Showing 81001 words to 84000 words out of 100561 words
ya sa ka na lafiya….”
Sai da ta ɗago ta ɗan saci kallonsa saboda yadda ta ji ya yi shiruuu, ganin ita kawai ya ke kallo ya sanya ta yi saurin mayar da kanta ƙasa ta shiga wasa da ƴan yatsun hannayenta da junansu.
A hankali ya sauƙe wata nannauyar ajiyar zuciya sannan ya ce “Afra kin san ina sonki ko? Sannan na san kin san na yarda da ke!”
Da sauri ta ɗago ta kallesa kafin ta maida kanta ƙasa jin ya kira sunanta yau! Tabbas abu mai mahimmanci ke tafe da Ya Isma’il dan haka ta sake nutsuwa bayan ta aiyyana hakan a ranta ta bashi dukkan hankalinta, sannan a hankali ta ce “eh”
“Good”
Ya ce kafin ya ɗaura da cewa “wasu mutane ne su ka fara kai sukarki gidanmu, har da cewa wai an ganki a hotel da ke da Samuel…”
Da mugun sauri ta ɗago ta kallesa da idanunta waenda a take! Su ka soma sauyawa…
Da sauri shima ya gyara tsayuwarsa cikin sigar rarrashi ya ce “sam! Ko kaɗan ban yarda da su ba, ki kwantar da hankalinki, amma pls i want to hear you say it…..
Ina so in ji kin ce mini ba ki je wajensa ba in ji daga bakinki, hankalina sai ya fi kwanciya…”
Cikin tarar numfashinsa ta ce “na je, jiya…”
Ɗiff!! Haka ya ɗauke wuta, ƙirjinsa ya shiga dukan uku-uku dan Ya Isma’l wani kalar mahaukacin kishi ke garesa…
“Haushi ki ka ji kenan, shiyasa za ki gaya mini abunda ba shi kenan ba ko?”
Girgiza kai ta yi, tsanar Anne na kokawar shiga cikin zuciyarta, dan ita dai tunda take a rayuwarta ba ta taɓa jin ta muzanta kamar na yau a yanzun nan ba…
Muryarta na karkarwa ta ce “haka ne Ya Isma’il, da gaske na je, kuma kaima na san ka riga ka yarda da aka gaya maka dan in da ba ka yarda ba to da ba za ka yi
mini maganar ba, sannan ba zan ganka cikin damuwa ba…”
Kukan da ta ke ji yana ƙoƙarin zubo mata ta yi ƙoƙari ta danne da kyar sannan ta ɗaura da cewa “Amma wallahi Allah ba abunda ka ke tunani ya kaini wajensa ba, Anne ce ba ta da lafiya kuma ciwon nata is very severe shine ya ce in zo in amshi kuɗin abunda Likita ya ce mata dole sai an yi, da na fita kuma ya kwatanta mini hotel…ka yi haƙuri Ya Isma’il…..”
A yau kam tabbas kishinsa da kuma ɓacin rai sun ci ƙarfin soyayyarsa gareta, dan wallahi shi kansa bai san lokacin da ya tari numfashinta cikin daka mata tsawa ya ce “in kin tambayeni kuɗi zan hana ki ne?”
Girgiza masa kai ta yi a hankali ta ce “Ya Isma’il kana ta ɗawainiya, kuma kai da kanka na ji kana kukan abubuwa sun matse kwana biyu.
Sannan ga batun aure a gabanmu kuma na ga ba abunda ya shafeni bane Anne ce”
Cikin katseta yanzun ma da faɗa sosai ya ce “Amma ae kin tambayi wani banza ƙato chan!!!
Ki rasa a wajen wa za ki yi roƙo sai a wajensa, sannan da ki ka fita ki ka ji ya ce miki hotel dan me za ki je? Ko jan ki ya yi ta ƙarfi ta yaji ban taɓa tunanin za ki je hotel ba!
Ko ba ki yi komai a chan ɗinba kin san yadda zuwan naki zai zame mana matsala kuwa?
Afra hotel fa! Idan ku a wajen ƴan gidanku zuwa hotel ba komai bane ba kin san a wajenmu babban abu ne ko?”
Ɗagowa ta yi kawai ta zuba masa dara-daran idanuwanta waenda suka kaɗa su ka yi jazirrrr!! Sosai sannan ga ruwan kwallah ya cika su tap!.
A take ya ji duk wata masifa da ta yunƙuro ya ci burin sauƙe mata ta gushe, sai kuma ya fara dana sani sannan hankalinsa ya soma dawowa jikinsa a take ya ga bai kyauta ba!
Bai taɓa mata ihu ba ko a wasa sai yau!…
“Damn it”
Ya furta a hankali ya na mai runtse idanunsa da masifar ƙarfi, kafin ya shiga ƙoƙarin buɗesu da kyar!
Ya na buɗewa ya ga wayam!!!!
A hankali ya ce “Ya Subahanallah…..”
Ya na mai ji kamar ya kurma Uban ihu, wae ko ya ji sauƙin kishi, baƙin ciki da tsantsar da na sanin katoɓarar da ya yi da suka mamaye shi su ka dannne shi a wajen sosai…
A hankali ya sunkuyar da kansa ƙasa zuciyarsa na ƙuna da susa.
“Kai dan *****uwarka goge mana plastar ka ke son yi ko
meye hakan? Uban me ya fitar da kai da asubar nan ma? Wuce ka tafi gida ɗan muguwa, shege mai kama da Ubansa.”
Muryar Anne ta dirar masa a dodon kunnensa, da alama Yaro ne ya ke taɓa bangon gidan shine za ta tashi jama’a daga barci da hayagagarta.
Bai yarda ya kalli direction ɗin da ya ke jiyo muryarta ba, kawai ya saka kanshi gaba ya wuce da saurin gaske! Ba ya son ko da jin sunan Matar ne.
Sai da ya sha kwana tukunna ta lura da shi (ya bar wajen) sakomakon Marin da ta tsaya kikkifawa Yaron ya ɗauke mata hankali daga kan Isma’il ɗin. Wae Yaron ya turo mata Baki.
Ta so ta bishi a baya ta na kwala masa kira har sai ya tsaya ya gada ita wallahi dan ubansa. Ta lura ko haɗa hanya da ita ba ya ƙaunar yi saboda raini, amma da ta tuna abunda ta taho da shi ba ta so a lura a gane sannan ba ta so a fahimci ta fita, sai kawai ta kyale Isma’il ya wuce a fili ta yi kwafa kawai ta shige cikin gidan….Yo in ta bar wannan ɗan talakan banzan mai shegen raini ya auri Afra ma ae ba sunanta Nuratu ba wallahi…..
“Daga ina ki ke?”
Ta ji muryar Baba a bayanta, a dake kamar ba shi ba.
Tun ɗazu da ta fita lokacin shi yana masallaci Ya Amir kuma cikin ikon Allah yau ɗin ya makara dan haka ya ganta……..
Ana idar da sallah kuwa ya sanarwa Baba Anne fa ta fita, dama idonsu a kanta ya ke dan sun san za ta yi wani abun, ya san Allah ne mai yi amma tsafi gaskiyar mai shi, shi kuma in sha Allahu wannan karon dai sai ya tsayawa Afra wallahi ba zai bari Anne ta yi galabar tarwatsa mata rayuwa da farin ciki ba! Tabbas ko shakka babu wajen boka ta je…
Ya na cikin wannan lissafin Anne ta waigo ta wani kalleshi sama da ƙasa, kafin ta ce “ikon Allah”
Ta na wani taɓe Baki sannan ta koma ta juya za ta wuceshi cikin wani kalar sauri Baba ya sha gabanta sannan ya sake jeho mata tambayar “daga ina ki ke?”
Idanunsa a kan ledar, ta windown Masallaci ya ga wucewarta kuma dama tun da ya idar da addu’o’insa ya ke tsammaninta, ya na so ya ga ta ina za ta ɓullo, dan ya sake fahimtar me ta ke shiryarwa. Tunda Allah ya sa ya hangi ledar hannunta shikenan ya ji tsigar jikinsa ta shiga tashi hankalinsa ma ya tashi sosai, shiyasa ya biyota a baya masallacin ma Ya Amir ya barwa ya kammala rufewa.
“Kai a su wa? Da za ka wani shiga gabana ka na wani huci kamar Namijin kwarai? Abeg dalla gafara in wuce soloɓiyo kawai.”
Anne ta faɗi hakan cikin ɓacin rai dan ta lura da yadda ya ke ta faman bin ledar hannunta da kallo.
Ya Abba tun da ya dawo daga sallah yau ma ya ke ɗaki dan har yanzu bai kammala hucewa ba, shiyasa da ya gaida Adda ya ke shigewa ciki ya zauna ko ya yi karatu ko ya yi tunani.
Duk wata sana’a wuyarta ya soma cikin hukuncin Ubangiji ba ta tasiri, ya rasa me ke faruwa da rayuwarsa.
A yanzu kamata ya yi ace ya na da mata har ma da ƴaƴa amma da ikon Allah shi kansa har yanzu ciyar da shi ake yi!
Wannan abu ya na matuƙar damunsa da sauran tarin abubuwa masu yawa da mahimmanci a rayuwarsa shiyasa duk dauriyarsa kwana biyun nan abun ya ke cin ƙarfinsa kwarai.
Tun ashar ɗinta na farko a ƙofar gida ya ji.
Kasancewar ɗakinsa a soro ya ke sannan shi ɗin hancinsa kamar wani mai stabilizer ya ke dan abu duk ƙanƙantarsa sai ya ji! Hakan ya sanya ta na shigowa ya fara jiyo ƙarnin abunda ta zo da shi.
Kamar ba zai kula ba, sai kuma ya ga ya dace ya kula tunda koma dai menene ta ke shirin yi family ɗin tamkar nasa ne bai kamata ya naɗe hannuwa ya zauna ba dan ko shakka babu wani surƙullenta ne ta je da sassafe ta zo da shi.
Dan haka a hankali ya miƙe ya ajjiye littafin addu’ar da yake yi ya buɗe ƙofar ɗakin nasa ya fito idanunsa a kanta.
Tun tijarar da ta yi masa a ƙofar gida sai yanzun ne ta ganshi, haka kurum ya yi mata kwarjini gashi ya kafeta da lumsassun idanunsa dan haka ta kawar da kanta ta maida dubanta zuwa ga Baba wanda ya tabbar mata ba zai barta ta wuce ba sai ta gaya masa daga ina take, ta ce “Habu ka dai san dambe da kai ba zai bani wahala ba ko? Ka matsa in wuce billahi ko mu kwashi ƴan kallo da kai a cikin soron nan…”
Dai-dai nan Su Afra su ka ƙaraso cikin soron, haka Adda itama kamar haɗin Baki har da Ya Amir shima ya shigo daga rufe ƙofofin masallaci.
Salati Adda ta yi sannan ta ce “Haba mana Anne, dambe kuma da mijin aurenki? A gaban ƴaƴanki?
Ku yi haƙuri dan Allah Baba kaima ka bari mana, kar ka yi abunda ba ka iya ba…”
Ta yi maganar itama idanunta a kan ledar ta na mamakin menene a ciki haka ya ke ƙarni…..
Ganin an soma tara mata jama’a ga abu nan a hannunta da ba ta so a gani ya sanya Anne ba ta biyewa Adda ba kawai ta yi banza da ita ta fara ƙoƙarin wucewa amma fafur Baba ya ce “ba fa za ki wuce ba sai kin gaya min daga ina ki ke da asubar nan sannan da izinin wa ki ka fita!!!!”
Ya na jira ya gama da wannan ya koma kan ledar da kowa a cikinsu bai yarda da ita ba, yau kam ƙaryarta ta ƙare! Ba za ta yi masa tsafin da ta saba yi a cikin gida ba wallahi.
Sosai ran Anne ya harzuƙa ta gagara haƙuri ganin wanda ta raina ya na yi mata magana kamar wani Ubanta! Yo ko Kaka Nura ae ƙaryansa ya yi mata haka wallahii…
Dan haka ta gyara tsayuwarta sannan ta ce “Mijin da ya isa! Ba wanda Matarsa ta ke ciyar da shi ba, shine in za a fita ake gaya masa sannan ake neman izininsa…”
A hankali Amal ta sunkuyar da kanta ƙasa ta shiga ƙoƙarin ganin ta hana kanta yin wani kukan, dama tun da Afra ta shiga ta fara bata labarin abunda ya faru tsakaninta da Isma’il su ke kuka tare gwanin ban tausayi, da kyar su ka rarrashi kawunansu su ka share hawayensu su ka fito yanzun…..
Wani kalar kallo, Ya Abba ya ke bin Amal da shi tun daga tsakiyar kanta har kan ƴan yatsun ƙafarta, gashi ba a isa a faɗi ransa a ɓaci yake, ko akasin hakan ba sam ba za a iya gane yanayin da ya ke ciki ba.
Ta na gama dannar kanta ta ɗago kenan karaff su ka haɗa ido, kamar wata marar gaskiya da gudu ta shige bayan Afra dan da masifar ƙarfi ƙirjinta ya buga! Bai taɓa yi mata irin wannan kallon ba, direct kawai ka na ganinsa ka san ita ya ke kallo har kamar ma bai san da kowa a wajen ba sai ita ɗaya tak!
Chan ƙasan maƙoshinsa ya ce “hmmm” kawai, wanda hakan ma da ya yi ba za ka gane haushinta ya ji, mamaki ta bashi, dariya ta bashi d.d.s ba.
Kafin chaan ya sauƙe ajiyar zuciya a hankali sannan ya gyara tsayuwarsa ta hanyar sake rungume hannuwansa a kan ƙirjinsa sannan ya ce “Anne faɗar Allah ki ke yiwa kwaskwarima ko me?”
Da masifar ƙarfi Anne ta runtse idanunta ranta na suya! Wato har da Abba ake titsiyeta yau a gidan nan tabbas zakanya ta yi sanyi! Kuma tunda shegen Yaron ya kulasu har ya saka Baki in ba da kyar ba sai ya tarwatsa mata shirintaa…a ranta ta ce “Ya Allah ka sa kar ya yi maganar ledar hannuna, Allah ka bani ikon wucewa da ledar nan zuwa kitchen lafiya…”
“Sannan menene wae ki ka shigo da shi gidan nan a baƙar ledar hannunki mai ƙarni sosai haka? Daga ɗaki fa ƙarnin ya fiddo ni..”.
A mugun mugun fusace Anne ta ce “Ubanka ne….”
Sai kuma ta juya da masifar sauri za ta bar wajen.
Da sauri Baba ya saka hannu ya ruƙo ledar tun ƙarfinsa, dama shima hankalinsa komai ya sake komawa kan ledar duba da yadda ƙarnin ya ke sake cika koina…..
Kasancewar da sauri ta juya ga kuma ledar kalar ta zamani ce waenda kullum ake rage musu kyau da karƙo ya sanya duka ledojin biyu da aka yi amfani da su wajen saka abun a ciki su ka yage! Abun ciki ya faɗo ƙasa taɓal! Ya baiyyana a gaban idanun kowa!
Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING*
Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING*
Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139*
Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudinku tested and trusted.
Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu....
location:Kano
Delivery:NationWide.
kar ku bari a baku labari, sai kun zo🙏
SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA
BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:25 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*
HUMAIRAH BULAMA
Yota011
*32*
•••••••••••••••
Ƙarfe takwas dai-dai na safiyar ranar ta buɗe idanunta a hankali ta sauƙe su a kan robber ceiling ɗin da ke a cikin ɗakin.
Wani mummunan mafarki ta yi wanda hakan ya sanya ta farka jikinta duk a mace, dan ko da ta buɗe idanun nata ma sai da ta shafe sama da mintuna ashirin a haka kafin ta samu ta miƙe
ta zauna sai kuma ta shiga ƙoƙarin tashi ƙafafunta su na yi mata zugi sama-sama.
Ba tunanin yin sallah, ba salati sannan babu godiya ga Ubangiji…haka nan ta ɗauki brush da macline ɗinta ta ɗauko pant da bra ta fito daga ita sai yololuwar rigar barcin da ke a jikinta komai nata a waje…fanɗarinka tsirara.
A ƙa’idar gidan kafin Yagwalgwal ta fito ruwan wankanta ya na ajjiye a cikin flask a bakin ƙofar ɗakinta da bokitinta an zuba mata ruwan sirki a cikinsa dai-dai da na flask ɗin.
Sai dai yau ɗin ta na fitowa ta ga wayam! Babu flask ɗin bokitan nata kuma ga shi a ajjiye a bushe ƙamas!!
“Tashin hankali”
Ta aiyyana hakan a cikin ranta zuciyarta ta na tafarfasa….
Sai kuma ta ɗaga kanta ta na kallon kowa ta na mamakin yadda ba a ma lura da ita ba ballanta a taho rututu kawo gaisuwa kamar yadda aka saba, instead hankulansu su na kan junansu ta inda aka yi group group ana ta ƙus-ƙus kamar wani dandalin munafurci, hatta masu wucewa suma bayani su ke yi a tsakaninsu ƙus-ƙus sosai.
Da gudu Aimana ta taho gareta da flask ɗin har kamar za ta kifa kamar wata Yarinya, ta na zuwa ta durƙusa ta ce “Afuwan Uwa, itace ne a jiƙe yau ɗin, da fatan kin tashi lafiya….”
Jikinta ya na karkarwa sosai ka na ganinta ka san bata cikin nutsuwarta…
Wato a kaff jama’ar cikin gidan aka rasa yadda za a yi a haɗa mata ruwan wanka har ƙarfe takwas ta wuce…sannan da ikon Allah har yanzu kamar wasu ba su ganta ba hankulansu na a kan munafurcinsu ƙalilan ne su ka nufota da niyyar gaisuwa….
A hankali Aimana ta ɗauki bokitin ta tafi da shi domin ta je ta kawo mata ruwan sirki, bayan Yagwalgwal ɗin ta amsa gaisuwartata da kyar.
Sai da ta gama amsa gaisuwar waenda su ka zo su ka gaisheta har ƙasa tukunna ta dakawa ragowar tsawa “Uban me ku ke tattaunawa ne?…”
Da sauri duk su ka waigo gareta sai kuma su ka taho rututu su ka gaisheta kafin a fara watsewa kaɗan-kaɗan su na tsoron kar Ladiyo ta gansu.
Wata Yarinya ce da Aimana su ka sirka mata ruwan su ka kai mata har bakin ƙofar banɗaki tukunna itama ta taho ta na tafiya da kyar kanta a ɗaure! Bara ta yi wanka ta shirya tabbas yau sai ta bawa Matan gidan nan mamaki akwai buƙatar ta tuna musu wacece Uwa.
Ta na zuwa ƙofar banɗakin ta tsaya chak!
Ranta a ɓace sosai ta ce “wae aljanun iya shege ne su ka shigi kowa ne a daren jiya? Ni zan ɗauki bokitin nawa da kaina in shiga…….”
Maganarta ce ɗiff ta ɗauke ta saki kayan hannunta su ka faɗi gabanta ya yanke ya faɗi sakamakon wani jibgegen Gardi da ta gani ya fito daga banɗakin daga shi sai boxer da bokiti a hannunsa.
Kallon-kallo su ka tsaya yi ita da shi kafin ya shiga kashe mata ido a ranshi ya na mamakin babbar mace mai irin dirin jikinta….
Cikin wata kalar razananniyar tsawa Yagwalgwal ta ce “wacce mai gangancin ce ta shigo mini da ƙato har cikin gida! Dan Ubanta…”
“Ni ce nan!!!”
Ta ji muryar Ladiyo a bayanta, sannan ta rarumo wani ashar ta dannawa Yagwalgwal ɗin a bakacin zagin Ubanta da ta yi itama….
Wani kalar masifaffen karkarwa jikin Yagwalgwal ya shiga yi, tsabar bala’i.
A fusace ta juyo su ka hau kallon-kallo ko wacce ta na huci…
Ladiyo kamar wata boss dama gata jibgegiya a fannin faɗin ƙashi.
Da kyar baƙin ciki ya iya barin Yagwalgwal ta ce mata “tafiyarki da mu ta