Showing 66001 words to 69000 words out of 100561 words
amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING*
Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING*
Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139*
Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudin ku tested and trusted.
Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu....
location:Kano
Delivery:NationWide.
kar ku bari a baku labari, sai kunzo🙏
SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA
BULAMA ✍️
0806 402 1951
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*
HUMAIRAH BULAMA
Yota011
*27*
Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING*
Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING*
Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139*
Daga haka Anne ta juya ta fita rai a ɓace dan ganin Amal ɗin da ta yi ya sake tuna mata asarar da ta janyo mata na kuɗaɗen da ta ke da tabbacin Mustaphan zai bayar in da ace ta tsaya ta saurareshi, sannan dan iskanci wai ta saka wani hijabi, ƙirar jikin Yarinyar kaɗai ta isa ta saka a kashe mata kuɗi daga kallonta ma kawai amma dan baƙin ciki sai ta yi ta faman ƙunshe-ƙunshe ta na barinsu a talauchi da wahala, kamar wata wadda za ta jiƙa jikin nata ne ta shanye.
………..
Kasa fitowa Adda ta yi bayan
Fitar Anne dan wani kalar kunya da tausayin Amal ta ke ji har cikin ɓargonta, bata jin za ta iya haɗa ido da ita bayan ta gagara bata ko wacce iriyar kariya ko da ƴar ƙanƙanuwa ce, sai da ta ji Yarinyar ta na jan numfashi da kyar tukunna ta buɗe ƙofar ɗakin ta fito ta ƙarasa gareta, ta na ɗagota Amal ɗin ta fashe da kuka cikin kukan ta ke cewa “Anne za ta kaimu wuta! Da ni da ke da su Baba da kowa duk za ta halakamu, dan Allah Adda ki zo mu gudu ba na son zaman gidan nan, ji na ke yi kamar zan mutu in ina ciki, ba na son ganin Anne…
Har yanzu fa Ya Afra itama ba ta dawo ba…”
Shiruuu kawai Adda ta yi ta gagara cewa komai zuciyarta ta na wani irin hantsilawa…ba ma ta san ta ina za ta fara ba sannan ga Abba shima wanda Amal ɗin ta gaya mata abinda Annen ta yi masa wanda a yanzun ta ke da tabbacin ya na chan ya na fama da ƙunci da zafin zuciya.
••••••••
Tsaye ta ke a gaban gas cooker, ta na juya liver sauce ɗin da ta kammala haɗawa yanzunnan.
Ta na girkin ta na murmushi wanda hakan zai tabbatar maka da tsantsar farin cikin da ya ke danƙare a cikin zuciyarta, “tabbas na fi kowacce Mace yin sa’ar Mijin Aure”
Ta aiyyana hakan a cikin ranta murmushinta ya na daɗa faɗaɗa….
Ba ta ji shigowarsa ba sai dai ta ji an rungumeta ta baya sannan ana sake shigewa cikin jikinta sosai kamar mai shirin haɗesu waje ɗaya su zamto abu guda!
Har sai da ta ɗan ce “auchh”
Tukunna ya ɗan sassauta ruƙon da ya yi mata, dai-dai saitin kunnenta ya ce “kwatankwacin yadda zallar zazzafar ƙaunarki ta ke nuƙurƙusar zuciyata kenan”
Ya yi maganar cikin kamo earlobe ɗinta ya haɗe da mannen earing ɗin da ke a jiki duk ya sakasu cikin bakinsa ya ɗan tsotsa kaɗan sannan ya fitar kafin ya sakar mata light kiss a kunne da kuma kumatunta sannan a hankali ya ce “i love you Matata”
••••••••
Tunda Anne ta koma ɗakinsu ta ke ta faman lallaɓa Hajiya Altine ta waya, dan yadda Matar ta ga ran shalelen Yaron nata ya na sake ɓaci ya sanya itama ta sake hawa fiye da farko.
Da mugun kyar aka samu su ka daidaita ta inda Mustaphan zai yi tafiya zuwa Europe na sati biyu amma da zarar ya dawo Amal ɗin za ta je ta sameshi su zanta su fahimci juna…
Dai-dai ta na ajjiye wayar Afra ta na shigowa cikin ɗakin bakinta ɗauke da sallama.
Da sauri Anne ta sake gyara zaman wayar sannan ta miƙe ta na kallonta…
Rigar jikinta irin doguwar rigar nan ce (Abaya) Mai igiya a tsakiya wadda kafin ta fita sai da Annen ta sakata ta ɗaure tsakiyar sosai tukunna sai dai kuma yanzun ta nemi igiyar ta rasa wanda hakan ya ke bata tabbacin Afran warewa ta yi ta ɓoye igiyar bayan ta fita daga gidan kenan!!
If not because ta na ɗan shakkar Afra sannan ta na son ta bata abunda ta zo mata da shi tabbas da sai ta tsinkawa Yarinyar Mari wallahi….
“Ina wuni Anne”
Siririyar Muryar Yarinyar ta katse mata lissafin da ta ke yi..
Sai da ta sauƙe ajiyar zuciya sannan ta rarrashi kanta tukunna da kyar ta iya ce mata “lafiya ƙalau Alhamdulillah”
Sai kuma ta kasa haƙura dan haka ta ce “ina igiyar rigar? Na ganki kamar wata Matar Mallan…kin saki riga ba fasali”
Ba tare da ɓoye-ɓoye ba kanta tsaye Afra ta ce “Ina fita waje na cire na sakata a aljihu, ba na so in yi miki musu ne mu yi ta hayaniya da ke shiyasa na biye miki ɗazun na bar gidan a haka, da kuma na ga babu idonki sai na bi dokar Ubangijina.”
Da mugun kyar Anne ta iya haɗiye wani malolon baƙin ciki da ya taso mata ya tokare mata maƙoshi sannan ta yi da gaske wajen danne fushinta a hankali ta ce “to ae shikenan”
Cikin nutsuwa Afra ta yaye Abayar jikinta ta saƙale a jikinn ƙusa sannan ta cire mayafin shima ta rataye ya rage daga ita sai riga da dogon wando tukunna ta kalli Annen ta ce “rigima kika yi a ƙofar gida ne yau ma? Na zo wucewa na ji Mallan iliya yana bada labarin yadda ki ka cukumi wuyar rigar wani har kin yaga..”
Sam ba wannan ne a gabn Anne ba, so ta ke yi ta ji dumuss kawai a hannunta amma sai ta daure ta ƙarawa kanta patience sannan ta ce “ni da wanchan shegen Yaron ne! Abba, take takensa Amal yake so kuma dan ****Ubansa bai isa ba wallahi. Ita kuma gaɓuwa ta barshi ya na shige mata shege talakan banza, zai jaza mata ba za a dinga kulata ba in ana ganinsu tare!
Shege mugu…”
Yadda ta ga Afran ta kafeta ta idanuwa ne ya sanya ta gagara ci gaba da cewa komai…
A hankaki Afra ta na mai ware abun hannunta ba tare da ta kalli Annen ba ta ce mata “amma kin san da Ubansa dai ko? Ki daina shegantashi babu kyau sannan in maganar kuɗi ake yi kuma na san kin san waye uban nasa…”
Cikin tarar numfashinta Anne ta ce “a banza ae wai ƙunshi a ɗuwawa! Mu gani a ƙasa in ya so sai
mu shaida…Uban da ya tsane shi ya tsani sunansa ne zai yi tinƙaho da shi?”
Ta ƙarashe maganar tata da tambaya da masifar ƙarfi, wanda ta yi hakn ne da gangan.
Wani zazzafan numfashi Afra ta sauƙe sannan ta ɗauke kanta daga dubanta ta mayar kan aljihun wandonta ta fara lalube kafin ta zaro kuɗaɗen da gaba ɗayansu ba za su wuce dubu ashirin ba…
Anne ba ta san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba, a ranta ta ce “Alhamdulillah”
Afra na ɗagowa Anne ta yi saurin kawar da dubanta irin bata gani ba ɗinnan, ƙasa-ƙasa ta na mai ci gaba da cewa “ae sai na nunawa Abba iyakarsa wallahi, hmm zai gane bashi da wayo shan ruwansa ma ya kusan ƙarewa a cikin gidan nan tabbas….”
“Hmm”
Kawai Afra ta ce, tukunna ta matsa ta kamo Hannunta na dama sannan ta saka mata kuɗin a ciki.
Da sauri Anne ta waigo sannan ta ce “laaa, kunga abun arziƙi”
Ta na mai washe Baki.
Cikin tsantsar damuwa da rashin jin daɗi Afra ta tari numfashinta ta hanyar cewa “Anne yau a hotel muka haɗu da Samuel dan ina fita bayan na kirashi cewa ya yi sai dai in je chan in karɓa! Anne dan Allah dan Annabi ki rufa mini asiri ki yanke duk wani abu da ki ke shirin ƙullawa tsakanina da Samuel kwata-kwata ba na son shi sannan ba na son alaƙata da shi ko da kuwa mutuncin ce…A harabar Hotel ɗin mu ka zauna amma ba ki ji yadda duk na muzanta ba.
Za mu samu kuɗin abunda ya ke damunki Anne in sha Allah amma dan Allah ki daina yi mini kuka kina tunzurani zuwa inda raina ba ya so.”
Shiruu Anne ta yi ta na mai sauƙe numfashi kafin ta ce “Afra Likita cewa ya yi in ban sayi alluran nan an yi mini ba tsaf zan iya mutuwa ko kuma abun ya fi haka…
Ban san mai yasa ki ke gudun Samuel ba ƴar nan! Ya taɓa yi miki maganar iskanci ne? Sannan kalli abin arziƙi bawan Allah baya rabuwa da kyauta! Kuma wallahi ya ce mini aurenki ya ke son yi…
Ki kwantar da kanki Unguwar nan fa kusan duk gidajen nasa ne ae ko ba komai…..”
Afra ba ma ta san lokacin da ta katseta ba ta hanyar cewa “Anne ba dai krista ki ke so ki ce in aura ba dai ko? Sannan for your information yau Samuel a yadda ya dinga nuna min bashi da wani burin da ya wuce ya taɓa jikina…
Above all Anne kin dai san inada wanda na ke so wanda zan aura ko? An yi magaana an gama komai da fatan dai ba hankalinki ne ya soma karkata daga batun Ya Isma’il ba…”
Ta ƙarashe maganar cikin tsantsar ruɗani da tsoron da ya baiyyana ƙarara a kan fuskarta ta na kallon Annen sosai…
Rarraba ido Anne ta shiga yi across the room ba tare da ta ce mata komai ba…
A hankali Afra ta matso kusa da ita ta ɗan dafa ta still har yanzu yanayinta bai sauya ba ta ce “Anne…kar ki ce min ba kya son aurena da Ya Isma’il, dan Allah”
Da sauri Anne ta kalleta ganin ta na shirin fashewa da kuka ya sanya ta kamo fuskarta zuwa cikin tafukan hannayenta sannan ta ce “ko ɗaya! Kar ki damu kin ji ko! Bara in je a yi min allurar kar wani ya ga kuɗin nan a ce a kawo a yi cefane ko wani hidimar gida tunda dama Ubanki ya ce ƙaryar ciwon na ke yi, yanzu ina hanawa kin san baƙin jini zan ƙara…”
Da kyar Afra ta haɗiye abunda ya tokare mata maƙoshi sannan ta riƙe hannayen Anne waenda su ke riƙe da fuskarta kafin ta ce “good! Saboda in har muka butulcewa Ya Isma’il da iyayensa tabbas Ubangiji da kansa ba zai barmu ba! Haƙƙinsu sai ya tarwatsawa mu.”
“Na ji na ji, kar ki damu.
Ba za ma a yi haka ba”
Annen ta ce ta na mai zamewa daga Afran daga nan ta nufi ƙusar da Afra ta saƙale mayafinta yanzun ta zari mayafin abayar ta yafa akan matsetstsen ɗinkin doguwar rigar da ke a jikinta ta yi waje!
Da sauri Afra ta yunƙura za ta bita sai kuma ta fasa kawai dan ta san ba sauya mayafin za ta yi ba!
A hankali
Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta fito daga ɗakin ta nufi nasu ita da Aliya da Amal wanda ya ke nan ɗan mistitsi sosai shiyasa ko kayan sakawarsu ba sa iya ajjiyewa a ciki ga shi ɗakin da uban rima kamar a kirata ta amsa, shiyasa hatta zannuwan da su ke shimfiɗawa a kan katifarsu duk sun fara dagargajewa ta wasu wajajen dan wuyarta a jingina abu a jikin bango yanzunnan rima za ta yi masa lalata, Anne kuwa ta ce sai dai su haɗa kuɗi su yi plasta a bayan ɗakin da kansu ba zata bayar ba ae suma mata ne su fita su nemo, Baba, Ya Amir da Ya Abba kam ba yadda su ka iya ne ta abinci ake a gidan shiyasa ba su samu sun yi
musu ba.
Fitar Anne sai da ta kira Malamai biyar, saboda dama kuɗi take nema kwana biyu ta yi broke sosai shiyasa ta tsaya, ta san ko zata biyasu da jikinta dole ana buƙatar kuɗin siyan kayan aiki da abun sadaka…
Dan haka ta kama hanya da ɗamarar yakice Isma’il daga rayuwarsu da dukkanin ƙarfinta, amfaninsa ya riga ya ƙare musu, yanzu lokacine da Afra za ta yi rayuwarta sannan ta yi auren hutu ba wai lokacin da za a kinkimeta a bashi ita ya aure ba!
Dama makaranta da ɗawainiyarta ya sanya ta sake masa amma tabbas ko a mafarki ba ta taɓa fatan Ubangiji ya nuna mata auren Afra da Isma’il ba! Ko da aka yi tambaya da ragowar abubuwa duk su Baba ɓoye mata su ka yi amma tunda Allah ya sa ta ji daga bakin ita Afra tun wanchan satin shikenan ta ƙudiri aniyar nuna musu iyakarsu.
Sam Afra ba sa’ar auren Isma’il bace ba! Gashi
Yaron daga shi har Ubansa arziƙinsu sai faman ja da baya yake yi! Yo hauka ake…ba zai yiu ba wallahi…
Masu kuɗi na bugawa a jarida duk ƴayanta za su aura ba wai auren je ka na yi ka ba!….
•••••••••
Cike da ɓacin rai Mai Unguwa ya ce “wanne kalar ɓata tarbiyya ne wannan wae ake yi a Unguwar nan amma duk kun ƙi ku taɓuka aikin komai a kai?
Fisabilillahi ta ya za su dinga fitowa da sigari sannan suna yawo
kusan a tsirara amma
an gagara tsawatar musu!
Yanzu jiya jiyannan fa da wasu Yara a Unguwar nan su ka yi walima a bayan layin Gidana! Har da sigarin takarda na wasa suka rarraba suna gwada yadda ake yi!
Gaskiya na gaji! Dan haka kawai inaga zan tara Yara majiya ƙarfi su yi musu shegen duka! A koresu a Unguwar, ba zan iya ba…..”
A hankali Baba ya sunkuyar da kansa ƙasa ya ɗan runtse idanunsa sannan ya ɗago ya na mai kallonsa tukunna ya ce “akaramakallahu yanzu ya kake so mu yi? Mutanen nan su na da ɗaurin gindi a wajaje da yawa, kuma ko wata fa ba a yi ba da Allah ya taimakemu Hisba ta shigo muka kai ƙara wajensu aka zo aka yi musu yasa.
A gabanka fa hukuma su ka ce muddin ba maza su ke shigarwa ba cikin gidan to ba mu da hurumin ma mu sake kawo ƙararsu…
Ko ba haka aka yi ba?”
Ya yi maganar cikin juya akalar maganar tasa zuwa ga lawyer ɗinsu.
Gyaran murya lawyer ɗin ya yi
sannan ya ce “tabbas! Haka ne, tunda ba wani abun aka ga suna yi da ya yi zafi sosai ba, shan sigari da yawo kusan tsirara wannan duk yanayin yadda suka tsara za su yi rayuwarsu ne ba mu da hurumin zana musu yadda za su tafiyar da rayuwarsu in muka ce za mu yi hakan to mun taɓo rights ɗiinsu wanda in suka kai ƙara tsaf hukunci zai iya hawa kanmu…
Actually,
hatta hanasu shiga da maza ma da muka yi ba mu da wannan hurumin fa Akaramakallahu, kawai an yi duba da yanayin gargajiyarmu ne sannan Hisba sun shigar mana shine aka bamu gaskiya…
Yasar da muka yi musu ne kawai za a iya cewa mun yi dai-dai tunda a makaranta aka sassakasu Yaran da aka kwace kuma ka ga society ta na son a kula da future ɗin youth dama….
Unlike yanzun da kake son hana mutanen da na tabbata a cikinsu har da masu kusan 50yrs yin abunda su ke so…
Mu bi komai a hankali, yanzun ba za mu iya cin su da yaƙi ba sun riga sun yi mana ɗaurin sarƙa sannan hujjojinsu sun fi namu kuma ka ga sun ɓoye komai an kasa samunsu da laifin dumu-dumu, amma mun fi su gaskiya dan haka i can assure you that very soon za mu ci galaba a kansu za a bamu gaskiya a samu a rabu da su har abada…”
Cikin fushi da faɗa sosai Mai Unguwa ya ce “wae ba za a cire min dokar turawa a sako mini zallar ta musulunci bane ba?!!”
Ganin duk sun sunkuyar da kansu sun kasa cewa komai ya sanyashi ya kallesu sosai one by one sannan ya nuna Baba da hannunsa ya ce “ba na son mutanen nan a unguwata, ku san yadda za ku yi….”
Daga haka ya juya ya fice kamar mai shirin tashi sama….ya bar ɗakin da su ke taron a cikinsa.
••••••••
Ta jima a ɗakin zaune ta na ta faman tunane tunanenta kafin ta miƙe ta nufi ɗakin Adda jikinta har yanzu babu lakka! Sai da ya Amir da Baba su ka ce mata kar a gayawa Anne da Kaka Nura har ma da Yadikko cewa an saka ranarta da Isma’il, aka yi komai a sirrince dan Unguwar ma duk an ɓoye saboda gudun ce-ce-ku-ce amma ta gagara ɓoyewa Anne wanda sai yanzu ne ta fahimci tabbas Annen ce ma main dalilin da ya sanya ake ta cewa ‘a ɓoye, a ɓoye’ ɗin…
Da sallama ɗauke a Bakinta ta tura ƙofar ɗakin ta shiga ciki a hankali.
Da Amal ta fara tozali kwance sai dai bacci ta ke yi wanda hakan ya bata mamaki dan ba ta yi tunanin ba ta je Islamiyya ba yau ɗin gashi ita take saka ran za ta riƙe mata ɗayan ajinta tunda itanma yau ba ta je ba.
Kamar wadda aka taso ta cikin barcin haka Amal ta shiga buɗe idanunta waenda su ka rine sannan su ka ƙanƙance!
Da sauri Afra ta ƙarasa zuwa gareta ta zauna sai kuma ta waigo ta na kallon Adda kafin ta gaisheta ba ta jira ta amsa ba ta ɗaura da cewa “Mai ya sameta? Wai akan faɗan Anne da Ya Abba ne kaddai ya shafeta har haka? Me aka yi mata?”
Murmushin takaici kawai Adda ta saki kafin ta gyara zama suka ɗan