Showing 90001 words to 93000 words out of 100561 words
ya shirya kawo ƙarshen komai in ya so ayi uwar watsi! Tabbas gara hakan.
A hankali ya buɗe rinannu kuma gajiyayyun idanunsa ya ce “Nuratu halinki ya isheni, ba na jin zan iya ci gaba da haƙuri…”
Duk rashin tsoro, tsaurin ido da taurin zuciya irin na Anne, ba ta san lokacin da ta ɗago manyan idanunta ta zuba masa ba cike da shock, dan sam ba ta yi tunanin zai iya furta mata hakan ba.
“Matsowa kusa da shi Ya Amir ya yi sosai sannan a hankali ya ce “Baba ka yi haƙuri, Anne da auren ma ya aka ƙare ballanta babu, dan girman Allah ka yi haƙuri Baba ka rufa mana asiri”
“Hmm”
Kawai Ya Abba ya ce shi kuma ba tare da ya ce uffan ba.
Wani kalar kallo ta ɗago ta watsawa Ya Abban dama ga takaici da shock ɗin da Baba ya jefata a ciki, ba ta gama dawowa dai-dai ba Baba ya ce “dan haka ki je har sai na neme ki.”
“A’uzubillahi”
Yadikko ta ce, sannan ta matso inda ta ke jin saitin muryarsa ta ɗaga sandarta ta kai duka, sai dai ba ta sami kowa ba, dan bata saita dai-dai ba, this time around.
“Ki tattara ki bar mini gidana, kafin in dawo, kar in tarar da ko ɗankwalinki ne.”
Ya faɗi hakan yana mai jin wani sanyi ya na sauƙar masa kamar an zare masa ƙaya.
“Ka na da hankali kuwa Habu? Tun wuri ka janye wannan batu naka kafin in tsine maka albarka wallahi.
Babu inda za ta je!
Kuma kar ka fita ko ina ka tsaya har sai an gama magana wallahi.”
Cewar Yadikko wadda duk ta bi ta gigice, yo in aka kori Anne ae tata ta ƙare sai dai ta bita…
ita kanta ta san ta riga ta gama zama addicted a abubuwan da ta ke sha, dan haka take da tabbacin muddin ta daina to sai dai a kwashi buzunta.
“Gara da Allah ya buɗe
maka idanunka! Tabbas wannan Mata taka musiba ce! Yadda ka yunƙuro haka Allah ya baka ikon rabuwa da ita gaba ɗaya, Congratulations dan wannan abun a tayaka murna ne.”
Cewar wani mutumi maƙofcinsa, wanda ya faɗi hakan a iyaka gaskiyarsa, yana gama faɗin haka ya juya ya fita gudun kar Anne ta yi masa ashar ɗin da shi kuma zai halakata a wajen.
Ya Abba dai da Ya Amir ba su ce komai ba.
Haka itama Adda da Afra, kowa ya sunkuyar da kanshi ƙasa.
Yadikko ke ta hayagaga ta na iƙirarin za ta tsinewa Baba in bai fasa korar Anne daga gidan ba, gaba ɗaya ta gigice.
Wata tsohuwa ce ta matso kusa da Yadikko sannan ta ce mata “yanzu ke ƴar Uwa aka ce miki hakan ba abun alkhairi bane ba? Murna ya kamata fa ki yi Allah zai rabaku da ɓaragurbi. Kamata ya yi ki yi fatan ya sauwwaƙe mata gaba ɗaya in ta tafi kar ta dawo, Inace ke da kanki ba kya son auren nasu a da, shin mai ya faru ya sauyaki yanzun ne…”
Cikin tarar numfashinta Baba ya ce “ga ta nan! Ya yi maganar cikin nuna Anne sannan ya ce “duk ita ce ta tarwatsa min rayuwata da ta ƴaƴana amma yanzu komai ya ɗauko hanyar gyaruwa in sha Allahu.”
Sai kuma ya nuna ta sannan ya ce “na ce miki ki fita ki bar mini gidana ko?”
“Allah Sarki rayuwa”
Anne ta faɗa muryarta ta na karkarwa! Tsabar bala’in da ya ke cinta. Sannan ta ce “Ɗan adam butulu.
A lokacin da ka ɗirka mini ciki aka ce a rufawa juna asiri a yi auren ae shiru ka yi akayi auren, sai yanzu da kake fakewa da ayoyin Ubangiji wae kai nan Malami kuma Limami kowa ya yarda da kai, ka ke ci da addini shine za ka tozarta ni ka tona mini asiri ka wulaƙanta ni ko? To bari ka ji! Wallahi wallahi babu inda zan je!, ae Yadikko ma tana da gado a cikin gidan nan kuma Ubana ta ke aure dan haka zan zauna a ƙarƙashinsu ko saki na ka yi ba zan bar gidan nan ba, ba zan wulaƙanta ba wallahi.”
Ta faɗi hakan ta na jin zuciyarta na sacewa, ranta fess!! Dan tabbas ko haka ta barshi ta san an yi 1-1, shi kanshi ya Amir ɗin ae ba ƙaunarta ya ke yi ba, munafuki! A bayan Ubansa ya ke, dan haka ba ta damu ba in an fara yi masa kallon shege daga yau! Ta san in sha Allahu ko hauka su ke yi daga yau har gaban abada ba za su sake yi mata wani shirmen da tujara ba, za su dinga shakkarta gudun kar ta sake yi musu kalar wannan tujarar sannan gara kowa ya san cewa suma fa akwai kashi a gindinsu…kalli fa yadda ake yiwa Baba murnar somi-somin rabuwa da ita kamar wata guba!.
Wallahi ba inda za ta je kuma ko da ace sakinta ya yi ba za ta yarda ba sai ta koma ɗakinta! Kamar da ƙasa! Yo
Hauka ake…..ba za ta yi accepting defeat ba, ba a isa a koreta a bata hutu ko a sake ta ba, in ma rabuwar ce gara ita ta barshi ba dai shi ya barta ba, sannan inama za ta je in ya kore ta, kuma ko da ace ba ta bar gidan ba ta san in har ta yarda da wannan yajin to fa duk tsiya sai powerta ta ragu a cikin gidan, kar ma ya auro wata! Inaa ba zai yiu ba.
A hankali Ya Amir ya zame ya bar wajen ya nufi ɗakinsa, yana ganin Adda ta biyoshi ya rufo ƙofar kawai ya saka sakata da sauri, ba dan ta so ba ta haƙura ta koma inda su ke ranta a masifar ɓace.
A chan soron kuwa gaba ɗaya ƙafofin Baba sagewa su ka yi a take kamar zai zube haka ya ji, ga jiri da ya ke kwasarshi kamar hauka!!! Tabbas Anne Annoba ce, ba ya ko tantama sarai ta san Amir ba shege bane ba kawai dan ta firgita kowa ta rama abunda su ka yi mata shine ta gwammaci ta yi haka a gaban jama’a….
Ƙus-ƙus aka fara yi a wajen…wanda hakan ya sake tsorata Baba.
Duk yadda Adda ta so ta hana kanta kuka sai ta gagara, ta na ƙarasawa soron ba ta san lokacin da hawaye suka shiga zubo mata ba ganin an fara magana ƙasa-ƙasa, ga takaicin abun, cikin kukan ta ce “haba Anne! Da ke da mu duk mun san ƙarya ki ke yi!
Wanne irin abune wannan? Wacce kalar zuciya ce da ke ne? Amir fa ɗanki ne”
“Eh ae ɗazu da ake ci mini fuska daɗi ki ka ji har kwanyarki, yanzu kuma da yake an taɓo
naki shine za ki yiwa mutane kukan munafurcin da ki ka soba. Munafuka Annamimiya kawai.”
Da sauri Ya Abba ya ce “Ya isa haka!”
Muryarsa na baiyyana ɓacin ran da yake a ciki, maƙura.
Tutture mutanen wajen Kaka Nura ya yi tukunna ya samu ya shigo, tun asuba ba ya gidan ya zagaya gidan wata Mata da su ka haɗa Ap, akan zai je da sassafe saboda dare unguwar a cike take sosai Safiya ce ba za a iya ganin shige da ficensa ba, dan haka ya tafi ko sallar asuba bai yi ba.
“Abba lafiyanka na ji ka na magana a dake kamar da ƴaƴan cikinka? In ce dai ba jikokina ka ke yiwa wannan gadararriyar maganar ba.”
Cewar Kaka Nura, yana maganar ya na kallon kowa one by one…
Cikin takaici Anne ta ce “da ni ya ke!”
Juyawa Kaka Nura ya yi ya sake kallonsa sosai sannan ya kalli Anne irin abun mamakin nan kafin ya sake maida dubansa zuwa ga Abban sannan ya ce “kai! Dan Ubanka ‘Mai Dala’ wanda ya tsaneka ya tsani jin ko da sunanka ne wannan ta yi maka kama da sa’ar wasanka?”
Ya yi maganar ya na nuna masa Anne sannan ya sake juyowa ya kallesa bai damu da yadda Yanayin Abban ya sauya a take a lokacin ba! Ya ɗaura da cewa “dan ka samu an yi maka gata? An rufa maka asiri shine za ka zaƙe?.
Ae da mun bar ka da Uban naka ka na binsa ya na korarka! Ka ga sai ka ƙare rayuwarka a kan titi ka na galantoyi.”
Da masifar ƙarfi Ya Abba ya runtse idanunsa trying very hard to control himself dan a yadda ya ke ji tsaf zai iya damƙo Kaka Nura kuma in ya ruƙosa zai yi wuya in bai masa illa ba…..”
Cikin tsantsar tsana Kaka Nura ya ce “ka kiyayeni wallahi! Ka kama kanka. Butulu kawai wanda bai san an yi masa halacci ba!
Tirr da kai, a haka za ka ƙare kai ba shege ba kai ba ɗan halak ba.”
Sai kuma ya waiga zuwa ga Anne sannan ya ce “menene wai ya ke faruwa ne, na ga an cika?”
Kafin ya kalli jama’ar wajen ya ce “bayin Allah lafiya kuwa!? A watse haka dan Allah…..”
Da sauri Ya Abba ya shige cikin ɗakinsa…
Cikin taɓe Baki Anne ta ce “Habu ne wai ya koreni daga gidan nan. Ya ce in fita in tafi koina ma har sai ya nemeni”
Rasss!!! Haka gaban Kaka Nura ya yanke ya faɗi amma sai ya dake!
Bai bari yanayinsa ya nuna hakan ba.
Sai da ya ɗan dawo dai-dai daga girgizar da maganar ta sanyashi ya yi, tukunna ya kalleta sosai kafin ya ce “ae ta kwana gidan sauƙi. Abu guda dai da na sani shine babu uban wanda ya isa ya koreki daga cikin gidanga, dan haka ki shiga ɗakinki ki kwaso kayanki ki koma ɗakin Yadikko ku zauna tare, babu inda za ki fita ki je ina cikin gidan nan…
Ki bashi lokaci, in bai ce ki koma ba sai mu nemi saki da kanmu. Kar ki wani damu ba kanki farau ba.”
Tunda Kaka Nura ya shigo dama Yadikko ta ɗan sha jinin jikinta shiyasa ta yi tsit. Da kyar ta iya cewa “a ganina da an sasanta abun, kar ka ce haka ka bari in har ni na haifi Abbakar to zan saka ya barta a ɗakinta, wanne kalar shirmene haka zai yi kamar a garin gaɓa-gaɓa, auren aka ce masa abun wasa ne, in sha Allahu wannan tsari nasa ba zai yi aiki ba.”
Juyawa Baba ya yi ya fita bai bi ta kan kowa ba, dan ba zai iyaba…..Tabbas dama ya san abunda za su yi kenan shiyasa kawai ya fasa sakinta dan kamar yadda Ya Amir ya faɗa Anne ba za ta fito da kwayar zarrar mutunci a bazawara ba kuma ba gidan za ta bari ba (ga zahiri ya gani) dan haka a fili za ta dinga tafka ɓarna a gaban idanunsu, ko dan ta baƙanta musu rai ma…
Ya na tafe ya na wannan lissafin hawaye su na zubo masa kamar wani ƙaramin Yaro, ba ya son Anne! Tabbas Azaba ce ita ga rayuwarsa!!!
A haka ya zagaya wani lungu a bayansu ya zauna a kan wani dandamalin sokaway, yana gama zaman kawai ya rushe da kuka sosai.
……..
Banza Kaka Nura ya yi da Yadikko, kamar wata banza ta na magana.
Kafin ya yi
kwafa ya wuce cikin kitchen kawai ya rarumo itace ya yo kan ragowar jama’ar da su ka yi gardamar tafiya da masifar gudu kuma wallahi da niyyar sauƙewa duk wanda ya sama ya taho…
Aikuwa rututu haka aka hau gudu har da ihu, cikin hukuncin Ubangiji bai samu kowa ba, dan haka ya mayar da ƙofar gidan ya rufe ya na haki!
Ba ya so a gane halin da yake ciki!
Ƴar sa aka kora? Kut sai da ya gama tsotse mata duk albarkatun jikinta ta haihu ta tsofe tukunna zai ce ya koreta, daga ƙarshe ya san cewa zai yi ya saketa.
Tabbas Habu ya na wasa da wuta.
Cikin sheshsheƙar kuka Adda ta ce “ita ɗin da kake goyawa baya yanzun nan ta gama sheganta maka jika a gaban idanun kowa…
Bayan duk ɗinmu nan na san mun san ƙarya ne…yanzu na san ta gama dasa zargi a zuƙatan jama’a, shikenan za a je a yi ta magaana.
Shin me za ka ce game da hakan shi kuma?”
Kallon Anne Kaka Nura ya yi kamar zai ce wani abun sai kuma kawai ya ɗauke kansa bai ce komai ba ya
mayar a Adda sannan ya ce “sannu mahaukaciya! Dukanta ki
ke so in yi yanzu kenan ko me? Ɗan uwanki ya ja na tabbata koma menene ta yi, magana kuma uban kowa ma ya ɗauki abunda ya ke so ya yi a kai, shi ya sani ko kin taɓa ganin alamun shakka ko gudun magaana a tare da ni?”
Lumshe idanu Adda ta yi a hankali, a take wasu kalar hawaye su ka shiga zubo mata rututuuuu na tsantsar baƙin ciki…ta matse bakinta sosai trying very hard ta hana kanta kuka!
“Ki kiyayeni kar ki ƙara kawo min munafurcin Nuratu ba na son shirme….ko meye ta faɗa akwai dalili ko kuma ma dai-dai ne.”
Juyawa kawai itama Afra ta yi ta bar wajen jikinta har yana karkarwa tsabar damuwa da ɓacin rai.
….
Tunda Ya Abba ya shiga ɗaki ya ke ta faman safa da marwa.
****“Eh tabbas ɗana ne! Ni ne na haifesa, amma ba ni da abunda na tsana in gani ko in tuna da akwaishi a doron ƙasa kamar shi!
Ba ni buƙatarsa in kuna so he’s all yours and dan Allah ku yi controlling nashi within yourselves…kar ya bari
In sake ganin fuskarsa har gaban abada!…”
Yana gama faɗin haka ya juya su ka ci gaba da hira shi da Abokinsa ya na dariya sosai kamar bai yi komai ba….****
Murya da moment ɗinsu da Daddy (Mai Dala) ya shiga dawo masa tarr a kwanya kamar yanzun ne ya ke gaya masa…..
Wani irin karkarwa jikinsa ya ke yi tsanar mutumin ta na sake shigarsa!!! A hankali ya ɗaga fuskarsa ya na kallon kansa a jikin madubin ɗakin nasa, fuskarsa sak!sak!! Ta Daddy ce babu kwaskwarima, har ma da yanayinsa…dan ko ba a gaya maka ba in ka kalli Abba ko da a duhun Magriba ne sai ka san cewa Daddy ne Ubansa….
wani irin bugawa zuciyarsa ta ke yi! Dan the fact that ya na kama da mutumin sosai sake tarwatsa masa lissafinsa ya ke yi. In Allah zai ara masa dama ya bashi kuɗi a ɗauke zunubi wallahi plastic surgery shine babban burinsa!!
Ba ya so da ƙaunar duk wani abunda zai haɗa shi da mutumin ko da kwayar zarrah ne….
Bai san lokacin da ya ɗaga hannnunsa ya daki mirrow ɗin ba! Ai kuwa a take ya tarwatse ya fasa masa hannu.
Da sauri sosai Adda ta bar su Kaka Nura a soron ta afka cikin ɗakin nasa ta na shiga ta toshe Bakinta ta saki kuka! Dama ta san za a rina….Tabbas sai Allah ya yi mata hisabi da Anne da Kaka Nura dan har ga Allah su na shiga haƙƙinsu su na ɗaga musu hankali matuƙa ita da Abba akan case ɗin Daddy.
“Ai da yanka kanka ka yi kowa ya huta shine zan san ka na da zuciya.”
Cewar Yadikko, cikin ɗaga murya sosai bayan sun ji ƙarar fashewar gilashin…. So take yi kawai ta yi koma meye domin ta samu Kaka Nura ya yaba mata ya daina fushi da ita ya kulata, dan ta san zafi ne ya ɗauka.
“Ƙunci yanzu ku ka fara ganinsa ai ke da ɗan naki, ni kuke so ku gani a haka amma ke ce a wulaƙance wallahi, ba dai ni ba.”
cewar Anne
“Ni anya ma kuwa ba ɗan naki ke biya miki buƙatunki ba, kullum ku na ɗaka ke da shi, ke ba aure shi ba aure.”
Yadikko ta sake faɗa, duk dan Kaka Nura ya yarda a bayansu take.
Bai kulata ba ya juya kawai ya barta a wajen, ya yi shigewarsa
ɗaki! Ya na lissafin ta ina zai biyowa Baba! Tabbas sai ya maida gidan upsidedown sai ya hanashi walwala wallahi, da shi da ƴarsa sun fi ƙarfin wulaƙancin talakan banza kamarshi.
Hatta Anne sai da ta gaji ta barwa Yadikko, ta shige ɗaki zuciyarta na tafarfasa, Yadikko kam sai da muryanta ya kusan dishewa tsabar hayagaga ta inda ta yiwa Abba da Adda tatas kafin ta haƙura itanma ta bar wajen ta nufi wajen Anne ta ce mata ‘kar ta wani haɗa kayanta ta zo, ta zauna a nan inda take za ta yi magana da Habu’…tukunna ta wuce ciki (ɗakintq) ta na haki sama-sama……
In sha Allahu
ta na jin motsin Habu za ta fito dan zuwa wannan lokacin ta fahimci ya fita ne tun ɗazu saboda ya rainata, shegen Yaro! Sai ya janye wannan hukunci da ya yiwa Anne.
A ɓangaren su Adda kuwa, Ya Abba ya so fitowa Amma ta tsaya a bakin ƙofar ta kare…ƙiri-ƙiri ta hanashi fita.
Ji yake kamar ya haɗiye zuciyarsa kawai ya huta ko ya samu sauƙin abunda ya ke ji, da kyar ya na ganin dishi-dishi ya ƙarasa ya zauna a bakin gado kawai…
Dan ba ya son ganinta haka ta na kuka sosai gashi ta hanashi yin komai ga baƙin cikin da ya ke a ciki.
Sai da ta tabbata ya ɗan sauƙa tukunna ta ƙarasa ta ci gaba da goge masa in da ya ji ciwo har yanzun ta na sharar hawaye…
…..
Tunda Anne ta shiga ɗakinta ta ke ta faman safa da marwa, Kaka Nura shima tunda ya shiga ya zauna ya ke lissafi, ya ma kasa zuwa ya sameta su tattauna! Wanne irin sanyi ne haka Nuratu ta yi da har za ta bari Habu ya yi mata hakan, ya aka yi ta bari ta sauƙo har haka!? Tabbas akwai gyara a gidanga.
Ya na kallon Yadikko ta shigo ta gama lalubenta ta na kiran sunanshi amma ya yi mata banza, in ta gama da kudu ya koma arewa in ta zo nan ɗin ya koma yamma.
Haka nan ta ƙaraci maganganunta ta na nemansa ta haƙura, daga baya ta fara tunanin to ko dai fita ya yi bai shigo cikin ɗakin ba!
Tabbas dole ta takawa Abbakar burki wallahi. Ba zai janyo mata fushin Nuratu da Nura ba….
Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING*
Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING*
Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139*
Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya