Showing 30001 words to 33000 words out of 100561 words
shi ba', kuɗi kuwa ta jikin Kakanta(Mallan) ya ke samu amma naira biyar ɗinsa ba ka isa ka ci ba gashi da shegen tsaurin ido Hakanan zai siyo Abu a gaban idanun kowa ya zauna ya ci ya yi ƙatt! Ya yi gyatsa ko magen gidan hakanan za ta ƙaraci kukan ta ta gama zagayeshi amma ba zai bata ba…
Wannan ɗabiar ta Mahaifin Nuratu (kaka Nura) ita ta janyo masa baƙin jini a wajen Mahaifiyar Mahaifiyarta saboda dama ita tanada ɗan zafi kuma ba ta son raini…Mahaifin Mahaifiyarta(Mallan) kuwa shi kam bai cika son gutsiri tsoma ba shiyasa bai taɓa biye mata ba ƙarshema ce mata ya yi ‘kar ta sake kawo masa ƙararsa, ai kowa da halinsa ake zaune da shi kuma har yanzu Nura (Kaka Nura ) Yaro ne dan haka baya son yawan zance iyakaci shi dai ya san zai ciyar da shi ya yi masa tufafi ya bashi muhalli har zuwa lokacin da Allah zai ƙaddara ya yi aure ya kama gabanshi.’.
Tsanar Kaka Nura ba ta sake samun wajen zama a cikin zuciyar Mahaifiyar Uwani ba sai lokacin da ya kawo ƙarfi, a lokacin mazan gidan guda biyu sun yi aure saboda dama duk sun girme masa sosai mutum biyu ya girma Uwani da yayanta, dan haka gidan sai ya rage daga shi sai Uwani da yayanta wadda take da shekaru sha huɗu dan yayunta maza biyu sun basu tazara sosai har ana tunanin ma Mallan ya daina haaihuwa ne tukunna aka haifi yayanta (saƙonta)itama aka haifeta.
A wannan lokacin shekarun yayan nata sha shidda sai Kaka Nura shima sha shidda dan watanni uku ne a tsakaninsa da yayan nata.
A lokacin ne Mahaifiyar Uwani ta fahimci shegen son matan Kaka Nura dan har Mata ta ji ƙus-ƙus ɗin ya na kaiwa shagon su wanda ke a waje saboda duk mazan manya sun yi aure kuma dama a ɗakinsu ya ke sai ya zamana ɗakin ya zama nasa shi kaɗai, dan Yayan Uwani wanda ya rage a cikin gida nasa ɗakin yake.....
Ita ta ɗagawa Mallan hankali akan batun amma sai dai ba a yi mata yadda take so ba ƙarshema abun caɓe mata ya yi dan Mallan cewa yayan Uwani na cikin gida ya yi 'ya tartara kayansa ya koma ɗakin Kaka Nura da ke a waje idan har gaskiya Mahaifiyar Uwani take faɗa to hakan zai takawa Nura burki daga ɓarnar da yake yi'. Sai dai kuma ko sati ba ayi da komarwa yayan Uwani shagon ba Kaka Nura ya yi ɓarnarsa da ƴan mata har biyu kuma ya shiga ya fita aka kama yayan Uwani da laifin dumu-dumu, laifin da har yau har gobe kowa yake ganinsa da shi, Mallan shima har ya rasu da laifin yake ganin yayan Uwani dan gani yake yi kamar shi ne ya aikata. Uwani da yayanta da Mahaifiyar Uwani sai shi Kaka Nuran ne kawai suka san asalin gaskiya…….
Fusatar da Mallan ya yi ne ya sanyashi ya cewa yayan Uwani ya fito da mata ya yi masa aure aka cire sa daga makaranta babu kalar kuka da roƙon da bawan Allahn nan bai yi ba amma haka yana ji ya na gani aka ciresa daga makaranta aka aura masa wata Yarinya ƴar makwabton su a lokacin shekarun sa goma sha shidda a duniya, to dai ya samu bayan auren ya ci gaba da karatunsa dan har aiki ya yi kafin Allah ya karɓi ransa...amma fa har Alhaji Ali(yayan uwani) ya bar duniya kwata-kwata baya son kuma ba sa shiri da Kaka Nura kamar Annabi da kafiri haka su ke…..
Nura ya na kammala secondary school shima akace ya fito da mata a yi masa aure, dan zuwa wannan lokacin Mahaifiyar Uwani cewa ta yi 'Wallahi sai dai Mallan ya zaɓa ita ko Muhammadu Nura.'
Wallahi abun kamar tsafi dan tashi ɗaya Mallan ya ce ‘ya ba shi Uwani’ wanda hakan ya girgiza Mahaifiyar Uwani sanadiyyar samun hawan jininta kenan har ta rasu ta na fama da shi...saboda ana sanar da ita zancen ta yanke jiki ta faɗi sai a asibiti ta farfaɗo.
Ta san halin Mallan ba ya magana biyu amma haka nan ta dage ta dinga gwada sa’arta har ƙaninsa sai da ta sako a cikin zancen amma furr!! Mallan ya ce ya gama magana ƙarshe ma da ta ɗaga masa hankali matso da ranar auren ya yi ya zaftare wajen watanni biyu a ciki wanda hakan ya sanya ta ja bakinta ta yi shiru ta zubawa sarautar Allah idanu..
Har da tsoron kar a bawa Nura ƴartata ne dama ya sanya ta azalzala ta ɗagawa Mallan hankali a kan ya yiwa Nuran aure saboda tun lokacin da ta lura da irin kallon da ya ke yiwa ƴartata hankalinta ya yi masifar tashi kuma ta lura har Abu ya ke siyowa ya bata abunda ba ɗabi’arsa bace ba shiyasa tun kafin ya furta ta so ta yiwa tufkar hanci sai dai abunda ba ta sani ba Nura ya fi ta sammako dan Allah kaɗai ya san kalar shige da fice da makirce-makircen da ya yiyyi aka basa Uwani, dan indai makirci ne da juya kwakwalwar ɗan Adam to tabbas ya ci a bawa Kaka Nura tutar yabo.
Mallan bai kai ga ɗaura musu auren da ya ci buri ba Allah ya karɓi ransa, gajeruwar jinya ta kwana biyu kacal ya yi yace ga garinku, tsabar bala’i irin na Kaka Nura ana kai Mallan makwancinsa ya nemi limamai da dattawan layi da su ɗaura masa aure da Uwani a cewarsa kar Mahaifiyar Uwanin ta dawo dai-dai ta raba abunda Mallan ya so ƙullawa, sun gasgata zancen nasa dan ƙiyayyar Mahaifiyar Uwani ga Kaka Nura a fili take ga kowa! Makwabta da ƴan uwa, yayinda shi kuma manya-manyan mugayen halaiyyarsa su ke a ɓoye, sun shaida kuma sun san Mallan ya bawa Nura Uwani shiyasa suka goya masa baya a ranar sadakar farkon rasuwar Mallan aka ɗaura auren Nura da Uwani a cewarsu sun cikawa Mallan burinsa.
Ga zafin baƙin ciki ga zafin rasuwa, su suka taru suka sanya Mahaifiyar Uwani ta kasa taɓuka komai ta kwanta ciwo ya yi mata ruff ko iya gane waye a kanta ba ta yi dama tunda aka yi rasuwar ta ke kwance, amma a hakan Nura ya ɗagawa kowa hankali ranar sadakar uku Uwani ta tare a gidansa wanda ke a Unguwa Uku mai ɗakuna biyu a jere da banɗaki da kitchen wanda ya tara kuɗi ya siya da kuɗin Allah ya Isa da kuɗin haram da na sata….….
Rigima sosai aka yi da shi aka yi baram-baram tsakanin sa da ƴan uwan Uwani kowa ya fita a harkarsa sai dai kuma tausayin ƙanwarsu bai sa sun janye ba hakanan Yusufa da Ali su ke ɗan leƙata from time to time dan idan akwai wanda ba ta so a kaff faɗin duniyar nan a wannan lokacin har da yanzu ma to Nura ne…..
Bayan aurensa da Uwani ya nuna mata soyayya kwarai dan har ya kai ga sanyawa ta ɗan fara shaƙuwa da shi abunka da zuciyar mace yau da gobe sai Allah miji da mata sai dai kallo wanda kwanciyar hankalin da Mahaifiyar Uwanin ta gani a tattare da ƴartata ne ya sanya ta ɗan kwantar da hankalinta dukda har gobe tun ranar da Kaka Nura ya tattara kayanshi ya tare a Unguwa Uku da Uwani bai taɓa zuwa ya gaishe ta ba amma ta zuba musu ido kuma sam ba ta ƙorafi kullum addu’ar ta Allah ya bawa ƴarta farin ciki da ribar rayuwa, ko a waya bayan waya ta fito har matar ta rasu ba ya kiranta baya kulata kwata-kwata a cewarsa ita ɗin maƙiyiyarsa ce, ita ma kuma ba ta zuwa gidansa sai dai in ta je gidan Baba Yusufa Uwani ta je har chan tukunna su haɗu su ga juna, dan ba ya hana Uwani zuwa chan ɗin ta gaisheta amma shi kam ba ya zuwa, ko gidanta ko gidan Baba Yusufa.
Ƴar soyayyar da ya nuna mata ta iyaka watanni uku ce kacal bayan aurensu da kuma shaƙuwar da suka yi ne ya sanya ta fi shan wahala a lokacin da ya juya mata baya, dan tun da ta rufe watanni ukun nan a gidansa shikenan uƙubarsa da cin mutunci kala-kala su ka ce salama alaikom..
Shekara ɗaya kacal aka ɗauka da yin auren su ya fara mitar shi fa ya ji shiru ko dai juya ce…a cikin shekara ɗayan nan wanda sai da aka ƙara shekar ɗaya da wata takwas tukunna ta ɗauki cikin Anne sai da Kaka Nura ya auri mata har guda biyu kuma matan ta farkon babbar ƙawarta ce ta unguwar, ɗayar kuma ƴar makwabta mai tayata kwana idan ba ya nan..kaff cikinsu ko alamun ciki babu a tare da su har ya sakesu amma a ko da yaushe cewa ya ke yi rashin haihuwar a jikin Uwani ne dan gashi kaff cikin danginta da suka yiyyi aure sau ɗaya tak aka haifi twins (Mustapha da Abbakar) ƴaƴan babban yayanta (Baba Yusufa) sai yanzu da matar ta sake ɗaukar ciki.
Cewa ma yake ita ce ta shafawa ragowar matan da yake aurowa rashin haihuwa sannan tsabar baƙin kishinta ne ya sa suka kasa haihuwa da shi.
Kasancewarsa mutum mai matsanancin son ƴaƴa ya sanya ya rufe ido ya dinga kafta mata ruwan takaici ba dare ba rana.
Ko da aka haifi Zainab Baba Yusuf ya so ya bawa Uwani ita tun da ɗanye cibinta sabida zaman kaɗaici da baƙin cikin da take yi, amman furr Kaka Nura ya ƙi yarda dukda masifar son ya ga Yaro a gidansa amma sai cewa yayi 'shi ya fi son tsattson sa'.. hakanan Uwani ta haƙura ta ci gaba da karɓar uƙuba kala-kala daga garesa gashi a lokacin Mahaifiyarta itama ta rasu dan haka hakanan take naɗar baƙin ciki ita kaɗai…
Gaba ɗaya sai da ya ja mata raina da ƙananun maganganu a wajen makwabta dan hakanan yake bin Yaran layi masu tasowa zawarawa da manyan mata...babu abunda ya shafesa zai kashewa wadda yake tare da ita kuɗi amma ita Uwani dai-dai da kukar kaɗa miya daga gidan Baba Yusufa ake aika mata kuma idan ta dafa ya zauna ya naɗa hankali kwance ya kuma je waje ya zubar da abunda ya tara a ƙadangarun bariki..
Baba Yusufa ya so ya raba auren amma sai Uwani ta ce ya barshi kawai ta ƙarasa a haka ba don komai ba ita kanta ta san ba ta da wani gata yanzun kam, ɗayan yayan nata soja ne a portharcourt ya ke shi kansa ba zama ya ke yi a gidansa ba, zamanta a gidan Baba Garba kuwa ba zai taɓa yiwuwa ba saboda yadda ya tsani mijita itama haka ya ke jin haushinta da kyar ya ke iya amsawa in ta gaishesa tunda ta auri Nura ta yarda ta zauna a gidansa shikenan ƙiyayyar da ya ke yiwa Nuran ta shafeta...gidan Baba Yusufa kuwa yau da gobe sai Allah dan ba wani shiri take da matarsa ba (Yadikko) kasancewarta mace mai son abun mijinta, shiyasa kawai ta zaɓi ta zauna ta ƙarasa a haka duk tsiya ita ɗaya dai ranta a gidan mijinta ta san wuya ba za ta kasheta ba...
Daɗin daɗawa kuma Kaka Nuran ya kafeta ne a gidan saboda ko ba komai ya san ya na morarta duba da yadda Baba Garba da Baba Ali (Yayanta na portharcourt) su ke ciyar da shi da ita, ya san ba duk mace zai samu a yi masa hakan ba.
BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*
HUMAIRAH BULAMA
Yota
*14*
Shekarar Zainab ɗaya a duniya lokacin Kaka Nura ya na tsaka da yiwa Uwani gorin haihuwa kwatsam sai ga cikin Anne ta samu da ikon Allah, dan kowa sai da ya yi mamaki saboda a yadda Kaka Nura ya ke shelar ita ɗin juya ce a Unguwa duk an ɗauka ya je asibiti ne an bashi shedar ba za ta haihu ba.
Kaka Nura har kukan murna sai da ya yi, ya kwana ya na sallar godiya ga Ubangiji ya yi azumi ashirin na godiya sannan ya ɗauki soyayyar duniya ya ɗaurawa cikin. Tun cikin ya na jinjiri dama yake addu'ar Allah ya sa mace za a haifa masa saboda shi a cewarsa idan ya haifi Namiji jidali ne dan kafin ya gama rainon sa ya yi karatu ya fara aiki za a ɗauki lokaci kuma aure zai yi dan haka ba lalle ya ci moriyarsa sosai ba amma idan Allah ya bashi ƴa mace ya san jari ce musamman ma idan Yarinyar ta yo kyawun shi da tsantsar farin jinin shi ya san tabbas kakarsa ta yanke saƙa, shiyasa ya duƙufa addua Allah ya bashi ƴa mace.
Tabbas Kaka Nura ya na son haihuwa kuma ya na son ƴa mace amma bayan an haifi Anne da ya ɗauketa ya san ita ɗin fa tashi ce anan soyayyarta ta nunku a cikin zuciyarsa fiye da tunanin mai karatu, ba yadda ba a yi da shi akan ya bari a saka mata wani sunan ba amma ya ce sunanta ‘Nuratu’, Nuratu Muhammad Nura..dan ko a suna ba ya ƙaunar abunda zai banbamta su.
Dama tun asali Kaka Nura ya kasance mutum mai tsananin son abunsa nan take gaba ɗaya tunda aka haifi Anne komai nashi ya sake fitowa fili kwata-kwata ba shi da kara a duk abunda ya shafe ta, ba kalar cin mutunci da zagin da Uwani ba ta fuskanta a duk lokacin da ya shigo ya tarar Anne ta na kuka…
Kai tsaye sannan tashi ɗaya za a saka Kaka Nura a cikin jerin talakawa amma tunda aka Haifa masa Anne aka fara cin abinci na gani na faɗa a gidansa saboda ruwan Nono, kalar kayan jikin Yarinyar kuwa abun kallo ne, ko kyalle bai siya ya bawa Uwani ba amma Anne kam sai da ya yi mata akwati uku duk wani abu da aka san Jariri zai buƙata babu wanda Kaka Nura bai siya ya ajjiye ba. Cs aka yiwa Uwani saboda ba zata iya haihuwa ba amma sam Kaka Nura bai damu da magani ko lafiyar ta ba shi dai kawai komai ƴarsa.
Gobara ce ta rabo su daga Unguwa Uku, ta inda gidan ya ƙone ƙurmus to the ground su kansu da kyar su ka fita, daga nan su ka bar Unguwa Uku su ka koma Mariri da zama lokacin tun bata kafu ba gidan Baba Yusufa, inda ya ware musu ɗakuna biyu ya zagaye a cikin gidansa suka zauna.
Baba Yusufa shima ba wani mai kuɗi bane ba, ya na da dai rufin asiri kuma ƴaƴansa biyu ne a gabansa dan Abbakar tun ya na ƙarami ya ke makarantar sojoji (a wajen ƙanin mahaifin nasa) wanda hakan ya kasance burinsa ne, dan haka Zainab da Mustapha ne kawai a gabansa sai matarsa guda ɗaya Yadikko shiyasa ba shi da wani nauyi sosai.....
Gidan nasa irin gida ne mai babban fili dan tun ana yankar fili da daraja a Unguwar ya yanka, su ne farko-farkon Unguwar. Hakan ya sa bayan gidansu Anne ya ƙone ƙurmus ya yi ƙoƙari ya gina ciki da parlour da toilet da kitchen a wawware ya zagaye musu, ita Uwani ma ta ɗauka a cikin kuɗin rabon gadonta wanda ke hannunsa ya yi mata ginin sai da ta tare ya bata kuɗinta a hannunta ya ce ta ja jari tukunna ta san tsantsar zumunci da so da tausayinta ne ya sanyashi yin hakan.
Dukda cewa a wannan lokacin ko kuɗin hayan gidan wanka Kaka Nura bashi da ikon biya amma sai da aka kai ruwa rana da shi ya kakkafa sharuɗansa tukunna ya yarda ya biyota aka tare a gidan da shi ya na ta kumbure-kumbure haka itama matar Baba Yusufa (Yadikko) ba kaɗan ba ta ɗaga masa hankali ta yi ta bori kafin daga baya komai ya ɗan lafa dan daga ita har Kaka Nura babu wanda ya tanka su….
Tun a kan Zainab da Anne Kaka Nura ya fara bawa al’umma mamaki da tsoro saboda ƙiri-ƙiri irin abun nan na Yara idan Zainab ta daketa muddin idanunsa suka gani to fa haka nan zai zage ya ɗaɗɗaka mata duka a cewarsa ai ta girmi Annen saboda ita Anne a lokacin shekararta ɗaya ita kuma Zainab ta doshi uku…Abun Yaro sai da ta kai ta kawo Zainab ta daina shigowa shashensu Anne ko Mustapha ya shigo da ita a hannu to fa ta dinga tsala ihu har sai an fitar da ita dan sosai Kaka Nura ya ke makarta ko bige Anne ne idan ta yi ba tare da sanin ta ba sai ta karɓi hukunci gashi kullum ya na gida dan zuwa lokacin ko ƴar kasuwar da ya ke zuwa ya daina a cewarsa shekaru sun ja mutumin da ko talatin bai rufe ba, tunda aka bawa Uwani jarinta idanunsa su ka gani ta fara sayarda gumama shikenan ya koma ya zauna ya naɗe hannuwansa ta ke yi musu komai, ƙarƙari idan aljihunsa ya yi ƙasa ya ɗauki asusunta ya fasa ya siyamusu kayan maƙulashe shi da ƴarsa kuma Uwanin ba ta Isa ta yi magana ba idan kuma buƙatar auren sa ta motsa hakanan zai ɗagawa kowa hankali da roƙo da bashi da kuɗin Allah ya Isa zai
haɗa ya yi…dan zuwa wannan lokacin Alhamdulillah tunda aka Haifa masa Anne ya daina neman mata ammafa aure-aure kamar an ce masa bismillah!
Hakanan zai tara ƴan kuɗaɗe da kyar ya kama haya ya yi sabon aure su tare, tare da shi da Amarya da Anne.
To dai tun bayan haihuwar Anne gaskiya kusan duk itace ta ke kashewa Kaka Nura aure, wanda a da halinsa ne amma fa tunda aka haifeta duk aurarrakinsa ita ce silar mutuwarsu…shi dama Kaka Nura ba ya aikin fari balle na baƙi kuma tunda Anne ta kai shekaru uku tun a zance ma tare ya ke zuwa da ita dan kullum