Showing 93001 words to 96000 words out of 100561 words
na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudinku tested and trusted.
Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu....
location:Kano
Delivery:NationWide.
kar ku bari a baku labari, sai kun zo🙏
SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA
BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:25 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*
*page 35*
Anne yau wuni ta yi a ɗaki, mirsisi kuma ko haɗa kayanta ba ta da niyyar yi kamar yadda Baba ya buƙata, haka nan ta zaɓi ta zauna a nan ɗakin nata ta yi yadda Yadikko ta ce…dan haka ta wanzu a ɗakin zaune abunta tana ta faman saƙa da warwara…
Tabbas sai ta saka Isma’il kuka wallahi, saboda yana daga cikin mutanen da su ka ɗaga mata hankali a yau su ka hanata walwala…
Tana cikin wannan lissafin, kamar
daga sama kawai ta soma jiyo sallamar Mama (Mahaifiyar Isma’il).
Kusan a tare su ka ji sallamar ita da Afra wadda ta ke zaune ta na karatu.
Ras!! Gabanta ya yanke ya faɗi kafin ta miƙe tsaye da sauri sai kuma ta jaa ta tsaya dan bayan ta tashin kuma sai ta gagara fita.
Da mugunn kyar ta tattaro courage ta nufi waje jikinta ya na karkarwa…
Kusan a tare su ka fito ita da Anne wadda ta nemo duk wata baiwar kissa da ke a gareta ta yi activating nata tukunna ta fito dan ko sunan Matar itama ba ta son ji kamar yadda ta tsani ɗanta! Mutame kamar mayu! Sun nace sai an basu Afra duk abubuwan da ta ke yi sai warwarewa su ke hakanan komai ya ƙi yin tasiri gaba ɗaya sun uzzurawa rayuwarta…
Ta na fitowa Afra ta fara gani ta ɗan durƙusa ta na da shirin gaida Mama, aikuwa da sauri Anne ta ware murya cike da hayagaga ta shiga gaban Mama ta tsaya ta na mai cewa “lale maraba da Mama, ma sha Allah Azahar Mai Albarka, Mama da kanki haka! Ai da kin aiko kawai da zuwa zan yi, bismillah shigo ciki mana”
Gaba ɗaya ta babbake ta yi kane-kane ta hanata ganin Afra ballanta ta ji gaisuwar tata…da ikon Allah kuma Mama ba ta ga Afran ba dan hankalinta bai kai wajen da ta ke ba ta dai ji kamar murya ta na gaisheta amma sai Anne ta janye mata hankali su ka yi ciki.
Amal bacci take yi a lokacin amma Adda itama ta ji sallamar Matar sai dai ba ta fito ba gudun kar su yi abun kunya a gaban suruka tunda ba shiri su ke yi da Anne wadda ta jiyota tare da Maman ba, haka Ya Abba da Ya Amir suma duk sun ji dan haka su ka hau addu’ar Allah ya sa alkhairi ne ya kawota, duba da yadda Matar ko fita daga gidanta ma bata cika yi ba ballanta zuwa gidan surukai haka nan kasafai.
Har darduma Anne ta shimfiɗa mata ta zauna a kai, Annen ta na ta rawar kai da hayagaga ita ala dole sai
Mama da Afra sun tabbatar ba ta da wata matsala da Isma’il, auren da danginsa.
A zuciyarta kuma addu’a take yi Allah ya sa zuwa ta yi a kan batun zuwa hotel, Allah ya sa matsala ce ta kutso kai akan batun auren ko kuma ma ace fasawa aka yi gaba ɗaya…
Da mugun kyar Mama ta ke iya haɗiyar yawu a cikin ɗakin, dan tun shekaran jiya da Baba ya hana su Afra gyara ɗakin ya ce Anne ta gyara da kanta bai ga tsintsiya ba, gashi ta tara uban wandunanta na ciki ta danna a ƙasan pillow gaba ɗaya tsaminsu ya cika ɗakin…sannan da ita da gashin kanta da ko wanne lungu na jikinta har ma da bakinta komai kawai tashi yake yi dan yau ba ta fita ba ballanta a yi kwaskwarima a fesa turaruka a samu abun ya ragu.
“Bara a kawo miki ruwa”
Cewar Anne wadda ke a zaune ƙyam ta na jira Mama ta ce a barshi..
“Laa kar ki damu ba komai”
Mama ta ce, tana ɗan murmushi sannan ta ɗaura da cewa “Barka da war haka, ya gida ya Yara?.”
“Alhamdulillah, ya kwana biyu ya kuma shirye-shiryenmu, sai ku ka ji mazan sun yanke lokaci ƙanƙani kwatsam!! Ni ban ma san ta ina zan fara ba duk na rikice wallahi, Allah dai ya nuna mana auren nan da rai da lafiya, ba ki ji farin cikin da na yi ba wallahi, a samu ta tafi a je a ci soyayyar da aka daɗe ana yiwa tanadi….”
A hankali Mama ta ɗan yi gyaran murya, wanda hakan ya sanya Anne yin shiru, ta na bin Mama da wani kallo wanda a zahiri ya ke kama da murmushi da kulawa a baɗini kuwa tsantsar tsana ce! Haka kurum ta tsani Matar saboda nacin su, Allah dai ya sa ta ji good news daga gareta a yau, a yanzunnan.
Ta na cikin wannan addu’ar ta ji sautin muryar Mama ta na cewa “am, dama na zo ne saboda akwai maganar da na ke so mu yi da ke ta fahimta…”
Sai da ta ɗan yi jimm tukunna ta ɗaura da cewa “In Allah ya kaimu nan da kwanaki 6 za a ɗaurawa Afra da Isma’il aure in sha Allah.”
A cikin ranta Anne ta ce “Mayya”
Sannan duk ƙoƙorinta sai da murmushin kan fuskarta ya baje a take.
Mama kam ba ta ma lura ba ta ɗaura da cewa “dan haka na ke ganin da mu da ku duk mun zama ɗaya, Afra ta riga ta zama ƴata dama ita kam tun ba yau ba…
In wani abun ya sameta ko sunanta tabbas kamar mu ya samu.
Shiyasa na zo in ji baasin shin me ya kaita hotel wajen Samuel?
Sannan dan Allah duk rintsi kar ta sake zuwa ko kuma ta yi wani abun da zai taɓa mutunci ko darajarta kafin Allah ya sa a ɗaura auren a samu su wuce chan Kaduna abunsu, ta fuskanci karatu da aurenta.”
Tsabar takaici da mugun kyar Anne ta iya haɗiye ƙululun abunda ya tokare mata maƙoshi sannan ta jaa numfashi ta sauƙe ta fuskanci Mama da kyau tukunna ta iya cewa “eh to Mama kin san Afra har yanzu Yarinya ce ƙarama, dan haka waennan abubuwa na aure kayan ɗaki kyale-kyle dole za su burge ta.
Akwai wani abun kwalliyar ɗaki da ta nuna tana so ni kuma na ce tunda kun ce akwai komai a gidan kawai ta barshi, dan tun kafin Alhaji ya faɗi cewa a Kaduna za ta zauna dama chan shi Isma’il ɗin ya gaya mana komai….
To ita Afra ta nace akan ta na son abun gaskiya kuma nima da na lissafa na ga ba fa za mu kaita da komai nata ba, gashi auren fari shiyasa ta bani tausayi dan haka da Samuel ya ce ta je ya bata gudummawa sai kawai na ce ta je ɗin saboda kaff gidan nan wallahi duk ta cikinmu mu ke ba mu da yadda za mu yi ballanta mu samu mu siya mata
kinga hatta sanwar rana ma ba a ɗaura ba yau kam.
Amma wallahi ni ban san hotel za su je ba, itama kuma Afran haka, kawai dai laifinta guda da ta fita ta kira shi ta ji ya ce mata ta je hotel da sai ta fasa zuwa..
Tunda kowa ya shaida soyayya ce yake yi mata to kinga kenan bai
kamata a ganta a hotel tare da shi ba.
Kuma dai ta dawo ta na ta ƙunci da na tambaya ta ce mini tunda ta je bashi da wani burin da ya wuce ya taɓa jikinta, to dai ban tsananta bincike ba gaskiya ta na bada kuɗin na fita na je na kai deposit ɗin abunda tace ta na so ɗin dan kuɗaɗen ba su cika ba har yanzu…
Kuma kinga an ce kar a tsananta bincike sosai ba daɗi shiyasa ban titsiyeta ba saboda na yarda da Afra ɗari bisa ɗari na san ba za ta taɓa yin wani shirmen ba.
Dan haka kema ki kwantar da hankalinki ba ta yi komai ba ni shaidarta ce ta na da tarbiyya da nutsuwa sosai kuma ta na son Isma’il, sannan na yi miki alƙawarin zan kafeta a gidan nan ba inda za ta sake fita daga yau har Islamiyya, in kin ga ƙafarta a waje to in sha Allahu an zo ɗaukarta ne za a kaita gidanta na Kaduna.”
Wani kalar juyawa kan Mama ya soma yi, dama gata matar ta na fama da hawan jini ya yi
mata katutu…
A ranta ta ce “anya kuwa….”
A hankali ta ke jan numfashi ta na sauƙewa, saboda tsabar yadda kanta ya sara tun lokacin da aka ambato maganar ‘Samuel yanata so ya taɓa jikin Afra’….Salati ta shiga yi ta na ta ƙoƙarin korar sheɗan ɗin da ya dage wajen buga mata gangarsa hankalinta in ya kai dubu to ya tashi, gashi Anne sai zuba ta ke yi ta ƙi shiru ta na ta bata labarin kalar nacin da Samuel ya dinga yi akan Afra wanda duk ba su san da wasu ba sai yanzu ne take ji.
Ba dan ta so ba ko dan ta gama abunda ya kawota ba dan ta so ta yi mata jaje sannan ta bata baki game da abunda ya faru da ita ake ta yamiɗiɗi a Unguwa, amma sai kawai ta miƙe ta rabu da ita.
A hankali murya cike da damuwa ta ce “na barki lafiya…bara in je gida akwai shirye-shiryen da na bari. Na gode”
Jinjina kai Anne ta yi ta na wani murmushi dan yadda jikin Matar ya ke rawa kaɗai ya isa ya tabbatar mata saƙonta ya kai.
A ranta ta ce “wannan hanyar ma da alamun za ta ɓille, ba ko sisina amma dukda haka gida biyu zan yi, bazan tsaya a dabara ɗaya ba”, sanna a hankali hankalinta kwance a fili ta ce”Allah ya bamu alkhairi…”
Daga haka Mama ta juya ta fita.
Wanda fitowar tata ya sa Afra wadda ta ke ta leƙe ta kasa tsaye ta kasa zaune ta yi saurin komawa cikin ɗakin nasu ta saki labule. Tunda su ka shige ɗaki ta ke fargaba da fatan Allah ya sa ba wani negative abu ya kawo Mama ba, dan dramar da aka yi da safiyar yau ma a gidan ta sanya duk ta ji ta muzanta kuma ta na ganin itanma(dramar) za ta kawo gudummawar makamashi a rura wutar kashe batun aurenta da Isma’il tabbas…
Da farko Anne ba za ta yi mata rakiya ba sai kuma kamar wadda ta tuno wani abun ta miƙe fit ta biyota a baya ta na cewa “sai haƙuri, Yarinya ce dai har yanzu ba za ta kuma ba in sha Allahu…”
Ita dai Mama “Ameen”
Kawai ta ce dan hayagagar Matar juya mata kai ta ke yi wallahi..
A haka ta fice ita kuma ta koma ɗaki ta zauna ta yi shiruu ta na kitsa ta yadda za ta soma.
Tunda su ka fito Afra ta sha jinin jikinta, hankalinta bai kammala tashi ba sai da ta ji abunda Anne ke cewa da ta fito. Ko da Anne ta koma ɗaki ta kusa mintuna uku tukunna da kyar Afra ta samu ta iya fitowa baiwar Allah ƙafafunta har karkarwa su ke yi a haka ta shiga ɗakin Annen wadda tunda ta ji motsin mutum ya na tahowa ta matso hawaye ta shiga zubda su bilhaƙƙi da gaskiya.
“Assalam alaikom”
Siririyar muryar Afra ta iso cikin ɗakin.
Da sauri Anne ta kauda kai sannan ta shiga goge hawayenta sosai irin ba ta so Afra ta gani ɗinnan.
Already ta riga ta gani wanda hakan ya sanya hankalinta ya ƙarasa tashi kwarai tsoronta ya hauhawa a take ta sha jinin jikinta.
Da mugun kyar ta iya ƙarasawa kusa da Anne ta na zuwa ta durƙusa a gabanta ta dafa guiwowinta a hankali ta ce “Anne”
Ta yi maganar da kyar murya da ilahirin jikinta su na karkarwa, dan tunda ta gaida Mama ɗazun ta ƙi amsawa ta san tabbas ba alkhairi ne ya kawota gidan ba.
Still har yanzun goge hawayenta Anne ta ke yi, kafin cikin sheshsheƙar kuka da dasashshiyar murya ta ce “ikon Allah kinga wani kwaro ne ya faɗa mini cikin idona na gagara fidda shi sai ruwa idon ya ke min…”
Duk dauriyar Afra kasa ci gaba da riƙe kukan da ya taho mata ya ci ƙarfinta ta yi, ba ta san lokacin da ta rushe da kuka ba dan duk abunda zai saka Anne kuka tabbas ba ɗan ƙarami bane ba. Gashi dama da kunnenta ta ji ana bada haƙuri, shikenan ita kam ta san tata ta ƙare Allah ya sa ba wani sharrin aka ƙulla mata ba…
Ta aiyyana hakan a ranta a lokacin da ta ke rushewa da kukan, sannan ta ce “Anne ki gaya mini ko ma
menene, zan iya handling dan Allah kukan nan da ki ke yi ya na sake gigita ni ne.”
Miƙewa tsaye Anne ta yi, sannan ta wani juyawa Afra baya cikin sauƙe ajiyar zuciya ta ce “ki tashi ki fita, saboda ni ba kuka na ke yi ba, abu ne ya shiga cikin idanuna.”
A hankali Afra ta zagaya ta tsaya a gabanta ta na hawaye ta ce “Anne dan Allah ki gaya mini ko ma menene” ta haɗe hannuwanta guda biyu waje guda alamun roƙo.
Shiruuuu, Anne ta yi ta na kallonta kafin kuma chaan ta koma bakin katifar ta zauna, ta dunkule tafukan hannayenta biyu a waje guda ta saka a haɓarta sannan ta zuƙo iska ta busar cikin kafe waje guda da idanu ta sauƙe wata ƙaƙƙarfar Ajiyar zuciya kafin ta soma magaana idanunta har yanzu su na kallon waje guda”….
………….
Mama ta na shiga direct ɓangaren Ya Isma’il ta nufa abunda ba ta saba yi ba dan sam ba ta cika shiga ɗakinsa ba.
Ba ta tarar da kowa ba amma ta tarar da wayarsa a kan gado, banɗaki ma ƙofar a buɗe ta ke wanda hakan ya shaida mata ba ya ɓangaren nasa ne kwata-kwata kenan amma da wuya in ba ya cikin gidan tunda ga wayarsa nan.
Dan haka ta juya ta fita direct ta wuce cikin parlourn.
Ta na shiga ta tarar da shi ya na zaune ya na kallo ya na cin indomie, kallo ɗaya tak za ka yi masa ka fahimci gaba ɗaya hankalinsa ba ya a kan indomien har da ma kallon da ya ke yi kawai ya na kalla ne ya na zira indomie…..
Ko da ta kalleshi sosai sai ta ga kamar har ya ɗan rame sannan fuskarsa saman hanci da idanunsa sun yi jaa sosai abunka da farar fata.
A take tausayinsa ya lulluɓeta, ganin ya na shirin cin galaba a kanta yanzun ma ya sanya ta yi
saurin korar lissafin ta nufe shi gadan-gadan shi bai ma san ta shigo ba.
Da sauri ƙanwarsa wadda fitowarta daga ɗakinta yanzun kenan ta ƙaraso ta kamo hannunta ƙasa-ƙasa ta ce “Mama, ki zo dan Allah.”
Shiruuu ta yi kamar ba za ta kulata ba idanunta a kan Isma’il
wanda da ikon Allah har yanzu bai ma san ta shigo ba, sai kuma ta ce “tam, mu je”
Daga haka ta juya suka bar wajen.
Su na shiga cikin ɗakin matashiyar budurwar ta mayar da ƙofar ta rufeta sannan ƙasa-ƙasa ta ce “ammm Mama dama…”
Sai kuma ta yi shiru ta hau kame-kame.
“Dama me?”
Mama ta faɗa a ɗan zafafe, dan duk haƙurin Matar yadda kowa ya burkita mata lissafinta a yau ɗinnan ya sanya ta shaƙa sosai ta ke a fusace.
A hankali Matashiyar budurwar ta ce “na san, its not important kuma duk ɗinmu ba zargin Ya Afra mu ke yi ba, amma ƙishin-ƙishin mu ke ji a bakin wata a Islamiyyarmu wae Samuel ya na da ciwon HIV….”
Sai kuma ta yi shiruuu, kafin ta ce “a asibitin da ƴar ajin namu ta ke aiki aka fara masa test aka tabbatar, a nan ta gani, har rantsuwa ta yi min ɗazu da muka haɗu da ita a islamiyya da safe……”
Yadda gaban Mama ya yanke ya faɗi ya sanya sai da ta ɗan durƙusa sannan ta dafe ƙirjinta, da sauri Yarinyar ta saki salati sannan ta ɗan ruƙota ta na mai sakin salati tukunna ta ce “sannu Mama, menene?”
Yanayinta ya na nuna damuwa sosai.
“La ilaha illa anta subhanaka inni kunta minaz zalimin, lahaula wala quwwata illa billah…”
Mama ta ambato, kafin ta ɗago a hankali ta zubawa ƴar tata idanu kamar mai son gane wani abun a kan fuskarta kafin kuma kawai ta juya ta fita bayan ta ce “ba komai, ina zuwa”
Ga shegantaka da ake zargin akwai a gidan, ga shaye-shaye, ga zina ga ga ga….. Anya kuwa in bar Isma’il ya auri Afra ba ta cuci Yaron nan ba kuwa!.
Ta yiwa kanta tambayar ba tare da ta san waye zai bata amsa ba.
Still har yanzun ya na zaune ya na cin indomienshi wadda ya ke jin ɗacinta akan harshensa kamar panadol, kwata-kwata cokali huɗu ya yi amma ji ya ke kamar ya yi amanta. Tun safe bai ci komai ba da kyar yanzun ya samu zazzaɓin da ya yi masa rubdugu tun ɗaga lokacin da ya dawo daga wajen Afra ya ɗan sake shi shine ya shigo ya cewa ƙanwarsa ta dafa masa indomie wadda itanma shigowarta daga makarantar Islamiyya kenan.
“Isma’il!!”
Mama ta faɗa da ɗan ƙarfi dan karo na biyar kenan da ta ambaci sunanshi bai ma san ta na wajen ba.
Numfashi ya shaƙa da ɗan sauri sannan ya ɗago idanunsa da su ka yi wani kalar jaaa ya zuba mata….
Da mugun maamaki ya ke kallonta dan ƙanwarsa ta ce masa ba ta gidan, sam bai san yaushe har ta shigo ta tsaya a gabansa ba.
A hankali ya ce “Mama ina wuni…”
Muryarsa ta na karkarwa sosai very low…
Tausayi ya bata sosai dan haka ta koma gefensa ta zauna ba tare da ta yarda sun haɗa idanu ba saboda ta gama tsarawa kanta ba za ta bari tausayinsa da ta ke yi ya cutar da rayuwarsa ba…
Cikin nutsuwa sosai kanta tsaye ba tare da kwana-kwana ba ta ce “ka ɗauki Afra gobe ku je a yi mata gwajin ƙanjamau.”
Bai san lokacin da cokalin hannunsa ya faɗi a kan tiles ɗin da ke shimfiɗe a parlourn ba…
A hankali ya ce “Mama wanchan satin mu ka je mu ka yo fa,