Showing 6001 words to 9000 words out of 100561 words
arzik’in yayan bai samu ba ta ce masa “Amir ba ni takardata nima na gaji….”
Ta yi maganar cikin mik’o masa hannu…
A hankali murya ta na karkarwa ya ce “Sajida ki jira za mu yi magana a ciki, ko?”
Ya k’arashe maganar a hankali…
Yana mai satar kallon Anne wadda tunda Sajida ta yi
mata shagub’e yanzun ta kid’ima sannan ranta ya k’arasa b’aci…
Sam! Har yau har gobe Ya Amir d’in shi kam ya kasa gane mentality d’in Anne na son kud’i, talauchi fa ba abun kyama bane ba..da wani mai kud’in ma gara talaka fa, ya fi shi kwanciyar hankali…
Har ga Allah he love his life a yadda ta ke, amma k’iri-k’iri Anne ta rabasa da matar da ya ke so ta manna masa Sajida k’arfi da yaji saboda lame dalilinta na kwad’ayi da buri wanda shi kam ya gagara sakashi a mizanin dalilai masu ma’ana…
Ya na wannan lissafin ya ji Sajidar ta haiyyayyak’o za ta yi magana Anne ta rigata ta hanyar cewa “wai dan uwar ubanka ba za ka sake ta ba? Y’ar gwal ce?
Sake ta a take a yanzu ko in tsine maka albarka wallahi…ka ji dae na rantse…”
Shiruu Baba ya yi ya runtse idanuwansa
kafin kawai su wuce ciki shi da Adda d’auke da Yadikko…
Suna jiyo ta tanata ife-ife ta na zagin karankatakaf danginsu ta na ik’irarin tsinuwa a Ya Amir d’in itama Sajida ba ta yi shiru ba sun saka shi a tsakiya….
Adda ta so fita amma Baba ya hanata saboda a halin yanzu ana tab’a Anne za ta huce haushinta a kansu ko ta fad’i abunda hankalima ba zai iya d’auka ba, shiyasa ya hanata fita yana mai jin zafin abunda ake yiwa d’an nasa fiye da shi Ya Amir d’in..
Tun lokacin da aka kinkimi Yadikko ta farfad’o, saboda dama ba suma ta yi ba mayen abubuwan da ta narkawa kanta ne basu gama sakinta ba shiyasanya ta yi likimo ta gagara motsawa
Dan haka suna kwantar da ita ta samu ta bud’e idanunta bakinta d’auke da salati…
Da yake d’akin akwai d’an duhu ya sanya ba su lura da Kaka Nura a farkon shigowarsu ba sai da suka zo kwantar da ita a kan gado tukunna suka lura da shi wanda hakan ya d’an basu tsoro dan daga shi sai boxer sannan yanata lullub’awa side drawer wani uban jibgegen bargo…..kana ganinsa ka san ba a dai dai yake ba sannan yana cikin tashin hankali.
K’uraa masa ido su ka yi sosai bayan sun tabbata Yadikko ta farka sai dai ba su yi wani motsin ba da zai sanya ta fahimci wani abun duk su ukun dan kowa akwai abunda ya ke rayawa a kansa, kawai sun kura masa idone shi da bargon da yake ta faman kaffa-kaffa da shi….
A take gaban Adda ya yanke ya fad’i sai kuma ta nufesu! Tana zuwa ta yaye bargon gaba d’aya!
Da sauri ta ja baya ta saka hannu ta toshe bakinta ta fashe da wani kalar kuka tana mai runtse idanuwanta da masifar k’arfi sakamokon Talatu mai k’osai da ta baiyyana a idanunsu bayan ta yaye bargon zigidir da ita!
Ko ta Ina ya iya shigowa da ita sai Allah!
Kaico Allah wadaran naka ya lalace…
Adda ta aiyyana hakan a cikin ranta wani masifaffen Abu mai d’aci da zafi yana tokare mata k’irji.
BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*
HUMAIRAH BULAMA
Yota
*03*
Cikin wata zazzafar zuciya Baba wanda bai tab’a sanin yana da kalarta ba ya yi wata super ya damk’i wuyan Kaka Nura tun k’arfinsa…so ya ke kawai ya kashe tsohon saboda dama yana ta tunanin yadda zai Mutu ya barsa da Mahaifiyarsa da wannan halin nasa! Adda mace ce ita ma rauni ne da ita ba zai bar mata
case d’in Kaka Nura a hannunta ba ya san ba iyawa za ta yi ba.
A rikice Adda ta k’arasa wajen ta fara k’ok’arin b’amb’are hannun Baba yayinda Talatu ta ke ta k’ok’arin ganin ta mayar da suturarta jikinta…
Babu damar yin ihu dan duk wanda su ka yi ihu ko magana da k’arfi ya ji to sai ya shigo
Ita kuwa Adda ko hauka ta ke ba ta bari a shigo a ga wannan gagarumin abun kunyar ba shiyasa k’asa-k’asa ta ke cewa Baba “Za fa ka kashe sa, ka taimaka ka cika shi dan Allah.
Cika shi kar ka yi b’arna.”
Ba tare da ta bari hatta Yadikko wadda su ke a d’akin tare da ita ta na ta faman cewa “kuna Ina ne?”
ta jiyo su ba.
Kaka Nura shima wanda duk idanunsa su ka firfito waje yau kam babu fad’a da duk wannan bala’i da haukar tasa
Dan tashi d’aya ya fahinci Baban yau ransa ya ke nema bagatatan dan haka da mugun kyar ya ce
“Ka yi mini rai dan Allah”
Wani irin kuka ne ya kufcewa Baba cikin kukan ya shiga cewa “in na cika ka direct ka fice
Ka saka jallabiya ka fice
kar in sake ganinka dan wallahi in na ganka idona idonka sai na kasheka!
Ka dai san mutuwa zan yi ko? Dan haka ba na jin tsoro a kamani da laifin kisa ko kad’an, gara in kasheka in Mutu hankalina a kwance akan in Mutu Ina tunanin halin da zan tafi in bar Mahaifiyata a ciki dan haka in har ka bari mu ka had’u sai na kasheka”
Ya fad’i hakan cikin d’acin zuciya wanda har k’asan ransa da gaske ya ke, ya tafi kawai in ya ga dama ya shiga duniya..kuma ko Yadikko ta tambaya Ina Kaka Nuran zai ce mata kawai shima ba su san inda ya ke ba. Sai dai in ya mutu ya dawo gidan wallahi.
Yana wannan lissafin ya na kuka wiwi sai dai a hankali sosai
Takaici goma da ashirin duk sun had’e masa…..
Tabbas zai fita yanzu
amma fa domin ya tsira ne kuma sai ya tabbata ya saka Baba kuka da tashin hankali kafin ya bar duniyar da yake ta faman ik’irari, in sha Allahu…
Saboda wannan cin mutunci da rainin da ya yi masa!
Wai yau har shi ake treatning ake cewa za a kashe! Tab ashe kuwa an ja ruwa..
Kawai dan ya san Baban zai iya aikata abunda ya ce ne shiyasa ya zab’i ya llallab’ashi ya barsa kafin ya sake waigowa kansa……
Kaka Nura ya aiyyana hakan a cikin ransa.
Sai da Baba ya ji Kaka Nura ya ce masa “Wallahi zan tafi…ka na cika ni zan tafi”
Tukunna ya cika shi ya na wani irin kuka!
Har ga Allah ya san babu kyau dai amma ya yi farin ciki matuk’a da abunda ya same shi!
Tunda ya auri Anne wallahi wallahi haihuwar da ake yi masa ce kawai ta ke sanya shi farin ciki amma kullum cikin bak’in ciki da tashin hankali ya ke!
Bai tab’a samun kwanciyar hankali da farin ciki daga gareta ba yanzu gashi ta d’aid’aita musu rayuwa daga shi har y’ayansa. Ji ya ke dama kamar ya gudu wallahi..bak’in cikinsa d’aya bai san wanne hali y’ay’an nasa za su shiga ba in ba ya nan amma tabbas gara ya tafin dan bak’in cikin ‘ga shi a raye tare da su amma ya gagara gyara rayuwarsu’ dama ya dad’e ya na nuk’urk’usar zuciya da walwalarsa…
Komai babu dad’i komai ya d’au zafi ta koina babu sauk’i sannan the worst part is that babu abunda ya Isa ya yi domin ya kawo sauk’i ko ya gyara hakan ko ya dakatar da abubuwa daga k’arasa tab’arb’arewa.
‘He is just so very useless’
Ya aiyyana hakan a ransa yana mai zama a k’asa dab’ass sannan ya sake sakin wani sabon kukan mai cin rai da k’una marar sauti….
Dan bala’i Ashe Kaka Nura shi da daduronsa ta window su ka shigo, dan haka su ka fice ta windown su ka mayar da burglar d’in wadda ashe ya dad’e da b’intiketa a jogane kawai ta ke sabida shigowa da mata…’tsabar idanunsa sun rufe shi kam bai ma damu b’arawo ya shigo musu ba…dan windown d’akin ya fita ta wani dogon lungu a unguwar ne wanda ba a ma binsa sosai saboda tsayi da duhunsa in dare ya yi…..
Tsoho da shi amma har yau bai bar bin mata na masifa ba!
Dukda cewa itama Yadikkon she’s not perfect amma tabbas ba ta chanchanci Miji kalar Kaka Nura ba sam! Halaiyyarsa sak irinta y’arsa
babu wani Abu mai kyau a tattare da su…’
Adda ta na wannan lissafin ta k’arasa kusa da d’an uwanta ta zauna kawai sannan ta saka hannu ta kamo na Yadikko wadda ta ke ta faman kiran sunayensu tun d’azu….
A chan waje kuwa..
Sai da Anne ta zabgawa Ya Amir kyawawan maruka guda biyu tukunna da kyar muryarsa ta na karkarwa ya furta kalmar saki d’aya ga Sajidar…
Sai a sannan tukunna Baba ya mik’e ya fito ko kallonsu bai yi ba ya bi bayan Ya Amir wanda ya fita da sauri, Adda kuwa a D’aki ta zauna ta na mai ci gaba da sauraren Anne ta na cewa Sajida “Alhamdulillah mun rabu da marar wadatacciyar zuciya, mai matsiyaciyar zuciya! Allah ya yaye mana alak’ak’ai…”
Cikin d’aga murya Sajida ta ce “Ae tsiya a gindinku ta k’are wallahi…matsiyatan banza masu jinin zina..Allah na tuba zani nawa na baki? Kuncen kayan Mahaifiyata nawa aka baki?
Ba ki da shi da dalilin samu, amma kin bi kin kwallafa rai akan y’ay’an da ki ka Haifa za su zamo silar samunki, kina jira su kula da dukkan buk’atunki na kud’i! Za ki sha mamaki wallahi wannan mutuwar zuciyar taki ita za ta janyo ki wahala ki k’are a cikin talauchi..
Ni Allah ya sa ma ba ki yi mana asiri a jikin kayayyakin da muka baki ba, Muguwa matsafiya kawai...A haka ne wae har ki ke da bakin cewa ba ni da amfani! Ae kuwa kafin in tafi sai kin fito mini da duk wani abun da na tab’a baki…”
Jikin Anne ya d’an yi sanyi a wannan gab’ar amma sai ta ce “Tsummokara ae ba wata tsiya bace! Kin bi kin ishi mutane ke y’ar masu kud’i shin Ina arzik’in ya ke? Ina gatan naki yake? Ae tunda ubanki ya bari aka kawoki nan wallahi an gama da ke..
Ba ki da wani gata y’ar nan….”
Tafi Sajida ta yi tae shewa sannan ta ce “Auhoo da so kika yi wato a bani gida? A yi muku ciki sannan a yi muku goyo…to bari ki ji Mahaifina ba dak’ik’i bane ba kamar ki…dabba mahaukaciya kamar ki ba ta isa ta damfareshi ta yi masa wayo ba wallahi k’aryanki!
Ni kaina ae da ke da Amir d’in kun san hanyar da ku ka bi na saurareshi, har na yarda na so shi na aureshi in ba haka ba wallahi ko a mai gadi ba zan d’aukeki ko shi ba
kuma gata an yi mini shi tunda har mutum kamar Mahaifina ya bi abunda nake so ya yarda ya kawo ni nan ae kuwa kema kin san Ina da gata wallahi ana son farin cikina…
Kawai dae wayo ne jahila irinki ba ta isa ta yi mana ba….”
Kasa ci gaba da danne zuciyarta Anne ta yi a take ta zabgawa Sajida Mari….
Wanda hakan ya kusan d’auke numfashi Adda wadda ta fito da niyyar yin rabiya.
Ficewa Matan da su ke d’aukar rahota su ka yi, dan kar ta shafesu yayinda Adda
ta k’araso inda su ke da sauri cikin karkarwar jiki ta na cewa
“Anne kanki k’alau kuwa? Me ki
ka aikata….”
Sai a lokacin Sajida wadda ta dafe kuncinta ta motsa..
Ta juya ta afka d’akinta jim kad’an ta fito rik’e da wayarta da mayafinta a hannunta da makullin motarta…
Ta na fita ta d’auki mota a gidan makwaftansu inda ta ke fakin ta bar unguwar zuciya na cinta….
Ko gama hawa Titi ba ta yi ba ta kira Abbanta wanda ya kasance baban mutum sosai a Nigeria, mai fad’a a ji..har khaki garesa sannan ana shakkarsa..ta na kuka ta ce masa ‘Anne da Ya Amir sun yi mata duka har sun kumbura mata fuska’
Dan da gaske fuskanta ya kumbura ta wajen kumatunta ya yi wani kalar jaa da alamun bruises kacha-kacha da shatin yatsu guda hud’u rass! Sun baiyyana duk a ta sanadiyyar marin da Annen ta yi mata na hauka…sakamokon ita Sajidar tunda ta ke a rayuwarta ko mintsini na gaske ba a tab’a yi mata mai zafi ba sai dai a wasa ko tsokana.
Tunda ta fita su ka yi shiruu hatta Anne ta gagara motsi kwata-kwata…
Yadikko kuwa tunda Adda ta fita ta ja pillow
ta kwanta ta soma barcinta, dan yadda ta ji Sajida ta yasar da ita d’azun ta tsorata kwarai..shiyasa tunda ta ji an sake ta ta b’uya a d’aki gudun kar a huce a kanta. Dan in Sajidar ta rarumo wani abun kafin ta nemi hanya ta gudu an sauk’e mata.
Bayan kamar mintuna goma da fitar Sajida, Baba ya shigo ya kallesu ya ce “wani abun ya faru bayan wanda na sani?”
Dan su kansu mazan da su ke waje sun ga yanayin yadda Sajidar ta bar unguwar rai a b’ace ga fuska ta kumbura ta yi jaa, tabbas sun san ba lafiya ba…shiyasa yana dawowa daga kai Ya Amir gidan Abokinsa su ka ce ya shiga gida fa ya duba dan kamar ba k’alau ba…
BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*
HUMAIRAH BULAMA
Yota
*04*
Da kyar Adda ta iya ce masa “Anne ce ta mareta…”
Shiruuu ya yi kawai ya na kallon Anne kafin chaan ya ce mata “ku zo mu bar unguwar na d’an lokaci, yi wa Yadikko magana ta fito yanzu-yanzu….”
Ya yi maganar jikinsa har ya na karkarwa saboda Abban Sajida ba shi da sauk’i! Ya ji ya shaida hakan, masifar tsoronsa ake ji gashi fad’ansa ba ya mutuwa.
Kwata-kwata da fitar Sajida da zuwan anti daba har da Sojiji bai kai mintuna goma sha a tsakani ba.
Motocin suna dira,
tun daga wajen zaman makoki suka fara nad’e jama’a, duk
wanda ya yi yunk‘urin guduwa kuwa take sa su ke yi ko su buga masa bindiga a ka…
Dan Sajida ta na kuka ta sanarwa Abbanta Anne da d’anta sun taru sun yi mata duka har sun farfasa mata jiki sannan an yi mata saki d’aya…’
Shiyasa shi kuma ya fusata, a ganinsa saki kam
ba komai bane ba dama abunda ya ke fata kenan amma duka kam
tabbas wannan sai sun yi dana sanin had’a zuri’a da shi wallahi…
Shiyasa ya yi kiran waya ya ce ‘a kwashe masa kowa hatta tsuntsu in ya zo wucewa ta saman gidan a had’a da shi! A gark’ame masa su a waje mafi tsananin takura da wahala kafin ya waiwayesu ya ji ba’asin dalilinsu na tab’a masa y’a da su ka yi.
Sannan ko da wasa kar a bada belinsu kar ma a bari a gansu sai sun yi 48 Hours a uk’uba…’
Maza bakwai su ka yi nasarar cafkewa a wajen zaman makoki aka saka su a mota, a cikin Yaran da su ke kallo kuma guda biyu su ka tafi yiwa wani a cikin sojojin rakiya har inda Ya Amir ya ke, yayinda ragowar kuma su ka shige cikin gidan kan su tsaye..
D’an gidan Aliya yana rungume a k’irjinta ta na kuka tshohuwar da ta ke tare da ita tana ta faman lallab’ata a kan ta kawosa a yi masa sutura amma ta k’i kawai su ka ji k’arar jiniya…
Kallon kallo aka hau yi kafin ka ce kwabo su ka fara jin ihu da durufta sai kuma a ka afko musu cikin d’akin…
Salati y’ar tsohuwar ta saka yayinda Aliya ta yi shiruuu kawai hawaye su na ziraro mata.
Ta na kallo cikin tsantsar wulak’anci aka kame tshohuwar ta hanyar saka mata ankwa su ka yi waje da ita a wulak’ance sannan wata mata ta k’araso gabanta ta tsaya ta ce mata
“Tashi mu je ki rungume jaririn a jikinki ke ba sai an saka miki ankwar ba…”
Kamar ba za ta yi magana ba sai kuma cikin sheshshek’ar kuka ta ce “gawa ce”
Shiruu matar ta yi kafin ta ce mata “taso ke da shi mu tafi, doka ce ba zai yiu mu karya ba…”
A hankali Aliya ta d’ago jajaye kuma daradaran idanuwanta ta na kallon Matar cikin tsantsar b’acin rai ta ce “ba ki fahimci yaren da na yi miki bane ba?
Doka ta zo daga sama ae kwa jira mu cika umarnin mai saman gaba d’ayanta ko?”
Wani murd’add’en mutumi ne ya zo ya saita kanta da bindiga ya saita bindigar wanda hakan ya sanya har sai da ta zabura ta ce “hhch” cikin tsantsar tsinkewar zuciya sannan ta mayar da dubanta garesa…
Cikin sanyin murya matar ta ce mata “ki yi hak’uri ki taso mu je. Bai kamata a yi hakan ba kam, amma kafin a yi miki illa ki zo mu je in sha Allahu zan san abun yi….”
Wani kalar tuk’uk’in bak’in ciki da zafin tashin hankali, nadama mai had’e da da na sani ne suka sanya Aliyar ta gagara motsawa daga inda ta ke! Sai wasu zafafan hawaye da su ka shiga zubo mata tsanar Mijinta ‘Mai Nasara’ da Anne su na sake kanainayeta..kaico!..
Tsawar da mutumin ya daka mata ce ta sanya ta d’an dawo cikin haiyyacinta.
A hankali matar tausayinta ya na shigarta ta saka hannu ta karb’i gawar jaririn
Suna ganin haka kuwa mazan su biyu su ka matso aka saka mata ankwa itama aka yi waje da ita…ta na tafiya da kyar ga azabar haihuwa ga ta d’inkin da aka yi mata.
A cikin motar ta tarar da gaba d’ayansu har da Ya Abba wanda yana shigowa unguwar (dawowa daga kai yadin da aka auna tsayin gawar) yanzu-yanzun shima aka had’a da shi da Ya Amir wanda suka d’auko daga gidan Abokinsa.
Motoci biyu taff aka cika da