Showing 69001 words to 72000 words out of 100561 words

Chapter 24 - BAKAR TUKUNYA hausa novel

07 Feb 2026

464

gaisa tukunna ta shiga zaiyyano mata komai abunda ya faru sannan ta ɗaura da cewa “Abban shima yana chan ɗaki ya ma ƙi ya buɗe ƙofar…”
Ta ƙarashe maganr cikin sanyin murya ta na mai yin ƙasa da kanta..

Shiruu itama Afran ta yi kafin kuma kawai ta yi hugging Amal zuciyarta na ƙuna, tabbas mugayen halayen Anne wasu yanzun ne ake launching nasu….”da na sani ban gaya mata batun aurena da Ya Isma’il ba, Ya Allah kar ka bata ikon yin komai game da hakan…”
Afra ta aiyyana hakan a cikin ranta
Dan tabbas hakan da Annen ta aikata a su Amal ya sake tabbatar mata she cannot be trusted kuma za ta iya cutar kowa ta baƙanta ran kowa domin zallar farin cikinta.

Kasa gayawa su Adda ta sanarwa Anne batun auren ta yi
Dan ta san wani sabon ɓacin ran za ta janyo musu kuma ba iya controlling Annen za su yi ba dan haka ta zaɓi ta mayar da hankali wajen kwantar musu da hankali tare da rarrashinsu, Anne kuma ta zaɓi ta durfafi addu’a game da lamarinta..


Tabbas Afra ta tabbata Yarinya mai hankali da kuma kamala dan bata barsu da ƙunci ba sai da ta yi iyaka bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta sanyasu nishaɗi da walwala.

Adda ta kan ce Afra ba rainonta bace ba dan haka dukkan halaiyyar da aka gani a wajenta baiwarta ce…
Afra ta sha wahala sosai dan Yadikko da Anne ba su bata kulawar da ta kamata ba gashi ita ba ta kusa a lokacin, Baba da Ya Amir za a ce su ka yi rainonta amma gashi ita ɗin ta tashi da son mutane da kulawa da gudun ɓacin ran kowa.
Ita kanta Amal ta san Afra blessing ce a garesu, da Ubangiji ya zana
musu ƙaddarar Baƙar Tukunya sai kuma ya sanyo musu Afra cikin familyn nasu ta zamto tamkar shield wani zubin kuma magani ga dukkan baƙin ciki da duk wani ƙunci na rayuwarsu.
…….
Misalin ƙarfe bakwai da mintina hamsin ta fito daga cikin gidan nasu ta na ta sauri dan ba ta so sam sam ta yi lattti a makarantar daren da ta shiryama zuwa.

Sai da ta karya kwanar makarantar tukunna ta ɗan jaa ta tsaya sannan lissafinta ya bata kamar fa tun ɗazu ta ji ana binta a baya, wanda saurin da ta ke yi da kuma hankalinta wanda gaba ɗaya ya yi ga isa makarantar ya gusar mata da lissafin hakan.
Sai da ta tsaya tukunna Allah ya bata ikon shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren Ya Isma’il wanda ko a ina ne sannnan ko a wanne hali in har ta ji to sai ta shaida shi.

A hankali Afra ta juya, ba tare da ta yarda ta kalli inda ta ke da tabbacin ya na tsaye a wajen ba ta na ɗan murmushi dan ta na juyawar ta fahimci ashe ma yana gab da ita ne sosai.

Tsaye ya ke sanye da jeans blue ya ɗaura jallabiya fara ƙal a kai, wadda ta taimaka wajen sake haska farar fatarshi.
Fari ne sosai Ya Isma’il sannan dogo sosai kuma ya na da faɗin ƙashi sai dai bai cika ƙiba ba dan kai tsaye za ka sakoshi sahun sirara. A fuska kuwa kai tsaye za ka kira shi da kyakkyawan gaske, ajin farko.

Sai da ya yi folding hannuwansa a kan ƙirjinsa tukunna ya ɗan rankwafa yanayinsa na nuna tsantsar girmamawa da shauƙi, ya ce “Barka da war haka sarauniyar duk Matan Duniya! Tauraruwa kuma hasken zuciyar Isma’il”

Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING*
Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING*
Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139*

Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudin ku tested and trusted.

Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu....
location:Kano
Delivery:NationWide.
kar ku bari a baku labari, sai kunzo🙏
SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA

BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*

HUMAIRAH BULAMA

Yota011

*28*


Murmushi Afra ta yi sannan ta saka tafukan hannayenta ta kare fuskarta da su, kafin a hankali ta ce “ina wuni Ya Isma’il”
Still ta na murmushin da ya ke samo asali daga tsantsar farin cikin da zuciyarta ta ke a ciki.

“Alhamdulillah Abar ƙauna, ya al’amura?”
Ya yi mata tambayar idanunsa ƙurr a kanta yana mai ji kamar ya haɗiyeta tsabar yadda tsantsar ƙaunarta ta ke addabar zuciyarsa.

“Alhamdulillah”
Ta ce har yanzun ba ta cire hannunta gaba ɗaya ba dan ta soma diriricewa daga kallon da ya ke yi mata…

Kamar wani ɗan ƙaramin Yaro haka nan ya ɗan turo Bakinsa gaba sannan ya yi kalar tausayi kafin ya ce “ki cire hannun mana, i want to see you fa.”
Ya ƙarashe maganar kamar mai shirin fashe mata da kuka.

Itanma cikin tsantsar shagwaɓar da ta dame tasa ta shanye ta ce “to Ya Isma’il ka fara daina kallona mana”
Ta yi maganar ba tare da intention na dasa masa wani abun ba amma shi gogan a take ya ji wani yanayi na musamman yana shirin kwance masa lissafinsa.
Shiruuu, ya yi kafin ya ɗan sunkuyar da kansa ƙasa ya ɗan cije lips nashi sannan ya ɗago ya kalleta a hankali ya ce “hmm” kawai, tukunna ya gitta ta ya wuce cikin sauƙe ajiyar zuciya ya ce “na daina my one and only….” Ya na ɗan murmushi ƙasa -ƙasa.
Murmushin itama ta yi sanna ta zare hannunta daga face ɗin nata completely kafin ta juya a hankali su ka jera su na tafiya, in ka kallesu gwanin burgewa…
Sai da su ka ɗan yi nisa tukunna a hankali ta ce “ya su Mama?”

“Su na ƙalau Alhamdulillah, ta ce in gaida ke.”
Murmushi ta yi cikin tsananin ƙaunar matar ta ce “Ayya, na gode ina amsawa”

Dai-dai nan su ka ƙaraso bakin makarantar dan haka ya sauƙe numfashi ya na kallonta da mamakin kunya irin ta Afra, dan har yanzun kanta ƙasa ya ke…A yadda su ka daɗe tare su ka shaƙu da juna ya kamata a ce ba ta kunyarsa har haka sosai, amma kullum ita dai kunya ko iya haɗa ido da shi fa ba ta yi har yanzun sai dai idanunsu su haɗe waje ɗaya by mistake kuma shima nan da nan ta ke janyewa.
Ya na wannan lissafin ya ga ta ɗan ɗago ta saci kallonsa sai kuma ta yi saurin sunkuyar da kanta ƙasa sakomakon haɗa idanu da shi da su ka yi ya kafeta ƙurr da ido ya na ta murmushi….
Sai da ya sauƙe ajiyar zuciya tukunna ya ce “Allah ya nuna min ranar da za mu yi gasar kallon kallo ni da ke…”

Murmushi ta yi yanzun ma sannan ta ce “Ya Isma’il bara in shiga kar in makara, na gode”
A hankali.
Shima a hankali kamar yadda ta yi ya ce “ban ƙoshi da ganinki ba.”
Irin kalar tausayi ɗinnan.

Murmushi ta yi kawai, ta kasa cewa komai.

Kamar masu tallar auduga haka suka wanzu a wajen daga shi har ita kafin chaan ya ce “Ɗazu Baba ya dawo daga Umara..”
Cikin nutsuwa ta ce “Ma sha Allah, Rabbi ya sa maƙabuliya ce”
A hankali ya ce “Ameen, sannan ya ɗaura da cewa “good news…ya ce wata biyu ya yi tsaho, wai a mayar sati biyu tunda an kammala shirye-shiryen komai…”
Da sauri ta ɗago a ɗan tsorace, sai kuma ta maida kanta ƙasa yanzun ma su na haɗa ido kafin ta ce “Ya Isma’il kuma na ga kamar ka na murna.”
Ɗan zaro idanu waje ya yi kafin ya ce “murna kai! Ji na ke yi kamar in suma tsabar daɗi, Allah Allah dama nake in aureki, na matsu sos…”
Sai kuma ya yi tsit bai ƙarasa ba ya fara dariya saboda yadda ta yi saurin rufe idanunta ta juya masa baya.

Juyin duniya Afra ta ƙi juyowa gaba ɗaya kunya ta gigitata har kamar ta na shirin fashewa da kuka,
ita dai gaba ɗaya ya Isma’il ya soma sauyawa tunda aka saka ranar aurensu, wata maganar in ya yi sai ta ji kamar ba shi ba wallahi…

Ba dan ya so ba haka ya haƙura ya kyaleta kawai, saboda ta yi latti sannan a yadda maganarsa ta kiɗimata ya san ba za ta sake da shi yanzun ba, dan haka ya juya ya bar wajen bayan ya yi mata adduar samun ilimi mai amfani.

Sai da ta tabbata ya bar wajen tukunna ta juya ta shige ciki yayinda shi kuma ya nemi waje a wani dandamali ya zauna kawai ya na ta murmushi…
Har gaban abada ya na godiya ga Ubangiji da ya bashi Afra kuma yanzun da yardarsa zai mallaka masa ita a matsayin matar aurensa…
Shi dai a gaskiya ya fi kowa sa’a tabbas! Dan duk wani qualities da ake buƙata a mace to Afra ta na da shi, ga shi dai Anne ce ta haifeta amma kamar wadda ta taso ta girma ta yi rayuwarta komai a gaban jiga jigan manyan Malamai bayin Allah…..
A hankali ya ɗaga kansa sama ya na kallon yadda taurari suka yi wa sararin samaniya ado gwanin ban sha’awa cikin sauƙe wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ya ce “Alhamdulillah”
……..
Bashi da wani abunda zai yi a gida ko wani wajen dan haka bai bar wajen ba kamar yadda ya saba in ya rakota ya je ya dawo daff da tashinsu ya kaita har ƙofar gida, wannan karon zamam dirshen ya yi a wajen ya na ta faman tunane-tunane da lissafe-lissafen auren da rayuwarsu har zuwa lokacin da aka tashi daga islamiyyar daren.


Dama Afra sai faman Addu’a ta ke yi Allah ya sa ya tafi, sai dai kuma ta na fitowa shi ta fara hanga dan haka ta sauƙe ajiyar zuciya kawai kunyar ɗazu ta na sake dawo
Mata sabuwa.

Har ƙofar gida ya rakata kamar kullum, sai dai bai sake yi mata zancen bikin ko aurensu ba dukda yadda ya ke ta so ya sake tsokanarta amma da ya fahimci a ɗarare take da shi sai kawai ya rabu da ita saboda sam ba ya so ya ganta uncomfortable ko cikin damuwa sam-sam, walwalarta ya ke biɗa kullum..
Sai da su ka zo
rabuwa tukunna ya ce mata “ta ji komai daga wajen Baba in ya so sai su yi magana gobe, saboda ɗazun ya baro Baba Babansa da Uncle ɗinsa su na tsare-tsare…””
Daga haka suka rabu cikin tsantsar so da ƙaunar juna.

Afra ta na shigewa mota ta yi fakin a ƙofar gidan, Isma’il
bai kai ga barin wajen ba dan haka ya waigo ya tsaya dan ga dukkan alamu gidan aka zo…
Da ikon Allah sai ga Anne ta fito daga cikin motar wadda tun fitar ɗazun nan da ta yi sai yanzun ne Allah ya bata ikon dawowa.
Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokare zuciyar Isma’il! Tabbas da ace Anne shi ta haifa ba Afra ba zai iya saka mata shinkafar ɓera ta ci in zuciya ta tunzuroshi wata rana…
Kayan jikinta sun fi komai ɓata masa rai, sai kuma motar mai uban tint wadda daga inda ya ke tsaye ya na iya jiyo tashin kiɗa a lokacin da ta buɗe ta, ta fito daga cikinta….

Bai san lokacin da ya yi tsaki ba, ya juya kawai, ya na juyawa su ka yi ido biyu da Ya Amir shima ya kafe motar wadda ta ke yin reverse da shirim barin layin ido, idanunsa sun kaɗa sun yi wani kalar jaaa.
“Assalam alaikom” kawai ya ce da Isma’il ɗin sai kuma ya kasa ci gaba da tsayuwa a wajen dan haka fiiii!!! Kamar wanda iska ta kwasa ya yi wuff!! Ya bar wajen ya karya kwana.

Shiruu Isma’il ya yi ya lumshe kyawawan idanuwansa kafin chaan ya sauƙe wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya tukunna ya buɗe idanunsa, ya bar wajen, jikinsa a mugun mace.
……..
Direct gidansu ya nufa, wanda a kaff layin gidan nasu kusan shi za a cewa Babba, gate ne fari sai dai ya ji jiki, kana shige gate ɗin za ka tarar da tsakar gida tafkeke da three bedrooms flat, sai wani boys quaters a jikin gate opposite ɗakin mai gadi wanda aka mayar ɗakin tara shirgi saboda babu mai gadin.

Mota ce kwalli
ɗaya a gidan fake a chan gefe, tsakar gidan kuwa a ƙalla zai kai a gina irin gidan sau huɗu a cikinsa tsabar girmansa….
Har Isma’il ya yi hanyar boys quaters inda ya ke da zama ya ji wayarsa ta ɗau ƙara, yana ɗagota ya ga sunan ‘Maama’ ya baiyyana ɓaro-ɓaro a kan screen ɗin wayar…
Ya na ɗauka suka gaisa cikin girmamawa sannan ta ce “kai ne ka shigo yanzu?”
Ya ce mata “eh”
Kai tsaye ta ce masa “zo”
Daga haka ta kashe wayar.


Ya na isa bakin entrance na gidan ya ɗaga hannunsa da niyyar yin knocking main door ɗin ya ji an murza key within seconds aka buɗe ƙofar ƙanwarsa ta baiyyana a gabansa.
Su biyu kacal dama aka haifa a gidan, cikin girmamawa ta gaidashi ya amsa daga nan ta wuce gaba ya bita a baya zuwa ɗakin Mahaifiyar tasu.


Sai da su ka yi knocking ta basu izinin shiga tukunna cikin tsantsar nutsuwa duk su biyun su ka shiga bakunansu ɗauke da sallama.

Zaune take akan darduma sanye cikin farin hijabi mai kwalliyar cin bakin lace, hannun damanta riƙe da carbi mai kyau da sheƙi ta na lazimi ta na jaa a hankali.
Ko da su ka shigo ba ta amsa ba sai da ta kai inda take so lokacin duk sun nemi guri sun zazzauna tukunna ta yi addu’a duk su ukun su ka shafa a tare.

Cikin tsantsar girmamawa ya ɗan rissina tukunna ya ce “Ina wuni Mama..”
Ya sake gaida ita.
A ransa ya na addu’ar ‘Allah ya sa dai lafiya’ Dan ɗazu kafin ya fita har ya yi mata sai da safe ta amsa, yanzu kuma gashi ta kirashi sannan da ya kalli fuskarta kai tsaye ya hango damuwa.

“Alhamdulillah”
Ta ce da shi, wanda hakan ya katse masa lissafin da ya ke yi, ya sake maida hankalinsa kacokam a kanta.
A hankali ta sauƙe numfashi ba tare da ɓata lokaci ba ta ɗauko maganar da ta sanya ta kirashi ɗin.

“Isma’il, na san wacece Afra da tarihinta da tarihin iyayenta da komai nata, wanda na san ka san cewa ba don so da ƙaunar da muke da tabbacin kuna yiwa juna ba da kuma nutsuwa da hankalin ita Yarinyar tabbas da ko da wasa ba za mu taɓa yarda mu haɗa alaka da ita ba…”
Sai da ta sauƙe numfashi tukunna ta ɗaura da cewa “dalilan nan guda biyu da na baka muddin ɗaya ya samu tangarɗa to ɗayan ma zai iya samun tangarɗa. Dan duk son da ka ke yi mata ba zan yi farin ciki in goyi bayan aura maka ita ba muddin na ga ɗabiunta suna sauƙa daga kan layi, haka zalika kuma duk nutsuwarta zan so ace ka aureta ka na mai tsnanin ƙaunarta domin farin cikinka.

Ba zan yi maka dole ba sannan i’m not trying to make your decision for you amma ina mai baka shawarar da ka tsaurara bincike na gaske! Sannan wannan auren da Mahaifinka ya ke gaggawar a ɗaura inaga ka ɗan yi masa magana a ɗan rage saurin….

Afra Yarinya ce mai hankali nutsuwa da tarbiyya amma fa ba a chanjawa tuwo suna wanda abunda na ji yau ya farkar da ni na fara lissafin abunda duk ban yi a baya ba…
Isma’il no matter what nonon Nuratu Afra ta sha kuma jininta ke yawo cikin jijiyoyin da su ke a jikinta sannan kowa ya san akwai jinin zina a jikinsu dan ubansu sai da aka kamashi da Uwar tukunna…”

Da mugun sauri Isma’il ya ce “Maaamaaa”
Ya na mai runtse idanuwansa da masifar ƙarfi.

Shiruu ta yi ta na kallonsa har sai da ya ɗan dawo dai-dai dan kanshi ya buɗe idanun nasa waenda har sun kaɗa sun yi jaaa sosai sannan ya ce “Mama, Afra Musulma ce (ƴar uwar ce, ya kamata ko dan haka a yi mata da sauƙi) kuma waennan lapse ɗin nata bai kamata ace sun rufe miki idanu daga ganin tsantsar good and golden values ɗinta ba…”
Cikin tarar numfashinsa ta ce “tabbas hakan ya sanya na ke goyon bayanka ɗari bisa ɗari a baya. Sai dai tunda aka sanar mini an ganta a hotel yau! Ita da wannan mutumin Samuel gaba ɗaya na gagara nutsuwa hankalina ya tashi sannan ba zan ɓoye maka ba har ga Allah na fara kokwanto.”

Ɗiff!!! Haka Isma’il ya ɗauke wuta, kafin kanshi tsaye ya ce “Mama sharri ne, zan iya rantse miki cewa ƙarya ne ake yi mata.”

Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING*
Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING*
Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139*

Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudin ku tested and trusted.

Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu....
location:Kano
Delivery:NationWide.
kar ku bari a baku labari, sai kun zo🙏
SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA

BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*

HUMAIRAH BULAMA

Yota011

*29*

Ɗiff!!! Haka Isma’il ya ɗauke wuta, kafin kanshi tsaye ya ce “Mama sharri ne…zan iya rantse miki cewa ƙarya ce ake yi mata.”

Cikin tarar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login