biyu ba ta yi wannan tsarkin ta inda ta zuba a hannunta ta goga a koina na gabanta ita kanta ta na jin yadda ta ke damalmale wajen da fitsari da ragowar abubuwa! Gaba ɗaya ita kanta ta san ba ta fita ba sai kazanta ma da ta ƙarawa koina a wajen amma haka nan ta miƙe ta saki zaninta ta fito waje ta bar banɗakin shima kacha-kacha da fitsarin da ba ta kwara ruwa ba yanata uban zarni.
Ruwa ta zuba a butar, ta sunkuya a bakin randar ta shiga alwallarta mai abun ban mamaki, ta inda ta wanke komai ɗaɗɗaya a gaggauce sam babu nutsuwa koina in an kalla sai an samo lamɓarsa kamar wata Yarinya.
Tukunna ta miƙe ta shiga ciki ta na tunanin wacce sallar ya kamata ta yi….ana binta bashin salloli dan rabonta da yin sallah an jima gaskiya….
A cikin kayan su Afra ta ɗauko Hijab babba a wanke a goge ta zura ba ta shimfiɗa komai ba ta tada sallar anan kan tangaryar sumintin ɗakin.
Fatiha kawai ta ke karantawa ɗaya da kwata a duk tsayuwa, ruku’u da sujood kam duddungurawa kawai take yi gudun kar ta tsaya karatunsu ta ɗauki lokaci mai tsayi ba ta idar ba. Ƙaratun zaman tahiya kuwa ta daɗe da haƙura ta shi dama dan ta gagara koya, dan haka a hakan ta gabatar da sallar isha ta jiya da asuba ta yau, ta idar ta zauna ta na istighfari, da ikon Allah kuma sai ta ji zuciyar da ta ke ta faman tunzurota ta na sauƙa.
••••••••••
Da mugun kyar ya iya cewa Jessica “excuse me..”
Muryanshi na shaking sosai.
Da sauri ta juya ta fita bayan ta yi mishi alamun girmamawa ranta babu daɗi sam! Ba ta so ta ga Ogan nata cikin damuwa, ko da ƙanƙanuwa ce.
Ta na fita ya miƙe tsaye ya ƙarasa jikin mirrow kawai ya tsaya ya na kallon kansa….
Sosai ya ƙurawa kansa ido ya na so ya ga wae ko zai ga wata shedar da za ta tabbar masa akwai matsala a tare da shi a jikin madubin amma shiruu.
Ya jima a hakan kafin chaan ya sunkuyar da kanshi ƙasa ya saka dukkan hannuwansa biyu ya dafa bangon da mirrow ɗin ya ke a jiki ya saka madubin a tsakiyarsa ya na mayar da numfashi bugun zuciyarsa har yanzun bai daidaita ba!
“Ya Allah, duk ƙanƙantar halitta Allah kar ka bani ikon ko da cutar da ita ne….”
Ya furta hakan a fili kansa na juyawa sosai….
“I can never hurt anyone, ban kashe kowa ba wallahi.”
Ya sake furta hakan idanunsa taff da kwallah ka na ganinsa ka ga super helpless, bai san ya zai yi ba sannan bai san ta ina zai fara ba tbh bai ma san menene wannan ɗin ba sannan bai san wa zai samu ya faiyyace masa ko ya taimakesa ba, above all he is super damn scared about the whole thing.
Shi a karon kansa tsoro ya ke bawa kansa….
A hankali ya furta “innalillahi wa inna ilaihirrajiun!!! La ilaha illa anta subahanaka inni kuntu minazzalimin…”
Wayar Jessica ce ta shiga ƙara wanda ƙarar ya razana shi ya juyo a zabure sosai.
Sai kuma ya lumshe idanunsa trying to calm himself down, dan tsoro ko ɓacin rai su ne last abubuwan da zai bawa damar shiga kanshi su samu gurbi a halin yanzu after what just happened.
Sai da wayar ta katse aka sake kira tukunna ya buɗe idanunsa da kyar ya ƙarasa inda wayar ta ke yashe a kan gado tana ƙarar taimakon a kawo mata agaji, ya na ganin number ya ji gabansa ya yanke ya faɗi…
A hankali ya saka hannu, hannun nasa har karkarwa ya ke yi, ya ɗauko wayar tukunna ya yi picking call ɗin ya kara a kunnensa sannan ya ce “good morning sir..”
Cikin kulawa mutumin ya amsa kafin Asad ya miƙa condolences ɗinsa zuwa ga mutumin, shima ya amsa daga mutumin, tukunna mutumin ya yi gyaran murya, kanshi tsaye ya fara magana cikin harshen turanci.
“Duk ɗinmu mun yi babban rashi, amma kasancewar akwai aiki a gabanmu mai tarin yawa ya sanya dole za mu yi saurin yin gyare-gyare sannan mu ci gaba da abubuwan da ke a gabanmu ba tare da ɓata lokaci ba, saboda mutane mu su ke jira akwai abubuwan da dole ya kamata a yi launching nasu very soon…..
…da ni da ragowar board members mun yi nominating naka as our new ceo. Za a kammala sannan a gabatar da komai jibi....."
Shiruu kawai Asad ya yi ya kasa magana ya na mai sauraronsa ya na ci gaba da cewa “because we shall be holding a meeting, next tomorrow in sha Allahu, at Abuja.
All the best and congratulations…”
Mutumin ya furta, daga nan ya kashe wayar ba tare da ya jira jin abunda Asad ɗin zai ce ba.
Ya fi mintuna goma kare da wayar a kunnensa kamar wani statue ya ƙurawa waje ɗaya idanu kafin finally ya zare wayar daga kunnensa ya ajjiyeta a gefe ya yi shiruu, bai ma san me zai ce ba! But one thing is for sure he’s not happy about their nomination! Yeah it has been his dream amma after what just happend gaba ɗaya komai ya fice masa a rai fit!!! He hate the job, but ya san idan ya yi rejecting a yanzun quenstions may rise and in bincike ya yi bincike wataƙila a kamoshi tunda shi a karon kansa bai san garin yaya ya aikata wannan aika-aikar ba shiyasa ya ke jin tsoron ma tambayar wani game da al’amarin dan ba ya so a zo bincike a kama shi dumu-dumu.
Da ma ace akwai tsayayyiyar uwa wadda ta shaƙu da shi ko Uban da ya damu da damuwarsa to da abun ya zo masa da sauƙi.
A take wata zuciyar ta ce masa “yanzu kenan ka ci buluss!!”
Kamar wani taɓaɓɓe, a fili ya ce “it was out of my control, it wasnt my fault…”
Sai kuma wata zuciyar ta ce “to maybe ma fa ba laifinka na komai, kawai ka uzzurawa kanka ne…”
Yanzun ma kamar ɗazu a fili ya ce “nooo…incidence ɗinnan i’m pretty sure it wasnt just a dream..i still can feel everything….”
Sai kuma ya saka hannunsa ya dafe kansa da masifar ƙarfi ya shiga ambaton sunan Allah….
Sai da ya ɗan dawo dai-dai tukunna ya ƙarasa ya zauna a kan gadon ɗakin…. ya jingina bayansa da jikin fuskar gadon ya miƙe ƙafafunsa a kai,
Baya ga abubuwan nan da su ke damunsa on top
of everything yanzu kuma wai Nigeria zai tafi….a hankali ya lumshe idanunsa ya ce “Nigeriaaa…”
Ƙasar da ya ke gudun kasancewa a cikinta kenan, amma to ya zai yi!!!
Ta koina kawai shi dai an ɗauresa an dagula masa lissafi.
Astaghfirullah….
••••••••••••••
An kai ruwa rana tukunna Ya Abba ya ɗan nutsu, sai a sannan ne Adda ta fito daga cikin ɗakin bayan ya tabbatar mata da ‘babu komai, bacci ne ya ke son yi.’
Ta na fita ɗakin Ya Amir ta nufa amma juyin duniya ya ƙi buɗe
mata kawai dai ya ce mata "he’s fine" dan haka ta haƙura ta wuce ciki da parlournta direct, a ciki ta samu Amal ta haɗa kai da guiwa ta na kuka sosai…
Wata nannauyar ajiyar zuciya Adda ta sauƙe kafin ta ƙarasa zuwa gareta ta zauna a hankali tukunna itama aka shiga aikin rarrashinta.
A bakinta bayan ta tsagaita kukan ta ji batun auren Afra wanda za a ɗaura nan da kwanaki 6 in Allah ya kaimu da komai da ya faru a jiyan.
Da farko Adda murna ta soma yi sai da ta ji yadda Anne ta yi da komai kuma sai jikinta ya yi sanyi sosai. Hankalinta bai gama tashi ba sai da ta ji yadda Afra su ka yi da Ya Ismail da safiyar nan…
A hankali ta gyara zamanta da kyau sannan ta furta “Allahumma ajirni fi musibati..
Ina ita Afran ta ke, ina son magana da ita…
tabbas ta tafka kuskure a batun zuwa hotel amma ban ga laifinta ba tunda Anne ta riga ta fita wayo, yanadaga cikin dalilan da ya sa ta ki sakewa a yi maganar ciwon nata da kowa sai Afran saboda ƙarya ne take yi garr ta ke, Baba ma ya ce ƙarya ne nima na san ƙarya take yi, duk a cikin ƙulle-ƙullenta ne….
Ita kuma Afra ta biye mata.”
Cikin sauƙe numfashi ta ɗaura da cewa “dan haka yanzu sai ta yi haƙuri da duk abunda zai biyo baya ciki har da ƙin biyewa Isma’il su yi faɗa tunda ita ce ta taɓo shi dan haka in ya hau ita ta dinga sauƙa, har a samu a ɗaura auren nan lafiya komai ya daidaita.”
“Nima abunda na gaya mata kenan ɗazu Adda kamar ki
na nan, amma a wuya take itama ta ce wai ya na yi mata gori kuma duk a cikin zugar Anne ce Ya Afran ta ɗauka, ya kamata ki sameta ki yi
mata magana…..
Ban san ina take ba. Tun ɗazu na shigo nan ni, inaga ba za ta wuce ɗakinmu ba…”
Cewar Amal
Numfashi Adda ta jaa ta sauƙe a hankali ta jinjina kai kawai ta na lissafi, a ranta ta na Addu’ar Allah ya bawa auren nan ikon ƙulluwa Allah kar ya bawa Anne ikon cimma burinta dan a yadda ta hayayyaƙo ɗinnan da dukkan ƙarfinta ta kirsa da asiri tabbas abun ya bata tsoro kwarai.
Jigummm…
Haka suka wanzu a cikin parlourn kafin Adda ta miƙa hannu ta ɗauko wayarta, sai da ta gwada kiran layin Baba ta ji a kashe, tukunna ta nemo sunan Aliya ta kira…da fatan Allah ya sa Baba da Ya Amir su na lafiya.
Sai da ta katse aka sake kira tukunna Aliya ta yi picking cikin muryar yanayin barci ta ce “Hello, Adda”
Murmushi Adda ta yi sannan ta ce “na’am ƴar albarka…”
“Na’am”
Itama Aliya ta ce, kafin ta yi hamma ta yi salati sannan ta ce “ina kwana, Ya Amalulu?..”
Yanzun ma Adda murmushin ta yi tukunna ta ce “Alhamdulillah…
Ga ta nan lafiyanta ƙalau.”
Sai kuma ta ɗan yi jimmm tukunna ta ce “auren Afra saura kwanaki biyar fa!”
Zaro idanu waje Aliya ta yi ta miƙe ta zauna daga kwancen da ta ke sannan with full of exitement ta ce “ma sha Allah, Alhamdulillah.”
Sai kuma ta ɗaura da cewa “amma mai yasa ya yi short sosai time ɗin?”
“Hmm, gida dai kamar kullum a rinchaɓe ya ke, sai kin zo dai. Yaushe za ki dawo?”
Cewar Adda.
Shiruuu Aliya ta yi kafin jikinta a sanyaye sosai ta ce “gobe in sha Allahu, yau ma ɗin inada abubuwan da zan yi covering ne shiyasa amma da na taho, ina Amalulu?”
Murmushi Adda ta yi cikin yaba ƙaunar da Aliya ta ke yiwa ƙanwartata ta ce “Allah ya taimaka ya kawo ki lafiya.
Ga ta nan, dama bata gama hucewa ba, karɓi ki ci gaba da aikin rarrashin ni na tafi haɗa abun kari…”
Murmushi Aliya ta yi sannan ta ce “tam shikenan Adda, also…
Inada good news da zan taho muku da shi gobe in sha Allahu its a surprise na san za ku ji daɗi kwarai. Duk ku shirya..”
“Allah ya kawoki da good news ɗin lafiya”
Adda ta ce ta na murmushi daga haka ta miƙawa Amal wayar ta tashi ta fita waje.
……….
Jigum haka gidan ya kasance kowa ya ƙule a ɗaka ya yi shiruu, Amal ta na gama waya da Aliya ta yi barci a wajen…Afra kam tun fitar Anne daga ɗakin ta ke karatun Al’qur’ani ta na kuka sosai, tun tana yi tana kukan har ta zo ta daina kukan.
So take yi ta kira Ya Isma’il amma kuma wata zuciyar ta na hanata! Ashe haka so ya ke? Ba ya tashi baiyyana kanshi muraran sai ka ga kana shirin rasa abun ko in saɓani ya gilma a tsakani…wani kalar zazzafan so da ƙaunar Ya Isma’il ne su ka yiwa zuciyarta sallama ga kuma fushin da ta ke yi da shi na abun da suka yi mata shiyasa gaba ɗaya ta ke neman sake burkicewa sannan ga case ɗin gidansu da baya ƙarewa kullum su na cikin drama.
Har ɗaki Adda ta kai mata abun kari wanda kunu ne kawai, dan sun yi ƙaƙaff sosai…bayaga kunun da ta samu ta dama musu da mugun kyar ba su da komai a kitchen ɗin nasu sai kanwa.
Ko da ta shiga ta tarar ta na karatu, sai ta ajjiye mata ta juya ta fito tausayin Yarinyar fall ranta, in ta huta ko zuwa anjima ne in sha Allahu sai su yi magana a nutse a kan Isma’il.
Yadikko kuwa ta na kai mata nata kunun da zagi ta bita, yayinda Kaka Nura ko
kallonta bai yi ba, ya tsani Matar sosai besides ba ya so Yadikko ta fahimci ya na nan.
Anne kam dama ba ta ko
ce mata ta gama ba, ta dai
bar mata nata a rufe.
….
Anne yau wuni ta yi a ɗaki, mirsisi kuma ko haɗa kayanta ba ta yi ba kamar yadda Yadikko ta ce, tana zaune abunta tana ta faman saƙa da warwara.
Tabbas sai ta saka Isma’il kuka wallahi dan yana daga cikin mutanen da su ka ɗaga mata hankali a yau su ka hanata walwala…
Tana cikin wannan lissafin, kamar
daga sama kawai ta soma jiyo sallamar Mama (Mahaifiyar Isma’il).
Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING*
Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING*
Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139*
Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudinku tested and trusted.
Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu....
location:Kano
Delivery:NationWide.
kar ku bari a baku labari, sai kun zo🙏
SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA
BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:25 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*
*page 33*
“To ka dai ji abunda Uwarka ta ce!
Dan haka ba yawo na tafi ba, idan kuma ka nace akan cewa yawon ne to ka ga da ni da ita ne mu ke da shirin zuwa, Allah bai yi itan ta samu zuwa ba a sabili da nannauyan baccin da ya kwasheta ba gaira ba dalili.”
Cewar Anne, ta ƙarashe maganar tata ta na wata dariyar rainin hankali ƙasa-ƙasa.
“Tabbas”
Yadikko ta ce cikin ƙoƙarin ganin ta yi supporting Anne duk rintsi.
Tunda Anne ta soma magana Baba ya runtse idanusa.
Ya lura so take ta wulaƙantashi ga Yadikko ta ƙi komawa ɗaki, dan haka