Showing 33001 words to 36000 words out of 100561 words
tana hannunsa maƙal-maƙal.
Da zarar ya yi aure a tare ya ke tarewa a gidan da ita ranar da amaryar ta tare sai an lallaɓata ta ci kaza ta ƙoshi ta yi barci an kaita ɗaki tukunna ake samun lokacin amarya, mai kirsa itace ta ke iya tolerating Anne a gidan na sati ɗaya mara kirsa mara haƙuri kuwa tun a ranar farko ake fara gani a kan fuskarta…..
Ba wai saboda tarairaya ko fifikon da Kaka Nura ya ke nunawa Anne ne silar janyo matansa jin haushinta ba, sam abun ba haka ya ke ba…
Ita dai Anne tun ta na Yarinya kwata-kwata ba ta san wani abu wai shi tsoro ba, dan tun ta na jaririya ko irin ƙarar nan ko tsawa kwata-kwata basa firgitata duk wani abu dai da za a ce ya na bawa jariri ko Yaro tsoro to sam ba sa bawa Anne tsoro, da ta taso kuma ta fara takawa tana daɗa wayo ko horo film ake kallo a talabijin manya da Yara su na rurrufe idanuwa ita kuwa nata idanun ƙurr!! Har sai ta ga kwal uwar daka..ta kan ji ɗar!! Idan kallon ya yi abun tsoro na fitar hankali amma ba dai tsoro ba.
A zahiri a real life kuwa babu abunda ya ke sakata ta ji ɗarr ɗin, sam babu shi!!.
Abu na biyu kuma game da Anne wanda shima da shi aka haifeta shine tsaurin ido, na farko bata jin tsoron mutum ko aljan ko wani abu a duniyar nan abu na biyu kuma shine tsaurin ido, duk girman Mutum Babba ko Yaro wuyarta ya taɓa mata abunta ko ya shiga sabgarta to fa ko tsayinta bai kai ba sai ta hau kan abu ta maresa idan kuma bata samu fuska ba to za ta daki duk inda ta samu kuma ba ta mantuwa sannan ba ta yafiya…
Abu kuwa indai har ta na so ranta na so to fa a bata ko kar a bata zata saka hannu ne ta ɗauka duk yawan harara ko zare idon mutum wannan sam ba damuwarta baceba idanun mutum ne za su yi masa ciwo a banza, kuma idan ka dake ta ta rama, idan akaci galaba a kanta kuma a fuskanci tujara da bala’in Kaka Nura...
Lokacin da ta ta fara baki kuwa tsaff ta ke haɗawa mutum har da zagi hakanan zata zubo maka ashar ɗin da zai ɗaure maka kai dan kafin ka gama lissafi da fahimtar ashar ɗin ya baka ma’ana ma ta yi gaba abunta….tsiwa da masifa kuwa a jinin Anne su ke tun ta na Yarinya, da ta taso ta fara wayo kuwa kwata-kwata ba’a cin galaba a kanta a cacar baki sai dai a bar mata .
Anne bata san defeat ba sannan ba ta san a fi ta ba, ga masifaffen kishi wanda tun ta na Yarinya ba ta so ko a kalar fata ta ga wadda ta fi tata kyau...
Duk girman mutum Anne bata san ta kirashi da Yaya, Baba ko Anty ba! Hatta Uwar da ta haifeta da Dije ta ke kiranta Mahaifinta kuma Nura sai da ta kai shekaru biyar ne ya ci sa’a ta ke kiransa da Baba Mahaifiyarta kuma ta mayar Uwani kamar yadda ta ji yayanta(ita Uwanin) ya na kiranta da shi amma shi kanshi mai gidan yayan nata da Yusufa ta ke kiranshi matarshi Yadikko kuma Mairo, idan ƴaƴanta suka dake ta a kwana ana bala’i da su, ita da Ubanta...
Gashi a duniyar nan ko Anne za ta tsolewa Sarki ido to fa sai dai
a haɗa da ita da Kaka Nura a tsire dan sam ba zai taɓa yarda ƴarsa ta yi laifi ba, shiyasa ta ke kashe masa aure cikin sauƙi saboda dukda kasancewarta Yarinya amma ta na da wani matsanacin kishi da ta ma fi Uwarta takaicin ganin ta ga ya yi aure sai dai kuma bata taɓa nuna mishi ba tunda ta yi wayo sai dai ta bi cikin sauƙi da kirsa kamar wata babba ta kashe auren murus, dan tun ta na ƙarama ma hakan ce ta ke faruwa ko kallonta matar ta yi haka za ta yi ta tsala ihu shi kuma ya ce 'an yi mata wani abun ne, ai ba zata yi ihu haka kurum ba ba haka take yi a gida ba.' Har tsoro matan nasa su ke yi su kasance a guri daga
su sai ita dan sun san ranar alƙiyamarsu ta tsaya kenan...
Wasu kuma fushi su ke yi su yi yaji su tafi shi kuwa dama bai taɓa biko ba, wasu kuma da ita da shi ɗin ne su ke yin yajin sai dai kawai Matar ta ga takarda daga baya.
Duk a cikin ɗabi’un Anne
Uwani ta fi jin takaicin ƙarya da makircinta dan ko shekaru bakwai bata rufa ba ƙarya da makircinta su ka baiyyana a idanun kowa ɓaro-ɓaro, kamar wata babba idan ta yi wani abun gashi ko harara idan Uwani ta yi mata haka nan itama zata zage ta rama kuma ta gayawa Baba ranar ya kwana yana ife-ifen sababi an hararar masa ƴa an takura mata ita da gidan Ubanta...
Duka kuwa ko bayanan idan ta dake ta ya dawo nan zata gaya masa shi
kuma ya riƙe Uwanin Anne ta rama, wannan tashin hankalin ne ya sanya kwata-kwata Uwani ba ta gigin dukanta dan tun lokacin da ya yi mata irin hakan har sau uku tun Annen bata ma gama wayo
ba shikenan ita kuma
Uwani ta shafawa kanta lafiya..maganin bari kar a soma.
Sosai Anne ta raina Uwani kamar kashin gindinta ba ta jin maganarta ba ta sassauta mata ko aike sai taga dama idan tanada gurin biyawa tukunna idan da kanta ta ce mata ta kawo ta je mata to fa shine Uwanin ta ke samun ikon aiken ƴartata…
BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*
HUMAIRAH BULAMA
Yota
*15*
Batun Makaranta kuwa tunda Anne ta nuna ba ta son islamiyya Kaka Nura ya ce ba a dole zai koya mata karatun sallar a gida.
Boko kuwa sau shidda ya na chanja mata makaranta, Ana korarta..
In ta tashi yin dambe wani zubin har da reza ta ke yi a ɓoye dan ba za a tashi fahimtar akwai rezar a hannunta ba har sai ta soma kakkarta fuskar Yaro ko Yarinya, shiyasa ta na aikata hakan ake korarta, yayinda wasu makarantun kuma su ke ƙin ɗaukarta.
Last makarantar da aka koreta kuwa repeating ne aka yi mata Kaka Nura ya ce ba su isa ba, dan ta ce masa ba za ta zauna a ajin Yara ba
shima kuma a nasa ganin repeating ɗin cin fuska ne shiyasa ya je ya na ta hayagagar a saka ta a class ɗin gaba ta tafi tare ita da sa'o'inta ƴan ajinta...
Kuma fa hatta ajin bayan ajin da aka yi mata repeating ɗin zuwa cikinsa da aka gwadata 2/70 ta ci a test ɗin shiga ajin, shiyasa su ka koreta daga makarantar cikin aminci saboda dama da kyar suma ɗin aka samu su ka karɓeta kuma kusan duk malaman haushinta su ke ji bayan ta shiga makarantar saboda in ana neman daƙiƙiya lamba ɗaya to Anne ce! Ga rashin kunya ga mugunta ga dambe da Yara, kuma duk wani salon iskanci, raina malamai da iya shege duk ita ta ke koyawa Yaran...
Gashi kwata-kwata ba ta maida hankali ballantana ta samu ta tsinci wani abun dukda kuwa abun da kamar wuya dan kwakwalwar Anne da karatu kamar rubutu ne a kan ruwa ana yi ya na gogewa....
Amma wani ikon Allah waƙa kam tsaf ta ke haddaceta ta zauna a harshe da kwakwalwarta daram! Dan in ta na rera waƙa kamar wata zabiya musamman in ta soyayya ce! Haka nan za ta ke rerota tsaf! A-Z har da ƙarin shauƙi da karkashe murya.......
Shiyasa ta ke zaman gida yanzun yayinda Kaka Nura ya ke ta fafutukar ganin ya nema mata gurbin karatu a wata makatantar, dan daga ita har shi su na so ta samu ilimin boko saboda a tasu kalar fahimtar shi zai sanya ta sake wayewa.
Sannan a kullum ya na jin takaicin yadda waenda ya yi secondary da su su ke da rufinɗ asiri amma shi bai da shi wanda a ganinsa bokon da su ka ci gaba da yi ne sila dan shi bai ci gaba ba kuma girman kai da son jiki sun hana su barshi ya ci gaba...amma ita Anne ta nuna masa ta na son boko sosai shiyasa ya ke so ya cika mata burinta...
Kuma dama gani ya ke yi rashin karatun da bai yi ba ne ba ya sanya shi bai samu rufin asiri irin nasu ba ba wai zanen ƙaddararsa ce hakan ba.
Ga shi duk sun san halinsa ba mai kyau ba ne ba shiyasa ko wata sana'a in ta taso ba sa saka shi a ciki..ƙarƙari in ya yi roƙo su bashi in sun ga dama dan sun san ya na barin inda su ke ya ke zaginsu zagi na cin mutunci da ɓatanci, saboda shi Kaka Nura a tsarin rayuwarsa ma kowa ya shaida ya fi cin mutuncin wanda ya tausaya sannan ya taimaka masa.
Akwai wata ranar da Uwani ta aiketa ta kai mata ƙuɗin adashenta...
Ita kuma Anne ta kashe kuɗin tass! Dama neman kuɗi ta ke yi a lokacin kuma ta ga Anne ta na neman ɗan aike dan haka ta amshe ta ce za ta je.
A lokacin shekarunta ba su kai goma sha biyu ba amma Hakanan ta siyawa saurayinta biscuit da alawa kala-kala na wajen ɗari biyar ta kai masa su ka sha zancensu a bayan gidansu Yaron tukunna ta koma gida.
Ta na shiga ko kallo Uwani ba ta isheta ba, ta ce mata "kuɗinki sun zube! Na yi neman duniya ban gani ba"
Daga haka ta shige daƙi ta barta a tsaye a wajen cikin matsanancin ɓacin rai, dan da mugun kyar ta iya haɗa kan kuɗin saboda ita da Ubanta.
Anne ba ta kai ga kwanciya a ɗakin da ta shige ba ta fara jiyo sallama!.....
Ba kowa bace illa Mahaifiyar Yaron, Yaron da biscuit da alewarsa tuli fuskar Yaron dagaje-dagaje kana gani ka san ya daku ya sha kuka…
Ko gaisuwar kirki Mahaifiyar Yaron ba ta bari ta yi da Uwani ba ta shiga zaiyyano mata zantuka tiryan-tiryan...haka nan ta zaiyyane wa Uwani cewa 'soyayya Anne da Yaron su ke yi tun a makaranta, to kasancewar ita Annen an koreta a makarantar ya sanya yanzu ta ke binsa har gida, har da su biscuit da alawa kuma yayan Yaron ya ce ya na ganinsu kusan kullum dan lokaci su ka ware su ke haɗuwa shiyasa ya saka ido, in ta je har rungume juna su ke yi kafin su rabu da wasu abubuwan da ba su dace ba…'
Saboda ita dai Anne ta koyi abubuwa bilaadadin daga wajen Baba da matayensa dan
tun ranar da ta taɓa farkawa ta gansu shikenan ta koyi yin barcin ƙarya…Tun abun ya na bata mamaki har ta fahimci komai da kuma dalilin da ya sanya ake yin hakan.
Cikin ɓacin rai Anne ta yi tsalle ta fito daga ɗaki cike da tsantsar rashin kunya ta kalli matar ta ce mata "yanzu da ki ka zo ki na zaiyyane mata aka gaya miki yanka ni za ta yi? Allah na tuba ai soyayya halak ce ba haram ba duk ku biyun da kuka tsaya ku na ta faman munafurcinmu inda babu soyayya ai da ba ku yi auren kun yi cikin da kuka haife mu ba!!!"
Shiruuu duk su biyun su ka yi jikin kowacce ya yi sanyi musamman Uwani wadda ta fara hawaye a take.
Ko a jikin Anne! Hakanan ta zuba tsaki
sannan ta sake cewa "a bar sawa mutum ido bashida amfani kuma a daina munafurci, soyayya kam yanzu na fara babu uban wanda ya Isa ya hana ni"
Da sauri Yaron ya matso jikinsa ya na karkarwa ya jefa mata ledar biscuits ɗin ya ce "ni kam babu ruwana dake kar ki sake kulani"
Sai kuma ya juya ya kalli Mahaifiyar tasa ya ce "Mama dan Allah ki yi haƙuri ki zo mu tafi kema kar ki yi kuka…”
Wani irin kuka Uwani ta fashe da shi wanda hakan ya sa matar ta yi saurin juyawa ta fita riƙe da hannun Yaron da sauri dan baƙin ciki da tausayin Uwani tsaff za su saka ta rufe Nuratu da duka kuma sarai ta san halin Ubanta..
Shiyasa kawai ta tafi tun kafin ta jangalo abunda za’a yi ta ce-ce-ku-ce.
Duk haƙurin Uwani ranar kasa jurewa ta yi dan matar nan ta na fita ta finciko Anne ta rufeta da duka…
Tsoro da dana sani su ne su ke sanya Yaro yin laushi a duk lokacin da na gaba da shi ya ke hukunta shi wanda sam Anne ba ta ji wannan tsoron ko
dana sanin ba dan ba ta san ma ya ake yin su ba dama chan...
In banda wani baƙin ciki da tuƙuƙi babu abunda zuciyarta ta ke yi shiyasa har ta samu ƙarfi da damar hankaɗe Uwani ta faɗi zaune daɓass a wajen, ba ta gama dawowa dai-dai ba Anne ta taƙarƙare ta kifa mata mari….
Dukda haka marin da ta yi mata bai isheta ba dan so ta yi ta rarumo abu ta maka mata saboda hakan ta ke yiwa duk wanda ya fi ta girma a yayin faɗa, amma da ikon Allah yadda Uwanin ta kafeta da idanu ta dafe ƙuncinta jikinta da bakinta su na rawa duk sai ta ji ta kasa aikata abunda ta yi niyya a gareta….a hankali idanuwanta (Uwani) su ka soma ƙaƙƙafewa kafin ta tafi luuu ta zube a wajen ta na wani kalar sassanƙarewa dai-dai nan Zainab wadda itama ba ta daɗe da shigowa ba shock ya hanata motsi ta rafka uban salati ta fashe da kuka ta yi kan Uwani da gudu.
Salatin nata ne ya janyo hankalin ƴan gidan gaba ɗaya dan duk su na tsakar gida a ta dalilin ziyarar bazata da Baba Ali ya kawo shi da matarsa da mahaifin matarsa (wanda ya kasance amini ga mahaifinsu lokacin da ya ke raye) da Abbakar...
Wanda abunda ya kawo Zainab ɗin ma kenan, kiran Uwani ta zo yi.
Gaba ɗayan su cikin sashen nasuu Uwanin su ka yo, ganinta a kwance a sanƙare ya sanya Abbakar, Mustapha da matar Baba Ali su ka yi kanta a gigice yayinda Su Yadikko su ka shiga tambayar ba'asi ita da su Baba Ali hankalinsu a masifar tashe...
Zainab ce ta sanar musu abunda ya faru wanda hakan ya sa duk suka ɗago su na kallon Anne da mugun mamaki kafin Baba Ali ya yi kanta a zuciye Mahaifin Matar tasa ya yi saurin ruƙosa saboda tshohon ya kasance mutum mai kawaici da tsananin haƙuri.
Duk wannan hayya-hayyar da su ke yi Anne ta na nan kyam a tsaye ko gezau bata yi ba ga dai mutum dattijo da khaki a jikinsa ya na shirin damƙarta amma sam bai ba ta tsoro ba.
Shiruu duk su ka yi, kafin su Abbakar su shiga cewa "bara a kaita asibiti" da ƙoƙarin ganin sun kinkimeta...
Baba Yusufa ne ya ce su jira ya nemo abun hawa dan motar da ta kawo su Baba Ali ta tafi shan mai, dan haka su ka dakata yayinda shi kuma ya fita da sauri jikinsa ya na karkarwar tashin hankali sosai.
Tsohon mutumin nan kuwa ya rasa ma ta cewa dan ya yunƙura ya fi sau biyar da niyyar yin magana amma sai yagagara dan abun ya girme masa matuƙa, tsabar al'ajabi da takaici a take jikinsa ya soma karkarwa, ya na tari ƙasa-ƙasa.
Tsaki Anne ta yi, ta ce "kana fama da tsufa, amma ba za ka zauna a inda Allah ya ajjiye ka ba, uban meye ya tado ka tun daga wani gari ya kawoka nan? Da ka zo nan ɗin ma ba ka tsaya a inda ka kawo ziyara ba ka leƙo munafurci sashen wasu!. To dan ka ji..karkarwa da tari yanzu ka fara."
Cikin ɓacin rai Baba Ali ya ke kallon Yarinyar wadda a yadda ya ke kallon nata ita kanta ta san ji yake yi kamar ya yi mata dukan mutuwa amma kuma babu damar yin hakan dan Mahaifin Matarsa ya hanashi….
Cikin fushi yace “duk iskancinki da rashin ɗa’ar ki ya tsaya iyaka kan iyayenki kar ki kuskura ki sako mini nawa iyayen a ciki! Shegiyar Yarinya mai kama da aljanu…"
Cikin tarar numfashinsa ta ce "eh lalle daɗin zama mai sa a ce da mijin iya Baba, ni dae na san shi ɗin uban matarka ne ba ubanka ba.
Aikin banza aikin wofi!! Zancen banza wanda yake fitowa daga bakin mutanen banza ma kenan!!"
Zaro ido sosai ya yi amma bata damu ba ta ci gaba da cewa” Ina ce da ƙafafunku ku ka shigo ba wani ne ya gaiyyotoku ba?
Me ya kawoku inda nake da har za ku tsomawa mutane Baki da har Uban naka na kale zai fara tarin ƙarya da ƙarairayi??? Bari ka ji to ko a shari'a duk abunda na yi muku ba ni da laifi tunda kune ku ka shigo har cikin gidana, gaiyyar wahala ƴan *****uba kawai!!!!"
Ba ta ga ƙarasowar sa ba sai Uban Marin da ya kifeta da shi ne ya sanar mata ƙarasowar tasa..dan duk yadda ya so yiwa Mahaifin Matar tasa biyayya wajen ƙin taɓata abun gagararsa ya yi.
Dai-dai kuwa lokacin da ya mareta Kaka Nura ya turo ƙofa ya shigo Marin ya faru a kan idanunsa!.
Anne ta na ganin Kaka Nura ya shigo; su na haɗa idanu da shi, ta kurma uban ihu ta kwanta a wajen ta fara birgima….
Cikin tsananin ɓacin rai Baba Ali wanda bai lura da shigowar Kaka Nura ba dan shi baya ya bashi, ya ce "Bari ki ji abunda baki sani ba nan ɗin ba gidanku bane ba dan Ubanki!
Da ke da Uban naki baku aka yi kyauta babu ko sisin kwabonku ballanta ki yiwa mutane tunƙaho!!!
Shegiyar Yarinya marar..."
Muryar Kaka Nura ce ta katsesa ta inda ya ke cewa "Na