Showing 54001 words to 57000 words out of 100561 words

Chapter 19 - BAKAR TUKUNYA hausa novel

07 Feb 2026

465

na sayar da fetir kuma cikin dare ne incidence ɗin ya faru so gaba ɗaya galolinsa su na ciki dan haka wutar da ta shiga gidansu(mai sayar da fetir ɗin) sai da ta cinye komai aka kasa kashewa mutane ma da kyar a ka fidda wasu dama wasu already sun fito tun da su ka ji hayaƙi... Sannan ta kama gidaje huɗu suma duk ta yi musu rauni ba na wasa ba, ciki har da gidan yawa inda mutum biyu ne kawai suka cika ragowar kuma su na kwance su na jinya sosai.
Sarai Nuratu ta ji kuma ta ga abinda ganganci da son zuciyarta su ka janyo, amma ko a jikinta! Dukda ita har ga Allah mutum ɗaya ta so kashewa hakan bai sa ta ji wani abu mai kama da rashin jin daɗi ko ɗarr game da yadda abun ya shafi mutane da yawa ba.

Rashin ganin Uwani da ta kasance mutum ɗaya da ba a gani ba ya sanya kowa ya shaida ita ce ta kunna wutar ta gudu ko kuma dai itama ta mutu ne a cikin wutar, sannan duba da yadda a shekarun baya ta ke kuka da ita kanta Nuratu da Nuran kafin yanzu da ta ke goyon bayansu ido rufe da aka kasa gane kanta ya sanya aka sake tabbatarwa tabbas ita ce ta so ta kashe kowa God knows y! Yayinda waensu su ka bada tabbacin ciwon hauka gareta shiyasa ta yi hakan.
Hankalin Kaka Nura a kwance dan ya sanar mata cewa "ita ake zargi dan haka ta tsaya a nan inda ya kaita case ya ɗan lafa tukunna" dan haka ya san ba za ta yarda ta baiyyana kanta ba, shiyasa ya ke jinsa wasai da daɗin yadda abubuwa su ke tafiyar masa yadda ya ke so.
Uwani ta so ta je ta tona musu asiri amma ko da ta kusanto Unguwar da labarinta ta fara cin karo a bakin mai machine ɗin da ya ɗauketa, dan ta na hawa ya soma bata labarin wata mata Uwani wadda ta yi sanaddiyar mutuwar mutane biyar da raunata mutane kusan ashirin, ya na ta tsine mata, kuma ta ji ana nemanta ruwa a jallo daga bakinsa shiyasa ta ji tsoro kawai ta haƙura ta koma dan ta san Nuratu da Nura
Allah kaɗai ya san me da me suka sake gayawa mutane har ake ta nemanta da zarginta haka...
Ita kam a wannan lokacin yadda ƴar da ta kawo duniya ta barta cikin wuta domin ta mutu ne ya sake hautsina mata lissafinta shiyasa ta ma rasa kuzarin yin komai kawai ta haƙura ta koma ta zauna a inda Nura ya kaita.

Neman duniya aka rasa Uwani ko ta yadda za a fara nemanta ma shiyasa kawai aka yi concluding akan ta mutu ne a cikin gidan dan banɗaki da kitchen ƙurmus su ka yi sosai ta inda aka kasa gane meye da meye ma a cikinsu, kuma Kaka Nura ya basu tabbacin banɗakin ta nufa lokacin da abun ke faruwa.

Yadikko kuwa azabar mutuwar da aka yi mata a jere ce ta sanya ta samu taɓin hankali wanda hakan ya dasa tausayinta kwarai a cikin zuƙatan mutane yayinda aka ci gaba da zagin Uwani, dukda zuwa wannan lokacin kowa ya na tunanin ta mutu ne amma hakan bai sa sun yi mata fatan rahama ba.


Da ikon Allah Yadikko ta na fita daga takaba yayanta guda da ya yi ragowa ya zo aka ɗaura musu aure ita da Kaka Nura babu hayaniya, ƴan Unguwa kuwa dukda a mahaukaciyar ta ya aureta cewa su ke yi tabbas an cuceta..

Kowa ya yarda an shaida Uwani ce ta kunna wutar nan sai dai ba a ja shariah ba tunda babu ita ana ma tunanin ta mutu ne itama a cikin wutar dan haka case ya mutu.

Habu shima da kansa bayan watanni uku lokacin da ya ga cikin Nuratu har ya fara tasawa ya ce ya ji ya gani a take a ka ɗaura musu aure zuciyoyin ƴan Unguwa fal takaici saboda sun san Nura da ƴaarsa Annoba ne amma tunda har su suka ce sun yarda a rufawa juna asiri shikenan
Abun na Habu ma ya fi damun kowa dan in banda ƴan gidan ba kowa ne ya san Nuratu na da cikinsa ba
An dai san an kamasu tare anmma ba a san abun har da su shigar ciki ba….


Kamar yadda Nuratu ta so sai da ta san yadda ta yi ta maƙalawa Yadikko shaye-shaye dan bayan ta auri ɗanta ita ke jinyar ta da bata magunguna ta nan ta dinga ɗura mata tun Yadikko bata iya ba har ta koya
yayinda Nura shima ya ke kula da ita ta tashi kalar kulawar dan ko ta na tashar barci ko tsaka da ciwo muddin buƙatarsa ta taso haka nan zai sauƙe ya ci gaba da sabgar gabansa...
Tunda ya aureta babu rigima babu faɗa kuma ko ɗanta surukiinsa (Habu) shima an ci sa'a ya ɗaga masa ƙafa batun kotu dama tunda ya auri Nuratu aka janye, ana zaman lafiya da shi kawai dai halaiyyarsa ce ta na nan daram da kuma shekaru su ka fara jaa sai ya dawo da halaiyyarsa ta neman mata itama har ta fi ta da! Dan dama Ƴadikko ta girme masa nesa ba kusa ba...
Haka nan zai ɗura mata kwaya ya kawo mace har cikin ɗakin ya yi abunda zai yi ya gama tana ta uban barci…
Dan dukda neman sa’a da bin Malaman da su ke yi shi da ƴarsa hakanan tun rasuwar Baba Yusufa su ka tsiyace talauchi ya yi musu sallama shiyasa ko kuɗin Ɗaki da hotel ba ya iya kamawa.
Anne kanta da take fita take karuwancinta da auren Habu a kanta kuɗiin in ta samo sai dai su ci abinci ragowar ta bi Malamai da bokaye.


Gidan nan dai na Mariri nan suka share su ka zauna, su na ciki a hankali aka dinga gyarawa su ka gaje shi har gobe in an tasa maganar sai an yi bala’i da su akan gidan.
Ba dai su isa su koresu ba dan Mai Unguwa ya ce gida na Habu da Adda ne amma iko, isa da mallaka kam su na ganinsa ganin idanunsu.

Tsakaninta da maƙoftansu kuwa da ƴan Unguwar sai dai kallo dan babu wanda ya ke shiga harkarta saboda yawanci duk an santa sabili da almost all gidajen arear na gadone so ƴaƴa ne su ka gaje daga wajen iyayensu su ke zaune a ciki (kamar dai su ma) shiyasanya labarinta ya ke nan daram a rayukansu ita da Ubanta, sabbin zuwa kuwa waenda ba su san wacece ita ba ko sun shigewa juna to fa ba a sati ana daɗi da ita dan ita dai Anne ko zaman minti kaɗan in ta yi da mutum to fa sai ta cucesa…
Mazajen layin nan kuwa masu kalle-kalle da bin mata babu wanda bai san Anne a macenta ba, wani ma in ta shiga gidan mace ta ga Mijinta da kanta ta ke kai masa tayin kanta!
Gashi a yi magana ita da ubanta su kusan tashin unguwar da bala’i dan Anne akwai farin jinin maza tsaf sai ta saka mutum a cell.
Zata iya kwana a waje ta na ife-ife da zage-zage da Habaici kala-kala wanda shine mai sauƙin ciki dan in hau ɗinta ya tashi da gasken gaske sunan mutum ta ke kamawa ta zage tass, jifa kuwa a wajen Anne abun ya ɓaci, akan abunda bai kai ya kawo ba ma sai ta yiwa mutum asiri, shiyasa kowa ya ke tsoronta ya ke gudunta.

Wannan dalili ya sanya yanzu haka dae a unguwar ba ta da gidan zuwa dan ko ta shiga sai dai a yi ta mata yaƙe ana Allah Allah ta fita, dan faɗa da Anne kam kai tsaye za a ce kaff arear tasu kowa tsoronta ya ke ji, ita da Kaka Nura.


Watannin auren Anne da Baba Habu bakwai cif-cif ta haifi ɗanta kyakkyawan Yaro ya ci sunan Baba Yusufa ake kiranshi da Amir...
Inda Likitoci da shi (Baba Habu) duk su ka tabbatar da ɗan watanninsa bakwai (bakwaini ne) saboda shi dai ya san ya ganta ta na period ko bayan aurensu da sati ɗaya...
Kwata-kwata Baba Habu bai san menene daɗin aureba, dan a fuska da jiki ne kawai Anne ta ke da kyawu amma bayaga mugayen halayenta mabambanta ko irin ɗumin jikin nan na mata babu shi a tare da ita, sannan baya neman mata bai taɓa yi ba amma tabbas ya san Anne ta na cikin mata masu ƙarancin ni’ima gata da shegiyar jaraba! Dan ko wata ba a yi da auren ba ita dai kullum mitarta 'ba ya gamsar da ita!'
Sannan ko Mahaukaci in ya kusanci Anne ya san ta san maza fiye da tunanin mai tunani dukda kuwa ta na gyara sosai amma duk a banza.
Gashi tunda ya aureta kamar ya auri karayar arziƙinsa ne komai ya tsaya masa chak!
Abunda ya tara da business ɗin da ya ke yi duk su ka taɓarɓare!
A ranar aka koresa daga aikin soja dan a yadda bincike ya basu an ce shine ya kashe iyayensa da ɗan uwansa domin ya aure budurwarsa(ɗan uwan nasa) dan haka ba shi da adalcin da za a basa amanar ƙasa da mutan cikinta.
Gashi ta na shiga gidan watanta bakwai cif ta haihu dan haka sai nauyin ya ƙaru a kansa, ga Yadikko
Itama wadda jima’in aurene kawai ya ke haɗata da Kaka Nura baya ga haka duk kuɗin maganinta da cin ta suturarta komai Habu ɗin ne sannan ga Adda itama..wadda Yadikko da Anne su ka sako a gaba!.

A lokacin Anne ta asirce kowa ta mallake kowa a gidan sai abunda ta ce, hatta Kaka Nura bata barshi ba sai da ta yi masa aikin mallaka shiyasa in ta yi magana kamar faɗar Allah jikinsu har rawa ya ke yi wajen saurin ganin sun yi mata yadda ta ke so.

Shiyasa Baba Habu ya sha wahala matuƙa!
Dan masifar talauchin da ya shiga ba a magana saboda har kamar bara ya ke yi a gidajen makwaftansa dan Anne ba ta san a ce mata babu ba! Ba ta jin wannan Yaren...


Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING*
Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING*
Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139*

Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudin ku tested and trusted.

Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu....
location:Kano
Delivery:NationWide.
kar ku bari a baku labari, sai kunzo🙏
SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA

BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*

HUMAIRAH BULAMA

Yota

*23*


Ƴaƴa huɗu kawai ta Haifa daga su ta tsaya dan a cewarta 'ba ta ga guri ba'.
Tsakanin ƴaƴan babu wani tazara sosai, dan haka jikinta sam bai wani nuna tsufa ba wanda gigin hakan ya sanya ta bazama duniya ta lalace kwarai da gaske dan ɓarnar da Anne ta ke tafkawa da auren nata ba ta yi a lokacin da ta ke budurwa ba ma, kawai dai shi wannan ta na ɓoyewa sosai, ko ba komai ta na son Baba Habu wanda ƙaddarar abunda ba ta so ɗin (talauchi) da kuma son da ta ke yi masa ne su ka kafeta a gidan nasa dan tun da ta shigo ta ga ya tsiyace ta so ta fece amma sai Allah ya nuna mata iyakarta har gobe ta ke rayuwa a hakan.
Sai dai fa ya na ganin ikon Allah dan bai isa ya sa ko ya hana ba...
Ta na dai ciyar da gidan wanda hakan ya ƙara mata ƙarfin iko...
Har hana Adda abinci ta ke yi duk ranar da ta yi gigin yi mata musu.

Zuwan su Yagwalgwal Unguwar ne ya ɗan ɗauke idanun jama'a daga kan Anne su ka mayar a kan su Yagwalgwal ɗin su na masu mamakin hali da tsaurin ido irin na mutanen dan haka sai su ka zama topic ɗin ƴan Unguwar a ko da yaushe zancensu ake yi shiyasa Anne ta ɗan yi sanyi da ido ya ragu a kanta.


Amir dama shi ta fara Haifa
Sai Aliya
Sai Afra sai Auta Amal...
Ƴaƴan nata kusan duk kamanninta su ka kwaso, Amal ce ma wadda ake cewa kamannin Baba da Annen ta haɗa, ba ta wani kama da Annen…dukkanninsu Kyawawa ne tubarkallah masu shiga rai gashi Matan tun su na Yara za ka fahimci ƙirar jikinsu mai kyau ce! Wanda hakan ya sake sanyawa Anne ta ɗauki wani kalar masifaffen buri ta ɗaura a kan ƴaƴannata Matan sannan ta ke sake godewa Allah da ya bata su…

Ba ita kaɗai ba hatta Kaka Nura idan ya kalli
Yaran wani sanyi ya ke ji dan ya san tabbas sun tara jari, musamman ma 'Amal'
Wadda idanuwanta ma kaɗai abun kallo da mamaki ne, ga ta da shiga rai kwarai da gaske.
Da ikon Allah tun daga kan Amir har zuwa kan Amal Yarane masu tsantsar kunya, nutsuwa, hankali, kawaici, biyayya, kamun Kai da son karatun AlQur’ani, ga tsoron Allah da kiyaye dokokin Allah dan tun su na ƙananu muddin Adda ta ce musu Abu babu kyau Allah ba ya so to in sha Allahu sun barshi kenan har gaban abada….ga su da mugun haɗin kai kuma sun shaƙu kwarai da gaske da juna musamman Amal da Afra dan in Amal ba ta da lafiya Afra kwana ta ke yi ta na kuka abinci kuwa ta ƙaurace masa kenan, abun hannu kuwa ko wanne iri ne Afra ta kan haƙura ta bawa Amal haka Amir da Aliya suma basa son abunda zai taɓa waninsu sannan kullum burinsu su dadaɗawa juna rai.

Wata tarbiyyar ba sai Baba da Adda sun koya musu ba kawai gani za a yi su na yi, dan in banda uban ashar, batsa da hayagaga ba abunda su ke ji daga Anne, Yadikko da Kaka Nura, dan Yadikko sai dai a ce da sauƙi kawai Likitoci dai sun ce ta warke amma halaiyyarta da wasu abubuwan da ta ke yi har gara ace ta yi haukar ma ya fi sauƙi, ga shi wani kalar masifaffen tsoron Anne ta ke yi ba ta laifi a idanunta......


Ganin Yaran su na da son karatun AlQur’ani ya sanya Baba ya ke yin wuff ya saka su a islamiyya tun su na shekara bibbiyu dan ba ya ma son zamansu da Anne dama, dama itanma kuma in ta Haifa Yaro shan nono wanda ya ke yi iyaka na wata tara shima a daddafe ne kawai ya ke Haɗata da su a cewarta ba za ta bari su yi daɗe su na sha ba haka kurum ta je su tsinka mata halittun ƙirjinta...
Wankansu, cinsu, shiryawarsu, Assighnment da dai komai nasu duk Adda ce!
Shiyasa su ka yi wata kalar shaƙuwa ta ban mamaki ita da Amal wadda ta fi ƙulafucin Addan tun ta na Yarinya kuma har ga Allah Yarinyar tun ta na ƙarama ba ta son Anne kawai ita matar ba ta yi mata ba hasalima tsoro ta ke bata, shiyasa kwata-kwata ba su wani shaƙu ba gashi ita kuma Annen duk ta fi ji da ita! Ba wai so ba dan ita ƴaƴan ma gaba ɗayansu kawai dan ta san za su yi mata rana ne ya sa ta ke alfahari da su, kawai ta fi ji da ita ne saboda duk ta fi ragowar Yaran nata kyau da shiga rai, dan haka ta na da tabbacin sai ta fi morarta.
Shekarunta biyu itama aka saka ta a islamiyya dan haka shirun sai ya yiwa Adda yawa.. gashi wani ikon Allah sam Adda ta tsani shiga cikin mutane kamar wata mai aljanu ko ƴan Unguwar tun ana zuwa mata har an daina
wasu dai sun ce kafiya ce Anne ta yi mata, wasu kuma sun ce Aljanin jikinta ne ya kafeta yayinda ƴan boko su ka ce depression ne da ita.
Yadikko ta na fita zuwa islamiyya a bayan layinsu Anne kuwa kullum ba ta gida
Baba shi kuma Yaron wani Babban shago ne a nan bayansu kullum ba ya gida cin abinci kawai ke kawosa wani lokacin in ya rufe ya taho sallah, shiyasa duk sai ta zama lonely, ta so ta haɗa kuɗin da kanta itama ta samu ta shiga islamiyyar dan tausayin Baba ta ke ji ba ta son tambayar sa kuɗi amma sai ta gagara haɗawa...
Sana’a kuwa ko wacce in ta fara taɓarɓarewa ta ke yi, ga shi daɗin daɗawa ma ta na jin tsoron shiga makarantar saboda kar su dinga abun kunya ita da Yadikko a gaban mutane....
Islamiyyar nesa kuwa itama ta san ba zata samu kuɗin motar zuwa da dawowa ba.


Zaman shiru, gori, kaɗaici da wulaƙancin Anne da Yadikko ne su ka sanya Adda ta yi adopting Abbakar Sadik (Abba)…
A bakin Titi ta ganshi ya na kuka lokacin babba da shi, ba za dai a ce masa saurayi ba amma ya kawo ƙarfi shiyasa abun ya bata mamaki dan shekarunshi sun kai kusan goma sha huɗu...
Ta na ganin Yaron ta ji ya shiga ranta matuƙa sannan ya yi masifar bata tausayi dan haka ta ce mishi 'ya zo su je ta bashi abinci' saboda ta na yi masa magana tashi ɗaya ya ce mata 'yunwa ya ke ji'.

Tun a day 1 da Anne ta ga Abba ta ji ta tsani Yaron!
Ba dan komai ba sai dan yadda ya ke kacha-kacha kayansa duk a yage sannan uban abinci da aka tula masa ya zauna ya narka a gabanta Mijinta ne ya siyawa Addan(dan Adda ita ke yin girkin gidan gaba ɗaya) dan haka ta yi ta azalzalar Adda ya yi ya gama ta sallamesa saboda haka nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login