Showing 72001 words to 75000 words out of 100561 words

Chapter 25 - BAKAR TUKUNYA hausa novel

07 Feb 2026

473

numfashinsa ƙanwarsa ta ce “Wallahi Yaya da gaske ne! Yayansu Asiya ne ya ganta fa”

A ɗan fusace ya waiga ya na kallon ƙanwartasa, kafin ya ce “wato ke ce ki ka kawo munafurcin kenan, ko?”

“Hmm” kawai Mahaifiyar tasu ta ce sannan ta ɗaura da cewa “a kan ta faɗi gaskiya shine za ka kirata da munafuka a gaban idanuna?”

Runtse idanunsa ya yi da masifar ƙarfi sannan ya sauƙe ajiyar zuciya kafin ya ɗaura da cewa “ba haka bane ba Mama, a ganina in ta ji irin haka ni ya kamata ta fara samu zan san abunda zan yi kuma zan yi bincike in yiwa tufkar hanci ba wai ta zo kai tsaye ta gaya miki ba…”

“Saboda ba ka ƙaunar ka ji laifin Afra ko? Saboda in ta gaya mini zan iya cewa a jira ko a yi bincike sosai kai kuma soyayya ta rufe maka idanu ba ka son duk wani abunda zai saka comma ko fullstop a maganar aurenku ko?
Isma’il are you even listening to your self kuwa? Straight up fa gaskiya ce ba ka so da kuma laifin Afra. Sannan har yaushe ne ka fara ɓoye mini abu da za ka ce kar a gaya mini a fara gaya maka tukunna…”
Mama ta jero maganganun ranta ya na sosuwa.
Sai kuma ta ɗan yi shiruu kafin kawai ta ce “ina yi maka addu’a sosai! Sannan kaima ka dage da addu’a, in har auren nan ba alkhairi bane ba, Ubangiji ya yi ikonsa ta ko wanne angle.”
A hankali ƙanwarsa ta ce “Ameen”
Amma da ikon Allah Isma’il sai ya gagara cewa ‘Ameen’ ɗin ya na mai jin kamar ya rufe ƙanwartasa da duka! Tabbas ya san Samuel ya na son Afra amma zai iya dafa Alqurani akan cewa ƙarya ake yi mata ba ta bishi hotel ba wallahi, ko meye Afra in za ta yi sai ta gaya masa, besides ya ma san ba za ta taɓa aikata wannan ɗanyen aikin ba! Inaa ba zai yiu ba ƙarya ne….

“Yaya ka dage da addu’a dan Allah, ba wai farin cikinka ne ba na so ba, ba na son ka ɗauko mana jidali cikin family azo ta zame maka da mu kanmu masifa shiyasa na gayawa Mama saboda a tsananta bincike a kanta sannan a ɗan dakata kar a yi sauri….”
Dukan da ya kai mata ne ya sanya ta yin shiru ta shiga neman wajen ɓuya dan haka maganar tata ta tsaya chak!!!

Cikin faɗa sosai kamar ba Isma’il ba dan bai iya faɗa ba sam ba halinsa bane ba amma haka yau ya rufeta da faɗa a gaban Mama har da cewa ‘ko a ya Afra ta ke zai aureta a hakan’
Sai kuma da ya gama hayaniyar sai kunyar Mama ta lulluɓeshi dan haka ya yi shiru kawai.

“Shikenan, tashi ka tafi, ko kuma y not in Allah ya kaimu gobe ka tambaya ka ji ta bakinta, ko?”
Mama ta ce da shi kawai ba tare da ta kalleshi ba.

A hankali ya lumshe idanunsa kafin ya buɗesu kawai ya ce mata “tam Mam in sha Allah, sai da safe”
Daga haka ya miƙe ya fita ransa a masifar ɓace, ta ya ma Mama za ta yi mishi haka gashi ba zai iya yi mata musu ba, yanzu fisabilillahi ta ya zai fara tunkarar Afra da wannan maganar, gani za ta yi kamar bai ma yarda da ita ba, zarginta ma ya ke yi….

Da wannan tunanin ya isa ɗakinsa ya watsa ruwa ya kwanta sai dai kuma kafin safiya shaiɗan ya yi nasarar dasa masa wani abu a rai dan a cikin daren ya kasa sukuni har sai da ya yanke shawarar tunkararta da zancen kamar yadda Mama ta buƙata.

Ya na fita Maama ta sauƙe numfashi.
She’s very certain about the fact that Afra ta je wajen Samuel dukda ba ta da tabbacin mai ya kaita amma a yanzu kam tana fata Allah ya sa abun bai wuce gaɓar da za a iya gyarawa ba, dan Isma’il ya tsoratata tabbas yanzun duba da yadda ya zuciya ya fusata daga an yi batun ɗaga aure dole za ta je ta ji baasi ita da kanta tunda a ganinta an riga an zama ɗaya yanzu kuma its obvious rabuwa da Afra barazana ce a rayuwar ɗan nata duba da abunda ya yiwa ƙanwarsa a gabanta da yadda duk ya bi ya firgice tabbas yadda ta ɗauki Afra a wajensa ta fi hakan kuma ya bata tausayi matuƙa, dan haka za ta je da kanta ta yi musu magana gaskiya kar ta ƙara ko dan mutuncinsu tunda a ganinta za ta iya yiwa yarinyar faɗa ta ɗauka, dan a yadda ya fita ta san ba lalle ya ji abunda aka gaya masa ba, in ma wani abun ne ta taimaka ta daina zuwa ko dan munafurcin ƴan unguwa sannan ta fita a harkar wani Samuel…

Babu komai in sha Allahu za ta yi bincike ta yiwa tufkar hanci ta haƙura za ta rungumi Afran kamar yadda ta soma tun farko, in sha Allahu wannan ɗin ma za ta shanye a tafi a haka, ta amince ta karɓi wannan ƙaddarar fatanta Allah ya sa Yarinyar ba ta kauce hanya ba kuma abun bai yi tsamari ba dan in haka ne kuma ba za ta rufe ido ta jefa ɗanta ga halaka ba gaskiya.
………..
Direct wajen Adda Afra ta nufa, a nan su ka zauna, suna cikin hira kiran Ya Amir ya shigo wayar Adda, dan ita dai Afra wayarta dama da ita gara babu za a ce, kullum ta na ɗaki a ajjiye, ba ta wani damu da ita ba.

Ta na ɗauka su ka gaisa, cikin nutsuwar da kullum ta ke a tare da shi ya ce mata “ku zo, Baba ya na son ganin kowa”
Daga haka ya kashe wayar bayan ta ce “tam”


Amal da Afra sun so Adda ta je da su amma sai ta ce “su je kawai”
Saboda ta san in har da Anne a meeting ɗin to ko ta je ranta ne kawai zai zo ya na ɓaci, dan haka ta ce su je, ta ji ko ma menene daga baya.

Har kawo wannann lokacin Afra ta gagara gathering courage ta gaya musu cewa Anne ta san batun aurenta, dan ko tunawa ma ba ta so ta yi, shiyasa tun da aka ce Baba ya na nemansu gabanta ya soma faɗuwa duk da kuwa dama Ya Isma’il ya tabbatar mata zai nemeta amma fargabar abunda Anne ka iya yi duk sai ya dameta ya hanata sukuni har suka ƙarasa ɗakin Amal na ankare da yanyinta sam ba ta da walwala……

Su na shiga ciki su ka tarar da Baba, Ya Amir da Annen wadda ƙamshin dsigner turarukan da su ke fita a jikinta su ka karaɗe kusan gaba ɗaya gidan dan tun kafin su shigo ɗakin ƙamshinta ya ke yi musu sallama.

Ta na zaune akan tulin kayan wanki ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya ta na daddanna wayarta ta na wani irin taunar cingam na kwararrun ƴan duniya, yayinda Baba ya ke zaune a kan darduma Ya Amir ya ke a gefensa kanshi a ƙasa kawai ya gagara ɗagowa, tun ɗazu da ya ga an sauƙe Anne a mota shikenan zuciyarsa ta dunƙule har yanzun ta ƙi sakewa sam-sam.

Da sallama Afra da Amal su ka shigo a tare, Baba da Ya Amir su ka amsa musu, cikin nutsuwa su ka ƙaraso su ka zauna a ƙasa cike da ladabi su ka gaida kowa one by one….
Da kyar Anne ta yi jimla ta amsa musu, dan ba ta ma so ta sake ta saki fuskar da har Baba zai ga ƙofar kawo mata raini, ta san sarai dalilinsa na tarasu bai wuce ya yi mata magana a kan daren da ta yi ba sai ko maganar faɗanta da Abba da kuma wataƙila zancen auren Afra wanda duk ciki babu guda da za ta karɓa da sauƙi, ita kanta Afra yau kam sai dai ta gano cewar ba ta son auren amma ƙiri-ƙiri za ta nunawa kowa ta na buƙatar a tura auren chan da nisa sosai….

Ganin babu Adda ya sa Baba ya sake ɗaga waya da kanshi ya kirata amma ko da ta yi masa bayani sai ya zaɓi ya barta ɗin kawai ya cewa Amal ta gaya mata komai yadda aka yi in Allah ya kaimu gobe…
A hankali Yarinyar ta amsa da “to Baba”

Taɓe Baki Anne ta yi kawai ta kawar da kai gefe ta na lissafinta…

“Sallu Alan Nabiyil Karim…”
Muryar Baba ta katsewa Anne tunanin da ta ke yi…

Cikin nutsuwa Afra Amal da Ya Amir su ka ce “sallallahu alaihi wa sallam”
A tare sannan ya Amir ya yi Addu’a, su ka amsa da Ameen tukunna Baba ya gyara zama ya soma maganar abunda ya san zai fishshesa dan shi kam lamarin Anne tabbas ya yakice daga kansa in ta ga dama ta yi yawo tsirara ko dan su Amal ɗin ma da ya ke cewa yanzu kam kawai su yi haƙuri su rungumi ƙaddararsu, ba zai iya ba.
“Dama dalilin da ya sanya na tara ku anan akan batun maganar Auren Halima (Afra) ne da Isma’il, kamar yadda wasu a cikinmu a nan su ka su ka sani wasu kuma za su ji yanzu…an sanya ranar auren nasu ta inda aka bari a kan watanni biyu masu zuwa.
Wanda an saka ne a lokacin da shi Mahaifinsa ya yi tafiya zuwa egypt daga nan ya wuce Umara….
A wannan lokacin shi da kansa ya ce mana duk abunda mu ka yanke ni da ɗan uwansa ya ji ya gani to kuma da ya dawo yau ya na jin kwanakin ya nemi ganinmu…”
Shiruu ya yi kafin ya lumshe idanunsa ya buɗe sannan ya ce “duk ɗinmu mun san yawanci jama’a ba sa ƙaunar auren nan, sabili da ana gani kamar an cuci Isma’il ne duba da yadda tarihin Afra ya ke a Unguwar nan da kuma yadda Mahaifiyarta ta ke!
Kasancewarta Yarinya mai cikar kamala ba shi zai sanya a chanjawa tuwo suna ba duk ɗinmu mun san da haka, gutsiri tsoma da munafunce-munafunce su kan yi tasiri a kan kowa kuma ba a cika son yawan magana a kan abu ba!
A duniyar nan bayan ku inaga ba ni da waenda zan ce su ka fiye mini Isma’il da iyayensa dan sun so ni kuma su na kan so na a yadda na ke a lokacin da ya kamata a ce sun guje mini dan shi da kansa mahaifin na sa ya ce saboda gudun ce-ce-ku-ce ya na so kawai a ɗaura auren wani satin idan Allah ya kaimu(rana ita yau kenan!).”
Da wani kalar azababben sauri Anne ta ɗago ta kalleshi sai kuma ta mayar da kanta ƙasa kawai ta shiga tsinewa Malaman da ta wuni wajensu yau! Saboda babu kalar duba da buga ƙasar da ba su yi ba yau ɗinnan amma duk cikinsu aka rasa wanda ya hango mata batun matso da aure kwana kusa ballantana ta soma shiri tun ɗazun sai yanzu ne ta ke ji daga bakin Baba.

Muryarsa jin ya ci gaba da Magana ne ya katse mata tunaninta…
“Dan haka mun tsara a kan nan da sati ɗaya za a yi auren in sha Allahu, Afra za ta wuce Kaduna gidan Amaryar Mahaifinsa wadda ya aura ta rasu, ya ce akwai komai a ciki ba sai mun kaita da ko cokali ba, komai sabbi ne dan wasu ma ba a taɓa amfani da su ba sannan ya ce za ta zauna a chan tunda dama shima Isma’il ɗin a chan Kadunar ne ya samu aikin nasa, har batun gurbin karatu da za a nema mata a chan duk mun yi da su kuma za ta soma da zarar an ɗaura sun tare in sha Allahu….”
Cikin sauƙe ajiyar zuciya Baba ya ce “dan Allah duk wanda ya yi sallah ina neman alfarmar da ya dinga saka mini mutanen nan a cikin addu’a yana neman musu yardar Ubangiji, tunda aka haifoku cikin wannan zuri’a tawa a kullum tsorona waye zai aureku!
Amma da ya ke Ubangiji ne me komai gashi zan fara ganin auren Afra waenda mutanen nan su ka zamto silar komai na auren bayan doguwar ɗawainiya da mu da du ka dinga yi, kuma in sha Allahu yadda aka aminta da ita har ake kwaɗayi da son aurenta haka Aliya da Zainab(Amal) suma duk za su samu mazaje masu nagarta waenda za su karɓesu hannu bibbiyu ba tare da sun dubi halin mahaifiyarsu ba”
“Babana”
ya yi maganar referring to Ya Amir sannan ya ce “kai ma in sha Allahu za ka samu mata mai nagarta da kamala bi’izinillahi ta’ala…”
Murmushi Ya Amir ya yi sannan a hankali ya sunkuyar da kanshi ƙasa a ransa ya amsa da “Ameen”
A hankali Afra itama ta sake yin ƙasa da kanta, ta san ta na son Ya Isma’il kuma aurensa shine burinta amma haka nan a take sai ta ji fargaba da tsoro duk sun mamayeta sannan wae ba ma a Kano za ta zauna ba a Kaduna ne, tabbas ita kanta ta san za ta yi kewar danginta….

“Sallu Alan Nabiyyil Karim”
Baba ya sake cewa, a tare duk su ka ce “sallallahu Alaihiwasallam….”

Wani kalar tashin hankali da masifa Anne ta ke ciki, ga baƙin cikin batun aure ga shi ba a nemi yardarta ko ɗaya ba sannan ga bala’in takaici da mamakin yadda yau Baba ya gaggasa mata magana a gaban idanunta ba shayi….

Ganin ya na shirin miƙewa ya sanya rai a ɓace ta ce “Dakata Habu!”
Shiruuuu kowa ya yi, yayinda Baba ya runtse idanunsa kamar ba zai kulata ba sai kuma ya koma ya zauna da kyau ya na mai sauƙe ajiyar zuciya sannan ya ce “ki na da magana ne Anne?”

Da sauri Ya Amir ya miƙe zai fita dan ya san in ba a yi sa’a ba Anne sai ta saka shi kuka a maganganun da ya ke da tabbacin za ta gaggayawa Baba……

Cikin daka masa tsawa Anne ta ce
“Koma ka zauna!!!Munafuki! Ɗan iska kawai ai har da kai aka haɗa komai saboda kun maida ni banza ko?”
Sai kuma ta maida dubanta ga Baba sannan ta ce “yanzu kai ba ka ji kunyar yadda ka saka ranar ƴar da na haifa a cikina ba sannan ka ɓoye mini kuma har ka ke da tsaurin idon wani ce mini ka san wasu a cikinku sun sani wasu kuma basu sani ba, sannan kai har ka isa ka saka ranar ƴata cikin sati ɗaya tak!! Sannan ka gaya mini yanzu ba tare da neman shawarata ba, ƴar tawa ƴar tsana ce???”

Kamar Ya Amir ba zai ce komai ba sai kuma ya kalleta idanunsa jazir ya ce “Anne saboda munafurce-munafurce da Bakin mutane kar ya yiwa maganar auren illa shiyasa aka ce a ɗaura da wuri kawai tun kafin batun auren ya zagaya koina…”

“Akan me ake munafurce-munafurcen??”
Anne ta tambayeshi ta na huci!

“Wai shin ni kam na taɓa yin zina a bakin ƙofa ne ko kuwa na taɓa cin mutum sannan tsirara aka ga ina yawo! Da har shi Usman(Mahaifin Isma’il) ɗin dan *******uwarsa zai dinga magana ya na nunawa kamar alfarmar zai yiwa Afra shin bai ga ƴar tawa bane ba?!
Ai sai dai mu mu yi masa alfarma wallahi, ke tashi su ganki da kyau ki kwaɓe hijabin su ganki su san mu ne za mu yi musu alfarma…”
Ta faɗi hakan ta na kallon Afra sannan ta ɗaura da cewa “ku kuma da yake gaɓayene, wawaye shine ku ka biye masa aka tafi a haka…”
Cikin daka mata tsawa Baba ya ce “Nuratu!”
Kafin ya rufe Bakinsa itama ta ce “Na’am Abbakar!!”
Da gudu Amal ta tashi ta fice ta na kuka sosai ta faɗa ɗakinsu dan ba za ta iya zama ta juri kallon faɗan iyayen nata har haka ba.

Tsaki kawai Anne ta yi bayan ta gama hararar inda Amal ɗin ta bi ta fice sannan ta waigo zuwa ga Baba ta ce “abu uku na ke so ka saka a ranka, na farko yadda ku ka tsara nima dole a bi nawa tsarin kuma ba zan aurar da ƴata kamar wata ƴar tsana ba wallahi, dole in yi taro dole in yi biki dole in yiwa ƴata kayan ɗaki in ya so along the way duk wanda zai saka Baki ko ya yi munafurci shi ya sani in ka ga Isma’il bai auri Afra ba tabbas ba Matarsa bace ba dama tun farko, abu na biyu kuma ko dan yadda ku ke kallona Allah sai an ja bikin nan saboda in nuna muku cewa baƙin fentin da ku ka yi mini bai hau ba, sannan abu na uku kar ka ƙara zama a gaban idanuna da ƴaƴana ka na ci mini fuska kamar ka samu mayya har ka na cewa wani wai saboda ni za a fasa aure Uban baban duk wanda ya bari aka yi dan Allah….”
Ta ƙarashe maganar ta na huci sosai, ranta na susa, wato Kaduna ma za a ɗauki ƴar tata a kai ta yadda kafin ta bata wani abun alkhairin ma sai an jima, yo ko da ace isma’il ɗin ya zamto choice ɗinta ace kuɗinsa ya yi kuɗin da za ta iya bashi Afra sam bai isa ya ɗauketa ya yi nesa da ita ba, ba ta haifi ƴaƴanta domin haka ba…


Shiruu Baba ya yi tun fitar Amal dan sai ya ji bai kyauta ba ya gama yiwa kanshi alƙawarin ba zai dinga biye mata ba, musamman ma in a gaban ƴaƴansu ne….

Da kyar da mugun kyar ya samu ya iya cewa “Afra ke da Amal ku gayawa Adda yadda mu ka yi da ku a nan.
In akwai wasu shirye-shiryen da za ku yi sai ku yi mini magaana…..”
Daga haka ya miƙe ya fice da sauri Ya Amir shima ya bi bayansa…
“Tashin balagar tsintsaye ma kena!!!!
Idan ita Addar ko Uwarta wani cikinsu ya haifa mini ƴar sai in ga hannunsu a cikin auren da ban aminta da date ɗinsa ba dan Uban Mutum”
Anne ta faɗi hakan ta na mai ji kamar ta zunduma Uban ihu dan baƙin takaici, shi dai Baba bai biyeta ba haka shima Ya Amir su ka saka kai su ka fice daga cikin gidan ma gabaɗaya dan sai ta yi barci tukunna za su iya shigowa yau kam, ko a inda su ka san za ta gansu ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login