Showing 99001 words to 100561 words out of 100561 words

Chapter 34 - BAKAR TUKUNYA hausa novel

07 Feb 2026

457

ce “sannu Ummi, congratulations komai ya kammala…”

“Yeah nima yanzu na ke shiga gida dan sai da na gama komai aka yi sealing deal ɗin tukunna na yarda na dawo. Congratulations to us…”

Dariya Matar ta yi wanda ya ke nuni da tsantsar farin cikin da ta ke a ciki sannan ta ce “to ya ku ka ƙare da Asad?”

“Zan waiwayeshi in na gama hutuwa”
Cewar Ummi, ta na mai kallon gidan sosai ta na rarraba idanunta zuwa ko wanne lungu da saƙo.
Matar ta na shirin yin magana Ummi ta ce "ina zuwa, i’m seeing something a little bit weird, zan kiraki daga baya.”
Daga haka ta kashe wayar ta na mamakin wayam!! Ɗin da ta gani gidan kamar ba kowa sannan idanunta a kan Akram wanda ya nufota da murmushi ɗauke a kan fuskarsa.
Ya na ƙarasowa ya karɓi hand bag ɗin Ummin daga hannun driban da ke tsaye a bayanta da suitecase ɗinta sannan ya ce musu “you can go…”
Daga haka ya juyo ya ce “welcome home Ummie, i just saw your text. Congratulations…”
Ya ƙarashe maganar ya na murmushi sosai.

A hankali ta sauƙe numfashi sannan ta ce “thankyou ɗan albarka.”
Ta na kallonshi..

Cikin yin ƙasa da kansa sosai ya ce “i’m soo sorry Ummie, wallahi Daddy ne ya saka ni aiki shiyasa na turo su.”

Ɗan ƙuraa masa idanu ta yi kafin ta matso a hankali ta dafa shi sannan ta ce “are you okay?”

Da sauri ya ɗago ya kalleta sannan a ɗan burkice ya ce “yeah sure, i’m very okay wallahi, ba abunda ya faru, mu je ki huta…”


Mai gadin gidan ta hanga sun nufi bayan gidan da shi da drebobin da su ka kawota yanzunnan ɗayan har da tuntuɓe ya na faɗuwa, kafin ya tashi jikinsa ya na karkarwa ya bi ayarin nasu su ka yi ciki….
Sai da mai gadin ya saita su a kan hanya tukunna shi ya dawo ya nufi waje domin ya zauna a gate saboda kar a bar wajen ba kowa.

Numfashi Ummie ta sauƙe ta maida dubanta zuwa ga Akram wanda ya gagara kallonta tukunna ta ce “Daddy ne ko?”

Da sauri Akram ya ce “babu abunda ya yi min fa Ummie…”


A hankali ta sauƙe numfashi kafin ta ce “shikenan Akram na yarda!.
To mai ya faru ake ta guje-guje?”
Ta jeho masa tambayar ta na kallonsa sosai.

Muryarsa har karkarwa ta yi wajen ce mata “Uncle Asad ya na hanya.”

Da mamaki sosai ta kalleshi, yayinda ta yi shiruuu kawai ta na mamaki…….
chaan kuma sai ta ce “su na ina?”

Sai da ya sauƙe numfashi
Sannan ya ce
“Baya. Ana gyara side ɗinsa ne, an gama wankewa yanzu ana chanja furnitures”

Da sauri ta ce “a nan gidan zai zauna? Mai ya faru da gidansa”

“Its like a chan ya ke son zama shima but Daddy ya dage akan a nan zai zauna”
Cewar Akram, wanda duk ya diririce .

“Okay…”
Kawai ta ce, daga haka ta nufi baya kamar yadda Akram ya ce mata su Daddy na wajen. Inda ta nan ce hanyar ƙofar shiga ɓangaren Asad.
Ta na wucewa shima ya wuce ya koma kan punishment/aikin da daddy ya bashi ya ce ya yi.

Duk wanda ka gani a wajen hankalinsa a tashe ya ke, domin kuwa kowa tsoron ya aikata laifi ko da ɗan ƙanƙanine ya ke yi…masu guje-guje su na yi masu aiki
tuƙuru su na yi amma hakan bai hana Daddy samun waenda zai hukunta ba (a cikinsu) zuwa anjima in an kammala komai….

Dogo ne sosai sannan ba shi da rama, ƙiba ma babu alamunta a tare da shi, ya na tsaye ya juya baya yana bada order ya na dariya, wanda in ba juyowa ya yi ku ka haɗa idanu da shi ka kalli idanunsa ba, to fa sam ba za ka gane cewa babban mutum bane ba dan sam jikinsa bai nuna girma ko tsufa ba ya fi kama da samari ƴan shekaru 33 haka, ba shi da alamun tumbi
A tare da shi da duk wani abunda zai nuna maka cewar ya manyanta bayaga furfurar da ta gauraya da baƙin gashin gemu da sajensa da kuma idanunsa waenda duk wanda ya kalla to zai san shi ɗin ba Yaro ko saurayi ya ke ba.

“Barka da dawowa Hajiya”
Muryoyin masu aikin da su ke tare da shi a wajen su ka ankarar da Daddy zuwanta.

Da sauri ya juyo, aikuwa su na haɗa idanu ya saki wata sabuwar dariyar kafin ya ce “welcome home sweetheart….”
Ya faɗi hakan ya na mai ƙarasawa inda ta ke, ya na zuwa ya yi hugging nata kafin ya zarota daga ƙirjinsa ya yi kissing forehead ɗinta…
Da sauri sosai ta ɗan jaa baya sannan ta saka hannunta ta turashi baya shima saboda ganin abun nashi ya na shirin zarce inda ya kamata…

Dariya ya yi yanzun ma wanda hakan ya sanya Ummie ta ɗan sha jinin jikinta, a hankali ta ce “mu je ciki Daddy pls i want to talk to you.”

“Okay My lady” ya faɗa mata hakan cikin nuna mata way forward da hannunsa ya na ɗan rissinawa alamun itan queen ce a garesa.

Gaba ta yi ya bita a baya su ka fito daga wajen direct su ka nufi ɓangarensa.

Shi ya buɗe mata ƙofar ta shiga ya na ta riritata kamar kwai…..su na shiga ta soma dana sani dan haka ta hau kame-kame ta na mai cewa “amm, dama na ga a gaban mutanene Daddy shiyasa na matsa saboda gudun magana da raini sannan ban san ma na tureka ba…”
Dai-dai ya na kammala locking ƙofar da tomb nashi..
Yadda ya damƙo hannunta ne ya sanya ta yin shiru! Dan da masifar ƙarfi ya ruƙo tafin hannun da ta yi amfani da shi wajen tureshi ɗin (ɗazun).
Ya na murmushi ya na kallon cikin idanunta waenda su ka yi jaaa sosai a take saboda tsabar baƙar azabar da ya ke gana mata ya ce “kin fi ni sanin abunda ya kamata kenan ko sweetheart…”
Ya ƙarashe maganar cikin yin kalar tausayi kamar ba shine ya ke shirin illata mata ƴan yatsu da tafin hannunta ba..

Wata kalar razananniyar ƙara ta saki jin yadda ya ke ci gaba da yi mata, a take ta daina jin motsin jini da rai a yatsun nata bayan wata gigitacciyar azaba da ta shigesu tun daga nan komai ya ɗauke mata ɗiff a wajen…sosai farar fuskarta ta yi jaa…
Ya na kallonta truly enjoying the moment and the pain da ya ke hanga ta cikin idanunta ƙarara ya ce “kar ki ƙara my baby, plss, sannan kar ƙi ƙara kirana a gaban mutane ni ba boyi boyinki bane ba…”
Daga haka ya cikata farat ɗaya wanda hakan ya sanya ta zube a wajen a take….ta durƙushe ta na mai ƙoƙarin hana kanta yin kuka dan kar ya ji ko ya gani ta je ta sake yin wani laifin.

Wata nannuyar ajiyar zuciya ya sauƙe ya na murmushi kafin ya ce “oya now stand up and hug me, also congratulations
Asad is coming home today in sha Allah.”
Ya ƙarashe maganar ya na murmushi, yayinda yanayinsa na baɗini ya soma sauyawa ganin ba ta miƙe ɗin ba kamar yadda ya buƙata.
Kamar ta san lissafin da yake yi
A hankali ta miƙe jikinta ya na karkarwa dan hannun nata ya dawo ta ci gaba da jin wani matsanancin zugi na fitar hankali.

Cikin nutsuwa ta yi hugging nasa gaba ɗayanta ta na karkarwa… yayinda ya yi murmushi ya ce “thats more like it”
Daga nan ya shiga ƙoƙarin neman halalinsa ba tare da ya bari sun ƙarasa ciki ba ko kuma ya yi laaƙari da yadda ya maida mata hannunta.

Ko kusa bai bi ta ita ba. Iyakacinsa duk abunda ya san ya na so shi ya yi…..sai da ya tabbata ya samu kansa a yadda ya ke so tukunna ya miƙe ya haura sama ya barta nan yashe a wulaƙance ta na maida numfashi a wahale kamar ba ita ce Matar gidan ba, gaba ɗayanta ta fice a haiyyacinta….da kyar ta iya saka hannu ta lalumo mayafinta ta rufawa jikinta ta dunƙule a waje ɗaya dan ba zata iya tashi daga bakin ƙofar nan inda ta ke ba, a take kawai ta rushe da wani kalar rikitaccen kuka zuciyarta na ƙuna.
Bai tambayeta ya gajiya ba!
Bai yi mata congratulations game da murnar nasarar da ta samu ta zuwan Asad kawai ya yi mata, kuma ta san ya sani dan a gabanta aka kirashi aka sanar masa komai ya kammala…
Bai yi duba da abinda ya yi mata a hannunta ba!
Ta kansa kawai ya ke, farin cikin nasa ma ta ƙarfi sannan a wulaƙance ya karɓa…
“Kaico!!”
Ta furta hakan a fili zuciyarta na tafarfasa.



Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING*
Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING*
Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139*

Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudinku tested and trusted.

Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu....
location:Kano
Delivery:NationWide.
kar ku bari a baku labari, sai kun zo🙏
SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA

BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login